Page 2
by @ummuaffan
...FARAR TUMFAFIYA.
©UMMU AFFAN
Page *2*
Sannan DK na da wata ɗabi'a guda na kula mata sam hakan bai dame shi ba, ko kuma a ce ba sa gabansa ma, burin shi dai ya sami kuɗi da hanyar da zai bi don kuɗi su riƙa shugo masa, ba kuma don bai samun 'yan mata masu ƙaunarsa ba, ko lokacin da suke karatu a Usmanu Ɗanfodiyo University, mata yaran manya sun sha tarar Mansoor su faɗa masa suna so ya haɗasu soyayya da shi, amma idan ya masa magana sai ya ce,
"Don Allah ka rabu da su Mansoor, ni ba mata ne a gabana ba, karatu nazo nayi domin samun gobe mai kyau."
Ko da suka kammala karatun akwai wata yarinya da ta nace ita a dole sai Mansoor ya haɗata da DK, nacin ta ne ya saka shi yi masa magana, wannan karon ma ce masa ya yi.
"Me na sama yaci ballantana ya ba na ƙasa ne? Ni fa Mansoor idan ka ga nayi aure yanzu to na zamo wani ne a jihar nan ko kuma a duniya ne bakiɗaya, bazan ɓatawa kaina lokaci ba balle na ɓatawa wata ita ma, don Allah daga yau ba na so muna irin wannan maganar da kai, ka bar ni inji da abin da ya damalmale mini a rayuwata kawai!"
Ba wai baya shauƙi akan matan ba ne a'a, yafi so ya gina rayuwar shi kafin tunanin wata mace da tara 'ya'ya, don a cewarsa komi yana lissafinsa ne kuma daki-daki yake gudanar da komi. Tun daga ranar Mansoor bai ƙara masa maganar wata mace ba, don shima kusan halinsu guda ta nan fannin, duk da shi a yanzu iyayensa sun samo masa yarinyar abokin Daddynsa da ake so a haɗasu aure nan gaba kaɗan.
Sadauki na hawa babban titin ya fesar da iskar da ya cika bakinsa da ita yana wani huci, zama a irin unguwarsu ma sai mai haƙuri idan kai ɗan wanka ne da son gaye, don idan ka fito babban titin sai ka rantse da Allah ba haka layin da ya fito yake ba, yana cigaba da tunanin tafiyar da yake son yi zuwa China da yadda rayuwarsa a can zata kasance har ya ƙarasa unguwar su Mansoor *Sama Road* unguwa ce babba ta masu da shi, wacce manyan gidaje na alfarma da kyawawan tituna suka ƙara ƙawata kyawun unguwar, har wata iska mai daɗi da babu irinta a nasu unguwar yake ji na ratsa shi idan yazo nan ɗin sai yaji wata sabuwar natsuwa na ƙara shigar shi.
Gaban katafaren gate ɗin gidan ya buga hurn da ƙararrawar mashin ɗinsa, sai da ya yi kusan sau shidda sannan mai gadin nasu ya leƙo ta ƙaramar ƙofar gate ɗin.
"Ah Umariri Sadaukin mazaje ka ce kai ne ya tafe?"
Ya faɗa cikin hausarsu ta Sakkwatawa da murmushi a kan fuskarsa, kasancewar ba mai gadi kawai ba, duk wasu ma'aikatan da ke gidan sun san da matsayin Sadauki na aminin Mansoor don suna girmama shi kwatankwacin yadda suke wa ɗan mai gidansu.
