7&8
by @autaralheri
🌊*NAMIJIN IZZAH*🌊
Very hot love romantic story 🌹
Writer By
Autar alheri✍️
🎷🎷🎷🎷🎷🎷
🎷🎷🎷🎷🎷
🎷🎷🎷🎷
🎷🎷🎷
🎷🎷
🎷
Marubuciyar 👇
MIJIN KILAKI
MEJOR NAJEEB
ME & MY LION
AHALIN HARIJAI
AL'AJABIN MASARAUTA
AND OTHER'S 💃💃
Bismillahirahamanirrahim.
Book 1
Page 7&8
"Suna ɗaukar hanya, driver dake gaba yakira wayar wannan guy ɗin mesuna "Yosuf yace "sir har yanzu fa ba'adena rigimar nan ba still hanyar batada kyau mubi hakan ko mubiyo inda mukabi dazamuzo? "No mubi ta inda muka biyo kawai jams, ai yafi muɓata lokaci akan hanya. "Okey sir, daga hakan ya yanke wayar. Shidai BG bace komaiba hasalima kamar bayajin abinda suke fada. Kallonshi yosuf yayi, kafin ya girgiza kai yana murmushi yace "boss hanyar cikin garifa bayada kyau tun tun dazu ake rigima anata zanga zanga, so idan munbican ma ɓata lokaci ne domin hanyar atoshe take, zamubi ta bayan gari ne. Banza yayi mishi kamar nada shi yake maganaba, to dama yasan halin kayanshi idan ya amsa ne ma abin ze bashi mamaki bawai yaƙi amsawarba. Hakan motocin ketafe damugun gudu suna keta ƙyauyuka domin a hanyoyin dasukebi babu cinkoson ababen hawa kana babu rashin kyawun hanya.
Agalabaice take tafiya tana lafi tamkar wadda ta shawo wani abun gaba ɗaya zuciyarta tarufe bata ganin komai dake gabanta, ko hannunta takara a fuskarta bata ganin komai se duhu, ga wani irin ƙugi da cikinta keyi, tama karkarwar zazzaɓi, amma hakan take jefa ƙafarta a duk inda tasamu domin batasan a inda takeba. Tundaga nesa jams ya hango mutum tafe yana haɗa hanya domin harga Allah ya ɗauka tsohuwa ce kasan cewar adduƙe take tafiyar sabida bazata iya miƙewaba, cikin azaba kafafunta ke harɗewa tana zuwa tsakiyar hanya tazube ƙasa somammiya. Wani mugun birgi jams yaja domin kaɗan yabi takanta, yana faɗar "subahanallah. Atare duk dukaja girki da sauran motocin kasan cewar a duk inda zasuje akan wayar haɗaka suke harsukai inda zasuje. Dasauri yusif yaƙara wayar a kunnenshi yana faɗar "lafiya dai jams? Miyafarune? "Sorry sir wlh wata tsohuwace tafaɗi a tsakiyar hanya ga dukkan alamu tana cikin mawuyacin hali domin har anan ina iya hango yadda jikinta ke rawar ɗari. Subahaballah, cewar Yusuf yana balle marfin mitar ya fito. Sedai ga mamakin shi BG yarigashi fitowa ma domin dudda yakeda mirɗaɗɗen hali akwaishi da tausayi musamman akan tsofaffi da talakawa, marasa ƙarfi. Atare da jams da sauran excort ɗin suka ƙaraso wurin. Ganin yadda tanaɗe wuri ɗaya ne tana karkarwa yasa Yusuf cewa "oyo jams lett we help her, mukaita asibiti yanzun nan, yafaɗa yana ƙoƙarin ɗaukota, sedai kafin ya ɗaukota tuni BG yarigashi ya tallabota kamar yar tsana, hijab ɗinta duk yarufe fuskarta, shiyasa dukkansu ba wanda yagane ba tsohuwa bace, mota aka buɗemai yasakata, kana yakoma cikin wadda suke, zasuja mota kenan idan jams yasauka akan jinin dake inda take kwance sedai bada yawaba, bebawa abin mahimmanci ba ya shiga motar sukaja motocin a tsiyace sukabar wurin dede lokacinda shafa'u da mlm sani suka ƙaraso. Domin tun daga nesa sun hango lokacinda BG ya ɗauketa kuma sunta ihu suna kiranta amma sam su basuma kusalada suba. Durƙushewa shafa'u tayi anan wurin tana rushewa da kukan rashin sanin mafita. Cikin sauri tamiƙe tsaye jin mlm sani na kwatantawa wani me bajet motocin yanacewa yabisu. Aiko ta haye mashin ɗin kafin mlm sani ya hau sukabi bayansu.
