ƊAURIN ZUCI

Chapter 24

by @maryamstar248

***

𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
         𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍

CHAPTER 24
Ababen cutarwa da zasu iya cutar da ita akan hanya.
     Da haske Kanzul yayi amfani wajen rage tsayin tafiyar Maryam ta yanda ita kanta ba zata gane ba.
   
A daidai tabkeken store ɗin KALAMU WAHEED SHOPPING MALL Maryam ta ci burki, sai da ta kalle gefe da gefenta sannan ta cira ƙafa zata tsallaka zuciyarta na luguden duka kamar zata faso ta ƙirjinta, ta yi taku ɗaya biyu ana ukunne ta tsaya tsam jikinta ya soma rawa kamar ana kaɗa mata mazari, sai kawai ta saka hannayenta ta doshe kunnuwanta tare da kulle idanuwanta ƙamƙam.
      A hankali ta saki hannyenta tare da buɗe idonta ta soma waiwayowa a hankali kamar me tsoron ganin wani abu.
     Tar take iya ganin Fuskarsa atacikin glashin motar na gaba, kuma kai tsaye ganinta ya sauka a tsakiyar idanuwansa da suka koma jajaye.

        Tun bayan da yayi wannan mafarkin gaba ɗaya ya burkice ya fita a hayyacinsa, ga kuma gwaruwar da kan shi yayi wacce ta ƙara ƙarfafa masa ciwon kan.
     Wayar Fahad ya kira tare da tambayar shi inda ya je.
    "Big bro kana buƙatar wani abune da gaugawa bana nan yanzu na fita ɗauko doctor amma ka jira ni nan da awa ɗaya." Fahad ɗin ya faɗa.
    "No kabarshi kawai dama aikenka zanyi amma yanzu turo min location ɗin wannan Mall ɗin zan siyi abu." Junaid ya faɗa a taƙaice.
     "Okay zan tura maka amma mike damunka naji voice ɗinka wani kala, baka jin daɗi ne?."
     Fahad ya faɗa cike da kulawa.
     "Nop na tashi barci."
   Daga haka bai jira abin da Fahad ɗin zaice ba ya yanke kiran tare da amsar key ɗin motar daga hannun driver ya shiga ya fice bayan an buɗe ma shi get ɗin.
     Da location yayi amfani har ya isa daidai titin da Store ɗin ya ke, tunda ya tunkari wajen daga can nesa yake hangon wani irin haske, hasken da kai tsaye yake shiga cikin idon shi, zai iya rantsuwa akan bai lura da akwai mutum ba sai sansa ya tunkari hasken gadan gadan sannan ya lura da ita, babu shiri yayi gaba tare da yin baya sanda ya take burki da tsananin ƙarfi wanda hakan ya ƙara ma shi ƙarfin ciwon da kan shi yake yi.

     Daƙyar ta zanye idonta daga kan shi ta tare zuciyarta da ke barazanar ɓallo ƙirjinta ta fito, da mugun ƙyarrr taja ƙafafuwan da lokaci ɗaya sukai mata wani irin sanyi ta idasa tsallaka titin, sai da ta tsaya ta saita kanta, sannan ta durfafi cikin store ɗin tana son dawo da ɗauki da murnarta akan zuwa store ɗin amma zuciyarta ta gama ɗaurewa taƙi bata haɗin kai, saima azalzalarta data dinga yi akan ta juya ta kalli mutumin da ya kusa banketa amma ta dake ta cije ta shige cikin store ɗin tana sauke ajiyar zuciya.

Wajen da aka tanada don parking ɗin motoci Junaid ya ƙarasa yayi parkin, a gaggauce ya fito daga motar tare da tunkarar mall ɗin.

     Hangota yayi a ciki wajen siyayya tana riƙe da Shopping Cart tana saka abubuwan data ɗauka, samun kan shi yayi da kasa cigaba da tafiya sai kawai ya tsaya tare da saka hannayen shi cikin aljihun yana ƙare mata kallo da jajayen idanuwansa.
       Sosai kan shi ya ɗaure bayan ta gama shopping ɗin ta nufi wajen Cashier, amaimakon ta bada card ko cash money sai yaga ta zaro hasken daga cikin hijabinta ta miƙawa Cashier shikuma ya amsa yana lissafa hasken kamar me ƙirga kuɗi.
    Sosai Junaid ya tsorata da abin da ya gani nan yake ya yanke hukuncin aljana ce ita ba mutum ba.
Receipt aka bata tare da saka mata cikin leda me ɗauke da tambari da sunan Mall.

