ZAWARA.

CHAPTER 16.

by @1239900

ZAWARA.








NA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨✍️ 








PAGE 16.






Da sauri Nasibah ta tashi zaune ta na rarraba idanuwa tsakanin bakin ƙofar shiga ɗakin nasu zuwa kan Samir da ya zuba hannuwansa a cikin aljihun baƙin wandonsa yana ƙare wa ɗakin kallo cike da ƙyanƙyami da mamakin ganin makwancin Nasibah. Muryar sa a shaƙe ya ce.

"How on earth do you sleep here comfortably?"

Harara Nasibah ta watsa masa sannan ta tura bakinta gaba ta miƙe tsaye ta ce.

"Malami ni ka je waje ka jira ni zan fito yanzu."

Murmushi Samir ya yi ya jingina da jikin ƙofar ɗakin ya ce.

"Ba zan iya yin hakan ba;saboda Baba ne da kansa ya bani izinin shigowa nan tinda baki da lafiya ba za ki iya fita waje ba."

"To ai ni na warke har makaranta na ci gaba da zuwa ma."

Ba tare da Samir ya ce mata komai ba ya hau takawa zuwa gabanta ya miƙa hannu zai taɓa goshinta domin ya ji yanayin zafin jikinta. Cikin wani irin hanzari Nasibah ta ja da baya ta dunƙule hannuwanta biyu tare da ware ƙafafuwanta ta mayar da ɗaya gaba ɗaya baya ta saita fuskar Samir ta kai mata naushi. Da sauri ya sunkuya hannunta ya harbi iska. Idanuwa suka zuba wa juna kowannensu na nishi kamar kajin dake shirin kacamewa da dambe. Sallamar Makaɗi da ke washe baki ne ta dawo da Nasibah da Samir cikin hayyacinsu. Ƙwafa Nasibah ta yi ta gyara tsayuwarta sannan ta fita daga ɗakin cikin matsanancin ɓacin rai ta shige ɗakin Kilishi ta kwanta a gadonta tana mayar da numfashi. Sosai Nasibah ta ji takaicin rashin samun kyakkyawar fuskar Samir da bata yi ba. Ƙwarai ta so ta yi wa fuskarsa tabon da daya kalla zai tuna ya taɓa haɗuwa da Nansy Ƙaya. Ƙwafa ta sake yi a karo na babu adadi ta kulle idanuwanta tana jiyo yanda Makaɗi ke zubar mata da mutunci kwando-kwando a gaban wanda yake iƙirarin za ta aura.

A can tsakar gida kuwa Samir ne ke sanar da Makaɗi zai aiko kayan gado a saka wa Nasibah a ɗakinta,dan bai ji daɗin yanda ya ganta kwance a ƙasa ba. Godiya Makaɗi ya zube a wajen yana zabga wa Samir har sai da Samir ya ɗaga shi. Cike da jin nauyin Samir Mama da Kilishi suka leƙa tsakar gidan suka gaisa. Kallon su ya yi ya amsa gaisuwarsu a tsaye sannan ya sa kai ya fita cike da takun taƙama da isa.

Yana fita daga gidan Rabi dake kitchen ta shiga ɗakin Kilishi a guje ta faɗa kan Nasibah tana murna ta ce.

"Kaiii ƙanwata amma gaskiya na taya ki murnar samun miji irin na nuna wa maƙiya su ji haushi."

"Sai kuma aka yi rashin sa'a Nansy bata da maƙiyan da za ta nuna wa shi su ji haushi ba."

Dariya Rabi ta yi ta samu waje ta zauna da kyau ta ce.

"Da dai Nasibah kika ce,amma Nansy ai ina ga har sarkin Kano yana da matsala da ita."

Murmushi Nasibah ta yi ta juya wa Rabi baya ba tare da ta sake cewa komai ba. Rabi kuwa sai ta zauna ta dinga yabon kyau da gayun Samir tana zuga Nasibah akan ta manta da Malam Luƙman ta amince da auren Samir. Cike da karyewar zuciya Nasibah ta juya ta kalli Rabi ta ce.

