BIYU A ƊAYA

Chapter 32

by @barista

BIYU A ƊAYA 
    ( Don't judge a book by its cover)


Page 32
Sayyada barrister ***
YOTA 13 
The five ink legends


"I don't care who you  are, duk da haka ina gargaɗin ka..

Yana nuna masa yatsansa tare da girgiza kansa sannan ya ci gaba da cewa 

 "Don't interfere between and my wife"

Cewar Abraham yana ji kamar ya shaƙo wannan mutumin da take kira da Uncle.
Ran Dr Waahab ya matuƙar ɓaci, sai huci yake yi, ya rasa me yasa wannan saurayin yake shiga rayuwar Angel, ya fahimci sai ya nuna masa iyakar sa...

"How dare you talk to me like that?"

Ya faɗa masa, yana jinjina kai saboda ganin yadda wannan saurayin yana ji da ɗanyen kai, Angel ce ta matso kusa da shi ta sassauta murya ta ce 

"Uhm Abraham please ka tafi, kada ka janyo hankalin mutane kan mu"
 
"Babu ruwanki da tafiyata ko tsayuwata"

Cewar Abraham yana basarwa, yana kallon Uncle, da Angel bata wajen sai ya saɓa masa kamanni.

"Ya zama dole ka tafi"

Angel ta faɗa cikin tashin hankali don ta san halinsa yanzo sai ya tara musu mutane...

"Ya za ki ce na tafi? Ba ki ji me yake cewa bane, ni ne ma yake ce min me zan yi? To zai ga abin da zan yi"

DR Waahab ya sauke numfashi da ƙarfi, ya kalli Angel tare da cewa 

"Ki tafi"

"Kai waye da za ka ce ta tafi? To babu inda za ta je"

A hankali Angel ta tako zuwa gaban Dr Waahab ta sauke idanunta cikin nasa, tana kallon yadda idanunsa suka fara sauya kala cikin ƙanƙanin lokacin, muddin bata dakatar da wannan faɗan ba, abin zai koma babban.

"Uncle please"

Ta faɗa kamar ta yi kuka, ya kura mata idanu duk da fuskarta a rufe take amma yana hango tashin hankali a tare da ita, ya ɗan kawar da kansa bai ce komai ba, ta sake cewa 

"Ka koma cikin hotel"

"Ke ma ki tafi"

"Yanzu zan tafi"

Ta soma ja da baya, Abraham ya tare mata hanya tare da cewa

"Tare za mu tafi"

"A'a ba zan bika ba Abraham don ba tare muka zo ba"

"Haka ki ka ce? Okay ya yi, za ki ga me zai biyo baya"

Yana gama faɗin haka yaja jiki ya bar wajen..

Ta sauke ajiyar zuciya tare da hamdala cikin ranta, don ba karamin mara tausayi bane Abraham yanzu sai ya ciro wuƙa, ya ce zai daɓa masa...

"Angel"

Ta ji sauƙar muryar uncle a kunnenta, ta juyo cikin nutsuwa ta ce

"Na'am Uncle"

"Bana so na takure ki, bana so na dame ki da yawan tambayoyi, amma kuma ina son sanin menene alakarki da wannan saurayin?"

A hankali ta lumshe idanunta tana jin ɗaci cikin zuciyarta, bata son tuno wasu abubuwan, sam bata son magana akan rayuwarta...

"Shikenan na fahimta, anyway, mu bar maganar, ki koma restaurant kada Oganniyar ki ta neme ki, bye sai na shigo cin abinci"

Ta ji daɗin hakan, tana kallon Uncle har ya shige cikin hotel, ta juyo ta dawo bakin titi ta hau mashin ya kawo ta tumbin Giwa, ya sauke ta, ta biya shi kuɗin sa sannan ta shigo ciki ta tadda ana gagarumin yaƙi...

"Yau zan tada yaki da ba a taɓa tadawa a wannan gidan ba, ni za ayi wa rashin mutunci!"

Cewar Zee Dollers, Babayo me bakin sigari yana tsaye saga gefe, yana kallon yadda take kumfar baki, tun farko yake so ya tanka mata, amma yadda take zaginsu cikin jam'u yasa ransa ya ɓaci, ya tare mata numfashi wajen cewa

"To bala'atu, uwar masifa, a dai gyara harshe asan da waɗan da ake yi"

Aiko me neman kuka aka jefe shi da kashin shanu, Zee Dollers ta harzuka tayo inda yake tana zazzaga masa bala'i tana nuna sa da yatsa ta ce

"Don ubanka na kasa da kai ne ballantana ka kwashe, waye kai a kayan miya"

"Ruwa nake kin ga ina babu ni babu miyar"

"Ai sai ayi souce aci ba tare da an zuba masa ruwa ba"

"A ba yadda aka iya ba"

"To me bakin sigari ko dai kai ne ka ɗaukar min kuɗina?"

