3&4
by @autaralheri
🌊*NAMIJIN IZZAH*🌊
Very hot love romantic story 🌹
Writer By
Autar alheri✍️
🎷🎷🎷🎷🎷🎷
🎷🎷🎷🎷🎷
🎷🎷🎷🎷
🎷🎷🎷
🎷🎷
🎷
Marubuciyar 👇
MIJIN KILAKI
MEJOR NAJEEB
ME & MY LION
AHALIN HARIJAI
AL'AJABIN MASARAUTA
AND OTHER'S 💃💃
Bismillahirahamanirrahim.
Book1
Page 3&4
"Ido tawaro kafin ta lailayo wata uwar ashar tamakawa khairiya, cikin bala'i tace "tulun bawa kuwa fasamin muguwa uwar ƴan asara? To wlh sekin biyani wlh sekin biyani tuluna, zanga uban daya tsaya miki agidan nan shegiya ƴar asara, wlh kigama wankin nan maza keje kinemomin kuɗin tuluna kafin nakarairayaki agidan nan muguwar banza muguwar wofi, shegiya uwar ƴan sharri, taƙarasa zancen tana kai mata ran ƙwashi kafin ta hankaɗeta rashige uwar dakinta. Da kallo khairiya tabita gartashige ɗakin kafin taci gaba da abinda takeyi.
Ajiyar zuciya mlm sani ya sauke kafin yamiƙe kawai ya fice daga gidan batare da yace komaiba.
Abuja
Wani kyakkyawan dattijone ke zaune awani tangamemen parlor kallo ɗaya zaki masa kisan cewar cikakken buzu ne wanda hutu da nera suka zauna wa, wayace maƙale a kunnenshi yana magana cikin faɗa ga dukkan alamu ranshi amugun ɓace yace "harshen turanci yake cewa "son, I swear to God? This time around, if you do not return to Nigeria, I swear you will just see your wife over there, I will bring her to you mysefe, and I will marry you off to any woman I choose. Since you have finished looking down on me...shiru yayi nawani ɗan lokaci kafin yayi ƙwafa kawai ya kashe wayar yana sauke ajiyar zuciya. Cikin tausasawa matar dake gefenshi tace "pls Alhaji Kabi komai ahankali kasan halin wannan yaron base anbaka labariba miyasa kekesi kaza ɗaya dashi ne iye? "Au hakama zakice? To shikenan aiko zega yadda zanyi dashi wlh tunda shi jinkai da izzar tashi har akaina, nima ban isa dashiba yake nufi, tunda yace bazeyi aurenba anufinshi kuwa bazeyiba, aiko zan nuna mushi be isa ba, nidashi zanga wanda ya haifi wani, domin wlh indai ina numfashi watan nan baze ƙareba bashi da aure, kuma muzuba mugani, daga hakan yamiƙe fuuuu yabar parlor. Cikin tashin hankali ummi ta ɗauki waya taƙara danna kira, harta katse bai ɗagaba, kafin ya kirata back. Aiko tana ɗagawa batajira cewarshiba tarufeshi da faɗa "Bilal wai kanada hankali kuwa? Ta wlh kasani a wannan karon kakai mahaifinka bango, kuma yarantse watan nan baze ƙareba seyayima, yanzu in kadawo ka kawo wadda kakeso ya aurama cikin mutunci, in kuma kaƙi kaga yadda bakaso, amma kasani wannan umurnine ba shawaraba karka yadda gobe tawuce baka cikin Nigeria, tana gama fadar hakan itama tayanke wayarta batare da tajira jin abinda zeceba."ummi miyafaru ne wai kiketa faɗa keda waye? "Hum nida waye fa bancin yayanka sarkin kafiya. "Au wai Yaa BG kike magana? Tab lallai yau antaɓo manya ashe tunda har kikayiwa yallaɓai BG faɗa, jalal yafaɗa yana dariya kafin yafice daga parlor.
