NAMIJIN IZZAH

5&6

by @autaralheri

🌊*NAMIJIN IZZAH*🌊

  Very hot love romantic story 🌹

       Writer By 
           Autar alheri✍️

🎷🎷🎷🎷🎷🎷
🎷🎷🎷🎷🎷
🎷🎷🎷🎷
🎷🎷🎷
🎷🎷
🎷

Marubuciyar 👇
MIJIN KILAKI
MEJOR NAJEEB
ME & MY LION
AHALIN HARIJAI
AL'AJABIN MASARAUTA

  AND OTHER'S 💃💃

Bismillahirahamanirrahim.


Book 1
Page 5&6


"Cewa, ke maza ɗauka ki wankemin akwai inda zanje da sassafe banaso narasa mota, taƙarasa zancen tana watsawa khairiya kayan data ɗauko ciki hadda inawest. Ko kallonta khairiya batayiba balle tasaran zata tanka Mata, harta juye ruwan data ɗauko kafin tajuya zata fice daga gidan. Aiko tayi kanta tare da fincikota kaɗan tafaɗi, tana cewa "ke dan uwarki nizaki wulaƙanta sekace sa'arki, tass taji saukar marinda seda taga taurari tayi baya tana buga ihu. Ita kuwa khairiya murya na rawa tana huci tace "duk abinda zaki ya tsaya iya kaina zan ɗauka amma wlh muddin kika sanyo uwata aciki to sedai uwarki ta haifi wata, kuma kayan bazan wankeba, sau ɗari nawa zan gaya miki ba ƙatuwar banzan dazan yiwa aiki eye? Kibari naji Dana uwarki amma ke wlh kinyi kaɗan. Tana rufe bakinta tanin na isowa wurin. Cikin tashin hankali take tambayar jamila abinda yafaru. Tana ihu kamar wata ƙaramar yarinya haka take gayama uwarta yadda khairiya tayi mata. "Kutumar ubanki, yanzu harkinyi wuyan dazaki daki yayarki agidan nan? Yanzu jamila ce abin duka awurinki shegiya tainanniya, wlh ko a gun munafukar uwarki jamila tawuce duka balle ke. "Ni wlh ba uwataba kuma kar aƙara zagarmin uwa, tafaɗa jikinta na karkarwa sabida ɗari. Wata muguwar ashar tanin talailayo tamaka mata, kana tafincikota danufin dukanta kawai setaga jinin arigarta. Han kaɗata tayi seda tafadi, cikin hargagi tanin ta buga kalima tana cewa "munshiga uku dama abin kunyar da kika ɗauko mana kenan ƴarnan cikin shege agidana? Kuma har kije kizubar banida labari? Wlh kin cuceni shegiya munafuka, dama shine simuy simuy ɗin dakikeyi Ashe kina nan kina guma ta asa? To wlh ba'agidan nanba, ohhh shiyasa jiya danace sekin biyani tuluna ko ajikinki tunda kinsan abinda kike gumawa? To wlh sekinbar gidan nan tunda bana ubanki bane shegiya karuwar banza karuwar wofi. Tana banbamin kuma duk beyimaba seda ta shiga dukanta tana hankaɗata har seda ta fiddata ƙofar gida, azzikin abin ba mutane sosai kasan cewar ko gari begama wayewa ba, ta hankaɗota seda ta faɗi tare da kwaso kayanta duka ta watso mata tanata famar surfa mata Allah ya isa, tamaida gida tarufe, tana bala'i. Cikin ƙunarrai ba baƙin ciki khairiya tajanye kayan data watso mata ajiki domin ita sam batasan dalilin yi mata wannan cin mutuncinba, zuciyarta tayi wani irin duhu, domin duk abinda tanin kemata betaɓa damuntaba irin na yau, wai itace keda cikin shege? To kodai dagaske tanin keyi taga cikin ne ajikinta? To idan da gaskene a ina tasamo cikin? Duk ita kaɗai takeyiwa kanta wannan tambayar, atake wasu zafafan hawaye suka biyo fuskarta, cikin ƙanƙanin lokaci mutane suka taru akanta, ana kallonta ana nunata tamkar wadda tayo sata, ke take ɗauke da cikin da gaske, gaya haske ya fito tako ina. Ganin yadda aka kewaye ta ne yasa tamiƙe jikinta na mugun karkarwa, ga azaber ciwon cikin yaƙaru, tayi fatali da kayan data watso mata, tamiƙe adaddafe tabi hanya kawai batareda tasan inda zata nufaba. Tana tafe yara na biye da ita suna mata kunwa domin basusan asalin abinda yafaruba kana jikinta duk jini ne, kuma ita bata saniba domin bata taɓayin al'adaba ballema tasan da jinin ajikinta, sunyi tafiya me nisa yara na biye da ita kafin sufara watsewa kasan cewar tayi nisa da cikin gari....shafa'u nafito daga gidansu zata biyawa khairiya ɗin suje wurin ɗibar ruwa wani yaro yagaya mata abinda ke faruwa, domin tun jiya data bar gidan takoma gidansu tana kuka bata ƙara fitowa ba se yanzu, kuma tayi karon da wannan mummunan labarin, cikin tashin hankali tanufi gidansu khairiya ɗin....Shima mlm sani yana masallaci labari yazo mishi cewar tanin takori khairi dan tayi cikin shege, hankali amugun tashe yanufi gidan kamar zekifa, sedai dagashi har shafa'u turus sukayi bakin ƙofar gidan kanin kayanta watse a ƙofar gidan gakuma alamar jini ajikin inda ta faɗi. Abirkice yariƙe wani yaro yana tambayarshi ina khairiya ɗin tayi? Nan yaron yanuna masa hanyar databi, ai cikin sauri sukabi bayanta shida shafa'u daleta famar rusar kuka. 