"Allah ya sauwaƙa ai ban kai haka talauci ba, ni Babayo Allah ya isa ban yafe ba, tsinanniya"

"Ai ko zaka ga tsinanci"

Ta ɗauko ƙaton dutse tayo kansa, Sadeebaby ta karɓa ta ajiye ta ce

"Haba Zee wannan zubda class ɗin da me ya yi kama, me yasa kike biyewa wannan sakaran"

Babayo ya juyo kan Sadeebaby tare da cewa 

"Shegiya uwar masu bleaching ke ce sakariya, ta biye min ɗin"

"Kul Babayo ka sanni ni ba ƙanwar lasa bace yanzu sai ba dirja bakin sigari"

Ya dire tare da cewa 

"Ki dirja mu gani, kun bi ku saka mutum a gaba to ni daku shege ka fasa"

Sadeebaby ta juyo kan Zee Dollers ta ce

"Friend kada ki damu, mu je ciki ki faɗa min nawa ne kuɗin"

"To na gode friend amma kai kam sai na ci maka mutunci koma yaushe ne"

Ta juya buguzum² ta shige ciki....

ANGEL da ƙyar ta samu hanya ta shige ɗaki ta cire niqabinta ta gyara jikinta, tana ƙoƙarin fitowa Abraham ya shigo, ta yi baya tana kare masa kallo, ya tako zuwa gare ta ya ce

"Waye wancan?"

"Wa kake nufi?"

"Kin fini sanin koma waye ne"

"Abraham bana son abin da kake yi min, me yasa za ka yi min haka?"

"Angel kin san ina son ki, kuma ina ƙaunar ki ba zan zuba ido wani ya kwace min ke ba"

"Mutunci ne a sakanina da shi, kuma ka saka a ranka babu aure a sakanin mu"

Ya daki garu da ƙarfi ta ji tsoro ta yi baya, a lokacin BINTA ta shigo tana cewa

"Waye yake ƙoƙarin rushe min ɗaki?"

Ta yi turus ganin Abraham ne, ta ja da baya don tsoro yake bata, akan Angel ya kusa yi mata duka, ta ce

"Ah Abraham kai ne ashe?"

Ya tako zuwa kusa da Angel ya ce

"Ba ki da miji sai ni"

Yana gama faɗin haka ya fice, Angel ta sauke ajiyar zuciya, ta kalli Aunty Binta ta ce

"Na gaji da abin da Abraham yake yi mani"

"Hakuri za ki yi Angel, kin san ba fasawa zai yi ba, tun da saura kaɗan ya mallake ki, ki amince...

"A'a Aunty Binta kin san waye shi, hakan ba zai yiwu ba"

"To naji yanzu ki yi sauri ki fice tun kan zance ya je kunnen Mamanki"

"To na gode Aunty Binta ga kayana ki ajiye min"

"To ba ki da matsala"

Angel ta fice da uniform na restaurant a jikinta, ta dawo har ta shigo bata hango ALAJA ba, sai da Majada ta iso ta ce

"Ƙawata how fah?"
 
"So far"

"Uhm ALAJA tana neman ki tun ɗazu"

Kirjin Bilqees ya buga, amma ta danne kada Majada ta fahimci hakan, ta ce

"Tana?"

"Ɗakinta"

Cewar Majada ta zauna kan kujera ta ɗauki wankakken carrot tana ci, Bilqees ta ce

"Bari na je na dawo"

"To"

Ta fito zuwa ɗakin ALAJA ta tadda tana waya don haka ta zauna har ta idar da wayar sannan ta ce

"Ke ina kika shiga ne ina ta duba ki?"

Bilqees da ƙyar ta haɗiye yawun da ya tsaya mata a maƙoshinta ta ce

"Ina nan fah Maa"

"Ba wani, ba inda ba a duba ki ba, ba ki nan"

"Ina toilet na baya"

"Duk toilet da muke da shi anan bai isa ba sai kin fita, to ki sani daga yau kada ki kuma irin haka"

"To Maa"

"Yawwa duba waɗan nan kiga abubuwan da za a gudanar ranar taron birthday party nki"

"To"

Ta karɓa ta gani, abubuwa masu sada Alaja ta rubuta za ayi, babban party ne da alama na gani na faɗa ne...