"Yah Rabi don Allah ki dena yi min irin waɗannan kalaman domin za su sa na ji kamar kema ba kya so na. Kin kuwa san irin zurfin son da muke yi wa junanmu? Har yau bashi da lafiya tun da ya zo Baba ya gaggaya masa baƙaƙen maganganu. A bakin Mami na samu labarin jininsa ya hau har yanzu suna faman zaryar zuwa asibiti."

"To Nasibah yaya za ki yi? Ai a hakan za ki yi haƙuri ki daure ki rabu da shi ya gama jinyarsa ya samu wata ya aura;kema ki auri Samir ɗinki..."

"Ni ba Samir ɗina bane. Malam Luƙman ne zaɓin raina har gaban abada. Ya min alƙawarin zai jira ni har na kammala secondary school,nima kuma na yi alƙawarin ba zan auri kowa ba idan ba shi ba."

Ajiyar zuciya Rabi ta sauke ta jingina da jikin gado ta ce.

"Nasibah ina so ki gode wa Allah domin ya kawo miki babbar damar da za ki huta wani naki ma ya huta. Kina gani ni har yanzu ko mai gyaran takalmi ban samu ba a matsayin manemin aurena,amma ke kin samu mutum kamar Samir kike ƙin sa."

"Don girman Allah Yah Rabi ki ƙyale ni da maganar wannan me kama da matan. Ni fa a rayuwata na tsani farin namiji,ganinsa nake yi kamar ni da shi bamu da banbanci. Amma idan kina son Samir ya zamo surukin Baba ki je na bar miki shi ki aura."

"Daga baki shawara shine zaki faɗa min bakar magana Nasibah? Allah Ya baki haƙuri ni na yi nan."

Rabi ta ƙarasa maganarta tare da fita daga ɗakin ranta babu daɗi. Tabbas da ita Samir ya nuna yana so ba za ta tsaya ɓata lokaci ba za ta amince,amma kuma tinda ƙanwarta yake so dole ta kama kanta,nan take ta yi wa kanta alƙawarin ba za ta sake saka baki akan rayuwar auren Nasibah ba ballantana har ta faɗa mata maganar da za ta ɓata mata rai.


A ɓangaren Samir kuwa yana fita daga gidan ya yi wa wani abokinsa waya ya yi order ɗin kayan ɗaki masu kyau har da carpet da zannuwan gado. Babu ɓata lokaci aka buga lissafi ya aika kuɗin sannan ya tura adireshin gidan Malam Sanda Uba Makaɗi. Yana gamawa ya koma gida ya hau shirin tafiya Abuja,domin gaba ɗaya Munirah ta hana shi sakat da kiran waya da saƙonni. 

A ranar da yamma Samir ya bar garin Kano zuwa Abuja,daf da magariba kuma kayan ɗakin da ya siya wa Nasibah suka isa gidan. Kamfanin da kansu suka shiga har ɗakin su Nasibah Makaɗi na yi musu jagora suka fitar da kayan ɗakin nasu suka share suka gyara shi tas bayan sun fitar da kayan ciki,sai suka jera wanda suka zo da su sannan suka kafa labulaye suka tafi.

Malam Sanda ji ya yi kamar ya kori yaran shi ya karɓi ɗakin,sai dai kuma yana tsoron kada Samir ya sani ya ji babu daɗi. A wannan ranar Malam Sanda har bayan Isha'i yana ɗakin suna ta hira shi da yaran nasa. Cikin hirar tasu ne yake cewa Usman.

"Ka ga abinda yasa nake son arziƙi ko Usumanu? Shi fa arziƙi har zumunta yake gyarawa,yanzu yaushe rabon da na zauna da ku irin haka a yi wasa a yi dariya uhumm? To ko da yaushe ina wajen ƙwadago,ina ka fito neman na kai ina zaka je neman na kai."

Gaba ɗaya yaran sun gasgata zancensa banda Nasibah da ta shimfiɗa tsohon soson katifarta ta kwanta a ƙasa ta juya musu baya. Lokacin da Malam Sanda zai bar ɗakin sai ya ɗaure fuska tamau ya ce.