Shima yakan ba kowa girmansa daidai gwargwado, sau tari idan baƙo yazo ya ga Sadauki a gidan zai ɗauka shi ɗan masu gida ne idan bai sani ba, saboda yanayin komi a gidan tamkar Mansoor haka Daddy da Mami suna ƙaunar duk mai ƙaunar ɗansu shi ya sa ma suke ji da Sadaukin, musamman ma shi da Mansoor kullum ba shi da magana sai tashi in har akan abokaine, ya ƙara shiga gidan yana ƙara yalwata fuskarsa da murmushi kaɗan, don dariya bata cikin ɗabi'unsa, yakan murmusa dai, shi ya sa da yawa a unguwarsu ake ganin kamar yana da girman kai, mafi akasirin sa'anninsa ma kallon da suke masa kenan, da ganin don suna abota da ɗan masu kuɗi shima ya ɗauka ya yafawa kansa salalar arziƙi bayan gaba da bayansa faƙiri ne shi, idan yaji ana wannan gulmar ya kan girgiza kai ko ya ɗanyi murmushi, shi wannan duk ba sa cikin abin da yake jin zai iya tsayawa ya mayar da hankali a kai, ba shi da ma wannan lokacin bayan na ganin ya tara abin da zai taimaki mahaifiyarsa da ƙannansa, yana son 'yan uwansa sosai.
Ɓangaren Mansoor da ke gidan ya nufa bayan ya ajiye mashin ɗinsa tun a harabar gidan wacce tsananin girma da faɗinta za ta iyacin motoci guda goma ko ma fi, yana tura ƙofar ya iske Mansoor zaune cikin ɗaya daga manyan kujerun da aka ƙayata madaidaicin parlourn nasa da su, zaman jiransa yake tun bayan da ya kira shi cewa yana tafe kuma akwai maganar da yake so su tattauna, yasan Sadauki baya kwansa sai da zakara, tunda har ya ce zasu tattauna yasan wani abu mai muhimmancin ne yake tafe da shi, yana ƙarasawa hannu ya ba shi suka tafa.
"Mutumina kana baza kala fa, irin wannan kyau haka!"
Mansoor ya ƙarashe maganar cike da zolaya yana kallonsa, dama mafi yawan lokuta Mutumina yake kiransa ko DK ɗin kai tsaye. Sadauki kuwa murmusawa ya yi tare da samun wuri ya zauna gefensa yana faɗin.
"Nasan yau kana fita aiki da wuri, shi ya sa na ce ka tsaya mu tattauna kafin ka fita, don ba na son zuwa office ɗinnan naka saboda ma'aikatan nan naku masu yiwa mutane wani kallo!"
"Kai dai ka ce matan ma'aikatanmu masu kallon ƙauna gare ka, kai kuma ba ka so."
Mansoor ya ƙara zolayarsa da alamun mutum ne shi mai son raha da barkwanci ba kamar aminin nasa ba. Sadauki ya fesar da huci tare da gyara zamansa da kyau ya ce,
"Mansoor maganar gaskiya nake maka, don Allah ka ɗauki maganar nan da muhimmanci ina son zuwa China ne."
"China!!"
Mansoor ya maimaita da sauti kafin ya dawo da duka hankalinsa ga Sadauki yana faɗin.
"Me zaka je yi a China DK? Idan na ce kasuwanci nasan ba ka wannan harkar, idan na ce aiki nasan ba ka taɓa neman aiki a cann ba, idan na ce yawon buɗe ido ban ga dalilin da zaka ce za ka je can ba?"
"Ka ce dai kasan ba ni da kuɗin da zani yawan buɗe ido ka bar wani kwane-kwane malam."
"To kusan hakan dai, amma dai yanzu ina jiran amsa daga gare ka."
Sadauki ya ƙure Mansoor da kallo kafin ya kuma cika baki da iska ya fesar da alamun yana son hakan duba da yadda yake yawan yi.
"Nasan ba zaka rasa sanin abin da ke tranding a 'yan kwanakin nan ba, na cewa da milliyan biyar za ka iya zuwa China tafiyarka wajen zamanka har ba da sana'a, ina son naje can ne Mansoor, aiki nake so na nema a can idan naje!"
