BABI NA FARKO
by @zainabb
Zaren Rayuwar Mu
(Oh, Zaren Rayuwar Mu is not my first book. I have written so many books I can't even remember their names. I lost some and I still have some)
NA JIMA a rayuwa ta ina ganin jajircewar Zaid a kaina. Wani lokaci har birgeni yake akan irin ƙaunar da yake faɗa yana min. Amma ni na kasa bashi lokaci na saboda dalilai biyu wanda nake ganin masu ƙarfi ne a wurina. Na ɗaya, Zaid ba sa'a ta bane. Na biyu kuma nayi aji ɗaya da ƙanin shi a makarantar boko anan Kaduna. Ina ganin waɗannan dalilai masu ƙarfi ne da ze sa kace ba zaka kasance tare da mutum ba. Se de kuma wani lokaci da ya taho a rayuwa ta wanda mahaifina ya matsa akan nayi aure. Babu wani namiji da zan iya nunawa nace shi zan ba damar aure na se Zaid kaɗai kuma ba saboda ina kaunar shi bane ba, a'a, se de babu wani wanda nake ganin ya cancanta na ba lokaci na daga cikin masu so su aure ni. Da yawan su, tarbiyyar su da yanda suke bata min ba. Shi fa Zaid makusar shi ɗaya ce a wurina, itace wannan alaqa da nayi sharing da ɗan uwan shi da muka yi aji ɗaya se kuma girman shi da nayi.
Tunani nake yi me faɗi ga irin namijin da zan kawo gida nace shi nake so na aura. Na duba na gama analyzing babu wanda nake iya fiddawa se Zaid shi kaɗai. Yawo na dinga yi a cikin ɗaki na tunani kala-kala na min yawo a cikin kaina. Zuciya ta na bugawa bana son aikata abinda zanyi haka nayi haƙuri na jawo waya ta daga bedside table na turawa Zaid saƙo.
“We can get married if you still want to."
Ban tsaya karanta saƙon ba na tura mishi duk da na jima ban ji daga gare shi ba. Ban sani ba ko yayi aure ko kuma ya samu wani babban chanji na daga ƙaunar da yake mun.
Zaid ya gama wani aiki da yake akan laptop ɗin shi ya ji alamun notification a cikin wayar shi. Hankalin shi be koma chan ba se bayan ya shiga banɗaki ya fito ya ɗauki wayar dake kan gadon shi. Wani irin yanayi ya ji ya ziyarce shi da ya karanta saƙon Hadiza. Nan take Zuciyar shi ta fara duka. Be san wani irin dad'i ne ke tattare dashi ba. Shin farin ciki ne na samun Hadiza bayan wannan lokacin da ya bibiye ta kode farin ciki ne na samun abinda yake so, matar da be taɓa ganin akwai wacce ta mishi kaman ta ba. Anan wurin yayi sujudu-shukr yana godewa Allah da ganin yanzu babu abinda ze hana mishi zama tare da Hadiza har abada. Yanzu abinda ze yi yaje ya sanar da Abba cewa ya samu matar aure.
Kafin ya wuce inda Abba, wayar shi ya ɗauka ya kira number Yayar sa, Hauwa. Bata jima da fara ringing ba ta ɗauka.
“Yaya, Hadiza ta yarda a nema min auren ta" yace cikin farin ciki wanda Hauwa ke iya faɗin kimarsa.
“Na fi kowa jin dad'i kuwa. Zamu huta da maganar soyayyar ka”
Murmushi yayi yace “Yanzu zan tafi na faɗawa Abba. Yaya, ko yau Abba yace aje a nema min auren ta har ma a ɗaura aure na yarda”
“Yaron nan anya lafiyar ka ƙalau kuwa? Wannan yarinyar bata gama zuzuta kanka ba kuwa?"
“Ba zaki gane irin ƙaunar da nake mata bane, Yaya. Bari naje na faɗawa Abba”
Murmushi Hauwa tayi tace “To shikenan kaje ka faɗa mishi. Na maka murnar samun wacce zaka zauna tare da har ƙarshen rayuwar ka”
"Nagode" Zaid ya faɗa kamar wanda yake cikin sauri “Nagode” ya ƙara faɗa.