******************************

8:00 pm daidai Dr Waahab suka shigo restaurant kamar kullum, yau kam ya sha kyau sosai, sanye yake cikin ƙananan kaya sun a shi jikinsa. Kai tsaye dining da yake zama ya wuce ya zauna kamshin turaren jikin sa ya baɗe ko'ina, yana zaune aka shirya wa sauran ma'aikatan dinner yana tunanin Angel, bai idda ba ta iso ɗauke da madaidaicin tray ta ajiye masa tare da yi masa sannu da zuwa ya amsa cikin sakin fuska, ta zuba, ta zuba masa duk abin da zai buƙata sannan ta ce

"Yallaɓai likita akwai abin da zan kawo maka?"

Ya ɗago suna kallon juna, ya girgiza mata kansa alamar a'a, sannan ya ce

"Thanks"

"Ok zan koma ciki zan ƙarashe aiki na"

"To, ba damuwa na gode"

Ta jinjina kai, ta wuce don ƙarashe aikinta...

Dr Waahab a nutse ya kammala cin abincin sa, sai 9:00 pm suka bar restaurant ya dawo hotel, ya yi shirin kwanciya, a hankali ya lumshe idanunsa kamar me son yin bacci amma ya gagara yi, wasu abubuwa suke masa yawo akansa, tunanin Angel yake yi, yana jin wani abu game da ita, a duk lokacin da ya sauke idanunsa cikin nata yake jin nutsuwa, yana jin zuciyarsa na hasko mata hotonta.

A lokacin da ya gane Angel ita ce Bilqees sai yake jin farin ciki, yana jin abin da bai taɓa ji ba game da mace, shi yawan hira da mace ma bai dame shi ba, yawanci da Mamie ko Mommie yake hira, amma lokaci guda ya kanza akan Bilqees.

Ya ɗauko wayarsa ya shiga message ya hau kan number Angel ya yi typing 

 _Angel_

Ya ɗan ɗauki mintina sannan sako ya dawo ya duba yaga ta yi masa magana 

 _Yes Uncle, barka da dare_ 

Ya lumshe idanunsa na wani lokaci sannan ya buɗe ya tura mata 

 _Yawwa barka dai, i hope you are doing good_

 _Yeah Uncle, Alhamdulillah_

 _"Ma sha Allah bye"_ 

 _"Thanks bye"_

Ya ajiye wayar, bacci me daɗi ya sace shi..

****

Ta sauke numfashi a lokacin da suka yi sallama da Yallaɓai likita ta text message, ta ajiye wayar, ta lumshe idanunta tana jin farin ciki yau Uncle da kansa ya tura mata sako yake tambayar lafiyanta, duk da yasan ita ce Angel amma bai sauya mata ba, a tunanin ta zai guje ta, sai taga akasin haka, gaskiya shi mutum ne na daban. Tana wannan tunanin bacci ya yi awun gaba da ita...

WASHE GARI 

Da wuri Bilqees ta tashi ta idar da sallah sannan ta shige toilet ta shirya cikin uniform na restaurant, tana zaune Mamanta ta shigo da abin karyawa, don ta hana Bilqees girki ita ke yi, ta ce akwai gajiya a tare da ita, ta ajiye soyayyar doya ce haɗe da fulawa sai kuma shayi me haɗe da madara da milo, ta zuba a cup ta ajiye a gaban Bilqees...

"Mama"

Ta faɗa a hankali, ba tare da Mama ta dubeta ba ta ce

"Na'am Bilqees"

"Har yanzu kina fushi dani?"

"Eh"

Kai tsaye ta faɗa, Bilqees ta yi shiru ta ci gaba da cin abinci, ALAJA ta yaye labule tare da cewa 

"Wai baki shirya bane Angel?"

Mama ta haɗa rai ta ce

"Abinci take ci"

"To sai ta kammala mu tafi yau sauri nake yi"

"Maa barka da safiya"

"Yawwa Angel barka dai, ki yi sauri mu tafi"

"To"

Ta faɗa tana shan shayinta, mamanta ta numfasa ta ce

"Haba ALAJA ki bari mana ta karya a nutse wannan azalzalan ta yi yawa"

"To sai ta gama ke kam akwai ki da damuwa, ina acen ma za ta ci"

"Duk da haka dai ta karya ya fi"

"To nan da wani lokaci za ayi taron birthday party Angel, na kusa kammala shirye-shirye sai ki zauna a ready"

"A'a ku yi kayan ku babu ni a ciki"

"To ke kika sani wallahi Allah ya shirye ki Maman Bilqees"

"Amin ALAJA"

Bilqees ta kammala ci, ta saɓa jakarta a baya ta ce

"Mama na tafi"

"A dawo lafiya"

Suka fito da Alaja suka dawo restaurant, Bilqees ta wuce kitchen....