     Cak numfashinta ya tsaya a cikin ƙirjinta, ya cakuɗe da bugun zuciyarta suka haifar mata da wani yanayi me wuyar fassaruwa, sau bakwai tana buɗe bakinta da zummar tayi magana amma kuma sai ta kasa cewa komi, saima sake damƙar ledar hannunta da take.

   Da wani irin sauri zuciyar Junaid ta shiga dokawa, ga wani irin gumi daya soma tsatsafo ma shi kamar wanda ya warke daga zazzaɓi, a baɗini yana son kaucewa ya bata hanya amma kuma ya kasa kaucewar, bai san dalilinda yasa hakanba amma zuciyarshi na ƙoƙarin tabbatar ma shi da tabbas aljana ce ita ɗin.
    Ƙara sarawa kan shi yayi da tsananin ƙarfi wanda hakan ya tilasta ma shi dafe kan tare da tsugunawa wajen cikin ficewar hayyaci. "Auch." ya fidda sautin a wahale, wanda hakan ga janyo hankulan mutane kan shi.
     Zare ido tayi a tsorace tana kallon yanda cikin ƴan daƙiƙu ya fice a hayyacinsa a firgice taja da baya tana furta kalmar "Subahanallah." a fizge sai kuma ta yi hanzarin raɓawa ta gefe ganin wasu maza sunzo sun kama shi ta sulale ta fice zuciyarta na ƙoƙarin fallowa ta fito.
    Ko gabanta bata gani kawai tafiya take a firgice sai faman ƙara damƙe ledar hannunta take   yi.
    Ganin yanayin da take ciki ya sanya bayan ta karya kwana Kanzul ya huro iska ta ɗauketa zuwa sama, kafin ƙyastawar ido harta isa ƙofar gida sannan ya dire ta, tare da sauka daga kan iskan ya koma ya kwanta a yanda yake, shima Hamzulu ya sauko ya koma siffar datasanshi da ita ta kaka Abu ya daidaita komi na ɗakin da suka hargitsa sukaci gaba  da tsumayin shigowarta, ganin har mintuna sun shuɗe ya sanya Hamzalul juyawa domin ya kallo abin da take yi.
    Tsaye ya ganta a ƙofar gidan ta danne ƙirjinta da tana sakin numfarfashi cikin wani irin yanayi, bai jinkirtawa wajen buɗe ƙirjinta yana kallon yanayin yanda zuciyarta ke tsallen bugu, da mamaki ya kalli Kaizul cikin wani yanayi, sai de yasha jinin jikin shi ganin irin murmushin da Kanzul ɗin ke yi alama yasan komi, girgiza kai yayi tare da saka hasken shi ya daidaita mata bugun zuciyarta sannan ya kulle ƙirjin nata ya koma yana siffarsa datasan shi da ita.

     Sallama ta yi cikin siririryar muryarta wacce ta sake yin sanyi ƙalau  fiye da yanda take a baya.
   "Wa'alaiki salam jikalle marhababiki lale."  Kaka Abu ya faɗa da fara'a a fuskar shi.
   Wani sanyi ne ya sake lulluɓeta sanda tayi tozali da fuskokinsu, su ɗin sune asalin rayuwarta bayansu batada kowa sai Allah tana alfahari dasu akowane irin yanayi zata tsinci kanta, da haka ta ƙwarara kanta tare da sake danne abinda take ji a zuciyarta saboda bata so su shiga damuwa da ganinta, ta ƙaƙalo murmushi me sanyi sannan ta ce.
    "Kaka ya jikin naka, yaude Allah yayi ba zaka sake shan kunun gero ba nayo mana siyayya harda wannan abin da kake tsananin so."
Ta faɗa tana aje ledar tare da cire hijabin jikinta ta sagale akan ƙusa, a zahiri kan ƙusa hijabin yake amma a  baɗini kan iska yake a sagale shi kaɗai ba tare da makari ba.
     Buɗe ledar ta yi tare da fito da robobin costerd guda biyu sai badara babaa guda ɗaya sai cube suger  da wasu buscuit masu sauƙin kuɗi.
     Cikin muryar marasa lafiya irin masu jin jiki sosai ɗinan Kaka ya ce da  ita. 
   "Sannu da ƙoƙari Maryama Allah yayi miki albarka ya inganta rayuwarki ya  jiƙan mahaifanki da rahama."
    Ya faɗa idon shi na kawo ruwa wanda har a baɗini yake jin zafin rashin mahaifanta da tayi.

