RU'UYAA (The dreams we never lived)

30. ...son shi nake...🖊️

by @autum17




'' Come kitten...'' ya riƙo hannuna muka bar wurin Diyaam biye damu... zuciya tana tsananin ciwo...

Jinginar da bayan shi akan seat ɗin shi farzan yayi yake binsu da kallo har suka ɓace

da murmushin nasara a fuskar shi yabar wurin. su Hajiya Momma kamar maƙoshi zai faɗi tsabar yanda take ihu...

Anan parlor'n shi Khalil ya zaunar dani Diyaam zaune a gefe na shi kuma ya zauna a kujerar dake kallon mu...su biyun sai lallashina suke da ƙyar na samu na dena kukan sai shaƙuwa...

Ruwa ya zuba min a cup ya bani na amsa na shanye duka Diyaam ta riƙe hannu na tana shafawa nayi ƙasa da fuskata suddenly naji duk kunya ta kamani

 '' Are You blushing?" Ya tambaya sai ya zaro wayarshi daga aljihun shi 

'' kalli nan..'' hannuna nasa na rufe fuska ta bai barni ba har saida nayi dariya Diyaam na tayani daga nan yake bamu labarin zaman su Chicago yanda Roman abu kaɗan yake kaiwa mutane duka kamar Jackie Chan..hakan yasa ya dinga zuwa detention every now and 

'' ai yanzu yayi sanyi,da dane ko magana ba zai yiba...cikin mu zai yi da duka dukan mu!" Nida Diyaam mun sha dariya har sai da cikin mu yayi ciwo...

da ƙarfe goma muka bar sashen shi,Diyaam ta wuce ɗakinta ni kuma na wuce namu sashen..samun Hansa'u nayi tsaye daga wurin gado na ina shigowa tayo kaina ta shaƙe min wuya 

''shegiya wane irin tsafi kikayi amfani dashi wurin kama maxan gidan nan a tafin hannun ki...'' 

ƙoƙarin cire hannun ta nake daga wuyana amma abu yaci tura,fim ɗin Chinese ɗin da muke kallo ya faɗo raina yanda suke shure mutum idan an musu irin haka,ƙafata na ɗaga na sauke mata a ciki...taja baya harda faɗuwa ƙasa tana mulmula...da ƙyar na samu numfashina...

Ta miƙe tsaye tana huci..nace '' idan kina neman tsafin da nake amfani dashi...''

 idona na nuna mata ina juyasu

 '' wannan ne,kuma ke baki dasu...kin gane? Duk wanda ya kalla dole yaji ya ƙyasa!" 

Na bangaje ta daga gabana na haye gado na...bada daɗewa ba Mama Asabe ta shigo ta samu Hansa'u na kuka data tambaye ta cewa tayi

 '' ba ruwanki tsohuwa..'' baki Alaikum Mama Asabe ta haye nata gado ta kwanta tan sauke ajiyar zuciya sai kuma ta fara juye juye 

'' Mama Asabe lafiya kuwa?" Na leƙo kaina 

'' lafiya lau Abeedah ciki nane ba daidai ba'' 
'' oh... Allah ya kawo lafiya...'' 

'' Ameen...'' bayan wani lokaci nace '' abin nan naki yana aiki Mama Asabe na gode sosai Allah ya ƙaro arziƙi!"

'' Ameen Ameen Abeedahtu..''

***

Washegari a gaggauce na shirya cikin uniforms ɗina, tunda ance ba zamu dinga aiki ba sai kawai na ɗauki littafina ina muraji'a...

Da ƙarfe bakwai muka sauko zuwa dining ɗin mu wurin kari...Su Fauziyya, Hansa'u da sauran wasu daga cikin masu aikin sai hararata suke kamar na tare masu wani abu..babu abinda ya shamin kai ko kaɗan...


'' Allah ya bada sa'a Abeedah yasa a rubuta a sa'a ba sai an maimaita ba!" Mama Asabe tayi min addu'ar.. waya'nda ba yan baƙin ciki ba suka amsa da Ameen Hansa'u taja tsuki tace

'' Allah yasa daga waec har neco ɗin kiyi ta maimaitawa har ƙarshen rayuwar ki!"


'' Ameen ya hayyu ya qayyum!" Su Fauziyya suka amsa da ƙarfi..

Naji ba daɗi amma sai na kauda kaina kawai...bada daɗewa ba na gama breakfast ɗin...Babban gida muka shiga tareda Mama Asabe dasu waleeda suka wuce wurin aiki Ni kuma na wuce sashen Khalil in duba shi...

