19&20
by @nkds
❤️BA DARAJA!!!❤🔥
©® Nainarh KD♡
19–20
“Gafaranku dai masu gida...
Maganar da Mama Tsahare ta sako kai gidan tana yi ya katse, lokacin da k'ofar ta bugi goshinta domin shi Abbas da bai san da tahowarta ba yake k'ok'arin rufe gidan kuma ko zuwa lokacin da ta yi magana aikin gama ya gama.
“Subhanallahi, D'anladi yanzu ciremin kan zakayi wannan turo k'ofar da kayi na sako kai, ai badan Allah ya kare ba k'aramar illa zakayimin ba.”
Ta ci gaba da sababinta yayin da shi kuma ya bata hanya ta shige cikin gidan tana ci gaba da fad'in.
“Haka kurum da ranar Allah kazo zaka rufe gida sai kace wasu marasa gaskiya...”
Sai kuma ta yi shiru ganin su Saddiqa zube a rana hakan ya sa batama lura da Halima da Ruk'ayya take k'ok'arin ganin sun ba wa hamma iska ba.
“Kai D'anladi ka fa dinga jin tsoron Allah fa, yanzu tsakani da Allah mene ne har yaran nan suka aikata da zaka zubar da su anan yadda ake zabga uwar rana haka ka fa dena wannan bak'in halin naku da 'yan boko fa.”
Ganin ba zata saurara ba ya sa Abbas fad'in.
“Mama kiyi shiru mana. Sannu da zuwa ga wuri ki zauna.”
“Ba za'a zaunan ba, nace ba zan zaunan ba, wato na isheka da surutu ko ai gaskiya nake fad'a maka gwara dai ka dena wannan tsananin naku irin na 'yan boko, wai ma ina matan gidan ne suka barni ina ta zuba ni kad'ai tsakar gida?”
Ta k'are maganar tana juyawa domin tun ganin su Hauwa'u a zube da ta yi sai ta juya tana yi ma Abbas tsiya, hakan ya sa ta bawa su Halima baya sam bata lura da su ba, su kuma zuwan nata ne ya hana Ruk'ayya daga k'ok'arin tunkarar Halima da take, yayin da Halima take tsaye daga k'ofar d'akinta tana jira taga abin da Ruk'ayya zata yi.
“Ah ah lafiya kuwa?”
Mama Tsahare ta sake fad'a ganin yanayin kowannensu.
“Barka da zuwa ga wurin zama.”
Halima ta fad'a tana aje ma ta kujera.
“Ai ni kam ban ga ta zama ba tun da ban ji meke faruwa ba naga kun yi curko-curko haka ga wannan mijin naku sai wani shune fuska yake kamar manomin da yaga hadarin da ba na ruwa ba.”
Sai da Abbas ya duba su Saddiqa dake zube a rana har lokacin Sannan ya basu umarnin su tashi su wuce d'aki kafin fuska ba walwala ya mayar da dubansa ga Mama Tsahare.
“Mene ne ma bai faru ba, ai komai ma ya faru Mama domin Wad'an nan matan dai sun bani mamaki wallahi...”
“Kai ni in zaka fito fili kayi min bayani to kayi haba mana ka tsaya kana ta wani nok'e nok'e.”
Mama Tsahare ta katse shi cike da fad'a, yana wani kukkumbura fuska ya ce.
“Sata suka yi min.”
Mama Tsahare ta kama baki tana sallallami da tafa hannu.
“D'anladi sata fa?”
Shiru ya yi ma ta dan tsaban takaicin abin da akayi ma sa ya sa yama rasa mai zai ce.
“To garin ya ya?”
