ƘAZAFI Book One

Chapter 2

by @abdulhakimumar122

     ***** **** 
Faisal wani irin mayen saurone ya fara hawansa yana cizon sa wasu na masa zuuu-zuuu asaitin kunne, babu shiri ya koma cikin motar yabzauna, sai kuma zafi da warin ƙwatocin unguwar ya fara addabarsa babu shiri ya ja motar ya bar wajen bayan yaci alwashi a zuciyar sa tunda safe zai mata dirar mikiya. 
Sireenah ko da tagama sallar ta fito asanyaye ta leƙo babu faisal babu motar sa sai taji wani sanyi ya ratsa zuciyarta a hankali natsuwarta ta fara dawowa ta furta "Alhamdulillah ". 
Da sallama ta shiga gidan nasu mai kama sa kango domin daga zaure sa ɗakuna suke da katanga duk sauran gidan ya zube wani wajan ansaka tanfal na buhu ankare wani wajan langa - langa, wani wajan da karare haka dai aka zagaye gidan da ƴan dabaru babu tsari. 
Turus taja ta tsaya a zauren tana kallon ikon Allah zuciyarta na luguden bugun ukku ukku, mahaifiyar ta ce kwace gaban murhu babu lumfashi atare da ita, sai yayarta saratu wacce ta kasance bebiya zaune gabanta tanata zauda hawaye tana jijjigata, kallo ɗaya zakai mata kasan tana son yin magana amma kuma babu dama, yayyen sireenah ukku ne mata kuma duk nakasassune babu mai lafiya acikin su, saratu ce ta farko kuma bebiya ce wacce sanadin cutar gyanda ta kurumce saboda rashin kuɗin magani da kulawa ga ƙafarta ɗaya ashanye bata iya tafiya kamar kowa sai ta ɗangyasa . 
Yaya salima ita ce ta biyu ita kuma duk hannayenta ashanye suke bata iya komai sai abinda akai mata, hatta da cin abinci ko shan ruwa sai an bata, fidimarsu tana yima mama yawa shi yasa kullum sireenah na gida tana kula da su. 
Yaya Na'ima itace ta ukku ita kuma makauniyace bata ganin komai sai duhu, amma tana ƙoƙarin yimakanta abinda zata iya, tun sireenah na firamare karatunta ya tsaya saboda fidimar ƴan uwanta da takeyi ita da mahaifiyar su wacce itama ba wata isasshiyar lafiya ke garetaba don bata son hayaƙi ko ƙura ko tsananin sanyi sai dai kawai aga tazube saboda cutar asamar da tai mata hawan ƙawara, gasu talakawa tilik don da kara suke sanwa ko wani binma da yaye-yayen cikin bola suke wura wurar da su. 
Sireenah ce ta huɗu kuma itace wacce Allah ya bama iyayenta mai lafiya, don haka itace wacce duk wani buri na iyayenta yake akanta, itace suke saka ran zata zama wani abu harta taimakesu a rayuwa sai ƙananta kuma auta Alƙasim shekarunsa shabiyar amma baya iya aikin ƙarfi kasantuwar yana da irin cutar mama ta amsa, mahaifinsu malam umar bada wata sana'ar da ta wuce dako akasuwanni. 
Shigowar baba da yaya salima wurjanjan shine ya dawo da sireenah daga duniyar tunanin da tashiga, ta kalli yaya salima fuskarta tai face face da hawaye da majina ga babu hannun da zata share wuyan abayarta ajirge tai wani iri babu kyan gani sai tausayinta ya kamani. 
"Garin ya ya hakan ta far? " cewar baba cikin tashin hankali 
" sireenah ce yau bata dawo da wuriba har magariba hakan yasa mama wura wuta zatai sanwa saboda baƙar yunwar da mukeji shine kararen suka tirniƙe gidan da hayaƙi sai mukaga mama ta yankejiki ta faɗi lumfashinta yana sama yana ƙasa ". 
“To Allah ya ƙyaita maza muje asibitin sireenah kamota mugani. ”
Kamo mamar sireenah tai Alkasim ya taro keke napep suka nufi asibiti. 