Da farko ƙofar ɗakin Roman na fara isa kamar in shiga kamar in ƙwanƙwasa daga ƙarshe na juya na bar wurin raina ba daɗi ..

Sashen Khalil na tafi na ƙwanƙwasa ya bani izinin shiga...na ɗan waro ido ganin su biyun zaune a parlor...Roman saye da jajayen kaya..gashin shi ya pake sama da ƙasa..ba ƙaramin kyau yayi ba... hankalin shi a kan laptop yana aiki..

'' Oh kitten...'' murmushi nayi mashi yace in ƙaraso ciki...ya nuna min ɗayar kujerar dake daga gefen hagu shida Roman zaune a kujera ɗaya...na zauna ina satar kallon Roman da bai kalli inda nake ba...

'' how are you today?" ya tambaye ni '' lafiya Lau,ya jikinka?" 

'' Alhmadulillah!" Na gyaɗa kaina...na ƙara satar kallon Roman...can ya ɗago ya kalli Khalil ya tura mashi laptop ɗin yace '' na gama yanzu zaka iya submitting ba dole sai kaje can ba!" 

Duba laptop ɗin Khalil yayi ya gyaɗa kanshi..Roman ya fita daga sashen..bai kalle niba...kenan yayi fushi dani...

Khalil ma ya shiga nashi ɗakin,ina nan zaune ya fito riƙe da chocolate irin wanda Diyaam ta taɓa bamu ya miƙa min na karɓa ina kallon shi '' good luck with your exams!" Murmushin shi yasa naji nauyin da zuciya ta tayi ya rage...'' na gode!" 

Na amsa..sai na miƙe '' bari in tafi kada inyi latti!" 

'' driver zai kai ki?" Ya tambaya na girgiza kai, naga ya ɗauki wayar shi dake saman table da sauri nace '' a'a nafi son tafiya da ƙafa ne...'' 

'' really?" Ya ɗage min gira na gyaɗa kaina '' okay...''

Fitowa daga ɗakin shi nayi ina tafiya slow slow naci karo dasu Seraphina..wani tsinannen kallo suka wurga min su uku dayasa zuciya ta bugawa da ƙarfi...

'' manta da cewa Ya Rome yace a rabu daku, wallahi sai zama a gidan nan ya gagari ku biyun!" Khaleesat ta faɗi hakan sauran basu cemin komai ba sukayi gaba...gabana ya shiga faɗuwa.. addu'a nayi na wuce ɗakin Diyaam itama ta shirya breakfast take yi ita kaɗai a ɗakinta

'' Toh ni zan tafi idan kin gama sai ki iske ni..'' da sauri ta tashi tasa hijabinta tace '' bari inzo mu tafi...''

'' ke da mota zaki ni kuma da ƙafa zani...''

'' zan faɗawa Hamma sai mu tafi taren...''

'' a ƙafa?" Ta gyaɗa kanta...

Jakarta ta ɗauka ta fito...ɗakin Roman muka tafi amma bai nan muka sake zuwa inda yake art..nan ma bai nan

Sai da muka fita muka hange shi a parking lot,Diyaam gaba ina biye da ita... fatan zai kalleni ko sau ɗaya ne amma da muka isa har sukayi magana suka gama bai kalli sashe naba...irin chocolate ɗin da Khalil ya bani ya miƙa mata tare da faɗin '' Ace your exams papillon (butterfly)'' ta amsa da '' insha Allah Hamma...'' ya gyaɗa kanshi sannan muka bar wurin.. zuciyata na ci da wuta..kamar inyi kuka sai Juyowa nake ina kallon shi...


Yau ko kyau'n anguwar ban gani ba...har muka iso makaranta raina ba daɗi kuma babu wanda yayi magana cikin mu...

Wurin ƙarfe takwas su Jadeedah suka iso muka haɗu cikin farin ciki muna yima juna Allah ya bada sa'a.. wannan lokacin har an canja mana lambobi...

Dukan mu ajujuwa daban daban muke...kafin mu shiga jarabawar sai dana raba mana chocolate ɗin da Khalil ya bani '' ina kika samu wannan chocolate ɗin Abeedah?" Jay d ta tambaya

'' Khalil ya bani...'' zaro ido Asma'u tayi '' ina kika ganshi?" yanda idonta ke sparkling naso in gano wani abu kafin in amsa malam Nura ya gargaɗa mu zuwa ajujuwan mu...

Tsaye mukayi a bakin ƙofa idan an kira mutum da number shi sai ya shiga aji...nice no 17... ana kira na faɗa ajin na samu wuri na zauna...kafin wani lokaci har kowa ya zauna...babu kowa a corridor'n...

