INUWAR KADDARA 🖤

BULALAR MADUGU😂

by @meelahbazata978

INUWAR ƘADDARA 🖤

Book 1

Page 6 ✍️

Meelah Bazata

Rooman tana shiga gida ta maida ƙofar gate ɗin ta rufe, zuciyarta cike da tausayin ƙawarta, domin ta san yadda take matuƙar tsoron yayan nata.

Ita kuwa Leenah, dama kusan mutuwar tsaye ta yi tun bayan jin amon muryarsa.

Kallonta yake yi da idanuwansa waɗanda suka fi komai firgita ta, kuma ya ƙi ba ta damar da za ta ɗauke nata idanun daga gare shi.

Rigarsa ya ɗaga ya ciro wata sharɓebiyar wuƙa sai ƙyalli take yi, ya ce wa Leenah.

“Ko ki gaya min abin da yake ba ki tsoro a jikina, ko kuma yanzu na yanke maƙogwaronki!”

Ya ƙarasa maganar yana daka mata tsawa, ba ta san lokacin da bakinta ya furta ba.

“Idon ka! Idon ka! Wallahi, idonka irin na aljanu ne!”

Cikin gigicewa take maganar, wanda ita ma ba ta san ta furta ba. Kawai abin da yake zuciyarta ne ya fito bakinta ba tare da ita ma ta shirya wa hakan ba.

“Casting!” Shi ne abin da ya fito daga bakin Madugu cikin mamakin abin da ta furta. Shi ɗin, idanunsa ne irin na aljanu? Lallai yarinyar nan yau za ta ga aikin aljanu kuwa.

“Ni! Idanun aljanu?” Ya faɗa yana juya wuƙar tasa, wanda tun ganin ta Leenah ta sake fita daga hayyacinta.

Ganin yana juya wuƙar ya sa Leenah ta sake yanka wani irin ihu tana faɗin:

“Don Allah, kar ka yanka ni!”

Tare da zubewa ƙasa a sume.

Wani irin tsaki Madugu ya ja yana tsallake ta ya yi saman layin, domin tabbas idan ya ci gaba da tsayawa zai iya saɓa mata kamanni a haka. Wai shi ne mai idanun aljanu? Lallai sai ya hukunta yarinyar nan, sai ta nuna masa inda yake kama da aljanu. Mahaukaciya kawai, ya faɗa yana jan tsaki.

Yana barin wurin Ammah tana ƙaraso wa wurin, daga farkon layin tana hango tafiyarsa.

A dai-dai ƙofar gidan ta ga Leenah kwance a ƙasa a sume. “Za a rina!” Shi ne abin da ya zo zuciyar Ammah, domin ta san tabbas wannan aikin Sayyid ne.

Jijjiga yarinyar take yi, amma da alama ta suma. Wani yaro da ya zo wucewa ta ce ya yi maza ya shiga ya ɗebo mata ruwa, aikuwa da gudu ya shiga gidan ya ɗebo ruwan.

Tana yayyafa wa Leenah, ta ja numfashi tare da zabura tana faɗin:

“Kar ka yanka ni, don Allah! Yaa... yaa...”

Ganin Ammah ya sa ta ƙankame ta tana faɗin:

“Ki ɓoye ni, Ammah, don Allah! Ki ce masa kada ya yanka ni, don Allah!”

“Kwantar da hankalinki, kin ji? Kinga, ba ya nan. Ki rabu da shi, zan yi maganinsa ai.”

Haka Ammah ta ci gaba da lallashin Leenah, sannan ta tashi ta ɗauki jakarta ta ce mata ta shiga gida, kuma ta zo su shiga ta gyara jikinta.

Ai Leenah na jin haka ta yi wuf ta nufi gidansu tana cewa Ammah:

“A’a!”

Kawai kai Ammah ta girgiza tana shiga gida. A zuciyarta take sake neman wa Sayyid ɗin shiriya, domin abin da za ta iya yi kenan. Ba ta san dalilin da ya sa Sayyid ya tsani yarinyar ba, kuma shi ba mai shiga lamarin mutane ba ne, amma ta lura Sayyid kwata-kwata ba ya ƙaunar yarinyar.

Tana shiga gidan ta tsaya cak, ganin ahalolin gidan gaba ɗaya a durƙushe, gwiwoyinsu a ƙasa cikin rana. Ga rana mai ƙunar gaske, sai uban zufa suke yi.

Ammah ta ƙara buɗe ido tana binsu da kallo, ta hango Hajiya Iya a tsakiyar rana ,ga ranar sai kwallar mata kai take, sai uban zufa take yi, ga gwiwoyinta a ƙasa.

“Subhanallah!”

Ammah ta furta tana jefar da jakarta a ƙasa, ta nufi wurin da sauri tana magana.

“Lafiyarku haka? Hajiya Iya, me ya faru haka?”

“Miye ma bai faru ba? Aikin abin da kika haifa mana a zuri’a mana! Wannan tambadadden ɗan nakine, in ba shi ba, aikin waye?”

Iya ta faɗa cikin kuka, domin ba ƙaramin gajiya ta yi da durkusawar  ba. Amma ta san ko giyar wake take sha, ba za ta iya miƙewa ba. Ta ji daɗin dawowar Ammah, domin ita ce kaɗai za ta iya cetonsu.

Ga waɗannan muggan karnukan, sai ƙara zagaye su suke yi kamar mutane. Ba ka da damar yin ko kwakwkwaran motsi, yanzu su hau kanka.

