RU'UYAA (The dreams we never lived)
28. ...yayi fushi...🖊️
by @autum17
Bayan na saki wannan ihun daya kusa fasa mashi dodon kunne, wurin yayi tsit...bai riƙe niba hannayen sa toshe da kunnuwansa fuskarshi kamar hadari yana wasa haƙoranshi kamar yana ƙara masu kaifi dan ya cije ni..ɗagowa nayi idon mu ya haɗu...takaici da haushi na gani a ciki...
'' Damn! It's just a rabbit,and here you're trying to destroy my ear drums!" turo baki nayi can kuma na fara kalle kalle idan da gaske hakan ne,wani farin zomo mai fato faton kunnuwa na gani riƙe da wani abu a hannun shi yana ci...'' shegen abu ya kusa bani hawan jini!"
'' zaki sauka ko cigaba da kasancewa a haka zakiyi?" Oh...sai lokacin naga yanda na ƙanƙame shi kamar rayuwata ta dogara dashi...da sauri na sauke ƙafafuna daga ƙugunshi na warware hannayena daga wuyan shi...
Ya juya ya cigaba da tafiya ina biye dashi kukan wannan abun kamar fara da sauran abubuwa duk ya cika dajin...na tabbar da yanda sama tayi duhu wurin ƙarfe shida da rabi ne..
'' Zom...ina nufin Romo ka tabbatar ka san hanya kuwa?'' bai kalle niba can yace
'' ina fama da ciwon mantuwa ai ...''
Tsayawa nayi na rufe bakina '' Innalillahi shine ka kawo mu nan? Yanzu ya zamu kumo gida?"
'' i didn't force you into my car did I?"
'' ai da sai ka faɗamin in fita!"
Ɗage kafaɗa yayi ya cigaba da tafiya...nikam ina tafiya gefen shi ina kallon nan da can sai nake ji kamar za'a iya kawo mana hari...
Kafafuna duka sunyi ciwo..tsoro ya fara shigata da gaske amma mutumin nan ko a slippers ɗinshi...
'' wai shekarun ka nawa?" na tambaya ina kallon shi
'' none of your business!" Muryar shi ta fito da zurfi da kuma fushi...to daga tambaya?
'' na faɗa maki.. don't try to get close to me baki ji ko?" ya sake faɗa..kallon space ɗin dake tsakanin mu nayi
'' akwai taku uku tsakanina da kai,taya na matso kusa da kai?" na haɗe fuska nima wa zai dinga raina ma wayo?
bai ce komai ba... badaɗewa ba muka iso ƙarƙashin bishiyar nan daya fara zanen shi nayi mamaki sosai... Kwashe abubuwan shi yayi nima na sako takalmi na yana gaba ina biye dashi
*****
Tsaye Khalil yake a ƙarƙashin shower ruwan sanyi na dukan shi idonshi sunyi jawur..hannun shi ɗaya dogare da bango ɗaya dunƙule daga gefen shi, jijiyoyin kanshi sun miƙe..ƙirjinshi na sama da ƙasa...ya karya alƙawarin shi! Ya sake yin abinda ya riga da ya rantse bazai sake komawa ba...how was he so weak? Meyasa bai hana kanshi ba?
Runtse idonshi yayi zuciyar shina tafasa... numfashin shina fita da zafi kashe ruwan yayi dan aƙalla yayi kusan awa ɗaya da rabi a wurin...kayan jikinshi ya fara cirewa ya jawo tawul cikin duhu dan bai kunna wuta..baya so yaga reflection ɗinshi...
Bayan ya ɗaura clumsily ya fito daga bayen ko kaya bai saba ya faɗa saman gadon shi yaja blanket ya rufa yana rawar sanyi,'' Astaghfirullah'' ya furta da muryar rashin lafiya....
