BAYA TA HAIHU

18

by @rabiattu0444

*BAYA TA HAIHU*
18
https://www.arewapen.com/book?id=6a9287eff3eaa6dc8f153f72

Ummu Maher (Mrs green)🍀

*AREWA WRITTER'S ASSOCIATION*


*My channel*
***


*🗣️Kar ki wuce ba tare da kin karanta ba Please👏🏻 domin na tabbatar da kuma watarana za ki zama kamar Ummufadeel da ga shirye sai ki fara siyarwa👏🏻🗣️💃🏼*

*_UMMUFADEEL!_*
_*UMMUFADEEL!!*_
 FOODMART🍊🍋🍎🍏🥦🥬🥑🥝🥥🍇🍓🍒🍌🥔
*UMMUFADEEL*
*Ƴar Jos💃🏼*
*UMMUFADEEL*
_Gidan sauƙi_
*Ummu fadeel me gidan gonar kayan marmari kowanne iri, da nau'ikan kayan tsirrai ko wanne iri, tana bayarwa akan sari*

*_SHIGA GROUP DOMIN GANIN KOMI DA IDONKA_*
***
*1_Citta ɗanya🫚 buhu ko bucket*
*2_Kaninfari kwano ko buhu*
*3_Cinnamon*
*4_Kimba*
*5_Masoro*
*6_Rosemerry*
*7_Tafarnuwa*
*8_Amla*
*9_Habbatussauda*
*10_Man kwakwa*
*11_Zaituun*
 Da dukkan nau'ikan kayan ƙamshi na gida da na waje, dukkaninsu za ku same su cikin sauƙi da kuma rahusa gami da aminci, trust and thrusted.
_______________
*_Kar ku ga Ummu Maher ta fiye faɗin sunan, ku tambaye ni menene? Tabbas Ummufadeel ta shahara a fannin kawo muku kayan tsirrai, da kayan lambu, nau'in su Fruits, vegetables, ko wani nau'in kayan fruit da na lambu tana kawowa, kamar su;_*
*Strawberry🍓*
*Roseberry🍒*
*Inibi🍇*
*Ayaba🍌*
*Fiya🥑*
*Kwasha kwasha🥝🥝*
*Apple 🍎🍏*
*Mango🥭*
*Plum*🍑
*Cocumber🥒*
*Latas🥬*
*Cornflower*
*Doya🥔*
*Dankalin turawa*
*Dukkaninsu tana siyarwa a raha da kuma rahusa, ku dai ku hanzarta ku neme ta akan lambarta kamar haka ****
*_Idan na ce zan jero muku za mu daɗe ba tare da na gama ba, sannan tana siyar da na'uikan tsirrai kusan rabi da kwatansu tana siyarwa cikin aminci da kuma rahusa, tana siyar da danƙwala-danƙwalan doya, dankalin turawa, dankalin Hausa, makani._*




_HAFSAH_


Kai tsaye Hafsah ta fara gudanar da aikinta, bayan Billy ta kawo mata maganin murna kuwa tamkar za ta yi tsalle, za ta mallaki abin sonta Habibu saboda rashin Habibu ya fi mata rashin Hamzah shi mijinta domin kuɗinsa take zaune da shi, shi kuma Habibu domin biyan buƙatarta da kuma ƙaunarsa da take yi saboda kyawun halittar sa.


Habibu kuwa kai tsaye har gida taje, ranar cikin Mero ya ƙara firgitata saboda yadda ya fito sosai kana ganinsa kasan ya kai watan haihuwa ita a tunaninta ma anya kuwa ba ƴan biyu bane?.
Kishi da tsanar Mero suka taru suka yi mata yawa, har ta gaza ɓoyewa ta ce"Mero anya kuwa Habibu yana kula dake? Na ga duk kin rame?.
Mero ta yi murmushi ga mi da ɗaga kai, amma ba tace komi ba domin tasan tun da ma yayarta da mijinta basa shiri dole dama tasan sai ta kushe da, saboda haka ma sai taƙi magana ta yi shiru.
Ganin ta yi shiru Hafsah ta ce"Mero zubo min abinci na ci mana".

Na murmusa sannan na ta shi zuciyata ɗaya, ganin hakan yasa ta yi amfani da wannan dama ta buɗe kular Habibu wacce ta ga alamar an zuba masa abinci, ta buɗe ta barbaɗa maganin sannan ta yi sauri ta rufe saboda ba za a gane maganin ba tun da ba gari bane wani abu ne kamar ruwan tofi.