    Murmushin daya ƙarawa fuskarta kyau ta saki sannan a tausashe ba tare da damuwa ta bayyana akan fuskartaba ta ce.
   "Ameen Kakana nikam sam bana cikin maraici Allah ya amshi rayukan mahaifana tun bansan kaina ba, amma kuma sai ya barni da ku kuka kula da ni kuka bani tarbiyya gwargwadon yanda ya dace, wataƙila da ace suna raye da yanzu ba haka nike ba ina alfahari da ku sannan ina tsananin godiya ga Allah da baibar rayuwata ta tagayyaraba silar maraicina Alhamdulillahi." Ta faɗa da dukanin zuciyarta.
(Ma sha Allah haka ake so mutum ya kasance me godiya dakuma tawakkali idan Allah ya amshi wani abu daga gareka hakan baya nuni da ƙarshen yazo ba, a,a sannan ma aka buɗe maka shafin wata rayuwar, sau dayawa muna ganin dan mun rasa mahaifanmu shikenan rayuwarmu zata taɓarɓare, gaskiya wannan ba tunani me kyau bani adu sanda muka tsinci kanmu cikin yanayin maraici ko ƙuncin rayuwa ko rashin wani abu me muhimmanci godiya ya kamata muyi ga ubangiji sannan mu fuskanci rayuwa adu yanda tazo mana, Ubangiji shike wadatamu sannan kuma ya karɓa daga garemu du sanda yaga dama mukasance masu hamdala da godiya adu sanda muka samu ko muka rasa Allah ya jiƙan iyayen da ƴan uwanmu ya sadasu da rahamarsa ya kyautata makwancinsu ya rahamshe su, mu kuma ya kyautata rayuwarya ya albarkacemu yasa mucika da kyau da imani Allahumma ameen🤲🤲.)

Jinjina kai Kanzul yayi hoton abin da ya faru shekaru ashirin baya na haskawa a idonsa kamar yanzun abin ke faruwa.

******
Aljani Kabisatul ƙamaru shine shugaban dake jagorantar jinsin fararen Aljanu wanda suka kasance haske shine tambarinsu, mafiya yawancinsu musulmai ne sai ƙalilan daga ciki, basuda wani yawa na azo a gani sun kasance halittar Aljanu mafiya ƙaranci a duniya, babu wata ƙabila da jinsi na Aljanu da basu san da su ba, saboda sunada wani irin kwarjini haɗi da tasiri wanda ƙarfin ibada da kuma riƙo da addini da suka yi ne sila.
    Basa cutarwa hasalima sukan taimakawa wanda aka zalunta, wannan ya saka sam basu shan innuwa da jinsin jajaye da baƙaƙen aljanu kasancewarsu mugaye na gaban ƙarshe, gaba ɗaya rayuwarsu ta tattaru ne wajen biyayya ga gafalallun mutane inda suke biyansu da jinin mutane ƴan uwansu suna yi musu aiki, asiri tsafi da bokanci.
        Duda kasancewar jinsin fararen Aljanu basuda yawa amma sunada ƙarfin iko adu inda suke, jajaye da baƙaƙen Aljannu da tsoronsu saboda ƙwarewa dasuka yi wajen warware musu aiyukansu na zalunci gashi babu yanda suka iya da su.
    Ko a cikin jinsin fararen Alhanu akwai wani aljani da   suke alfahari da shi, shiɗin ya kasance bawa da mahaifansa suka sadaukar da shi wa shugabansu me adalci wato Kabisatul ƙamaru wannan aljanin ba kowa bane face Kanzul mujulu wanda ya kasance bawa na musamman da sarkin fararen Aljanu ke tsananin ji da shi.
    Bayan sun bayarda kanzul sai suka samu ƙaruwa inda suka haifa ma shi ƙani wanda yaci sunan Hanzul Dhakar wanda tunda ya tashi yaji labarin sadaukin ɗan uwansa Kanzul sai shima ya maida kan shi bawa ga sarki dudan ya kasance kusa da ɗan uwansa, du wani aiki a tare suke yin shi ko hidima koma minene Kanzul zai yi to ɗan uwanshi na tare da shi wannan yasa suka taso da wata iriyar shaƙuwa da soyayyar junansu.
     Kasancewar su basa rayuwa a cikin dazuka gaba ɗayansu akan iska suke rayuwa ko cikin manyan tekunan duniya, wannan yasaka basu cika yin rayuwa tare da mutane ba saɓanin Baƙaƙen aljanu dake zama a cikin bishiyu ko dazuka inda yanzu mutane suka mayar da wajajen wajen rayuwarsu, ana sare bishiyu ba bisa ƙa'ida ba wanda hakan ya ke fusata mazauna wajen har suke shiga jikunan mutane suke rayuwa, ana kuma ƙona dazuka mutane na rayuwa a ciki hankulansu a kwance ba tare da sunsan sun taɓo wasu masu rayuwa a wajen ba, ana maida dazukan wajen zama ko wajen yawon shaƙatawa da buɗe ido saboda tsabar jin daɗin rayuwa, ba tare da mun saniba muna janyowa kanmu abinda ze damemu, Allah ya kyauta. 

