INUWAR KADDARA 🖤

THE FEAR 😳

by @meelahbazata978

INUWAR ƘADDARA 🖤

Book 1

Page 5✍️

Meelah Bazata


Kawu Manu dai yana nan ƙasa, ya kasa tashi daga inda yake kwance, duk da ƙoƙarin da yake yi na motsa jikinsa, amma hakan ya gagara saboda azabar raɗaɗin cizon Karen da kuma faɗuwar da ya yi, ga fitsarin da ya sake a wandon sa. Kunya har ta yi masa yawa, a zuciyarsa yake ƙara tsinewa Madugu da ɗebe masa albarka.

A gefe kuwa, tun da Rooman ta yi wa Rocky magana, ya ja gefe yana ta zaro harshe. Leenah kuwa, wacce ta yar da jakarta ƙasa, take ta faman rusa uban kuka, ta ƙarasa. Rocky zai biyo ta, tace ya tsaya a gurin, ita kuwa Leenah kuka take sosai, jikinta na rawa, ta runtse idanuwanta tana ganin kamar ita ma Rocky zai cinye ta. Cikin kuka take faɗin:

“Rooman, wallahi ni tsoro nake ji! Ki ɓoye ni don Allah, kada ya cinye ni!!” Leenah ta faɗa cikin kuka da tsoro tana nuna Rocky da yatsa, kuma idanunta a rufe.

Rooman ta juyo ta kalle ta, sannan ta dubi Rocky wanda yake ta zazzaro harshensa kamar bai san abin da yake faruwa ba.

“Ke dai Leenah, kin cika tsoro wallahi. Me ya sa kike tsoron Rocky ne haka? Ai kin san ba ya yi wa mutum komai sai Yaya ya sa shi. Ba ki ga bai yi mini komai ba?”

“Ni dai ki ɓoye ni! Ni fa bai san ni ba, cinye ni zai yi. Yanzu ki duba yadda ya yi wa Kawu Manu! Wallahi tsoro nake ji!”

Rooman ta yi shiru na ɗan lokaci, sannan ta juya ta kalli Kawu Manu wanda yake ƙoƙarin tashi, amma ya kasa. Ta san tabbas abinda ya sa Yaya ya yi masa haka saboda abinda ya yi musu jiya ne. To, wa ya gaya masa? Ko da yake ta san halinsa, dole ma ya sani.

“Kawu, kana lafiya?”

Kawu Manu ya ɗago kansa da ƙyar. Ganin Rooman ya sa shi jin kunya, domin shi bai san ma wanda ya taimake shi ba. Abu ɗaya ya sani, sai dai kila Rooman din ce, domin idan ba ita ba ko Ammah, to babu wanda ya isa ya dakatar da hukuncin Madugu, musamman saboda yadda yake cikin fitsari kace-kace. Amma da yake ɗan duniya ne, sai ya sake zafga mata harara yana nishi.

“Ke ce dama kika hana wannan azzalumin karen ya kashe ni?” ya tambaya cikin fushi.

“Kawu, Rocky ba ya tsallake umarnin Yaya. Ni dai ban san abin da ya faru tsakaninku da Yaya ba, amma na san ba zai yi wannan abin ba haka kawai.”

“Kaji shegiya mara mutunci, kina goyon bayansa kenan? Dama bakin ku ɗaya-ɗaya ai, shegu marasa tarbiyya,yayan tsiya” ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa, amma ya kasa.

Rooman ba ta amsa masa ba, ta kama hannun Leenah, ta juya za ta tafi.

Har ta juya za ta tafi sai ta tsaya ta kalli Kawu Manu, tace:

“Kawu, idan kana son zaman lafiya,da Kuma tsira da lafiyar  ka daina tsoma baki a cikin rayuwar Ammah, Ammah ba ta taɓa maka komai ba, ko rayuwar da Yaya yake yi, ita ma ba a daɗin ta ba. Yaya ba ya son a taɓa ta, kuma kowa a gidan nan ya san da haka. Idan ba ka ji ba, ba ku fara da Yaya ba, domin ba zai ƙyale ba.”

Ta ƙarasa maganar sannan ta wuce tare da Leenah, Rocky yana biye da su.