FADILANCY SPEACIAL HOSBITAL
"To ya zamuyi tinda munzo muje kawai duk yadda ta kaya ayi kawai. "
Haka sireenah ta kamo mama baba ya taimakamata suka shiga cikin asibitin, sai da baba ya fara juye kuɗinsa dubu goma kafin aka fara duba nama, kuɗin da baba ya bada kaɗin wayarsane da yasaida don biyan bashin da ake binsa da yaci wajen biyan kaɗin makarantar islamiyyar sireenah , domin yana son ganin ƴarsa tayi karatu mai zurfi don ta zama wani abu har yau har gobe yana takaicin karatun bokon da sireenah ta rasa, yana samun sauƙine idon ya tuna irin makarantar addinin da take zuwa domin tananma zan iya samun ɗaukaka idon Allah ya so, saboda akwai wani ɗan abokin sa da aka ɗau nauyinsa zuwa ƙasar ( Egyt) yacen yana karatun sa hankali kwance har da na zamanin wato boko. 
Zaune suke a (reception) suna jiran jin sakamakon halin da mama take ciki 
Can sai ga wata likita mace ta tafo inda suke tace "waye malam umar mijin Amina? "
"Gani nan "
Cewar baba yana miƙewa 
" yauwa gashi waɗannan magungunan za asawo da Allurar dake ciki su ake buƙata da gaugawa, "
"To " baba yafaɗa yana amsar takardar ya nufi (phamacy) ɗin da ke cikin asibitin sai da ya isa ya tuna babu ko sisi ajikinsa don haka ya dawo da sauri yana kiran sireenah. 
Zaune take ta haɗa kai da gwiwa tana tunanin makomar ciwon mama ta tsinkayo muryar baba tana kiranta, da sauri ta miƙe tace "gani baba da matsala ne "
' eh da matsala sireenah babbama domin kuwa babu ko sisi ajikina, amsa takardar nan kije wajen malam sabo ki samo mana rancen kuɗi idon kuma babu kije wajen Najeeb ya sake taimakawa. "
Asanyaye ta amsa takardar maganin tace to kafin ta fice. Ranta na mata zafi tunowa da tai da faisal domin kuwa ciwon mama ne ya haɗasu har yake bibiyarta duk inda tayi. 
Wata ranar larabace wadda tai dai dai da shabiyu ga watan September ranar sireenah bata da lafiya sosai bata iya sanwa, shine fa mama tayi sanwar ciwon ta ya taso, sukaje Asibiti babu kuɗi shine fa baba yace ta nemi taimakon wajan Najeeb, ita kuma taji bazata iyaba, saboda tanajin kunyarsa Najeeb shine namiji ɗaya da yake sonta so na tsakani da Allah domin burin aurenta yake, talaka ne kamar su domin magi yake sayarwa akan tebur duka jarin nasa bai huce na dubu ishirin ba, a haka kullum sai ya yima sireenah fidima don shi yake bata kuɗin makaranta duk ranar juma'a sai ya sawo mata tsire ko balango taci har ta bama ƴan uwanta , baccin shi da sireenah zata iya rantsuwa daga shekara sai shekara zata ga nama sai kuma hana rantsuwa idon makwabta an haifu ankawo na suna, Najeeb yana ƙoƙarin saimma sireenah sabulun wanka man shafa da turare don kawai ta haska acikin al'umma. 
A can baya kafin sireenah ta hadu da Najeeb al umma gudunta suke duk inda ta shiga sai adingayin nesa da ita wai wari take bata wanka, sireenah bazata ƙaryataba domin bata sabulu suleba ta abincin da zasuci suke da ruwa kawai take wanka, sai da Najeeb ya bayyana gareta tasamu damar yin wanka da sabulu harma ta fesa turare, kuma ƴan uwanta ma suna ƙaruwa ,. 
