1&2
by @autaralheri
🌊*NAMIJIN IZZAH*🌊
Very hot love romantic story 🌹
Writer By
Autar alheri✍️
🎷🎷🎷🎷🎷🎷
🎷🎷🎷🎷🎷
🎷🎷🎷🎷
🎷🎷🎷
🎷🎷
🎷
Marubuciyar 👇
MIJIN KILAKI
MEJOR NAJEEB
ME & MY LION
AHALIN HARIJAI
AL'AJABIN MASARAUTA
AND OTHER'S 💃💃
Bismillahirahamanirrahim.
Book 1
Page 1&2
"Ƙaramar yarinyace ke kwantace bakin tabkin ruwa tanata murƙususu cikin azabar ciwon dake damunta, sosai take kuka tana ƴarfa hannunta, cikin muryar kuka wata matashiyar budurwa dake gefenta ke faɗar "Kiyi haƙuri khairiya kitashi muje gidanmu inna tabaki magani kinji. Shiru bata amsa mataba illa kukanta kawai datakeyi. Sunjima a wurin kafin tamiƙe wannan budurwar na riƙe da ita, suka ƙarasa bakin rafin ɗibar ruwan sukayi, ita budurwar ta ɗauki na khairiya kana tariƙa hannunta suka nufi gidansu wannan budurwar, sunyi tafiya menisa kafin su isa kasan cewar khairiya da ƙyar take iya tafiya, bayan sunje inna ta tarbesu tana cewa "subahanallah shafa'u miyasimi khairiya ɗin kuma? "Wlh bansaniba inna kawai tana nuna cikinta ne tana kuka. "Innalillahi khairiya cikinki ne ke ciwo? Kai taɗagawa Inna batareda tace komaiba domin bazata iya maganar ba.
Ganin hakan yasa bata ƙara cewa komaiba tace ta ɗauko wata ƙwarya ta haɗa maganin gayayyaki tazo tabawa khairiya tasha tana ɓata baki tana ƙarawa. Bayan tagama sha talafe nan ajikin inna bacci yayi awun gaba da ita. Ajiyar shafa'u ta sauke domin taci kuka harta gode Allah kamar itace me coyon, ganin khairiya tayi bacci, cikin mutuwar jiki tamiƙe tana cewa innarta, "inna zankoma rafi na ɗauko nawa tulun. "To shikenan shafa'u sekin dawo. Daga hakan ta fice daga gidan, taɗauko ruwan ta dawo khairiya bata farkaba, seda tayi bacci kusan na awa, uku kafin ta farka kuma cikin ikon Allah da buwayarsa ciyon yaragu sosai. "Khairiya sannu kinji ya jikin naki yanzu da sauƙi? Kai taɗaga kafin tabuɗe baki cikin wani irin sexy voice tace "dasauƙi inna zanje gida. "To shikenan tashi kuje shafa'u tarakaki nasan yanzu haka tanin nacan na duban inda zata ganki. Bata ƙara cewa komaiba tamiƙe shafa'u ta ɗaukar mata ruwan kamar farko suka kama hanyar gidansu, gaban shafa'u se faɗuwa yakeyi amma ita kam khairiya ko ajikinta.
Har suka ƙarasa gidan sedai abinda shafa'u kejiwa tsoro shine yafaru, domin kuwa tun asoron gidan sukejin muryar tanin tana surfa bala'i tamkar zata ari baki. Atake idon shafa'u yacika tab da kwallah tana kallon khairiya amma taga babu inda tadamu da idan dasabo tasaba da halin wannan masifaffiyar matar meji da bala'i tamker wutar habo'habo. Hakan sukayi ƙalular shiga ciki aiko suna shiga tayo kan khairiya da duka tana bala'i ta uwa ta uba, ihu shafa'u tasaka tareda riƙe khairiya tana kare dukan da tanin kekawo mata, hakan yasa ta haɗasu duka tana dukan cikin masifa take faɗar "nizaki renawa hankali shekiya renon makirai, naturaki tun ɗazu ɗebo ruwa kije kiyi zamanki seyanzu zaki dawo dan ubanki, to sauran aikin wa kika Barwa yayi miki? Nace wakika barwa munafuka? Wlh yau sekin faɗamin ranar dana koma abokiyar wasarki, da har zaki shanyani inajiranki sekace kayan wanki munufukar banza me baƙar anniya, haka taketa banbaki tana dukansu, amma khairiya ko gizau batayiba balle tagujewa dukan. Dama haka takeyi aduk lokacinda taso dukanta, to harta gaji tabari bata guduwa sedai takasheta. Itakam shafa'u taso ta gudu amma ganin yadda ake dukan ƙawar tata yasa takasa tafiya illa kukanta kawai datakeyi har seda tagaji dan kanta tabarsu tanata famar haki.
Abin mamaki kuma duk wannan uban dukan datakeyiwa khairiya mlm sani yana gefe zaune yana kallonsu yana kukan zuci amma yakasa koda kotsi balle yayi yunƙurin hanata har seda tagaji dan kanta tabarsu.
Uwar ɗaka tashiga tana masifa takwaso kayan wanki se uban wari sukeyi ta watsama khairiya, tana faɗar "indai dan wannan ne kikaƙi dawo gida da wuri, to wlh baki tsiraba dekinyishi kozaki mutu agidan nan kuma wlh awa ɗaya na baki idan baki gamaba zamu haɗu dakene, taƙarasa zancen tana jefo mata ledar omo viva ɗaya, tareda juyawa tana kallon shafa'u dake tattara kayan danta taya khairiyar wankewa, tace "ke dan uwarki lantana kibar gidan nan kafi nayi watandarki na aikawa uwarki naman, tafaɗa tanayowa kan shafa'u, aiko ta kwasa aguje tana kuka tafice daga gidan.
Komawa tayi ta zauna tanata famar surfa bala'i tanacin gwaɗa, ita kuwa khairiya ta tattara kayan wankin tafara wankewa, bancin uwar yunwar dake cinta domin har hanjin sun ƙulle, gakuma ciyon ciki tanaji har yanzu yana nata kaɗan kaɗan, kana ga azabar dukan dataci. Kallon yawan uban kayan da tanin ta ajiye mata tayi, kana ta kalli ledar omon ɗaya data bata, batace komaiba kawai ta ɗauka tafara wankin cikin ƙunar rai.
Tanin nagefe tana kallonta tana bala'i tana cikin gwaɗarta, hakan har wata matashiyar budurwa ta shigo gidan taci uwar kwalliya irinta mutanen ƙauyen tasha janbaki da ja gira, sedai dagani ta girmi khairiya nesa ba kusaba, tanin naganinta ta washe baki tana faɗar "oyoyo da kutan biki oyoyo da ƴar albarka, harkin dawone? Ahh lallai yau abin beyi tsayiba kenan? Hala bakije gidan amaryarba jamila? Zama tayi tana yatsina fuska kafin tace "washhh nagaji wlh inna tani, kuma yunwa nakeji. "Au aigajiya dolice Kuda kukasha biki, bara kiga nakawo miki abinci, tafaɗa tana ƙoƙarin miƙewa. "Aa kibarshi kawai awarar bayan layi zanci bazan iya cin komaiba yanzu. "To to shikenan karɓi wannan jeki kisamu yaro yasiyo miki, bataba ƴar ɗari biyu, tafice daga gidan. Tanin kuwa se washe baki take tana murna ƴar gwal ɗinta ta dawo. Bayan fitar jalima tamiƙe zata shiga ɗakinta idonta ya ɗauka akan gawar tulunta wanda itace tafasa abinta garin gidan khairiya.....!
Autar alheri✍️