9&10
by @autaralheri
🌊*NAMIJIN IZZAH*🌊
Very hot love romantic story 🌹
Writer By
Autar alheri✍️
🎷🎷🎷🎷🎷🎷
🎷🎷🎷🎷🎷
🎷🎷🎷🎷
🎷🎷🎷
🎷🎷
🎷
Marubuciyar 👇
MIJIN KILAKI
MEJOR NAJEEB
ME & MY LION
AHALIN HARIJAI
AL'AJABIN MASARAUTA
AND OTHER'S 💃💃
Bismillahirahamanirrahim.
Book 1
Page 9&10
"Suna isowa wurinsu mlm sani yace "dan Allah inatake? Ina ƴata? Awane hali take ciki dan Allah kugayamin yaran nan, yana maganar yana share kwallar idonshi. "Ikon Allah baba ka kwantar da hankalinka fa, mune muka ɗaukota kuma tana ciki ana bata kulawar data dace, amma abinda nakeso nasani baba, tayaya kukabar ƙaramar yarinya da irin wannan lalurar kuma tafito tana yankan jeji? Tana cikin irin wannan condition ɗin dakomai ze iya faruwa da ita, wannan wane irin ganganci ne? Yanzu badan Allah yasa muda tashigo hannu ba mugayen mutane neba, ya kake ganin zefaru idan mugun hannu ta shiga? Miyasa kuke sakaci dayaranku ne baba? Bayan kunsan amanace Allah ya bamu? Yusuf yaƙarasa zancen yanajin kamar ze shaƙe mlm sani domin yaji haushin yadda yanzu yake nuna damuwa akanta bayan acikin jeji suka tsinceta.
"Hakane ɗan nan kanada gaskiya amma wlh wannan abin daya faru wlh ba laifina bane, hasali ma bansan yafaruba ina masallaci aka sameni dazancen tani takoreta, shiyasa nazo gidan cikin hanzari sedai koda nazo bansametaba, sekayanta kawai da muka gani a ƙofar gidan shinefa muka biyo bayanta, amma wlh bada sanina wannan abin yafaruba sedai kawai nace Allah yasaka mata, domin tanin tazalunceta, allah yabi miki hakkinki mamana Allah yasaka miki wannan baƙin zaluncin da tanin kemiki tun a duniya, yaƙarasa zancen yana rushewa da kuka.....da mamaki Yusuf ke kallonshi kafin yace "subahanallah baba, kuka kuma? Miyayi zafi hakan? Tukunna ma wacece tanin dakake magana akanta? Cikin sauri shafa'u dake kuka tace "kishiyar mamanta ce, itace tanin. Ido yawaro yace "kishiyar mamanta dai? To ina maman tata take da har hakan ke faruwa? "Mamanta tarasu, shiyasa tanin kewahalar da ita, jiyama da mukaje rafi debo ruwa, cikinta na ciyo tajima bayan narakota gidan seda tadakemu dagani har ita, kana tasakata wankan kayan saukawa, kullun hakan take mata baranar da bata dukanta, shine kuma yau ta ƙoreta bayan tadaketa kuma batada lafiya. Itama shafa'u tafaɗa tana kuka domin ta nuna musu cewar ba hannun baba sani aciki, dudda tanajin haushin yadda yake ƙyale tanin tanayiwa khairiya yadda taga dama amma dudd hakan bataso ace shine yabari ƙawarta ta shiga wannan halin bayan babu hannunshi aciki. "Ikon Allah, to Kai Baba kace ƴarka ce? Idan kuwa hakane kenan ita wannan matar matarkace, to amma miyasa ba zaka ɗauki matakiba anama ƴar ka wannan zalinci kuma agidan ubanta? Yanzu fa Allah kaɗai yasan mike damun yarinyar nan, haba baba dan Allah. Yafaɗa kamar zeyi kuka. Cikin muryar kuka mlm sani yace "wlh ɗan nan bazan iya bane, narasa dalili amma wlh duk abinda tani keyi ban isa nayi magana ba, konaso nayi bazan iyaba, tun yarinyar nan naƙarama naso narabata da tani amma nakasa, kasan cewar bansan inda zan kai takaba, shiyasa har akazo wannan lokacin, amma in sha Allah anzo ƙarshe akan matsalar mamana domin bazata ƙara ganintaba balle harta cutarda ita, daga asibitin nan in sha Allah se ɗakin mijinta wannan masifar ta isa haka. "Humm Yusuf ya sauke numfashi, kafin yace "innalillahi wa'innailaihi rajiun, Allah yarabamu dasan zuciya. Ameen ameen, da sauri shafa'u tace "baba wazaka aura mata kuma yanzu? Tafaɗa hankali amatuƙar tashe domin dai tasan ƙawar tata ko saurayi batadashi. "Karki damu ƴata zan aura mata duk wanda Allah yanufa shine mijinta in sha Allah. Shiru tayi bata ƙara cewa komai ba amma har cikin ranta bata buƙatar wannan auren da batasan yaze kasanceba.