Parlourn Abba ya wuce. Koda ya shiga ya samu Abba zaune yana kallon labarai. Gaida Abba yayi cikin girmamawa bayan ya zauna. Mahaifin shi mutum ne me dattako wanda ya cika uba babu inda ya gaza musu. Permanent secretary ne wanda yake jin daɗin bada labarin rayuwar shi da kuma faɗin mahaifinsa cikin girmamawa da ƙauna. Dashi da mahaifiyar su sun yi aure lokacin da suke da ƙananun shekarun su. Bayan ta haifa Hauwa har se bayan shekaru bakwai ta haifa Zaid. A ranar da Zaid ya cika shekaru biyu mahaifiyyar tasu ta rasu. Shiyasa Hauwa take ganin tausayn Zaid kuma take bari yana tafiya da duk wasu abubuwa babu hukunci.
Bayan rasuwar ta, quarter na kulawar shi ta dawo kan abokiyar zaman mahaifiyyar su, Mummy A'isha. Wani lokaci tayi, wani lokaci kuma bata yi se de idan mahaifin su ya dawo ya mishi duk abinda ya kamata tunda Hauwa lokacin itama ba wani girma ne da ita ba se an kula da ita. Ita Mummy Malama ce anan jami'ar Abuja. Tana da yara uku a gidan; Muhammad, Khalifa da Shahida. Wani lokaci Zaid na mata kallo na uwa, wani lokaci kuma akasin haka saboda be san dalilin da ze sa ta dinga musu halayen da take yi ba. Kuma shi ko kaɗan idan ta ɓata mishi baya jin zafin yi mata magana saboda yasan idan mahaifiyyar shi ce ba zata mishi abinda Mummy A'isha ke musu ba wani lokaci.
Yana cikin parlourn be faɗa abinda ya kawo shi ba ta shigo.
“Abba, dama da akwai wata yarinya da nake gani a Kaduna. Ko za'a nema min auren ta, na shirya“
Murmushi Abba yayi saboda Zaid ya bashi dariya da yace ya shirya. “Ka shirya? Ka shirya me?”
“Idan bada rashin kunya ba, kaine zaka taho ka faɗa wa Abban ka a nema maka mata? Ni ba zaka taho ka faɗa min ba se na sanar dashi?”
Nan take ran Zaid ya fara ɓaci. Menene ruwan ta dan ya taho yayi magana da mahaifin shi irin wannan? Shin idan ya faɗa mata yau zata taho ta faɗawa Abba yau ko se bayan ta gama jan magana? To shi idan maganar Hadiza ce baya jira.
"Kuma ka rasa inda zaka nemo matar aure se Kaduna. Me yaci Abuja to?”
“A Kadunar ne na samu wacce ke min" ya bata amsa
“Ya isa. Kuma ai babu shamaki tsakanina da ƴaƴa na komai zasu iya zuwa su faɗa min”
Wani kallo na samun nasara Zaid yayi wa Mummy A'isha yana jin daɗin abinda Abba ya faɗa.
“Yanzu yaushe kake so aje a nema maka auren ta?”
“Abba ko yau kace bashi da matsala”
"Yau kuma Zaid? Yanzu ƙarfe nawa? Ka taɓa ganin anje neman aure ba'a sanar da mahaifan amarya ba? Yaya sunan amaryar dai ma tukuna?”
“Sunan ta Hadiza, Abba”
“Madallah. Yanzu ka gane, zanyi magana da Baffan ka se naga lokacin da ya kamata mu tafi. Amma kar ka damu ba ze wuce satin nan me shigowa ba”
"Abba nagode”
"Yawwa. Ta gama karatu ko kuma aiki take?” Abba ya sake tambayar shi yana son sanin abubuwa game da yarinyar da yaron shi yake son ya aura.
"Ta gama karatu Abba. Lauya ce” Zaid ya faɗa ya kuma kasa cewa komai saboda be san ko tana aiki ba tunda ba wani kula shi take ba se idan taso.
"Lauya?! Ma sha Allah. Ta fara aiki kenan?"
Shiru Zaid yayi yana nazarin abin faɗa, chan yace "Eh tana aiki” saboda yasan yanda take.
Gyara zama Abba yayi yana tunani yace “To yanzu yarinya na aiki a Kaduna zaka ɗauko ta ka dawo da ita Abuja? Kuɗin jirgi zaka dinga biya mata tana zuwa Kaduna aikinta ko ka shirya nemo mata wani a nan Abuja?”