Kai tsaye BG SPECIALIST HOSPITAL suka nufa, suna zuwa aka buɗe musu get suka danna hancin motocinsu ciki, kana aka ƙara rufe get ɗin, suna gama Peking ya fito cikin tafiyarshi mecikeda ƙasaita yafito, cikin sauri wani excort yabuɗemai inda khairiya take kwance ya ɗaukota kana yanufi cikin asibitin da ita, Yusuf na biye dashi abaya. Emagency room ya shiga doctors naganinshi suka taso cikin girmamawa suka karɓeta daga hannunshi, koda basuga fuskarshiba sun gane shine sedai suna mamakin yoshe ya shigo gari. Suna karɓarta idonshi ya sauka akan jinin dake tafin hannunshi ɗaya daya riƙo gefen ƙugunta. Wani irin waro ido yayi cike da ƙyanƙyami yace "whatt? Yafaɗa cikin wani irin cool voice me masifar ratsa zuciya. Haba ai har rige rige doctors ɗin keyi, wurin kawo masa hand soap da iding sabida yawanke hannunshi, sedai yana dubin yadda zesaka ɗaya hannun yawanke ɗayan dakeda jini. Fahimtar hakan yasa Yusuf girgiza kai kawai ya wanke mai hannun shi, yana faɗar "to ina kuma tsohuwa ta haɗu da jini? "No sir ba tsohuwa bace ai, she's small girl fa, kawai yajigatane sosai. Cewar wani doctor. Atare duk suka waigo suna kallonshi, amma ba wanda yaƙara cewa komai. Sukuwa suka shiga bata temakon gaggawa ganin ogansu yakawota...acan waje kuwa tuni su mlm sani sun iso amma fir masu gadin ƙofar sun hanasu shiga domin dokar asibitin ce bameshi ciki se wanda keda izinin shigar ta, daga likitocin, ko kuma transfer daga wata asibitin sabida tsaro, domin ba gama garin asibiti bace kawai, setakai ta kawo ake kawo mutum nan.
Acan ciki kuwa Yusuf yacewa gams sukoma inda suka ɗaukota sugani ko zasuga wani abin daze sadasu da ahalinta.
Shidai BG tun lokacinda yaga jini ahannunshi ranshi yaƙara mugun ɓaci baran ma dayaji ita yarinya ce ba tsohuwa ba, cikin Izza da isa yafito daga cikin asibitin, Yusuf da gams na biye dashi, suna fitowa suka hango mlm sani da shafa'u wadda keta famar rusar kuka. Yusuf ne yacewa gams yaje yaga mike faruwa acan. Cikin minti biyu yadawo yana faɗar "sir inagafa sunada alaƙa da wannan yarinyar da muka ɗauko domin abinda tsohon kefaɗa, wai yanaso subari yashigo, domin wasu motoci baƙaƙe yabiyo da suka ɗauko yarinyarshi akan hanyar ƙyauyen galadimawa. "Okey to cesubari sushigo, BG bara muga tsohon pls dan senaji dalilinshi nasakin ƙaramar yarinya tabiyo jeji cikin irin wannan mawuyacin halin da take ciki. Bece masa komaiba, kuma be motsaba, har gams yaje ya shigo dasu mlm sani.....!
*NAMIJIN IZZAH* Paid book ne kibiya kuɗinki abaki, 1k kacal 👌
7037092176 opay sha'awanatu kasim,ƴan Niger na zaku iya tura kuɗinku a wannan account ɗin 👉*** My Nita sha'awanatu kasim, kana kituramin shedar biyanki a wannan nomber👉 *** on WhatsApp 🙏
Autar alheri✍️