"Ke Nasibah tashi ki haye gado kafin na saɓa miki a cikin daren nan. Ka ga min shegiyar yarinya mai kafurin taurin kai? Halayyarki fa ta fara kai ni maƙura Nasibah."

Makaɗi ya ƙarasa maganarsa yana mai nuna wa Nasibah yatsa yana ƙanƙance ido. Waje ya fita yana ci gaba da rantsuwa idan Nasibah bata hau gado ta kwanta ba sai ya koma ɗakin ya yi mata dukan tsiya. Kan dole ba dan ta so ba ta hau gadon tana gunjin kuka kamar wadda aka yi wa shegen duka. Su Faihah tuni suka yi bacci a saman gadon.

Rabi kuwa da ta ga yanda Nasibah ke cike da ƙunci sai ta yi shiru bata ce mata komai ba, bayan fitar Usman daga ɗakin sai   ta sauka daga gadon ta kulle musu ƙofa. Gidan abokinsa da yake kwana ya yi wa iyayen nasa sallama ya tafi. Tun daga wannan ranar Nasibah ta saki jiki ta ci gaba da hawa gadon ba dan ranta yana so ba. 

Bayan kwana biyu ta kama washegari sunan ɗan gidan Hanifah. Dan haka Yah Hauwa da Yah Lawizah sun zo gidan daga su sai kayansu,sun baro yaransu a gidan mazajensu gudun kada Makaɗi ya yi musu cin mutuncin da ya saba. A wannan ranar da ta kama lahadi babu makaranta sai gidan ya kacame da murna. Hatta Nasibah da ta saba yi musu rashin kunya ta yi murna sosai da zuwansu. Suna shiga ɗaki suka ga ƙaton gadon da aka girka a ciki sai suka hau yaba wa suna sake zuga Nasibah akan ta amince da auren Samir kawai ta manta da Malam Luƙman. Baki Nasibah ta kumbura tana ƙunƙuni ta fice waje ta bar musu ɗakin. A wannan ranar a ɗakin Mama Nasibah ta kwana saboda yanda ɗakin nasu ya cika.

Washegari da safe duka ƙannenta sun yi shirin tafiya gidan suna,ita kuma sai ta yi shirin tafiya makaranta. Ko da Mama ta yi mata magana sai ta ce.


"Mama idan an tashi daga makarantar zan wuce can,kin ga kayana nan na ɗiba a jaka."

"To shikenan sai kin dawo."

Wajen Malam Sanda Nasibah ta je ta tsaya tana wani ciccin magani,shi kuwa sai ya saki fuska ya kalle ta ya ce.

"Ƴar Baba ke ba za ki je gidan sunan ba ne a samu yau a ɗaga wa girki ƙafa a gidan nan?"

"Ni sai na taso daga makaranta zan je Baba. Baba ka bani kuɗin break na tafi kar na makara."

Haɗe fuska Makaɗi ya yi ya ce.

"Ke matsala ta da ke Nasibah bani-bani. Yanzu fisabillahi ba za ki tausaya wa aljihuna ba saboda ciyar da bataliyar da na yi da safen nan?"

"Habaa Baba in da ina da kuɗi ai kai ma ka san ba zan ce ka bani ba. Rashin lafiyar nan da na yi kwana biyu ne ya sa bana iya kitso da lalle,shi yasa bani da ko sisi. Kuma Baba ka ga su Yah Hauwa duk sun yi lallen suna da sabon kitso,Yah Rabi ma ta yi sabon lalle da kitso ni kaɗai ce ban yi komai ba."

Cike da hargagi da hargowa Makaɗi ya zaro ɗari biyar ya miƙa wa Nasibah ya ce.

"Ƙalatacciya ga su nan a je a kashe. Kar kuma ki kuskura ki faɗa min ba za su ishe ki ba,dan ba wasu zan ƙara miki ba."

Jujjuya kuɗin Nasibah ta yi a hannunta ta buɗe baki za ta yi magana,kamar Makaɗi zai dake ta haka ya yunƙura yana sababi,da gudu Nasibah ta bar gidan tana ɓata rai domin ba haka ta so ba.