Wani irin abu Zaid ya haɗiye saboda be yi tunani irin haka ba. “Zan yi ƙoƙarin nema mata wani Abba. Duk yanda tace”
“Abinda kuka yadda dai ku biyu ko? A cikin zamantakewa, dole ɗaya yayi sacrifice kuma ina fatan ba ze zame muku matsala ba. Yaya sunan mahaifin ta? Zan sa ayi muna binciken su”
“Sunan shi Tahir”
“Wace unguwa?”
“Unguwar Rimi, Abba”
"To Allah ya tabbatar muna da alheri, Zaid. Allah yasa albarka” Abba ya mishi addu'a yana me jin dad'i. Yanzu idan Zaid yayi aure, saura Khalifa da Shahida.
Cikin farin ciki Zaid ya amsa da “Amin Abba”
A CHAN gefen Hadiza, wayar ta take ta dubawa domin duba ko Zaid ya turo mata da amsa amma har yanzu bayan awa ɗaya be ce komai ba. Tsoro taji sosai kar ace ya nemi mata ko kuma ya chanja ra'ayin shi a kanta. Idan ɗaya daga cikin abinda take tunani ya faru, bata san ya zata yi ba saboda irin matsin da aka mata a gida akan kawo namijin da zata aura. Mahaifiyarta, a duk wasu lokuta ta kan ce “Ke fa ba yarinya kike zama ba. Ya kamata ace kina da naki gida da naki iyalai. Ki taho tunda wuri kiyi aure kafin lokaci ya ƙure miki.” Wani lokaci kuma zata ce “Yaushe zaki kawo namiji a gidan nan a matsayin mijin da zaki aura? Shekarun ki ashirin da takwas, lokaci ba tsayawa yake ba.” Tana tuna min shekaru na nawa da kuma pressure akan yin aure se kace ni na mance shekarun. Ina ganin har depression ya kama ni akan kawai maganar aure. Kai zaka jawo namiji ne kace dole se ya aure ka? Ko kuma zaka yi abinda Allah be ƙaddara ba? Su fa mutanen mu, gani suke suna jin tsoron Allah tunda suna faɗin Allah a bakin su a kodayaushe amma chan ƙasan zuciyar su basu yarda dashi ba kuma yanda suke ambaton shi a kodayaushe ba haka bane a zuciyarsu ba. Suna so ka kasance me sa abubuwa su faru idan wani abu ya faru dakai bayan kuma ko akansu wani abu ya faru, baza su iya abinda suke so ya faru ba. Shi mahaifina be taɓa min irin maganar aure ba se yanzu kuma nasan itace ta matsa mishi akan ya bani lokacin fitar da namijin da zan aura. Shin iyayen mu, maimakon matsa maka zuwa yin aure, mesa ba zasu tambaye ka ko kana so kayi aure a rayuwar ka ba?
A cikin ɗaki na nake zaune nayi shiru ina tunanin abinda Zaid kan iya samu a cikin kwakwalwar shi. Ƙarar notification naji, hannuwa na na fara haɗewa wuri ɗaya kafin na jawo waya ta na duba saƙo na. Saƙon Zaid ne an rubuta “Yes, yes, Hadiza. I still want to marry you and I have talked to my father about you. Will soon come to Kaduna and ask for your hand. Thank you.” Maimakon naji farin ciki a cikin zuciya ta, se na dinga jin haushi. Kwantawa nayi a gadona ina kuka saboda ina jin haushi da fushin bada kaina ga wanda nake jin kunyar kasancewa da, da kuma jin nauyi da kuma mutumin da bana jin ƙaunar shi a cikin zuciya ta.
Kukan ba ze taɓa isa ta ba amma nayi shiru ina tunanin rayuwa ta da irin kallon da Muhammad ze min. Ze tsaya yana kallo na yana mamakin yanda akayi na aure ƙanin shi bayan kuma dani dashi mun yi aji ɗaya har gama secondary. Nasan za'a dinga yawo da magana akaina da kuma irin auren da nayi wa Zaid. “Dube ta ko kunya bata ji ta aure ƙanin wanda tayi aji ɗaya dashi”. Haka mutane zasu faɗa. Za'a ce “Ta fa girme shi. Wawa, ya rasa wacce ze aura se wacce ta girme shi.” Rufe idanu nayi ina tunanin irin kunyar da zan kwasa amma ba zan taɓa janyewa ba da maganar auren Zaid. Dama ba a kodayaushe ne mutum yake auren irin mijin da yake so ba. Wani lokaci muna auren wanda suke available ne koda bama ƙaunar su kuma mu zauna tare dasu zama har na abada.