Mukhtar kuwa zaune yake a gaban madubi ya ɗauko first aid box yana kula da ciwon da Abeedah ta jima shi, every now and then he groans, bazai bar yarinyar nan ba,ko badaɗe ko bajima sai ya cimma burinshi...it was her fault! He got seduced kawai bayan ta kalle shi yanzu kuma sai ta hana shi? Impossible!
da yafita don cigaba da party'n kowa sai tambayar shi yake mai ya same shi '' mind your business '' shine amsar...can ya zauna a wata kwana sai ga Hansa'u ta saci jiki ta zo wurin shi tana yauƙi..baƙaƙen uniforms ɗin jikinta sun matse ta sosai '' yallaɓai kana buƙatar wani abu ne?" ta tambaya in a slutty voice
Kallonta yayi da takaici ya daka mata tsawa '' get out!" kamar wacce ta haɗu da zaki ta bar wurin da sauri kamar zata kife...shima tashi yayi ya fita daga gidan cikin motar shi...
Tsaye take a ɗakinta ta kasa zaune ta kasa tsaye sai nan da can take...wurin ƙarfe goma ta leƙa window'n ɗakinta ta hangi motar Roman ta shigo cikin gidan...bayan yayi parking a parking lot gani tayi ya fito ya buɗe ƙofar baya ya ranƙwafa ya faɗi wani abu sai aka buɗe ɗayan side ɗin Abeedah ta fito
Zallo zuciyar ta tayi daga ƙirji zuwa maƙogaro idonta zazzare..it can't be right?
Da sauri ta koma bakin gado ta ɗauki wayarta ta shiga contacts wata lambar da bata kira ba in years ta zaƙulo sai da tayi kokonto na yan mintuna kafin ta danna layin...
wayar ta kusa katsewa kafin a ɗauka '' I have got a job for you...''
******
Ban san sanda muka shigo gidan ba dan bacci ya ɗauke ni naji ya buɗe ƙofar bayan yace '' ki fito ki kwanta nan ƙasa...i want to lock my car!" ina yabon shi sallah zai kasa alwala '' na gaji sosai kaɗan ɗauke ni ka kaini sashen mu...'' na miƙo hannuwa na kamar da gaske ina ƙoƙarin riƙo wuyanshi
Ja baya yayi '' I'm too lazy to do that! Ki fito ko in rufe ki ciki.. '' da gaske yake fa hakan yasa na shafawa kaina lafiya na fito ƙafafuna sunyi tsami.. Allah yasa munyi salla a wani masallaci bakin hanya harda abinci ya siya min ashe yana ɗan da mutunci...
Rufe ƙofar yayi,ina gaba yana biye dani baya har muka kawo sashen mu...na tsaya bakin ƙofar wurin har zai wuce nace '' Romo...''
Ɗage gira yayi hannayen shi cikin aljihu '' kai kaɗai zaka kwana a wannan ƙaton ɗakin naka?"
'' so?" ya furta da rashin haƙuri '' bari in kwaso kayana inzo in taya ka...'' kallo ya ƙare min daga sama har ƙasa yace '' fitsarin kwance nake gudu...'' yayi gaba abinshi ya barni da sakin baki..
'' Goodnight Roman...'' na faɗa ina juya mashi hannu da murmushi a fuska ta ɗan dakatawa yayi ya juyo ya kalle ni ya gyaɗa kai kawai baice komai ba...
Nayi tsaye har saida ya shige gidan su Sannan nima na nufi ɗakin mu.. zuciya ta da farin ciki da kuma tunanin shi...mai yasa nake tunanin shi? he's growing on me isn't he?
Wanka nayi na canja kaya na kwanta murmushi yaƙi barin fuskata...sanda bacci ya ɗauke ni mafalkina cike yake da Romo a wurin da muka tafi da kuma wasu wuraren daban... kuma Nasan daga wannan lokacin baxan sake kallon shi iri ɗaya ba...
Washegari mutum uku ne basu zo wurin kari ba,harda Mukhtar dasu Romo da Khalil...ko meya sa...
Su Seraphina babu abinda suke magana akai sai party'n jiya...Farzan na lura da yanda yake kallona...ba irin kallon Mukhtar ba amma nashi kallon yafi tsoratar dani,ƙasa nayi da kaina...
Yauma mun ci sa'a ba aci mutuncin mu sosai ba...wurin ƙarfe goma muka shiga lambu dan zaƙulo shukokin da suka mutu naji yanayin wurin ya bambanta dana koda yaushe rana taɗan hudo glass roof ta haska wurin kaɗan sai ƙamshin furanni dake tashi da kuma sanyayyar iska...