Mummunan tarihi tun daga ranar na kasa gane kan Habibu, saboda yadda yake mun ada yanzu ko kallona baya son yi sannan uwa uba ba ya dawowa gida sai 12 watarana ma da muka ta shi, sai muka tarar ma baki daya bai kwana a gidan ba tashin hankali wanda ba a saka masa rana, ranar har naƙudar dole ce ta kama ni hankalin Ammin Habibu ya tashi sosai ganin yanayin da nake ciki, aka kai ni asibiti suka ba ni gado saboda sun ce idan ba a kula dani ba zan iya yin jijjiga.

Tashin hankali sosai ahalina suka shiga, sannan ga matsalar mijina wacce a yanzu take bawa kowa mamaki canjawarsa na ɗan lokaci kaɗan, na yi kuka tamkar raina zai fita ba Habibu babu labarinsa har na yi kwana uku a asibiti wanda a ranar ne suka sallame ni, babu inda ba a nemi Habibu ba amma shiru na rasa wani irin tunani zan yi, na rame na lalace sosai na ƙara wani irin fari duk da ni dama ba fara bace wankan tarwatsa ce ni, Hafsah da Humairah su ne farare ni kuwa baƙa ce amma kuma duk na gudu kyau tun da baƙi na me kyau ne.



Abin mamaki muna komawa gida muka iskesa a kwance akan gado, sosai na waro ido ganin yadda ya ƙara wani gari shi dama ga shi kamar bature ya yi wani irin kyau fatarsa sai sheƙi take, tuni na ji wani irin kuka ya zo Allah yasa dai ka da a raba ni da mijina domin alamu sun nuna min cikin kwanciyar hankali yake, ba ɓarayi ne suka kama shi ba ko kuma ƴan damfara ba sannan ba ƴan kidnaping ba, kana ganinsa dai ba sai kowa ya ba ka amsa ba za ka bawa kanka da kanka amsar tambayarka, shin ina yake zuwa? Wannan tambayar ce tasa na fara tunanin tashinsa saboda na ji komi a bakinsa domin ance waƙa a bakin me ita ya fi daɗi.


Kasa tashinsa na yi, saboda son Habibu a jinina yake ko me zai yi min bans ganin laifinsa bai taɓa yi min laifi na ɗora masa alhakin laifin ba a kullum ganinsa nake tamkar ubana sannan zan iya yin komi akan Habibu matuƙar abin bai taka wa shari'a ba, ina yiwa Habibu wani irin mugun so ko da ba zai dinga yi min magana ba har karshen rayuwarmu ba zan rabu da shi ba, na ƙwammace ko naman jikina yake yanka na zauna da shi, a kan shi har mahaifiyata na bijirewa saboda ina sonsa kuma a lokacin nan da an raba ni dashi ta ƙarfi da ya ji to da wallahi mutuwa zan yi.


Na sanya shi a gaba na yi ta kallo har ya tashi daga barcin, da kanula a hannuna domin akwai alluran da ba a gama min ba.
Ya kalle ni kaɗan, sai kuma na ga ya juya tuni na saki kuka ina cewa"ba zan jurewa fushinka, ba zan jurewa shariyarka Habibina ina sonka da ƙaunarka ba zan iya share ka ba". Tana kai wa nan sai ta fashe da kuka tamkar dai wacce aka aiko mata iyayenta duka biyu sun rasu, kukan na ta mai tsuma zuciyar me sauraro.

Sosai maganar ta ratsa sa, amma ya rasa me yasa ya tsani Mero sannan ko son ganinta ba ya yi, shi dai kawai a halin yanzu Hafsah ce a cikin idniyarsa ba ya ganin kowa idan ba shi ba, sannan bai yarda ko kusa da shi ta zo ba sai ya ji har wani wari take yi, ba domin har yanzu da sauran son ta a zuciyarsa ba da tuni ya rabu da ita.


Shi yasa ma kwana biyu ya yi tafiyarsa yake gidan Hafsah ya yi kwana biyu, tun da mijinta ba ya nan kuma ba tada me gadi ko ƴar aiki, har yau Hafsah ba ta son Hamzah ya yi mata zancen ƴan aiki a ganinta ai tonon asirinta ne zai zo saboda haka koma menene ba za ta bari a kawo mata ƴar aiki ba tun da ita dai ba mahaukaciya ce ba.


Ganin Mero tana wannan kukan da ya tsana ya sa ya tashi zai fita, da sauri na komar da shi na goge hawayena da ƙarfin tuwo wajen goge hawayen ma har sai da kanula ta ta cire amma ban bi ta kanta ba, na ce"yi haƙuri Habibina na goge hawayena don Allah don girman Manzon tsira ka yi haƙuri in sha Allah ba zan ƙara kuka ba".