Ya ƙarashe maganar yana sake cika iska a baki. Mansoor kuwa kallonsa yake sosai yana ƙara juya kalamansa a cikin ƙwaƙwalwarsa, ya Sadauki ke yin abu da ka haka sai ka ce wanda ba shi da ilmi. Kafin ya nisa ya ce,
"Shin kasan irin bizar da suke yiwa mutum? Abin da na sani idan bizar ziyara (tourist visa) ce, ba za ta ba ka damar zama na dindindin ko yin aiki a China ba. Idan bizar aiki ce, yawanci dole ne ka fara samun aikin da kamfani a China ɗin, idan ka samu ne har ka ke da irin wannan bizar, idan bizar karatu ce kuwa sai ka samu gurbin karatu sannan a bi sauran matakan, saboda haka, ina so ka sani naira miliyan 5 ba na da tabbacin cewa za ka samu damar zama a China. Idan wani ne ma ya tallata maka hakan, ya kamata ka yi taka-tsantsan, domin akwai masu damfara da ke amfani da irin waɗannan alkawura suna cutar mutane, duk da ina da yaƙinin kai ma ba zaka yarda da irin wannan shaɓuraton ɓangaron ba."
Sadauki da tunda Mansoor ya fara maganar fuskarsa ke gefe yana kallon wani wurin, amma duk abin da yake faɗa yana shiga kunnuwansa kuma duka hankalinsa na kansa, amma ba zaka taɓa lura da hakan ba saboda yadda ya tsurawa Tv da ke nuna wani Hausa film ido sai ka rantse da Allah kallon tv ɗin yake, amma ko ɗaya hankalinsa na ga maganganun da Mansoor yake, lokacin da ya kai aya ya juyo suka haɗa ido, sai kawai ya yi murmushi kaɗan ya miƙe tsaye.
"Ni zan wuce, ammaa ina so ka sani duk wata hanya da ta kamata zanbi domin ganin mafarkin nan nawa ya cika, zan yi fafutuka domin ganin tabbatuwarsa."
"Ni kuma a shawarce zan ce da ka haƙura da tafiyar nan DK, da ka je da kuɗin da ka faɗa wata ƙasar ai idan har kana da su gara ka gina kanka ka fara sana'a da su sai ka ga ka samu abin da ka ke so a gaba, zuwa ƙasar China ba naka ba ne yanzu domin ina guje maka sammakon bukukuwa wahalar can da nan ba ɗaya ba ne."
Sadauki ya taɓe baki yana kaɗa key ɗin mashin ɗinsa.
Tare da nufar hanyar fita bai sake duban inda Mansoor yake ba, da sauri kuwa ya fara kiran sunansa amma bai juyo ba, ko kafin ya shiga ciki ya ɗauki hula da takalmi tare da key ɗin motarsa har Sadauki ya ɗauki mashin ɗinsa ya bar gidan, duk da yasan idan yazo ya kan shiga ciki su gaisa da Mummy amma da alama yau kam bai leƙa ba, Mansoor ya fesar da huci mai zafi yana ganin kawai Sadauki yana son ɗaurawa kan sa dala da gwauron dutse ne, don haka shima mota kawai ya shige domin nufa wurin aikinsa da tunanin zuwa anjima idan ya huce zai kira shi domin su ƙara tattaunawa akan lamarin, ya kuma ƙara ba shi shawarar tafiyarsa ƙasar ba dubara ba ce ko kaɗan.