Tunda suka fara magana bece musu komaiba illa duk yana sauraransu, abu ɗaya ya tsaya mishi arai shine kalimar aure, itada ake masa barazana da ita, domin duk wasu kalaman dady seda suka dawo kunnenshi ayanzu, gyaran murya yayi yana na'am da abinda zuciyarshi ta amince dashi, kafin yasaka hannu ya cire glass ɗin idonshi tare da kyallen daya rufe fuskarshi duka. "Woww watafarakallah bi'ahasanilkhaliƙin. Haƙiƙa tsarki ya tabbata ga uban gijin talikai wadda ya halicci kyau kuma yasanya son kyawun azukatan bayinsa. Tabbas duk inda ake neman kyakkyawa idan akazo gun BG amrufe ƙofa domin kyawunshi har yazarta duk tunanin metunani, komai Allah ya bashi ba ƙarya. Domin idanuwanshi kaɗai abin ɗaular hankali, yadda suke wani lumshewa suna buɗewa tamkar wanda yasha wani abin, gasu manya masha allah, eyelashes ɗinshi kaɗai abin kallo ne yadda suke zara, zara. Yanada dogon hanci sosai wanda yayi Dede da kyakkyawar fuskarshi, kana ya ajiye saje me kyau wanda yazo har kan gemunshi daya ajiye dede gemun gayu bawai irin na hauka ɗinnan ba, sumar kanshi kuwa ba'amagana kasan cewar tanada tsayi sosai zaka ɗaukar sumar mace ne, bana namijiba. Ido yazubawa mlm sani wanda seda mlm sani yaɗan tsorata domin harga Allah ya ɗauka ba mutun bane, to hakan yake ko agurin shafa'u sabida kyawu guy ɗin yayi yawa tamkar wani aljani. Cikin wani irin cool voice me masifar daɗin saurara yace "baba, sunana Bilal maina kange, inkiya BG, inaso Zan auri yarka idan ka amince. Yafaɗa kamar bashine yayi maganarba. Ido mlm sani yawaro hakama Yusuf, sedai kafin wani yayi magana sukaji yaƙara cewa, Sunan mahaifina Muhammad amina kange, kasaka ayima bincike akaina da mahaifina abisa koyarwar Islama, nima zan saka ayimin bincike akanku yau ɗinnan, domin banaso abin ya ɗauki lokaci yau nakeso a Daura auren idan harka amince Dani, ɗan shiru yayi yana tsotsar pink lips ɗinshi, kafin yaɗora dacewa munada lokaci da zamuyi bincike Akan juna, kana kaima kanada lokacin yin tinani kafin yamma domin banso komai ya wuce yau. Yaƙarasa maganar tamkar anyi masa dole, domin maraba da yayi irin wannan maganar me tsayi maybe afi wata huɗu tun lokacin da ya ziyarci wani meeting aƙasar Japan. "BG, cewar Yusuf, ko kallonshi beyiba hasalima ɗauke kanshi yayi. Shi kuwa mlm sani cikin fargaba yace "yallaɓai bawai naƙi zancenka bane, aa, amma sam kaiba tsaran mamana bane, kafi karfinta tako ina, banaso nakai ƴata inda batada kima, dudda munacikin tsaka mai wuya amma banaso naƙara yimata rashin adilci akaro na biyu, shiyasa nake ganin kamar abin bazeyuba, dadai mubar wannan zancen kawai. Yafaɗa yana zubda hawaye.