A wannan ranar gaba ɗaya ahalin Makaɗi suka ɗunguma suka tafi suna,domin kuwa da kansa ya kulle gidan ya tafi da makulli. Cikin ransa kuwa sosai yake jin daɗin tafiyar su gidan sunan saboda ɗauke masa nauyin ciyarwar wannan ranar.

Da misalin karfe biyu da rabi Nasibah ta isa gidan Yah Hanifah,a nan ta tarar da ƴan'uwanta gaba ɗaya suna zaune a ɗaki ɗaya an kawo musu abinci mai rai da lafiya suna ta ci suna hira hankalinsu kwance. Gaishe su ta yi sannan ta sauya kayan jikinta ta fita wajen Yah Hanifah suka gaisa. Da yamma aka kirawo me hoto ya ɗauki hotunan tarihi. Da za su tafi sai dangin mijin Hanifah dake kan abinci da naman suna suka cika musu ledoji da kayan suna har da naman suna,ɗaya daga cikin ƙannen Baban Aslam ɗin ce ta karɓa ta kai musu har ɗaki. Ta na zuwa ɗakin da su Yah Hauwa suke sai ta tsaya tana kallon su Yah Hauwa da su Mama a yatsine ta ce.


"To tinda ku ba a cin naku saboda tsiya da ta yi muku yawa gashi nan ku tafi da guziri. Allah Ya bada ladan zumunci."

Shiru kowa ya yi saboda mutuwar jiki da kunya da ta kama su. Nasibah kuwa nan take ta hasala ranta ya ɓaci. Cike da tsananin ɓacin rai ta isa gaban matashiyar da za ta girme ta da kaɗan ta ce.

"Uwarki da ubanki ne matsiyata amma ba mu ba. Shi mai kuɗi dama yana faɗa ne?"

Ƙanƙance ido yarinyar ta yi ta ce wa Nasibah.

"Ke ni kika zagar wa iyaye?"

"Ni turame kika gani a bayana da kike zaginsu ba iyaye ba?"

"To wa ya sani ko tura..."

Kafin ta kai ayar maganarta tuni Nasibah ta gaura wa fuskarta mari. Nan take dambe ya kacame a tsakaninsu. Da ƙyar su Yah Hauwa da sauran dangin mijin Yah Hanifah dake waje suka iya raba faɗan. Sosai yarinyar ta sha baƙar wahala a hannun Nasibah,banda hawaye babu abinda take yi ta kasa cewa komai. Ganin haka sai kowa ya yarda da abinda Nasibah ta faɗa,dangin mijin Hanifah sai suka ba wa su Mama haƙuri suka tattara kayan flour da lemon roba tare da naman sunan da ya zube a ƙasa suka sauya musu leda suka basu. A nan ne Nasibah ta yi tsalle ta dire ta ce ba za su karɓi kayan ba tunda aka kira su da matsiyata. Sai da Yah Lawizah da ke da zafin rai ta daka mata tsawa sannan ta shiga hankalinta ta fita daga gidan cikin fushi ta kama hanyar tafiya gida ita ɗaya a ƙafa. 

Har bakin ƙofar gate ɗin gidan Hanifah ta rako su Mama tana sake basu haƙuri. Basu jima suna tafiya ba suka samu adaidaita sahu,Yah Hauwa ta tsayar da shi ta biya kuɗi ya ƙarasa da su gida. Ko da suka isa gida sai suka tarar da gidan a buɗe,su na shiga Malam Sanda ya washe baki yana yi musu sannu da zuwa. A tsakar gidan suka baje suna ba wa Malam Sanda labarin yanda sunan ya kaya,amma basu bashi labarin faɗan da Nasibah ta yi da ƙanwar mijin Hanifah ba. Kilishi ce ta raba kayan da suka dawo da shi Faihah ta miƙa wa Makaɗi nasa ya hau ci yana faɗin.

"Shine da ake so a tatattaro ta dawo gida mu yi raba daidan kuɗin lalurar iyalinsa ko? To da ban matsa ta koma ba kun je ku ci ku sha har ku yo guziri?"

Shiru suka yi masa ya ci gaba da surutansa yana jefa naman suna a bakinsa. Sai da ya kusan cinye wa sannan ya ce.

"To wai ina kuka baro min Nasibah?"