******************************
Bayan kwanaki 

Bilqees ta shiga cikin damuwa sosai, har bacci ma gagararta yake, Mama ta ƙi saukowa daga fushin da take yi da ita, ta bata hakuri taki hakura, sai ma fushi da ya ƙaru, kuma tasan duk tana yi ne saboda kare mutuncinta, hakan kuma ya shafi lafiyarta, ciwon kai Bilqees ke yi sosai, duk da tana shan magani amma abin sai karuwa yake yi, yau ma haka da kyar ta fito restaurant sai da zuwa yamma duk ta galabaita, hakan yasa ALAJA ta ce ta shiga ɗaki ta kwanta. Tana kwance har lokacin zuwan Uncle, bata fito ba, Dr Waahab ya shiga damuwar rashin ganinta har suka kammala suka dawo hotel yana tunaninta, bai ci abinci sosai ba, don baiyi masa daɗi ba, sam ba kamar na Angel ba. 

Haka suka dawo gida bata jin daɗi, bata faɗawa Mama ba, washegari suka sake fitowa restaurant still ba ita ce ta girka masa abinci ba, ya shiga damuwa ga shi ya rasa yadda zai yi ya ganta, kawai ya yanke shawarar zai je Tumbin Giwa dubota...

9:00 pm ya shirya cikin ƙananan kaya, yayi kyau sai ƙamshi yake yi, ya fito daga cikin hotel kai tsaye ya wuce Tumbin Giwa ya iso ya zauna ya kira layin Angel a kashe, ya tura mata sakon yana waje yana zaune a inda suke haɗuwa.

Shiru bata fito ba, har 9:30 pm, ya ɗan jingina da jikin ƙafe dake bayansa, ya lumshe idanunsa yana jiran nan da wasu mintina in bata fito ba sai ya koma...

"Yallaɓai likita"

A hankali ya buɗe idanunsa ya zuba mata su, zuciyarsa tayi sanyi take farin ciki ya mamaye sa, ya bi jikinta da kallo, first time da yazo Tumbin Giwa ba tare da ta saka niqabi ba, sai kuma first time da yaganta da personal dress.

Da uniform na restaurant yasanta, sanye take da doguwar riga ta abaya york tayi mata kyau sosai, ta yafa gyallenta...

"Sannu da zuwa Yallaɓai likita"

Ya gyara zamansa tare da cewa 

"Angel"

Ya sauke numfashi ya ce

"Yanzu nake shirin tafiya"

"Ban samu fitowa ba sai yanzu"

Ta faɗa a hankali, ya nuna mata wajen zama ta zauna, ya dubeta da kyau yaga ta ɗan faɗa, ya tambaye ta 

"Kwana biyu ba ki restaurant"

"Ina cika fah Yallaɓai"

"Shi ne ba za ki kawo min abinci ba?"

"Bana jin daɗi a lokacin ina kwance"

"Subhanallah, Allah ya sawwaƙa"

"Amin"

"Me yake damunki?"

"Uhm ciwon kai na"

"Sannu shi ne ba za ki yi min text message ba, shiru babu motsin ki"

Ta sudda kai ƙasa tana wasa da siraran yatsun hannunta jikinta ya yi sanyi, Yallaɓai ya burge ta, duk da yasan wacece ita amma bai guje mata ba, ta sauke ajiyar zuciya ta ce

"Da na dawo nake bacci"

"Ok ya kike jin ciwon kan"

Ya fara yi mata tambayoyi irin na kwararrun likitoci, ta numfasa ta ce

"Gefen kai na ne yake yi min ciwo amma yanzu da sauƙi"

"Stress ne"

Bata ce komai ba, sannan ya ce

"Ba ki cin abinci sosai shi yasa ki sa samu rashin kuzari"

"Ina ci fah"

Ya yi murmushi ya ce

"Ga shi ban zo da abin dubiya ba"

Ta sudda kai ƙasa ta ɗan yi murmushi, ya kalli dimple nata ya lotsa, a hankali ya kawar da kansa, yana mamaki akan yarinya duk ya sauya, ya mik'e tare da cewa 

"Mu je"

Ta kalle shi kamin ta yi magana, ya yi gaba, ta bi bayansa, a hankali suke takowa zuwa tukubar tsire, ya jido mata, ya saya mata kayan sanyi sannan suka dawo duk da bata so amma ganin baya son gaddama yasa ta yi shiru.