Sadauki kuwa yana tafe yana tunanin kawai Mansoor ya yi ma sa haka ne don yana ganin shi ne sama da shi a dukiya, idan ba haka ba yasan ko shi bai da kuɗin da zai ara masa mahaifinsa yana da su kuma idan ya yi magana tsaf yasan a kyauta ma zai iya ba shi, ballantana shi a matsayin bashi ma yake son kuɗin, sai dai kuma yasan idan bai samu a wurin Mansoor ɗin ba tafiyar tasa za ta zamo da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa. Yana saƙe-saƙen har ya kusan bige wani tsoho a hanya, da sauri ya tsaya yana ba shi haƙuri da cewa bai lura ba ne, tsohon ya amsa masa da babu komi ya yi tafiyarsa kawai, Sadauki ya koma kan babur ɗinsa yana sauke numfashi tare da jin daɗin da bai sami tsohon ba, da haka ya koma unguwarsu yana sake jan tsaki, ƙofar gidansu wata yarinya ke suyar dankalin hausa, ƙawar Maryam ƙanwarsa ce, tana ganinsa kuwa ta fara washe haƙora da karairaya ita wai nan a dole son shi take, ya daɗe da fahimtar hakan saboda yadda take nuna masa da aiko masa da abu da take, haka yana yawan ganinta wurin Maryam ko da ba ta nan tana zama gurin mahaifiyarsa, akwai ranar da ya taɓa tsintar hirar Inna da Maryamahn tana sanar da ita wai saboda shi Sadiya ta dawo suyar dankalinta ƙofar gidan nan don kawai tana ganinsa, har cewa take tana matuƙar ƙaunar shi kuma duk masu nuna suna sonta cewa take tana da miji a hannu kuma ba kowa take yiwa wannan ganin ba sai shi Sadauki, a ranar ya sha takaici kuma abin ya ba shi dariya kaɗan ya kuma ga wautarta na wannan tunanin don shi ko giwar wake yasha ba zai iya soyayya da Sadiya ba, duk da masu iya magana na cewa iya ruwa kuma iya tsaki, haka ko wacce kwarya da abokin burminta, idan auren zai yi a matsayi irin na iyayensa Sadiya ce daidai karfinsu da shi kansa, sai dai bai taɓa kallon talaucinsu a wani rauni ba, musamman duba da yadda yaran manya suka yi ta ƙaunarsa tun suna makaranta, sai yake ganin an wuce wannan ƙadamin a yanzu na cewa kwarya tabi kwarya, a faɗarsa, ba lallai ba ne dole sai kwarya tabi kwarya, sai dai idan ba tayi niyyar bin akushin ba.
"Sannu da zuwa Yaya Umar." Muryar Sadiya cike da azarɓaɓi da ƙauyanci ta doki kunnuwansa, don shi duk macen da ke local unguwa irin wannan, bai mata kallon wata mace mai wayewa duk da akwai wayayyun, sai dai rawanin tsiyar da ya ɗaurawa kansa musamman ganin yana da kyau sai yake ganin kamar yafi ƙarfin hakan, bai amsa ba ko kallon inda take ma bai yi ba ya gungura babur ɗinsa zuwa ciki, baki galala tabi shi da kallo cike da tsananin ƙaunarsa, wani matashin saurayi da yake miƙa mata kuɗin Dankalin da ya saya ya ce,
"Oh ni Allah! Sadiya ko kin yafe mini kuɗin dankalin ne nayi gaba?"
Da sauri ta juyo tana ɗan murmushi ta amshi kuɗin, bayan ya wuce ta kuma kallon hanyar da Sadauki ya shiga ciki ta saki numfashi a hankali, wasu hawaye suka gangaro mata tayi saurin sharewa tana ɗan girgiza kai.
Ummul Salama ce za ta wuce ciki da sauri ta kira sunanta, kusa da ita ta tsaya tana cewa, "Ya akayi ne Sadiya?"
Leda ta ɗauka ta zuba Dankali zai yi na ɗari uku ta miƙawa Ummul Salama, ta ce, "Ummul idan kin shiga ki bai wa Yaya Umar!" Ummul ta kalli ledar ta kuma kalli Sadiya ta ce, "Sadiya da kin bar dankalinki, don idan dai Yaya Sadauki ne ba ci yake ba, a ƙarshe mu yake ba muci, kin ga gara ki sayar da abinki kar kiyi asara!"
"Haba Ummul, don na ba shi shi kuma ya ba ku shine zan yi asara? Wannan maganar da ki ka yi bai dace gaskiya kuma ban ji daɗinta ba." Ummul ta amshi ledar a zuciyarta tana tausayawa Sadiya da wannan ƙoshin wahalar da ta ɗaurawa kan ta. Ko da Ummul ta shiga gidan ɗakinsa da ke farkon shiga ta leƙa, yana tsaye ya kasa zama ta iske shi sai kaiwa da komowa yake, sallama ɗauke a bakinta, sai da ya amsa mata ta ce,
"Yaya!" Ya ɗago ya kalle ta fuskar nan ta shi a haɗe, ganin haka tasan yau kam Sadaukin a Sadaukin nasa yake sai ta ɗanyi murmushi ta gaishe shi, ya amsa ba yabo ba fallasa ta fara ƙoƙarin ajiye ledar a ɗan madaidaicin benji mai faɗi da ya ajiye kusa da madobin da ya buga a bango daga ƙasa, anan yake ajiye turarukansa da su kum da sabulin wankansa da mai.