Kafin su bashi amsa Najlah ta ce.

"Da ƙafa ta taho bayan sun gama dambe da Lailah ƙanwar Baban Aslam."

Cikin sauri Malam Sanda ya ɗaga kai ya ƙure su Yah Hauwa da ido,ransa a matuƙar ɓace ya ce.

"Ku kuma kuna uban me har dangin mijin Hanifah suka yi wa ƴata taron dangi?"

"Baba ba fa taron dangi aka yi mata ba,ita yarinyar ce ta zo ta mana rashin kunya shine Nasibah ta kama ta da kokowa suka yi dambe."

Da hanzari Makaɗi ya tari numfashin Lawizah ya ce.

"Ku kuma taron tsintsiya babu shara sai kuka zura ido har aka daki ƴar'uwarku baku ɗauki mataki akai ba ko?"

"Haba Malam ta ya za a yi mu haɗu dika mu yi faɗa a gidan surukai? Itama Nasibar dan bata jin magana ne..."

"Dakata min Maryama kada ki ƙara ɓata min rai don Allah."

Shigowar Nasibah gidan fururu ne ya katse musu ka-ce-na-ce ɗin da suke yi. Nasibah na jin yanda Malam Sanda ke faɗan barota ita kaɗai da aka yi tun a soro,shi yasa ta shiga gidan tana ɗingishi ta na hawaye. Nan take ran Malam Sanda ya ƙara ɓaci. Fuska a cure ya ce.

"To ku tabbata da safe kowaccenku ta tattara nata ya nata ta koma ɗakin mijinta."

Lawizah na jin haka ta miƙe tsaye tana faɗin.

"Ni dama ko baka ce ba Baba gobe da sassafe zan koma gidana."

"Lawizah ni kike mayar wa da magana ko?"

Tura baki ta yi gaba ta shige ɗaki ta saki labule tana ƙunƙuni. A hankali tsakar gidan ta watse aka bar Nasibah da Malam Sanda yana ta faman rarrashinta.


Haka rayuwar gidan Malam Sanda Uba Makaɗi ta ci gaba da tafiya har aka kai lokacin da Nasibah ta kammala SS 1 ta shiga SS 2. A wannan gaɓar ne kyau da cikar halittar Nasibah suka ƙara bayyana. Hakan sai ya ƙara gigita Samir ya ƙara tabbatar wa da kansa duk duniya bashi da matar aure sai Nasibah. A ɓangaren Nasibah kuwa har a wannan lokacin bata cire rai za su yi aure ita da Malam Luƙman ɗinta ba,sai dai rashin wata mu'amala a tsakaninsu na ɗaga mata hankali sosai tana jin kamar haƙonta ba zai cimma ruwa ba. 

Lokacin da suka shiga second term aka saka ranar auren Nadiyah. Sosai su Nasibah suka dinga murna suna tsara yanda za su cashe su raƙashe a bikin Nadiyah. Bayan sati biyu da sanya ranar auren Nadiyah da yamma Nasibah na gida tana kitso Nawwarah ta je gidansu cike da tashin hankali. Da ganin haka sai Nasibah ta miƙe ta ja hannun Nawwarah suka shiga cikin ɗakinsu na ƴammata ta ce.

"Ke me ya faru na gan ki haka?"

Yatsa Nawwarah ta kai cikin bakinta tana cizgar farcen hannunta ta ce.

"Wai kin san kuwa wa Nadiyah za ta aura Nasibah?"

Murmushi Nasibah ta yi ta ce.

"Ba ta ce mana ɗan abokin Babanta za a aura mata ba?"

Hannun Nasibah Nawwarah ta kama ta zaunar da ita a bakin gado sannan ta zaro wayarta ta kunna,nan take hoton Nadiyah da Malam Luƙman ya bayyana a saman screen ɗin wayar Nawwarah. Wani irin bamagujen ashar Nasibah ta saki jikinta na rawa ta karɓi wayar Nawwarah tana kallon Malam Luƙman ɗinta yana yi wa Nadiyah murmushi kamar dama can sun jima suna soyayya tare.......



*Ku yi haƙuri da ji na shiru da kuke yi please.*