Gloves muka sa a hannayen mu dan wasu daga cikin shuke shuken suna da guba...can sai ga Diyaam ta shigo itama...muka taru dasu waleeda da Aina'u muka zaɓi section ɗaya muna aiki akai suma sauran abinda sukayi kenan...
ranar tayi min daɗi amma ban haɗu da Khalil ko Roman ba..meyasa? naji raina ya fara min ba daɗi...
Ranar Monday muka tafi makaranta, su Asma'u suka zo da ɗan tamalele aiko gaba ɗaya yan ajin mu aka zagaye seat ɗin mu..an face kowa ya jira aci da guda guda amma haka yaran nan suka daka wasoso daga ƙarshe wasu basu samu ba,mu kuma hijaban mu sun ɓaci da manja...amma waya damu? abu mai muhimmanci shine muna tare kuma muna farin ciki...
Jay d taxo da wayarta mukayi hotuna da video.. jarabawar mu zata fara ranar laraba..duk da ina farin ciki dan nayi karatu,hakan bai hana jikina sanyi ba daga lokaci zuwa lokaci...
Yau ma da kaina na koma gidan, DIYAAM kuma dama tana da dreba... mutum na farko dana fara cin karo dashi bayan na wuce gate ɗin shine Roman... zuciya ta tafara bugu da ƙarfi...wani irin murna ta kamani..kafin in yanke hukuncin zuwa wurin shi ƙafafuna har sun kaini..zaune yake saman mashin ɗinshi kayan jikinshi baƙaƙe kamar ranar...ya riƙe helmet zai sa na tsaya gefen shi...na kai hannu na zan taɓa wani button akan hannun mashin ɗin ya juyar da kan..tare da kallona sau ɗaya ya ɗauke kai
'' inzo muje?" Na tambaya da murmushi...'' no thanks!" Ya bani amsa yana tada mashin ɗin '' wayyo bafa damunka zanyi ba!"
'' You look dirty...matsa kada ki shafa min!" turo baki nayi
'' xan taya ka hira fa..'' na share abinda ya faɗa game da uniforms ɗina '' nace ina buƙatar abokin hira ne?"
'' exactly! Nasan ba zaka iya faɗa ba shine yasa nake yimaka tayi...'' wani jan botin na latsa saman mashin ɗin ya fara tsuwa jar wuta na kawowa tana ɗaukewa
'' bar wurin nan!..''
'' Bar wurin nan!"
Muka faɗa a tare dan dama nasan abinda zaice kenan...ƙanƙantar da idonshi yayi..nayi dariya... helmet ɗin yasa na kunce igiyar daya gama ɗaurawa na tsere da gudu nabar wurin...
Su Fauziyya na gani zaune suna kallo.. da gani na suka rakani da harara '' yar wata sai ƙoƙarin cusa kanta take a wurin masu gida... yallaɓai Roman babu abinda zai yi dake!" Rasheedah ta faɗi hakan...ban tanka ba na shige ɗaki..
Bayan na sauya kaya na koma ƙasa naci abinci na tafi babban gida nayi ƙananan ayyuka harda wanke ma seratena pants yarinyar ƙazama ce...yan matan zaune suke a ɗakinta suna hirar soyayya...
Mufeedah tace '' ai idan kana son mutum zaka so ka kasance tareda shi koda yaushe sannan zaka ji kana farin ciki idan kuna tare kuma zaka so kaganshi cikin farin ciki da abubuwa da dama...''
'' toh magulmaciya mai kike saurare?" Jameelah ta jefeni da pillow
'' abinda har abada bazata samu ba da wannan mummunar fuskar tata!" Khaleesat ta bata amsa
'' da yake Allah ke bawa Kowa nashi rabo!" Ina jin yanda suke kirana in dawo su cimin mutunci na share su nayi gaba abina...
Haɗuwa nayi da Farzan a hallway naga yana tunkaro ni...ji nayi gabana ya fara faɗuwa yana isowa inda nake baiyi wata wata ba ya rungume ni..na shiga shock...Roman yazo ya wuce mu kamar babu mu a wurin da sauri na ture Farzan da bai ko kalle niba bayan wucewar Roman...amma dai wannan gaye...fushi naji ya cika ƙirjina naja dogon numfashi na wuce ɗakin DIYAAM..
ganinta nayi tana karatun jarabawar mu..na zauna muka cigaba a tare duk da ba wani fahimta nake ba saboda abinda farzan yayi min da kuma Roman daya gan mu...