"Mene ne a nan?" Ya faɗa yana kallon ledar ransa a ɓace, cikin inda-inda ta fara cewa.
"Da...dam...man.. Sadiya ce ta ce in ka...!"
"Ɗauke abin ta ki mayar mata."
Ya faɗa cikin daka tsawa, da sauri kuwa ta suri ledar ta fice daga ɗakin, shi kuwa tana fita ya rufe ƙofar ruf yana jan tsaki ƙasa-ƙasa, yana cikin damuwa da neman mafita za ta wani zo ta ƙara masa wata. Haka ya dunga zagaye ɗakin cike da tunanin hanyar da zai samo mafitarsa, domin yadda ya kwallafa rai da zuwa China, hangowa yake tamkar matuƙar yaje to matsalarsa ce za ta zo ƙarshe.
Ummul na fita ba tayi waje ba, sai ta shige cikin gida, ta sani daman idan Sadiya ta aiko ta ko ta aiko Maryam baya amsa sai ya ce suje gida suci, bai taɓa cewa a mayar mata ba sai ranar, hakan ya ƙara tabbatar mata da gaskiya Yayan nasu yana cikin damuwa. Sanar da Inna komi tayi wacce cikin damuwa ta miƙe zuwa ɗakinsa, amma sai ta iske ƙofar rufe, tana turawa ta saki duk da ta ga mashin ɗin nasa a gida sai ta ɗauka ko fita ya yi ƙofar gida, hakan ya sa ba tare da ta buga ba ta koma ciki, cike da tausayin halin da yake ciki ta koma ciki. Innaa tana ƙaunar Sadauki sosai, kullum burinta ya samu rayuwa mai inganci ne.
Barirah.
Jiki a sanyaye ta ajiye ƙaton zanin gadon da take wankewa, ta samu guri gefe ta zauna tana sauke numfashi, yau tun safe ta tashi da wankin mutanen gidan, wanda Andi ta tarkato mata na 'ya'yanta duka, Yaya Aliyu Yaya Usman, na Faruk har da Saudatu wacce suke sa'o'in juna, ga shi kayan mazan babu daɗin wanki kasancewar yadda jeans suka yi yawa musamman kayan Yaya Aliyu da yawanci suturarsa sune, tun da safe ganin rana ta fara fitowa Andi ta ce tayi wankin a yau tunda da alama za a yi rana sosai, tunda yanayi ne na damuna kusan kullum a satin ana samun ruwa sama yau ne dai aka zuba rana mai zafi kuma da alamar zuwa yamma za ta iya zubda ruwa. Wajen sha biyu na rana ta gama wankin, don ta riga ta saba da wankinsu tun tana shekaru goma a duniya, shi ya sa yanzu da take shekaru na sha shidda ta riga da ta saba kuma ta iya, sai dai a kullum idan ance za tayi wanki sabo yake zo mata, don a kaf aiki babu abin da ta tsana sama da wanki ko don kayan maza sun fi yawa ne oho, ga shi wandunansu masu kauri ne da ake wankewa da ƙyar.
Ganin ta gama wankin sha biyu na rana shi ne fa ta walgo mata zanin gadon tana faɗin shima ta wanke shi, tun da suna da ruwa gidan bohul ne sai dai ta kunna ta zuba son ranta, ta zuba tagumi tuna yadda ta wulgo mata zanin a jiki.