Ajin duk wanda ka kalla zaka ga fuskar shi ɗauke da damuwa sai yan ƙalilan...ajiye pencil da biro da cleaner nayi saman table ina addu'a zuciya ta fal da tsoro
da ƙarfe goma za'a fara jarabawar,a tunani na kafin nan,fargaba da tsoro sun gama damu... Finally lokaci yayi aka shigo ana rarraba mana tambayoyin da amsa booklet bayan an gargaɗi masu ɗauke da takarda ko wani abu na satar amsa su fitar dashi...

da ƙarfe goma da rabi exam ta kama zamu gama huɗu da rabi... numfashi naja kafin na jawo pencil ɗina na fara rubuta amsa bayan na cika duk bayanan da aka buƙata

Malamai ne ke bi row by row suna karɓar kuɗin ɗalibai suna basu amsa...sanda naga hakan ba ƙaramin mamaki nayi ba sannan naji wani abu ya daki zuciya ta...idan anyi magana sai suce taimako suke bayan kuma babbar illa suke haifar wa na cin hanci da rashawa da kuma daƙile ɗalibai wurin karatun jarabawa...

sanda suka tambaye ni idan ina so in biya ɗari biyar na girgiza kaina wani irin kallo suke bina dashi,bani kaɗai ba harda sauran wa'yanda suka ƙi...

Da ƙarfe sha biyu da rabi muka gama objective aka bamu hutun awa ɗaya kafin a koma ayi essay...

Ƙarƙashin bishiya muka zauna mu biyar... Asma'u ta sake tambaya ta ina na haɗu da Khalil

'' wai ke ko son Khalil ɗin nan kike ne?" Anaam ta tambayi Asma'u tana riƙe haɓa... blushing Asma'u take kafin tace '' wai ma...ni nace ina son shi?"

Jay d tana dariya tace '' to bagashi ba duk kin bi kin isheta da ina suka haɗu....''

'' in sonshi kike Gara ki faɗa tunda wuri!" Anaam take tura kafaɗar Asma'u da zolaya

'' ba so ba ƙauna... mtschewww!" Tashi tayi tabar wurin bayan ta faɗi hakan...

Sallah mukayi kafin muka sake komawa aji..nan ma an karɓi kuɗin mutane,nidai da kaina nayi wannan jarabawar kuma ina roƙon Allah yasa hakan ta kasance har ƙarshe...2:00 muka gaba paper essay aka zo oral test kuɗin wannan sashen yafi yawa har dubu ɗaya acewar malaman wai wannan yafi wahala...

Wani abun mamaki harda invigilators aka haɗa baki ana biyan su...faɗin yanda nake jin ƙunci a zuciya ta game da hakan ɓata baki ne ...


Da ƙarfe huɗu muka gama jarabawa...muda bamu biya kuɗi an bamu amsa ba,cewa suke mu jira ranar mathematics..dole muma mu shigo layi... nikam insha Allah har ƙarshe da kaina zanyi...

Ƙarfe biyar da rabi muka isa gida nida Diyaam..muna tafe muna magana akan jarabawar duk da nidai nace kada ta faɗa min wanda ke daidai da wanda ba daidai ba gudun anxiety...

Sashen mu na tafi ita kuma ta shige babban gida... 

Wanka nayi na canja kaya naci abinci cikin kwanciyar hankali... tunanin haɗuwa da Roman yasa bugun zuciya ta ya ƙaru kafin nishaɗi ya mamaye ilahirin jikina...


Da sauri na gama cin abincin na shiga can ciki... sashen Khalil na fara zuwa na same shi yana kallon ƙwallo...yana ganina ya saki murmushi '' Oh.. kitten!" Murmushi nayi mai haɗe da dariya kullum haka yake cewa '' oh kitten..''


'' Oh Khalil..." Nima na faɗa tare da zama can ƙarshen kujerar dake gefen shi,shafa ƙeyarshi yayi '' ashe kaima kana ɓata lokaci haka? '' ɗage gira yayi nace '' wai mutum yayi ta guje guje cikin fili ana sharɓe shi yana faɗuwa...wai duk dan ya kamo waccan abun!"

'' it's entertaining...'' ya ban amsa taɓe baki nayi nace '' ai nikam idan nayi aure mijina yace zai kalli wannan abun sai dai ya kwana waje!" Sosai yayi dariya...sai ya miƙo min remote yace '' to ki kalli abinda kike so..''