Ina ɗakin Diyaam har lokacin sallah'r Isha'i sannan na wuce dining
Samun su nayi suna magana akan wannan Fateemah Cora Maman Roman suna faɗan baƙaƙen maganganu akanta... musamman Hajiya Momma.. Hajiya Hafsah dai tayi shiru abunta da gani bata son hayaniya
Can anjima Roman yazo wurin amma duk da haka basu dena maganar taba... dunƙule hannun shi yayi saman cinyar shi Hajiya Momma tace '' An apple doesn't fall far from the tree ai,wayasani shima abinda yake kenan...''
'' dayake jini yafi ruwa kauri ba!'' Hajiya Wareesha ce ta faɗi hakan...
Slowly Roman yace '' da gaskiyar ki...i suggest kafin Kiyi magana akan wasu,ki fara duba naki ya'yan..after all we won't want you eating your words do we?" Ya ƙarashe yana kallon Mukhtar,Wurin yayi tsit bayan ya faɗi hakan...
'' baka da kirki yaron nan! Baka san ka girmama na gaba da kai ba!" inji Hajiya Zeenatu
'' unfortunately wannan kalmar 'girmamawa' babu ta acikin dictionary ɗina.. especially ga mutanen da basu girmama kansu ba first!"
Ya miƙe tsaye yana kallon Hajiya Momma yace '' you talk big on morals...idan akan tarbiyya ne,baki kama ƙafarta ba...'' Hajiya Momma ta ƙwalalo ido dining yayi tsit
Ya juya zai bar wurin ya ƙara da faɗin '' none of you are qualified to talk about her with your contaminated mouths!"
Hajiya Momma kamar zata kama da wuta tsabar haushi da takaici... Farzan bai ce komai ba...suma sauran matan sai hura hanci suke
naji Roman ya ƙara bani tausayi...rashin uwa ba ƙaramin abu bane ... amma ina take? ko tabar gidan ne?
Da ƙarfe tara na yanke shawarar zuwa ɗakin Khalil in duba tunda kwana biyu ban ganshi ba...
Tura ƙofar nayi na ganshi kwance saman gado rabin jikin shi rufe da bargo..ƙarasawa ciki nayi ɗakin ba haske sosai nake kallon fuskar shi datayi alamun rashin lafiya...ashe baida lafiya? wake kula dashi to?
Buɗe ƙofar akayi,da sauri na juyo naga Roman ne ya shigo saye da kayan bacci baƙaƙe da takalmi masu laushi suma baƙaƙe hannunshi riƙe da plate...ƙarasowa yayi ya tsaya ɗayan gefen bai cemin komai ba ya yaye bargon ya taɓa gefen wuyan Khalil..sai ya tashi ya shiga Baye ya ɗebo ruwa cikin rober ya zauna gefen shi yana goge mashi goshi da kulawa...bayan lokaci kaɗan Khalil ya buɗe idonshi kafin ya yunƙura ya tashi zaune...
abinda ke cikin robar ya fara ba Khalil a baki...sai ya mutse fuska yake alamun bai so...'' if you don't eat,taya zaka ji sauƙi?"
Khalil yace '' wannan Italian recipe ɗin naka ne ba daɗi.. '' muryar shi da rashin lafiya...nake kallon su biyun yanda Roman keta ƙara cusa ma Khalil koma meye shi kuma yana ƙoƙarin kauda kanshi...daga ƙarshe dai sai daya shanye tass, Roman ya share mashi bakinshi sannan ya kwanta...ya gyara mashi blanket..
Ya tashi zai tafi Khalil ya riƙe hannun shi,ya juyo slowly yace '' thanks Rome...'' gyaɗa kanshi Roman yayi...ya nufi ƙofa..da alamu Khalil bai ganni ba yasa nima na fita cikin shiru
Lokacin har Roman ya ɓace..naso inyi mashi magana amma ba dama...
Washegari ban tafi makaranta ba dan Nasan babu abinda zamu yi... babban dalilina na zama gida kawai ina so in haɗu da Roman ne...