International airport dake garin Abuja. 

Manyan motocine fake tako ina kuma duka kalarsu ɗaya black ɗaya de kawai fara aikinsu, kana kowace tana ɗauke da sunan BG, acikin nomber kowace motar, excort ne tako ina sun ƙame ƙam suna jiran saukar jirgin, daga gefe ɗaya kuma wani kyakkyawan matashin saurayine ke tsaye cikin mota yana waya, cikin harshen turanci, duka saurayin bazewuce 34y ba aduniya amma yana da kyau Masha Allah. Yajima yana wayar kafin ya kashe yana faɗar "zankira back ya ga jirgi nan ze sauka yanzu. Aiko cikin ƙanƙanin lokaci sega jirgin ya sauka me ɗauke da sunan BG AIR da manyan ha ruffa. Yana gama sauka aka buɗe ƙofar jirgin, sedai ba wanda ya fito aciki ko mutum ɗaya, tun bayan fitowar wasu sojojin Malaysia. Kusan minti sha biyar, kafin sufarajin takon tafiya ɗaya ɗaya cikin isa da gadara irinta ƙasaita annufo ƙofar jirgin, 
Wani haɗaɗɗen guy ne yafito mecikar zati da kamala, mutun ne majiyi ƙarfi wanda kuɗi da hutu suka zauna ajikinshi, ayanayinshi idan ka kallah Sam baze wuce shekaru 34 ba aduniya, sedai yarufe fuskarshi da wani baƙin kyalle, kana yasaka baƙin glass, kuma sumar kanshi duk tazubo agaba tamkar akamata aƙitsa. Ayanayin halitta idan mutum ya kalleshi sau ɗaya bayaso ya ɗauke idonshi daga kallonshi sabida yanayin haɗuwarshi, tsarin shi, da kuma IZZAR shi gwanin birgewa. Humm wannan guy ɗin ƙarshe ne wurin haɗuwa, BILAL MAINA KANGE, kenan inkiya, BG, matashin maikuɗib da duniya ta alfahari dashi da campanoninshi, dudda yake cikakken Dr amma hakan besa yayi watsi da kasuwanci ba, hasalima kasuwancin shine mafi rinjaye akan aikin likitanci gareshi,Kenan.
Ahakan ya shiga takawo harya sauko baki ɗaya. Cikin sauri wannan guy ɗin dake tsaye yaƙara gare shi cikeda far'a yana faɗar "welcome to Nigeria BG, yafaɗa yana hugging ɗinshi. hugging din guy yayi kawai back amma bece komaiba, domin dudda fuskarshi take arufe, yanayinshi yanuna baya tareda walwala didda kasan cewarshi muskili kuwa. Atare wannan excort ɗin suka sara mishi tareda haɗa baki wurin faɗar "we are welcome sir. Bece musu komaiba, illa farar motar dake tsakiya da aka buɗemai ya shiga, wannan guy ɗinma yashiga kana duka excort ɗin suka shiga cikin sauran motocin suka harba kan kwalta....! 

*NAMIJIN IZZAH* Paid book ne kibiya kuɗinki abaki, 1k kacal 👌
7037092176 opay sha'awanatu kasim,ƴan Niger na zaku iya tura kuɗinku a wannan account ɗin 👉*** My Nita sha'awanatu kasim, kana kituramin shedar biyanki a wannan nomber👉 *** on WhatsApp 🙏






Autar alheri✍️