Rooman da Leenah suka bar Kawu Manu a kwance a tsakiyar layi, inda yake ta faman ƙoƙarin motsa jikinsa duk da zafin da yake ji. Tsoro da kunya sun haɗu sun hana shi ko ɗaga kansa sosai, ga shi mutane har sun fara taruwa. Wasu daga nesa suke kallonsa, yayin da wasu waɗanda ba su hango Madugu a ƙofar gida ba suka fara matsawa gurin Kawu Manu.

Su kuwa su Rooman, ba su tsaya ba. Rooman na tafiya cikin nutsuwa, kamar babu abin da ya faru, amma Leenah kuwa kuka take yi a hankali, hannunta na riƙe da jakarta da ta ɗauko daga ƙasa.

Suna tafiya tana rusa kuka kamar an zane ta, kuma ga shi tace ba za ta tafi ba. Rooman tace dole su tafi tare, in ba haka ba sai ta kira mata Yaya. Ga azabar fitsari da take ji kamar zai zubo, kuma ba za ta iya jerawa tare da Rooman ba, sai dai ta bi ta a baya saboda Rocky.

A can kuwa, Madugu yana tsaye a bakin gate ɗin gidan, hannayensa a cikin aljihun wandonsa, fuskar nan tasa babu alamun tausayi bare fara'a. Duk abinda yake faruwa tsakanin Rooman da Kawu Manu yana kallo. Bai ji daɗin da Rooman ta zo a lokacin ba, ya so ace Rocky ya yi masa ƙace-ƙace.

“Jagwa!”

Ya kira ɗan nasa, saboda kiran da ya yi masa a waya, saboda akwai saƙon da zai ba shi, shi ya sa.

“Na’am, Mahadi nai dogon zamani!”

Jagwa ya faɗa yana sunkuyar da kai.

“Ka je ka ɗauki wancan mutumin, ya bi ku, ku ɗakko kayan nan gaba ɗaya. In kuma ya tsaya bata lokaci, a yi masa sabuwar kaciya, sannan a yi masa uku-uku a fuska.”

“An gama, Mahadi, amma akwai wani abu da nake son sanar da kai.”

Madugu ya juyo a hankali. Idanunsa suna tsaye kan Jagwa cikin kallon sa na ko yaushe, da yanayi na kosawa yace:

“Me kuma ya faru?”

Jagwa ya ɗan yi shiru kafin ya amsa.

“Mai gida, mutumin da muka ce maka yana ta yawo a wajenmu tun jiya, an sake ganinsa a kusa da tsohon compound ɗinmu.”

“Har yanzu bai fahimci cewa ba a yawo a gonar Madugu haka kawai ba? Yana ina mutumin, kuma waye shi?”

“Mun yi ƙoƙarin bin sa, Madugu, amma ya ware kafin mu isa gare shi.”

“Ku kuma, da yake ba ku da amfani, kuka bari har ya wuce? Yanzu ɗan ubanka da kake gaya mini, me zan yi? Iyeehhhh!”

Jagwa ya sunkuyar da kansa ƙasa yana faɗin:

“A salance haka, Madugu.”

“Ka ajiye wannan haƙurin naka. Ni ba na cin sa ai. Idan na ba ku aiki, ina so ku dawo mini da sakamako, ba labarin yadda kuka kasa ba.”

Ya gyara agogon hannunsa, sannan ya kalli Jagwa kai tsaye.

“Daga yau, duk wanda kuka ga yana yawo a yankinmu, ku fara gano dalilin zuwansa. Ba na son hayaniya, ba na son rikici, amma ba zan bari wani ya zo ya yi bincike a kan rayuwata ba tare da na san dalilinsa ba.”

“Sai me ka sha, Mai gida.”

Ya faɗa yana ɗaga hannu sama yana yi wa Madugu kirari, sannan ya juya ya bar gurin.

Jagwa ya yi saurin barin wurin.

Su kuwa su Rooman a lokacin suna shirin ƙaraso wa gurin. Ita Leenah ba ta ga Sayyid ba, shi kuma tun daga nesa yake hangonsu. A zuciyarsa har sai ta safa take ganin yarinyar yadda take ta kuka kamar yarinya 'yar shekara biyar. Wai uban me aka mata ma? Ya tambayi kansa, fuskar sa na sake cika da takaici. A zuciyarsa yake faɗin, anya yarinyar nan ba mahaukaciya ba ce kuwa?