Zagaye gidan na fara yi har na kawo wurin ƙofar XXX...babu kowa a corridor'n kuma ƙofar da alamu buɗe take yasa na tura na shiga...cikin sanɗa...
ƙanshin turpentine (ruwan wanke brush) da zaitun da tsofaffin littattafai ya daki hancina...ƙanƙame jikina nayi cikin hijabi saboda sanyi
Babban taga daga ƙasa zuwa rufi, gilashinsa fari ƙal . Hasken safiyar ya shiga ya faɗa akan wani ƙaramin akwati baƙi mai ratsin zinari mai bala'in kyau
Baƙar kujera ta fata a tsakiya, . A kusa da ita akwai easel na itace, an fara painting akai amma ba'a gama ba
Bangon dama duka shelves ne. Akwai 🖌️🖌️ painting brush ko wane size , sai wasu ƙananan drawers da diary ɗinsa a sama mai baƙin cover
Bangon hagu kuwa... komai baƙi ne. Yana cike da zane-zanen da idan mutum ya kalla zai iya jin emotions da kuma ciwon da suke fuskanta
A ƙasa akwai tabo-tabon paint. Ja, baki, blue. Kamar taswirar raunukansa....
Akwai wani rubutu da Yaren daban gane ba da alamu da baƙin painting aka yi shi da hannu
Questo è il mio mondo... dove esisto da solo.`**
(Wannan duniyata ce... inda nake wanzuwa ni kaɗai.)
Ɗauko allon nayi daga inda yake na ajiye a gaban bangon glass ɗin nan na ɗauki brush da painting na cigaba daga inda yatsaya kamar wata ƙwararriya a harkar zane...daga ƙasa na rubuta sunana nayi signing
Ja baya nayi na goge zufar data tsatstsafo min a goshi da murmushi a fuskata kamar na cinye lottery... sosai zanen yayi kyau a idona,ba wata yarinya bace yake drawing ni kuma na iyar mashi...
''WAYA CE KI TAƁA MUN?'' muryar shi ɗauke da fushi da sanyi mai illatarwa ta sauka a kunne na, a firgice na juyo hakan yasa plate ɗin dake kai yabar hannu na yayi sama kamar ana controlling ɗinshi ya sauka akan fuskar shi sannan yayi ƙasa ya ɓata rigar dake jikinshi kafin ya faɗi ƙasa ya baltsu a takalmin shi farare...nima garin Juyowa na rasa balance na faɗa cikin painting ɗin dana gama yi yanzu nida allon painting ɗin crashed on the floor...datse bakina nayi dan hana ƙarar data kawo maƙogwarona fita...
Tsabar yanda ɗuwawuna suka sauka akan katakon da ƙarfin daya sa na ɗauka for a second baxan sake iya zama ba...ido waje ina numfashi sama sama
Ƙafafuna buɗe gashi babu damar sosawa tsabar yanda yake kallona da takaici.. fuskarshi tayi ja..ƙirjin shina sama da ƙasa bakin shi a tsuke kamar yana hana kanshi magana
Nuna ni yayi jikin shi na tsuma yace '' You...! Why does my painting have to pay the price for your clumsiness!" Sai ya koma shafa goshin shi kamar tsohon daya gaji da rashin jin jikokinshi
Da ƙyar na miƙe tsaye nace '' ba kaine ka tsorata niba...'' idonshi ya sauka akan painting ɗin shi dana lalata
'' Oh my God what have you done?'' ya ɗaura hannunshi saman kai..ya wuce ni zuwa allon dake kwance ƙasa....ya ɗauki brush ɗin daya karye sanda muka faɗi
Da matsanancin fushi a fuskar shi ya miƙe yayi cikina samun kaina nayi daja baya zuciya ta na tsananin bugu....hancin shi har wani huci mai zafi yake fitar wa
Hannu na ya damƙo yaja ni da ƙarfi ya fitar dani daga ɗakin....na juyo zan bashi haƙuri ya buga ƙofar da ƙarfi kamar zai ruguje gidan duka...
Kin ƙetare iya ka...hajiyar su🤭
***
RU'UYAA…📖
₦500 ne idan ya kammala zai koma 800
Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay
Shaidar biya ta ***
Autumn writes 📖🖋️