Ya zauna a kan dakalin, ya kalleta a lokacin 11:00 pm ya yi ya ce

"Ki shiga ki kwanta"

"Na gode Yallaɓai likita amma...

"Sai da safe"

Ta juya ta tafi yana kallonta ta shige ciki, ya sauke numfashi ya tashi ya tari mashin ya kawo sa hotel...

*******

A hankali Bilqees ta turo ƙofar ɗakinsu ta shigo, hannunta riƙe da lada, ta rasa yadda za tayi, duk ɗakunan gidan a rufe, da sai ta kyautar, ga shi waɗan da suke farfajiyar gidan duk sun bugu babu me motsi suna ta shan bacci, ta shigo ta rufe ƙofar a hankali tana takowa zuwa cikin ta ji muryar Mamanta

"Daga ina kike?"

A tsorace ta yi baya, ta ajiye leda, zuciyarta na bugawa ta ce

"Mama...

"Ba bayani na ce ki yi min ba, daga ina kike?"

"Waje"

Ta faɗa jikinta yana rawa, Mamanta daka mata tsawa tare da cewa 

"Waje wajen waye?"

"Mama..

"Kin san Allah Bilqees ina tambayar ki kina wani son yi min dogon bayani zan ɓata miki rai"

A hankali hawaye shar³ ya zobo mata, ta ce

"Wajen Yallaɓai likita?"

"Waye shi?"

"Mutumin da nake yi wa aiki a hotel"

"Me ya kawo shi"

"Yazo ya duba ni"

"Dalili"

"Bani da lafiya"

"Me yasa ba ki gaya min ba?"

"Tsoro naji don kada ki hanani"

"Ki fice min a ɗaki"

"Mama dare yayi..

"Na ce ki fice..

"Wai menene haka? Kin dame mu da hayaniya"

Cewar ALAJA a lokacin da ta shigo sanye da gajeren wando da vest sai hular bacci a kanta, gani faɗa take ake yi wa Angel yasa ta rike hannun tare da cewa 

"Menene haka?"

"Dole ta fice ta bar min ɗaki, tun da rayuwar da ta zaɓawa kanta kenan"

Cewar Maman Bilqees cikin ɓacin rai, Alaja ta ce

"Kamar yaya ta fice, ina za ta je?"

"Ta je duk in da take son zuwa"

Bilqees ta fashe da kuka ta zauna har ƙasa tana baiwa Mamanta hakuri amma ido rufe ta ƙi, haka ta kinkimo akwatin Bilqees ta fito mata da shi ta ce

"Ta tafi"

ALAJA ta ce

"Haba menene haka? Ya za ki ce ta tafi? Ina za ta je a wannan daren?"

"Ta koma in da ta fito, ba ni zata maida mara hankali ba"

ALAJA ta kama hannun Bilqees, ta riƙe jakarta, ta ce

"Mu je side nawa"

"Ta dawo ta ɗauki ledan da ta shigo da shi"

Ta dawo ta ɗauka, suka fito ɗakin ALAJA, suka zauna, sai kuka take yi ta ce

"Maa ki baiwa mamata hakuri"

"Ki shiga ciki ki kwanta, in taso sai na bata hakuri da safe"

"A'a Maa, yanzu"

"To ina zuwa"

ALAJA ta shigo ɗakin Maman Bilqees ta tadda ta rafka uban tagumi, ta zauna kusa da ita ta riƙe hannun tare da cewa 

"Me yasa za ki yi mata faɗa?"

"Ta ɓata min rai ne"

"Tsoro kike ji kada a ɓata ta?"

"Eh"

Dariya ALAJA tayi sosai ta ce

"Ke ba ki ɓata ta ba, kike tunanin wani zai ɓata ta"

Wani kallo Maman Bilqees ta yi wa ALAJA, sannan ta yi murmushi ta ce

"Ba ki da dama"

Murmushi ALAJA ta yi ta sake hannunta ta ce

"Gobe ki je ki yi bikonta"

Su ka yi dariya....







Har yanzu ina me ba ku hakuri akan rashin update aka akai, in sha Allahu komai zai yi kyau.


Ayi hakuri da typing errors




Comment and share fisabilillah