    A wata ranar asabar da daddare Kanzul na shawagi a kan iska ya je amso wani saƙo da sarki ya aike shi amsowa wajen wani malamin addini me taimako abisa tafarkin Allah wanda yake mu'amala da  jinsinsu wajen taimakawa mutane, ba tare da sanin Kanzul ba ashe Hamzul ya biyo shi a baya ta inda shi ya kasance yana bin iskar ƙasa saɓanin Kanzul daya kasance yana bin iskar dake sama yana shawagi.
    Daga can ƙasa ya jiyo wani gurnani da   tsawa wanda hakan ya tilasta ma shi saukowa ƙasa babu shiri, yana buɗe duka hasken shi tare da ganin abin da ɗan uwanshi ya gani.
    Masu mutane ne mata da miji da ɗiyarsu ɗaya a wani gida, wasu ɓatagari kuma azzalumai suka shiga har inda suke suka kashe su bayan sun nemi dukiyar basu samuba, uwar da uban duka sun mutu sai yarinyar da take cikin wani hali, nan take Hamzalu ya sakarwa mugayen mutanen hasken ya tarwatsa su, kai tsaye Kanzul ya nufi yarinyar tare da ɗaukarta yana jin kanshi wani iri a game da ita, ba tare da tunanin komi ba ya ɗauketa tare da juyawa yabar wajen da ita.
   Hasken da Hamzalu ya saki ne ya haddasa gobara ta tashi a gidan, inda yabi bayan ɗan uwansa  ranshi a mugun ɓace.
    Koda Kanzul yajewa Sarki da yarinyar nan take ya karanci abin da ya faru, sai de nan take ya nuna rashin amincewa akan ta rayu a cikin jinsin Aljannu, yayinda Kanzul yaji sam ba zai iya barin yarinyarba don sosai yake jinta a jikinshi ga kuma tsananin tausayin da take bashi, nan Sarki me adalci ya bashi damar zuwa ya rayu da ita a duniyar mutane domin sam zamanta atare da su ba mai yuwuwa bane ya kuma ce zai neme shi adu sanda buƙatar hakan ta taso yayi mashi hakane don saka ma shi da alkairi akan hidimar da yayi mashi, a ranar Kanzul da Hamzalu suka tattaro suka dawo cikin mutane da zama sukaci gaba da rainon Maryam bayan sun binciko asalin sunanta kenan saide ko kaɗan basu bata damar da zata gane suɗin ba jinsita bane suka raineta tamkar yanda ake rainon ɗan mutum suka zame mata ahali bango abin jinginuwarta sam basu bari tayi kukan maraici ba bayan ta taso suka sanar da ita asalin abin da ya faru da mahaifanta gobara ta cinye su su kuma kakaninta ne, a haka rayuwa taci gaba da tafiya.
*****
A yanzun da Kanzul ke kallon Maryam da tsananin tausayawa abinda ke shirin tinkaro rayuwarta wannan yarinyar da suka ɗauka yake gani wacce ke cikin mawuyacin yanayi tsakanin rayuwa da mutuwa, yana kallonta ne a asalin yanda take a yarintarta.
    "Nifa banda wata damuwa yanzu a duniyar nan data wuce ciwon Kaka shine kawai abin da ke tsananin damuna."
     Sassanyar muryar Maryam ta daki dodo kunen Kanzul wanda hakan ya dawo dashi duniyar zahiri.


Tofa wata sabuwa dama mutum ba rayuwa tare da aljannu 😯😳 ikon Allah me tsayar da wando ko ba zariya.
    Somin taɓi kenan daga cikin cakwakiyar dake sarƙafe da wannan zazzafan labarin me taken ƊAURIN ZUCI nice taku har kullum.

Haƙiƙa naji daɗin addu'o'in agareni nagode sosai masoyana na haƙiƙa Allah ya ƙara mana lafiya baki ɗaya allahumma ameen 🤲.


MARYAM STAR

#Masyamstar
#Ɗaurinzuci
#Hausanovel.