Ta sake maganar tana duban Halima duk da ita kanta ta sani sata ba halin Halima ba ne kuma idan za'a kasheta kan ta fad'a wani mummunar halin Halima guda batasan me zata ce ba, domin ko a baya da take yi mata duk abin da ta yi ita kanta ta sani son zuciyarta kawai take bi takeyin wasu abubuwan wa Haliman, amma tun bayan lokacin da Abbas ya auro Ruk'ayya zuwa yanzu Mama Tsahare ta fahimci Abbas bashi da wata mata ta rufin asiri da ta wuce Halima domin ko kad'an Mama Tsahare basa shiri da Ruk'ayya musamman akan tijarar da Ruk'ayya ta yi a haihuwarta na fari a gidan, abin nan ya dad'e yana cima Mama Tsahare tuwo a kwarya kuma yana daga cikin dalilin da ya sa taji Ruk'ayyan duk batayi ma ta ba.
“Ai gasu nan wacce ta d'auka cikinsu sai ta yi miki bayani, kawai idan banda ma rashin lissafi na wasu matan ka rasa wanda zakayima sata sai mijinka.”
Abbas ya yi maganar cikin zafin zuciya yana jingina da mashin d'in sa.
“Da dai kabi komai a sannu d'an nan kar yaje ana zaton wuta a mak'era kuma a sameta a masak'a, lamari irin wannan ba'a yanke hukunci kai tsaye har sai an yi bincike an kuma tabbatar, ta yiwu ma kana nan kana tuhumarsu kuma kud'in suna can ka adana a wasu wurin ka manta, na fa san halinka D'anladi indai akan son kud'i ne, domin ban manta lokacin da kake wuceni k'iri k'iri idan ka sama kud'inka ko ajiya baka bani saboda kar na hanaka sai dai kaje can gidan Alhaji Sammani ka bashi ajiyar saboda ka san shi mai kud'i ne ba zai cinye maka kud'i ba.”
Cike da k'osawa Abbas ya ce.
“To Mama kuma mene ne ya kawo wannan batun da ya shud'e da jimawa fisabilillah nifa yanzu cewa kawai nayi koma wacece cikinsu ta d'auki kud'in nan ta fito min da abina kawai.”
“Hmmm a dai dinga sara ana duban bakin gatari D'anladi domin shekaru d'aid'ai har goma sha shida kuka kwashe tare da Halima ko kusa irin wannan abu na zargi bai tab'a giftawa tsakaninku ba saboda haka kasan abin da kake yi idan hankali ya b'ata hankali ke nemosa.”
Ruk'ayya da tun da Mama Tsahare ta shigo gidan ta tarar da abin da ke wakana ko gaisheta batayi ba tsabar yadda zuwan nata ya bata haushi kuma jin irin kalaman da takeyi ya sa ta ce.
“Idan ma zargi ake ni nayi satan nan to wallahi an yi k'arya domin ni nafi k'arfin na d'auki abin wani ni da nake da aiki ina aiki ina samun kud'ina ai abin wani ba zai tab'a rud'ata ba wallahi.”
Ta k'are maganar har da wani jijjiga jiki.
Rai a b'ace Abbas ya dubeta, cikin kakkausar murya ya ce.
“Rakiya kina a hayyacinki kuwa mahaifiyar tawa kike fad'a wa hakan saboda baki da hankali ?”
“A'a fa Darling ni kam ban kira sunan kowa ba ah to.”
Ruk'ayya ta fad'a tana kauda kai.
Mama Tsahare da batayi mamaki ba ta girgiza kai tana yaba rashin kunyar Ruk'ayya a zuciyarta ta raya.
'Ai gashi nan garin kwashe kwashen Abbas ya aurowa kansa k'ak'ani kayi.'
Ta raya hakan dan ta gama fahimtar matar sam bata k'aunar a zauna lafiya ita wallahi har tausaya wa Halima take.
A fili kuma sai cewa ta yi.
“Ai da ka kyale ta D'anladi ai dama ta samu shi ya sa take abin taga dama.”
Ta yi maganar tana mayar da dubanta ga Halima dake jin su bata ce musu komai ba ta ce.
“Ni zubomin abinci kinji dan na lura idan na biye ma rigimar gidan nan naku sai yunwa ma ta yi min illa ban ankara ba.”