Bai san me yasa ba, sai kuma ya koma ɗin kamar yadda ta nema amma maimakon ya yafe mata su koma kamar da ya cigaba da yi mata murmushi gami da zolayarta, kawai sai ta ga ya ɗakko wayarsa yana ta murmushi wataƙila ma saƙo yake karantawa.


Wasu irin zafafan hawaye ne suka taru a ƙwarmun idona bansan lokacin dana rufe bakina ba na fara wani irin kuka me tsuma zuciya, ko kallona bai yi ba haka nasha kukana na ƙoshi ba tare da ya yarda yaji tausayina ba haka ya rufe idonsa ya dinga chart ɗinsa yana dariya.



Rayuwa ta yi min zafi, mijina ya canja min ga shi na ƙi yarda Ammi ta gane komi saboda in har ta gane za a samu matsala babba wataƙila ma daga haka ya sake ni, ni kuma abin da bana so ya faru kenan ko da zai dinga yankan naman jikina yana ci ba zan taɓa bari yabuɗe bakinsa ya ce ya sake ni ba, ina sonsa tabbas sai yanzu na gane shi ne rayuwata.


Uhum ni kuwa na ce so hana ganin laifi, gaskiya labarin Mero akwai taɓa zuciya da ban haushi, wallahi ba so ba ko ciki data muka fito sai na rabu da kai rabuwa ta har abada.







***


_BILLY_


Tafawa suka yi gami da shewa, Billy ta ce"gaskiya fa Hafsah kina wuta wallahi tallahi asirin nan y karɓe ki sosai ki ga yadda Hamzah yake turmoso miki kuɗi tamkar bai san zafin su ba? Gaskiyar magana dolea daɗawa malam kuɗi".

Hafsah ta ƙyalƙyale da dariya da cikinta wanda a yanzu yake da wata huɗu ya fito sosai tamkar ɗan wata 6, ta ce"uhum ba dole ba ai gaskiya malamin nan ya ceci rayuwata sannan kema ina ƙara miki godiya zan miki alkhairin da za ki daɗe kina mora, sannan ni wallahi asirin da aka yiwa Habibi ya fi kowanne asiri yi min daɗi, kin ga kuwa yadda yake ririta ni tamkar ƙwai rannan fa dana ce ya tafi gida ƙin tafiya ya yi, wallahi ya kwanta abinsa tuni kafin ya tashi na yi masa ferfesu me rai da lafiya".
Ƙara tafawa suka yi a karo na biyu, Billy ta ce"shegiyar ƙawata kin mallake har mutum biyu mallakinki da ma wanda ba mallakinki ba gaskiya kina wuta".
"Uhum ke dai bari Billy wallahi sai na koyawa Mero darasin rayuwa, har ni za ta bawa labarin mijinta jarumi ne kin ga kuwa ga shi yanzu yana gwada min jarumta ita ya yasar da ita tamkar wata bola".
Billy ta yi dariya sannan ta ce"yauwa kar fa a samu matsala BAYA TA HAIHU, Malam ta ce duk yadda za a yi kada a bari Mero ta haihu Habibu ya ga ɗan da ta haifa duk ma yadda za a yi ayi, amma fa kada a bari ya ga yaron ko yarinyar in har aka bari ya ga wannan ɗan to wallahi asirin ya bar jikinsa har abada kuma ba za ki ƙara cin galaba akansa..."

Tsawa Hafsah ta bugawa Billy, saboda idan akwai abin da ta tsana bai wuce ace za a raba ta da Habibu, saboda haka ta ce"yi shiru ka da ki ƙarasa nasan duk abin da zan shirya in sha Allah babu abin da zai faru ita da kanta ba za ta ga ɗan ba balle ubansa".


Tana faɗar hakan ta miƙe tsaye da kofin lemo a hannunta, tana wata irin dariya wacce kana jinta kasan tsantsar rashin imani ce.





***
Mrs green ce.


ONLINE CLASSES BY N&N HERBS 🌿 💃🏻💃🏻💃🏻
Shin kuna da labarin online classes mom noor collection taxo wa da mata abubuwa daxu koya su tsara da qafafunsu domin mata dayawa subar xaman bansa su do gara da kansu a kan kudi qalilan xata koyar da dukka wadannan abubuwan tare da bayanansu mataki mataki karku Bari wannan dama ta wuce ku xata fara gudanar da class dinta on Monday inshaallah xakuyi register Akan 1k only ga abubuwan da xata koyar 👇🏼
-turaren wuta 
-kabbasa spray
-humra 
-colecture
-room freshener 
-morning fresh
-moping mix
-man gashi 
-skin care products 
-skin care for the kids 
-snacks 
-drinks
-yogurt
@***
***