Baba najin daɗin fidimar da Najeeb yake sosai akan sireenah kasantuwar ya sauke masa wani nauyine da ya rataya a wuyansa ya kasa saukewa, domin duk abinda baba zai samo a kasuwa wajen dakonsa to kan abinci yake ƙarewa, 
Wannan dalilin shine yasa sireenah kasa tunkarar Najeeb da wannan takarda kawai sai ta yanke shawarar kiran abokin sa Badaru tana sanar da shi ashe faisal yana bayanta kuma yaji duk abinda tace sai kawai ya biya kuɗin da ake buƙata da nufin taimako har dubu ishirin, sai godiya sireenah take zuba masa kamar tayi masa sujjada, bayan an sallami mama ya fito da halin sa , sai da yakira sireenah suka kebe ya kalleta yaya " sireenah ina son ki amma kuma bana aureba inasone kawai muyi soyayyar shan minti mu ɗan shana kawai zaifi, na zaɓi gayamaki gaskiya ne domin bazan iya auren kiba, kai sai mun shaku kice na cuceki kona yaudareki, to bani cuta kuma bani yau dara da haɗin kanki nakeson ayi komai zan biyaki ko nawa kikeso amma karkice bazakiyiba don bani neman buƙata a ƙiyi ko mai naso to haka za ayi ga wannan, adreshina ne kisameni zakiji daɗin harka da ni domin ina da kuɗi kuma hanna asake yake ba rowa, ". Yakai ƙarshe yana mikƙamata wani ɗan ƙaramin kati. 
"Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un Subhanalla dama ba don Allah kataimake niba wannan wacce irin rayuwa ce kake burin muyi, to kayi haƙuri gaskiya bazan iyaba, don mutuncina yafiman komai da nai abinda kake so gara na mutu wallahi naje ga ubangiji na a cikin tsarki da tsarkaka, Allah ya haɗaka da irin ka amma ni dai bazan iyaba nan gani nan bari, dumaman mayiya. 
Ganin babu nasara sireenah taƙi aminta shine fa ya takurata sai tabiyashi kuɗin sa duka, bakuma domin yana buƙatar kuɗin ba, a'a sai don ta yarda idon ta gaza samo kuɗin don burin sa kenan ya ganta kusa da shi, sireenah bata da wannan kuɗi hakan yasa suka fara wasan boya kamar mage da ɓera, domin kuwa ya sha alwashin fanshe kuɗin sa ko da ƙarfine duk inda suka haɗu ba zai barta ba sai ya cika burin sa kumar yadda zuciyarsa take ayyana masa surarta da kyawon fuskarta . 
Har yanzu sireenah taƙi yadda su haɗe sai dai tana cikin tsoro da zullumin abinda zai mata middin ya kamata, don haka ko ina binta yake yana son a ɗakko masa ita. 
Tafiya take tana tunanin inda yau kuma zata dosa , baba ya haɗata da aiki ko don yaga wancen karon anyi nasara shi yasa yanzu ma yace ta koma oho, gashi dai ita an sakata acikin wani hali na zullumi da tsoro. 
To yanzu ina zaki nufa sireenah? Haka zuciyarta take tanbayarta cikin rashin sanin madafa, waken malam sabo wani sashi na zuciyarta ya bata amsa atakaice. 
Take tai amanna da haka ta nufi wajen malam sabo, ko da ta isa duƙawatai har ƙasa ta gaishe shi kafin tasa kuka tana sanar da shi halin da mama take ciki a asibiti rai hannun Allah, da saƙon baba na son yabashi rancen kuɗin da zasu bada na maganin da ake buciniki
" Taufa a na wata ga wata wallahi yanzu aka kawoman kaya duka kuɗina na kwashe na bada, gashi yau kasuwar sai godiya babu ciniki, har yanzu naira ɗari biyu ce kawai ajikina, amma idon har ansamu zan kira nace kuzo ku amsa, Allah ya bata lafiya. "
"Amin " sireenah ta furta acen ƙasan maƙoshinta zuciyarta na mata wani irin abu marar daɗi haka ta tashi jiki babu ƙwari kamar wacce kwai ya fashemawa acikin aciki, kuma har yanzu ba ta iya tunkarar Najeeb don shima ta kansa yake, idon ya kwashe jarin nasa ya bada to da me zai riƙe kansa har yayi mata fidimar da yasaba, kawai sai ta yanke shawarar shiga (G. R. A) don neman taimako a wajan masu kuɗi domin unguwar ta manya ce kasantuwar nan gidan gwamnati yake a Dougirei (80 units).