FreeArewaPen original
Zaren Rayuwar Mu
- 1views
- 13chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
’Whenever an idea lands in her head, she doesn't rest until she writes it out.’
Sample · Prologue
Zaren Rayuwar MuTana zaune a parlour na kawo mata ruwan sha kafin abinci yayi Zaid ya shigo ciki. Ban tashi daga inda nake ba na ɗago kaina na kalle shi nace “Welcome home, Zaid” Nodding kai yayi sau ɗaya suka fara magana da Yaya Hauwa. Ban tashi domin wucewa ba. Nayi zaune ina sauraren duk abinda suke faɗa duk da ba wani ji sosai nake ba. Idan da dama zan iya cewa su buɗe murya domin naji duk abinda suke faɗa. Cikin wasa naji tace mishi, ƙasa-ƙasa “You renovated your house? It looks beautiful. Are you bringing in another wife?”Allah kaɗai yasan abinda nake yi domin naji abinda Zaid ze ce, naji kuwa yace “It looks beautiful right?” “Yes, it does” “I just decided to renovate the house. The colour is fantastic”Nodding kai Yaya Hauwa tayi da murmushi akan fuskar ta ta kalle ni tace “Lafiyar ku dai ko?” “Alhamdulillah” na faɗi mata “Nayi ta dubawa ko zaki zo amsar turare baki zo ba” tace tare da kallon ledar dake wurin ƙafar ta ta ɗauko ta ba Zaid domin ya bani. Miƙo min ledar yayi na amsa nayi godiya amma kuma kamar Yaya Hauwa jira take na faɗa mata dalilin rashin zuwa na amsar turare. Tunani nake ko na faɗa musu su biyu na ji suna shawarar sakin da Zaid ze min. “I came” na fara cewa se ta ɗan ɗaga girar ta Zaid ko kallona baya yi kuma ba waya yake dannawa ba, maybe it's irritating and disgusting for him to even look at me. “I think I overheard you and Zaid talking so I went back” “Really?” Yaya Hauwa ta faɗa tare da crossing ƙafafuwan ta “I think that was the time he was considering divorcing you” ta faɗa min tana kallona. Nayi mamakin abinda tace amma nuna min take ba maganar ba'a so naji ne akayi ba, cikin su babu me tsoro na.Shiru nayi bana kallon ɗaya daga cikinsu se naji Zaid ya tashi ze fita. Yaya Hauwa tace “Ka zauna mana”Tsaye yayi ya kai aƙalla seconds ashirin se ya koma ya zauna. “Kina saurare Hadiza” Yaya Hauwa ta fara magana “Ni fa ba tsanar ki nayi ba. Halayen ki dai ne a wurin Zaid bana so saboda duk yadda zan so ki a rayuwa, kin san se nafi son Zaid. Kuma ni ba zan taɓa cewa Zaid ya sake ki ba har se kin sake aikata irin laifin da kika mishi domin ba zan zauna ki maida shi shashasha ba because he's not one. Ko ke ake yiwa ɗan uwanki abinda kike yiwa Zaid, you'll be very alert and angry. Haka kuma duk abinda ya faru bana so nayi sanadiyyar sakin wata mace da za'a yi se idan cutarwar ta ga mijinta yayi yawa ta yanda ba'a tsammani. He told me he loves you and I know how your parting will affect him because of the love he has for you but I told him the obvious: if you continue with your attitudes, he'll have to divorce you. He told me you have changed which is good. But I just can't wrap my head around what you did. Why will you do what...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.