Ita kuwa har lokacin ba ta daina kuka ba. Sosai take kuka tana yarfe hannu, kuma har yanzu ba ta yi shiru ba, da alama tana da surutu gaskiya.

“Rooman, wallahi ni tsoron wannan kare nake ji, wayyo Maama!”

Rooman ta juyo ta kalle ta, dariya na ƙwace mata. Ita wallahi Leenah dariya take ba ta, tsoronta ya yi yawa. Tace:

“Wallahi in ba ki yi mini shiru ba, yanzu sai na haɗa ki da Rocky ɗin, mu ga ta tsiya.”

Ai da sauri Leenah ta girgiza kai, tana riƙe bakinta tare da share hawayenta.

Sosai Rooman ta yi dariya. Ta san tsoron da Leenah ke yi wa Rocky, musamman idan yana tare da Madugu. Kuma ta san ba Rocky kaɗai ne ke tsorata Leenah ba, Madugu ne babban dalilin tsoronta.

Ba da daɗewa ba suka iso bakin ƙofar gidansu. Rooman ta ɗaga kai, tana kallon yayan nata yadda ya daure fuska yana harararta.

Ta san laifinta, hakan ya sa ta sunkuyar da kai ƙasa ba tare da tace komai ba.

Leenah kuwa dama kanta a ƙasa yake, ba ta ganin gabanta, domin ba ta son ta ɗaga idanu bare ta ga Rocky. Ganin Rooman ta tsaya ne ya sa ta ɗan ɗago fuskarta wacce ta yi ƙace-ƙace da hawaye.

Tana ganinsa, ta tsaya cak, tare da ɗora hannu a kai ta runtse idanu, jikinta na wani irin rawa. Fitsarin da take matsewa take ya ƙwace mata, duk da tana ƙoƙarin danne kukan da har yanzu yake son ƙwace mata, amma inaa! Hakan bai yiwu ba, sai da ta yi ihun nan tana faɗin:

“Wayyoooo Allah! Maama, ki ɓoye ni!”

Madugu wani irin kallo yake mata na, anya wannan tana da lafiya kuwa? Wani takaici da ya ƙara kama zuciyarsa, shi ne yake kamar ya yi mata shegen duka, sai dai yana jin ko marinta ya yi, za ta iya mutuwa. Kallon Rooman ya yi yace:

“Wannan yarinyar ba mahaukaciya ba ce?”

Ya yi maganar tasa ne a taƙaice, muryarsa ƙasa-ƙasa, duk da ransa a ɓace yake.

Rooman ta kalli fuskarsa, tace:

“Yaya, wallahi ba mahaukaciya ba ce, tsoro take ji, shi ya sa.”

“Lallai na gani.”

Ya faɗa yana waigawa zuwa ga Leenah ɗin, yadda har zuwa lokacin jikinta yana rawa, fitsari ya wanke mata jiki.

“An taɓa karya ki?”

Tamkar saukar aradu Leenah ta tsinkayi muryarsa. Girgiza kai take da sauri ba tare da sanin ma tana hakan ba.

“A'a... Ya... Ya...”

ji yake kamar ya balla ta, sai dai kallon ta yake, domin ko hannunta ya riƙe, take za ta balle ai.

“Kin san abin da na ce miki tun da farko?”

Leenah ta sake girgiza kai, tana tuna gargaɗinsa, kuma ba ta son ya sake yi mata magana saboda muryarsa tsoro take ba ta.

Rooman tana kallonsu, ganin yadda Leenah ta firgita sosai. Ba ta san yaushe Leenah za ta daina tsoron Madugu ba. Ta matsa kusa da ita ta riƙe ta. Leenah dama jiran inda za ta jingina take, domin jikinta yana gab da gaza ɗaukar ta.

Aikuwa jin Rooman ta riƙe ta ya sa ta ƙankame Rooman ɗin, jikinta na sake ɗaukar rawa, har wani zazzabi ne yake shigar ta.

Ya mayar da idanunsa kan Rooman yace mata:

“Sake ta ki shige gida.”

Rooman ta san wannan yanayin nasa. Magana ɗaya yake yi, idan ya yi magana haka, ba ya son a katsesa ko kuma a yi masa musu.

Ba don ranta ya so ba ta saki Leenah ta shige gida, jikinta a sanyaye.