FreeArewaPen original
ƘAZAFI Book One
- 1views
- 1chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 2
***** **** Faisal wani irin mayen saurone ya fara hawansa yana cizon sa wasu na masa zuuu-zuuu asaitin kunne, babu shiri ya koma cikin motar yabzauna, sai kuma zafi da warin ƙwatocin unguwar ya fara addabarsa babu shiri ya ja motar ya bar wajen bayan yaci alwashi a zuciyar sa tunda safe zai mata dirar mikiya. Sireenah ko da tagama sallar ta fito asanyaye ta leƙo babu faisal babu motar sa sai taji wani sanyi ya ratsa zuciyarta a hankali natsuwarta ta fara dawowa ta furta "Alhamdulillah ". Da sallama ta shiga gidan nasu mai kama sa kango domin daga zaure sa ɗakuna suke da katanga duk sauran gidan ya zube wani wajan ansaka tanfal na buhu ankare wani wajan langa - langa, wani wajan da karare haka dai aka zagaye gidan da ƴan dabaru babu tsari. Turus taja ta tsaya a zauren tana kallon ikon Allah zuciyarta na luguden bugun ukku ukku, mahaifiyar ta ce kwace gaban murhu babu lumfashi atare da ita, sai yayarta saratu wacce ta kasance bebiya zaune gabanta tanata zauda hawaye tana jijjigata, kallo ɗaya zakai mata kasan tana son yin magana amma kuma babu dama, yayyen sireenah ukku ne mata kuma duk nakasassune babu mai lafiya acikin su, saratu ce ta farko kuma bebiya ce wacce sanadin cutar gyanda ta kurumce saboda rashin kuɗin magani da kulawa ga ƙafarta ɗaya ashanye bata iya tafiya kamar kowa sai ta ɗangyasa . Yaya salima ita ce ta biyu ita kuma duk hannayenta ashanye suke bata iya komai sai abinda akai mata, hatta da cin abinci ko shan ruwa sai an bata, fidimarsu tana yima mama yawa shi yasa kullum sireenah na gida tana kula da su. Yaya Na'ima itace ta ukku ita kuma makauniyace bata ganin komai sai duhu, amma tana ƙoƙarin yimakanta abinda zata iya, tun sireenah na firamare karatunta ya tsaya saboda fidimar ƴan uwanta da takeyi ita da mahaifiyar su wacce itama ba wata isasshiyar lafiya ke garetaba don bata son hayaƙi ko ƙura ko tsananin sanyi sai dai kawai aga tazube saboda cutar asamar da tai mata hawan ƙawara, gasu talakawa tilik don da kara suke sanwa ko wani binma da yaye-yayen cikin bola suke wura wurar da su. Sireenah ce ta huɗu kuma itace wacce Allah ya bama iyayenta mai lafiya, don haka itace wacce duk wani buri na iyayenta yake akanta, itace suke saka ran zata zama wani abu harta taimakesu a rayuwa sai ƙananta kuma auta Alƙasim shekarunsa shabiyar amma baya iya aikin ƙarfi kasantuwar yana da irin cutar mama ta amsa, mahaifinsu malam umar bada wata sana'ar da ta wuce dako akasuwanni. Shigowar baba da yaya salima wurjanjan shine ya dawo da sireenah daga duniyar tunanin da tashiga, ta kalli yaya salima fuskarta tai face face da hawaye da majina ga babu hannun da zata share wuyan abayarta ajirge tai wani iri babu kyan gani sai tausayinta ya kamani. "Garin ya ya hakan ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.