Ƙyauyen galadimawa
Khairiya dai seda taƙaracin wani dukan agun tanin kafin tagama wankin, domin kuwa tafi awa uku tanayinshi, bayan tagama ta share gidan tass ta gyara komai, cikin wahala, kafin tanin takaɗata nemo mata kuɗin tulunta ko abinda taci bata samubo, hakan tafito zuciyarta abushe tanaushi hanya batareda sanin inda ta dosaba. Seda tayi tafiya me nisa kafin ta haɗu da abbanta, mlm sani ɗauke da sabon tulu. Yana ganinta, ya tareta yana tambayarta lafiya ina zataje? Amma bata amsa mishiba, sauke tulun yayi ya rungumeta yana rarrashinta yana kuka, sunjima ahaka, kafin yace "kiyi haƙuri mamana narasa yadda zanyi da tanin ne, bazan iya hanata abinda take mikiba, amma wlh da inada inda zankaiki wlh da zankaini narabaki da azabar tanin, dan Allah ki gafarceni ƴata nakasa riƙe amanar da mahaifiyarki ta barmin kiyafemin dan Allah, yaƙarasa zancen yana rushewa da kuka domin shi kashi azabar tanin ta ishe shi kawai dan besan yazeyi bane. Cikin sauri tashiga sharemai hawaye murya narawa ta danne kikan domin tana baƙin cikin yiwa tanin kuka ayanzu, kafin tace "kayi haƙuri abba nibakamin komaiba dan Allah kadena kuka. "To to mama nadena kema kiyi haƙuri komai ze wuce da ikon Allah, ina roƙon Allah yabaki inda zaki huta ta yadda se tanin takoma baiwarki mamana. Itadai batace komaiba. Kusan minti huɗu suna haka kafin yamiƙe yamiƙo mata kedar soyayyen hankalin Hausa daya siyo mata ahanya. Aiko ta karɓa cikin sauri sauri tafaraci tamkar wata mayya tana ɗura wannan wancan nafita. Da ƙyar tasamu tanutsu tanaci cikin tsanaki yana bata ruwa harta cinye, kana taƙara korawa da ruwa, tukunna yabata tulun yacai takai mata, kuma kartace mata shine yasiya mata, seda yaga ta ɗauki hanya tukunna yanufi masallaci.
Koda ta isa gida ana kiran magarib hakan yasa tanin takarɓi tulunta tana cewa seta gaya mata gun kwarton data samo kuɗin siyo sabon tulu, sedai khairiya bata kulataba taje tayi alwala tashige ɗan ƙaramin ɗakin da aka bar mata, wanda yake ɗauke da kayan komatsai kala,kala, acikinshi, duk wani shirgin tanin yana cikin ɗakin kuma shine ɗakin khairiya na bacci, sedai ta tattara komai gefe ita gefe. Kwanciya tayi har akayi isha'i tayi sallah anan inda tayi sallar anan baccin wahala yayi awun gaba da ita. Sedai me? Ƙarfe biyu na dare ciwon ciki yatadata kamar zata mutu, hakan taketa murƙususu hadda su amaye amaye, atake zazzafan zazzaɓi yarufeta, ga kuma azabar ciwon ciki, a wannan daren dai khairiya bata runtsaba yadda taga rana hakan taga dare.
Washe gari tunda asuba tanin tazo tadata ta ɗebo mata ruwa rafi, tana zuwa kamar yadda tasaba, haka ta sheƙa mata ruwan sanyi ajiki, tana faɗar "makirar banza maza tashi kije kiɗebomin ruwa zanyi surfe yanzun nan kuma wlh kika yadda gari yawaye baki dawaba kona lahira seya fikijin daɗi. Haka tamiƙe tana rawar ɗari tafito tamkar zata kifa, ga azabar ciwon da cikinta keyi, ga zazzaɓi kana ga ruwan da tanin tayi mata wanka dasu alokacin sanyin asuba.
Muryar ta narawa haƙoranta na haɗuwa da juna tace "bara nayi sallah sena ɗebo miki. Cikin tsawa tace "kiyi sallah hala ruwan sallar gareki? Maza ɗauki ki ɗebomin ruwa wlh kona tattakaki nan.
Allah sarki baiwar Allah ba kusu ta ɗauka ta fice daga gidan, kai tsaye rafin tanufa domin seta ɗauko kusan sau biyu ana uku ne suke tafiya da shafa'u domin ita se lokacin take fitowa daga gidansu. Cikin wahala ta ɗauko ruwan da ƙyar takawo gida, wai tana shigowa ko tulun bata ajiyeba taji saukar muryar jamila tana cewa.....!
Autar alheri✍️