'' a'a ka barshi kawai tunda kallo kake...''bai saurare niba ya turo min remote ɗin...ɗauka nayi na canja zuwa YouTube na nemo MSA 

Ya ɗan zaro ido '' Cartoons kike kallo?" 

'' nayi girma da yawa?" ya girgiza kanshi sai muka mayarda hankalin mu muna kallon tare...

'' ya exam?" Can ya tambaya..ai ko kamar an buɗe tap na fara bashi bayani yanda yan kaɗan cikin mu kaɗai sukayi jarabawar da kansu...

Da kuma yanda ake karɓar kuɗi aba mutum amsa harda invigilators ɗin.. duk cikin bashi labarin ne na taso daga inda nake zaune na zauna gefenshi.. 

'' You did well,kada ki bada kuɗi a baki amsa, kiyi da kanki kinji?" gyaɗa kaina nayi ya sakar min murmushi na dawo da kallona akan tv'n dai dai an kawo wani wuri a cartoon ɗin, inda akwai wasu kaloli da yawa kamar hayaƙi suna bin sama..kalolin akwai green,pink,blue da sauran su...

Sosai idona ke ƙyalli '' ya maki kyau ne?" Khalil daya lura da yanda nake kallon wurin ina zallo kamar zan shiga cikin TV'N ya tambaya '' sosai ma...akwai wuri irin haka da gaske?" gyaɗa kanshi yayi '' it's called Aurora..ko northern lights...''


'' Innalillahi ina so in tafi wurin...'' na faɗa cike da murna '' I'll take you some day...'' yaban amsa '' da gaske? amma ai babu a Nigeria...'' 

'' akwai a Norway...da Canada da sauran ƙasashe...''

'' xan yi farin ciki kuwa...'' na faɗa da gaskiya..ya ɗan matso yace '' kin san a US idan mutum yana farin ciki...they used to give a hug like this...'' ya matso zai rungume ni, pillow'n dana rungume na tura mashi na miƙe ina dariya nayi ƙofa '' idan ka kaini sai nima inyi maka...''

Shafa gefen fuskar shi yayi '' remember your words!" Ya faɗa daga bayana...


Ƙofar ɗakin Roman na tafi na bubbuga amma ba'a buɗe ba kuma ba'a bani izinin shigowa ba...ƙila bai nan...studio ɗin shi na tafi nan ma bai nan


Naji yanayi na ya koma na rashin farin ciki...wurin lambu na tafi a can na same shi ya ajiye painting tools ɗinshi yana painting

Zuciya na zallo na ƙarasa wurin...'' Roman...kayi haƙuri..'' na riƙe gefen hannun rigar shi...mutumin nan ko gezau kamar bai san dani a wurin ba

'' kaji...'' na ƙara jijjiga hannunshi ina turo baki...'' kaji Romeo...'' cije bakina nayi kada inyi dariya dana kira shi Romeo hannunshi dake shafa painting ya daskare

'' Kaji..bazan sake ba!" 

'' Are You trying to annoy me,cuz it's working!" Ya faɗa sharply tare da Juyowa ya kalleni da fushi a idonshi

'' a'a..''

'' to bar wurin nan!" Ya nuna min hanyar fita sakin hannun rigarshi nayi...sai kuma na lakato painting na shafa mashi a kumatu ba zato ba tsammani...sakin plate ɗin painting yayi ya fara tattare hannun rigar shi kamar zai kama da wuta da alamu..abinda yayi ma securities ɗin nan zai yimin...da gudu na juya na fita 


Daga nan ya dena yimin magana kona mashi bazai amsa ba,bazai kalle niba..duk nabi na damu.. fara'a ta ta ragu...su Jay d sun lura da wannan dan haka...ranar juma'a ta titsiye ni akan sai na faɗa mata abinda ya faru...cikin kuka na zayyane mata gidan su Khalil nake aiki...kuma yanzu...well ban sani ba ko sonshi nake amma dai baya min magana kuma hakan na sani a baƙin ciki...

Rufe bakinta tayi bayan na gama kafin ta saki dariya hakan ya ƙara ƙular dani..tsagaitawa tayi ta fara lallashina sannan ta faɗamin abubuwan da zan yi dan ya kula ni..harda..bashi haushi, tambayar shi abubuwa marasa ma'ana...da flirting...nidai ban san ko wannan good ideas bane...but I was determined to try!


masu cewa Roman ya fara son Abeedah..toh nidai na faɗa tun farko yarinyar tana da rawar kai..ga shi harta faɗa tun kan aje ko ina 🙆🤣

shi kuwa bamu masan abunda ke wakana a ranshi ba....tsabar kamun kai😏😏



***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️