Matar Kawu Auwalu ta yi zaraf ta ce:

“Iya, kin manta da abin da ya ce ko? Ki yi wa Allah da Manzonsa, ki daina zaginsa kar ya ji ki, ki sake jefa mu cikin wata masifar. Yanzu ma ke ce kika jawo mana wannan.”

Ammah dai ta rasa abin da za ta ce, ga kowa yana kuka a wurin. A zuciyarta take faɗin:

“Anya Sayyid lafiyarsa ƙalau kuwa? 🤔 Ta yaya zai sa kakarsa durƙusawa akasa  tare da ’yan uwan mahaifinsa?”

Abin  ya ba ta haushi sosai, amma addu’a dai ba za ta fasa yi masa ba, tana roƙon Allah Ya shirya shi. Domin kuwa muddin ta yi masa faɗa a kan hakan, to fa abin da zai sake musu ya fi wannan. Hakan ya sa ta ce:

“Ku yi haƙuri, don Allah, Iya. Ban san hakan za ta faru ba, da ba zan bar shi ba. Amma ku tashi, don Allah.”

Aikuwa nan take wasu suka yunƙura za su tashi, sai karnukan suka nufo su tare da wani irin mahaukacin haushi.

Da gudu suka koma ƙasa suka zube, suna neman taimako.

Tsawa Ammah ta daka wa karnukan tana nuna musu hanyar da za su bi, aikuwa kamar mutane suka juya suka tafi suka bar wurin.

Sai da suka gama wucewa gaba ɗaya sannan suka sauke ajiyar zuciya.

Wasu suka miƙe suka nufi ɗakunan su ba tare da sun ce uffan ba.

Masu ƙarfin halin ne suka tsaya suna ta raɗa-raɗin maganganu. Ɗan Kawu Manu, wanda kusan sa’an Madugu ne, ya yi ta huɗin banza da ƙarya wadda ba ta isa ba a gaban Madugu. Faɗi yake:

“Sai ya ga maganina wannan ƙaramin marar kunya! Zai san ba shi kaɗai ne ɗan iska ba!”

Dariya wasu suke yi masa duk da halin da suke ciki. Karima ma ta ce:

“Kaji Yaya Idi da ƙarya! Yo, me ya hana ka lokacin da yake wurin ba ka yi maganinsa ba? Kuma me ya sa da ya fita ba ka tsallake ka wuce ba? Ko faɗa ma ba ka iya yi a gabansa ba, amma yanzu ka zo kana mana kurin banza da hofi.”

Ta faɗa tana kyalkyala dariya.

Wani irin wawan ashar ya lailayo ya kunduma mata, take ta rama. Aikuwa faɗa ya ɓarke, aka fara, nan take iyayen suka shiga gidan, ya sake kacamewa.

Ita dai Ammah juyawa kawai ta yi ta nufi ɓangaren ta.

Iya dai ta kasa miƙewa yadda ya kamata, ga ciwon ƙafa da dama take yi.

A zuciyarta ta tsine wa Madugu ba adadi, kuka har yanzu bai bar idanunta ba. Ta haife shi, amma ya yi mata wannan cin mutuncin. Duk bala’in da ake yi, Iya ta kasa cewa komai.

Dama ba baƙon abu ba ne a gare su a saba yin hakan, sai dai babu wanda ya isa daga maƙwabta ya leƙo, balle kuma ya raba.

Duk gulmar irin ta ’yan unguwa, babu wanda yake shiga gidan Madugu. In ma ka shiga, ka san inda ka kai kanka.

Saboda akwai wani lokaci da aka yi faɗa tsakanin matan Baba Auwalu da matan Kawu Manu. Mutanen da suke son ganin kwakwaf suka shiga gidan. Ga su sun cika gidan, amma ba raba faɗan suke yi ba, sai ma zuga sauran ɓangarorin da suke yi.

Aikuwa a ranar sun ga takansu, domin kuwa suna cikin gidan Sayyid ya shigo. Yana kallon yadda gidan ya cika, ya ja ƙeya ya kulle gidan, ya ɗauko bulalarsa.

Duk wata yarinya ko yaro wanda ba shi da aure, ko da kuwa ya girme shi, sai ya zanesa kafin ya fita daga gidan. Haka ya dinga binsu ɗaiɗai yana zaune a kan kujera kamar sarki. Haka suka yi layi yana binsu da bulala, sai da ya yi musu bulala goma-goma ba imani, ba tausayi. Wanda duk girmanka, idan ya yi maka wannan bulalar, sai ka shaida Allah ɗaya ne.

Haka ya gama musu wannan hukuncin tare da dogon gargaɗi.

Su kuwa matan aure, kowacce da tsallen kwado ta bar gidan har zuwa gidanta. Haka yake binsu tun daga gidan har zuwa gidansu, sai kin shiga da tsallen kwado.

saima da akazo kan wata ƙawar matar Kawu Manu, irin masu kibar  nan ne sosai, tafiya ma da ƙyar take yi. Amma a ranar kam ta shaida Allah ɗaya ne, domin kuwa tun daga gidan su Madugu sai da ta kai har gidanta. A ƙarshe, da ta gaji da rarrafe, ta ƙarasa tana kuka tana magiya,amma baibarta ba karshe Rocky ya hadata tashi yace inbatayi Rocky ya hukuntata,aikuwa har cikin zauren gidanta saida Rocky ya Rakata,tana shiga kuwa ta zube a kasa.

Shi ya sa tun daga lokacin babu wanda ya sake gigin shiga gidan su Madugu idan aka ji hayaniya.