Dukkansu ido suka zuba mishi na wani ɗan lokaci, domin haka kawai sukaji ya birgesu dagashi har yusuf dabe nuna kwaɗayi akan dukiyarsu ba, sedai shi BG beƙara cewa komaiba ya nufi dandazon motocinshi, shikuwa Yusuf Cikin tausasa murya yace, "baba dan Allah kadena wannan zancen bilal sam bahaka yakeba, badan yana abokinaba amma nasan cewar baze taɓa wulaƙanta ƴarka ba ko yanuna mata rashin darajaba, domin kuwa yanada ilimin addini dede misali yasan cewar da me ƙarfi da marar ƙarfi duka bayine na Allah, kuma ba wanda yafi wani agunshi sewanda yafijin tsoronshi, dan Allah ka ajiye wannan gefe, nasan bakomai yaja hankalinshi akan auren yarka ba illa tausayinta, dakuma yadda kake neman aurar da ita, batareda ma kasan wazaka aurawaba, wannan kaɗai ya isa ya tabbatar ma dacewar shi ɗin mutumin kirkine, amma ba komai zamu baka lokaci kafin zuwa sallar azahar kayi tunani akai domin muji hukuncin daka yanke. Shiru mlm sani yayi nawani ɗan lokaci kafin ya nisa yace "shikenan ɗan nan na fawwalawa Allah komai banida wani zaɓi ayanzu domin kagama zance, idan wannan auren alkhairi agaresu gabaki ɗaya Allah ya tabbatar idan kuma ba alkhairi bane, to Allah yazaɓa musu mafi alkhairi. "Wow Masha Allah, ameen ameen ya Allah, ai kaine kagama zancen tunda kabarwa Allah komai, to rabbi kayansa hakan alkhairi ne. "Ameen ameen yanzu zamu iya ganinta? "Eh to gaskiya aa, baba amma zo na haɗaka da doctor dake kulada ita, wanda zekaika gare ta idan tafarka, domin zamu wuce gidane yanzu daga airport muke saukar BG kenan ƙasar wannan abin yazo yafaro ko gida bejeba nasan yanzu su dady nacan hankalinsu atashe sunga munjima bamu dawoba. "Oh Allah sarki aibasani to sannunku da ƙoƙari Allah yasaka muku da alkhairi. Ameen ya Allah baba, daga hakan Yusuf yaje yahaɗa baba sani da Dr Mansoor kana yabi bayan BG Wanda tuni ya shige mota.
Koda yashiga har jikinshi kerawa kafin ya rufe motar yace "BG kanada hankali kuwa? Tayaya zakace zaka auru yarinyar dako ganinta bakayiba? Mi hakan kenufi BG? Dan Allah kamin bayani domin nakasa fahimta, kuma kasani nasani nafi kowa sanin waye kai, zancen so babushi nasani, kuma bazance tausayiba sedai wani abin daban. Ya ƙarasa zancen idonshi tarr akan BG ɗin da yayi masa banza tamkar badashi yake maganaba. Ganin yaƙi kulashine yasa yace "kaifa ɗan iskane wlh mutun na magana serious Amma kanamin banza. Ɗan yatsina fuska yayi Shima cikin gajiyawa yace "kaikuwa sarkin surutuba, da ko gajiya bakayi, yaja ɗan gajeren tsaki. Banza Yusuf yayi mishi domin yau wannan halin nashi ya bashi haushi tunda aƙagare yake daji manufarsa akan wannan lamarin, amma yaƙi yayi magana, kusan minti shida suna hakan, har Yusuf yaɗeben ran zeyi magana kawai yaji yana faɗar "dady ne damuwar Yusuf is insisting that I must get married this very month, but marriage is completely out of my plans right now. I don’t know what to do with him, especially since I am no longer a child and I am independent.
But sam yahanani sukuni, wannan daliline yadawo dani Nigeria yanzu, kuma ni babu tsarin aure acikin lissafina, balle nace akwai wadda zan aura, so bansan wace ze auramin ba, shiyasa ba yanke hukuncin kai masa wannan matsayin wadda zan aura, zan aureta, dan dady yajante lissafin banyi aureba, ita kuma na fiddata daga tarkon stepmom dinta, da auren da akeso ayi mata da wannan ƙananun shekarun, well dukkanmu zamu temaki juna ne, zan aureta ne, a idon duniya she's my wife, Amma azahiri she's my girl house, shine kawai, yaƙarasa zancen tamkar bashine yayi maganarba. Ido Yusuf yawaro cikin mugun mamaki abokin nashi, kafin yanisa yana tunanin abinyi....!
Humm tofa nikaina tunanin abinyin nan nakeyi, koya wannan rikicin zeƙare?🤔
END OF BOOK 1
munzo ƙarshen free page kuma yanzu zamu ɗora daga inda muka tsaya, wannan littafi na kuɗine, idan kinaso aci gaba da wannan tafiyar dake to kibiya kudinki nera dubu ɗaya ne kacal 👌
*NAMIJIN IZZAH* Paid book ne kibiya kuɗinki abaki, 1k kacal 👌
7037092176 opay sha'awanatu kasim,ƴan Niger na zaku iya tura kuɗinku a wannan account ɗin 👉*** My Nita sha'awanatu kasim, kana kituramin shedar biyanki a wannan nomber👉 *** on WhatsApp 🙏
Autar alheri✍️