"Ga shi nan ki wanke shima, don idan ba wankin ba baki da wani amfani a gidan nan, ni dai bazan aike ki ba ballantana ki jazamin asara a banza a wofi ba, ba kuma zan baki abuna ki riƙe ba balle ya lalace, baƙin hali mugun abin iyayenki na bibiyar taki rayuwar, wallahi Allah wadaran naka ya lalace." Barirah ta share hawayen da ke sakko mata ta dubi ƙaton zanin gadon da ta rasa yadda za tayi tashi ta iya wanke shi, duk wankin da take yiwa Andi ba ta taɓa ba ta zanin gadon nan ba, wankin sa ake kaiwa, ba ta san me ya sa yau ɗin ta bata ba duk da sanin yafi ƙarfinta sosai.
Ɗaga kanta da zatayi kawai ta ga wata tsuntsuwa ta zuba mata idanuwa, ta kalli tsuntsuwar sau ɗaya ta kauda kai, sai taji a jikinta kamar tsuntsuwar nan fa kallonta take yi kuma ba ta wuce ba, hakan ya sa ta ƙara kallon wurin da sauri, ai kuwa tsuntsuwar tana nan kuma ita take kallo, da fari taji gabanta ya faɗi tsoro ya shiga sassan jikinta, sai kuma yadda ita ma ta ƙure tsuntsuwar da kallo sai taji tsoronta na ta raguwa.
"Barirah! Barirah!!"
Ta ɗago a furgice jin yadda aka kirata da sauti. Iyah ta girgiza kai ta ce, "Me ki ke kallo haka ina ta kira baki ji ni ba?"
Da sauri ta kalli tsuntsuwar, har lokacin tana nan, kuma ba ta daina kallonta ba, Iyah ta kalli inda take duba ta kalle ta, inda ita ma Barirah ta dawo da kallonta ga Iyah.
"Barirah lafiyarki kuwa? Me ki ke kallo haka?"
Wannan tambayar da Iyah tayi ya tabbatar mata ita kaɗaice ke ganin tsuntsumar ba tare da Iyah ba, sai ta miƙe tana cewa, "Na gaji ne na zauna ina hutawa, bari na ƙarasa." Ta koma kusa da inda take wankin, Iyah ta girgiza kai ta ce,
"Wannan zanin gadon ma ke ce ke wankewa?"
"Eh."
Ta amsa mata a takaice, sai Iyah ta girgiza kai tare da ƙarasawa ciki don ta fita ne da safe dawowarta gidan kenan. Tana jin Iyah nayi wa Andi magana akan Barirah ba zata iya wanke waccen zanin gadon ba, ya mata nauyi, amma Andi ta saki baki tana ta masifa har da cewa Iyah wai ina ruwanta? Ko ta mance Kawu Balarabe ya ce, kar ta kuma saka baki akan duk wani abu da ya shafi Barirah ne? Haka Iyah ta wuce ɗakinta amma Andi ba ta daina mita da masifa ba, tazo kuma ta ja wa Barirah kunne akan tayi azamar kammala wankin nan kafin a fito sallar ƙarfe biyu, idan ba haka ba kuwa jikinta ne zai faɗa mata....
***
Ina masu buƙatar kyawawan atamfofi da lace, mayafai, shoes and bag. Tare da kyawawan kayan kitchen na 'yan gayu masu kwaliti, zaku iya tuntuɓar ASHNURR COLLECTION wacce ke Kano kwari market domin ƙarin bayani ku tuntuɓeta a lambar waya kamar haka *** Tana aika kayanta ko ina a cikin aminci.
Shin kuna da labarin AK ASHKAD COLLECTION to ku matso kusa ku ji, ita ce wacce take kawo muku kyawawan abayas na gani a faɗa na shiga ko wanne guri kai tsaye, haka tana kawo muku kitchenwares masu kyau da aminci cikin farashi mai rahusa zaku iya tuntuɓarta a 070444564938 ko *** shafinta na Instagram ashkad_collection adireshinta Daura, Katsina State tana aika kayanta ko ina cikin aminci.
Kuna da labarin UmmuAffan GHT Supplement, tana sayar da Supplement na kamfanin ght masu kyau da inganci tana garin Kaduna tana aika kayanta duk inda kuke a faɗin ƙasar nan dama wajen ƙasar nan, kai tsaye kuyi mata magana ta lambar waya kamar haka *** sayen na gari mai da kuɗi gida, sai kunzo.