“Ayi dai abin da za'ayi ni dai ba b'arauniya bace kuma duk wanda ya d'auki kud'i ya san kansa. Ai Darling idan ma zaka tuna tun da ka dawo gidan daga makaranta ni ban shiga d'akin ka ba ina wanki ne ma a tsakar gida.”
Shiru Abbas ya yi yana nazari domin maganar da Ruk'ayya ta yi sai ta ankarar da shi wani abu, ya tuna ko'a lokacin da ya dawo gidan sai da ya duba lafiyar kud'in ya gansu daidai sannan ya fito ya zaga bayan gida kuma kafin ya dawo ne ya tarar da Halima a d'akin tana jiransa sannan bayan fitarta daga d'akin ne ya tuna da kud'in ya nema kuma ya rasa.
Ya yi ma Halima wani duba ya bud'e baki zai yi magana Mama Tsahare ta katse shi.
“A'a D'anladi ban yarda ka furta wani abu da zaka zo kana danasani ba daga baya ka tsaya kabi komai a hankali.”
“Ai kuma batun bi a hankali ya k'are tun da bai yarda damu ba yana zargin cikinmu ne d'aya ta d'auka masa kud'i, ba sai ya yi caje ba kawai ya duba ko'ina har d'akunan mu ko hankalinsa zai kwanta kuma zarginsa akanmu ya kau.”
Gaba d'aya duban Ruk'ayya da take maganar cike da kwarin gwiwa suka yi. Halima ta jinjina kai tana mamakin yadda Ruk'ayya take k'ara zak'alk'alewa akan lamarin amma sai ta sauke ajiyar zuciya tun da dai ita ta san tana da gaskiya saboda haka bata shakkar koma mene ne zai faru, ba caje ba ko caje caje zai yi bashi da matsala da ita.
Mama Tsahare da take galla ma Ruk'ayya wata harara a sakaye taja kwafa tana duban Halima ta ce.
“Yar nan ana ta magana bakice komai ba.”
Halima ta sauke ajiyar zuciya tana kawar da dubanta daga Abbas ta mayar ga Mama Tsahare.
“Mama ai ni bani da matsala koma mene ne zai yi domin kud'insa su fito ya yi kawai.”
Jin abin da ta ce ya sa Ruk'ayya ta yi wata 'yar shewar da ya sa Mama Tsahare da Abbas dubanta sai dai ban da Halima ita kuwa ta maze fad'i take.
“Tun da an baka wuk'a da nama ai sai ka fara.”
Ta fad'a tana baza riga ta juya zata nufa wurin da take wanki domin ta ci gaba hankali kwance.
A daidai lokacin shi kuma yaronta Mahmoud mai shekaru uku ya fito daga d'akinta yana tunkararta tare da mik'a ma ta damin kud'ad'en dake hannunsa fad'i yake.
“Ansha sweet and chocolate, Mom I wan chocolate da biscuits.”
Ya fad'a yana tura ma ta kud'in. Ita kuwa tsananin mamaki da al'ajabi yasa ta mak'ale wuri guda kamar wata statue ita bata yi gaba ba kuma batayi baya ba sannan bata motsa ba.
“Tashin hankali wannan ba kud'ad'ena bane?.”
Abbas ya fad'a cikin wani irin zafin ran da ya sa yaron sakin kud'ad'en suka zube a k'asa shi kuma ya saka kuka saboda a tsawace Abbas ya yi maganar kuma yana tunkararsa fuska ba rahama shi ya sa yaron yaji tsoro.
Durk'usawa Abbas ya yi yana tattare kud'ad'en a fili yake fad'in.
—
|Da kuka jini shiru kwana biyu ai sai kuyi cigiya 🥱 amma mutane kaɗan ne suka nemeni 😒an ya ba zan datse free pages ɗin nan haka nan ba, mu had'e a paid group kawai, posting kullum ne a can ba fashi and no Delay 🤸