Chapter 25
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍
Chapter 25
Kama hannayenta yayi a cikin na shi yana karanto ƙaddarar da zata faru da ita nan gaba kaɗan, ƙaddarar da bai isa ya hana wanzuwarta ba ƙaddarar da baida wani kataɓus akanta wanda hakan ke nuni da ƙarfin ikon Allah, kuna ana gab da zuwa gaɓarda bazai iya wani kataɓus ko tasiriba a rayuwarta.
A fili kuwa cikin muryar shi ta tsofafi wanda cuta taci ta cinye ya soma faɗin.
"Allah ya albarkaci rayuwarki Allah yaci gaba da baki kariya adu inda kike, sannan ina ƙara roƙonki akan ki riƙe azkar da ibada karkiyi wasa da wannan alƙawarin da kika yi min."
Murmushi ta kuma yi kafin a tausashe ta ce.
" Karka damu kakana nayi maka alƙwari bazanyi sakaci da ibada ba zanci gaba da kasancewa me riƙo da ibada kamar yanda ka koyar da ni Allah ya wadataka da lafiya."
Ta faɗa tana saka hanni ta share ma shi hawayen idonci cike da kulawa.
Suna a wannan yanayin ne aka kirayi sallah wanda hakan ya katse su Kaka Abu ya soma yiwa Kaka Alwala bayan ya gama shima yayi, ita kuma Maryam ta fice tsakar gida domin gabatar da tata sallar, da haka suka yi amfani wajen ɓacewa daga ɗakin zuwa masallacin madina inda suke gudanar da ibadunsu bayan sun bar innuwoyinsu a wajen incase koda zata zo kafin su dawo....
***
MUHAMMAD
Cikin abin da bai rufe sati ɗaya ba wata iriyar azababbiyar ƙauna gami da tausayin Zunaina suka baibaye rayuwarsu, zuwa wannan lokacin ya gana sadaƙarwa akan yabbas ta zama jinin jikin shi du yanda ya ƙware wajen iya pretending ya gaza ɓoye hakan saboda a kullum ƙaunarta daɗuwa take a ƙalbinshi.
Cikin sati ɗayan nan sosai suka shaƙu da junansu suka rungumi ƙaddarar data kusantar da su ga juna, daga sanda Muhammad ya kusanci Zunaina daga lokacin wasu al'ummura suka soma faruwa, daga ciki akwai samub sassauci da zukatansu suka soma yi, sannan kuma yanzun Zunaina na ɗaukar lokaci me tsayi a cikin cikakken hayyacinta, tana gane komi kuma tana fahimta, yanzu gaba ɗaya fatansu bai wuce wu fice daga wajen ba domin suyi rayuwa atare da junansu rayuwa tahar abada.
Shafa lalkausan gashin kan Zunaina daya kwanta luf Muhammad yayi yana jin yanda so, ƙauna, shaƙuwa, haɗi da tsananin tausayinta ke jin jinin jikin shi, cike da kulawa yace.
"Zunainah." Ya kira sunanta da wani yanayi me nuni da tsananin shauƙin da yake ciki.
Lumshe farare tas ɗin idanuwanta Zunaina ta yi tana jin yanda amon muryarsa ke ratsa har can ƙasan zuciyarta, sake ƙanƙame hannun shi dake a ƙirjinta ta yi da wata iriyar kasalalliyar murya can ƙasan maƙoshi ta ce. "Uwummm."
Cigaba da yamutsa sumar kanta Muhammad yayi yanajin ƙaunarta na sabunta kanta a jini da ruhinshi, sannan ya ce.
"Kinsan wanu abu?." Bai jira ta amsaba yaci gaba da faɗin.
"Kafin ki shigo rayuwata ina jin kamar ni kaɗaine banida farinciki rayuwa nayin min tsananin zafi, ak'amurra ba cakuɗe min ina rasa inda zan tsoma kaina inji sanyi, saifa idan ian tare da Aboki, ɗan uwa kuma aminina me share min kukana.
A yanzun kuna da nike tare da ke ina jina cikin tsananin farinciki irin wanda ban taɓa hasashen zan samu ba nan kurkusa banma san da akwai irin wannan faruncikin ba akafatanin rayuwata, ke ɗin kin zama haske a gare ni wacca ta fitar da ni daga cikin ƙungurmin duhu.
Kinsan wani abu?."
Ya sakw jefa mata tambayar yana saka hannunshi ya birkitota ta dawo rigingine yana facing ɗin shi, kai tsaye idanuwansu suka sarƙafe waje ɗaya ta wani irin salo ta lumshe idonta a cikin nashi sannan ta buɗe su warrr akan shi tana fito da girmansu sai kuma ta girgiza ma shi kai alamar a'ah.
Sai da yaja bumfashi me tsayi sannan ya ce yana kallon kyakkyawar fuskarta.
"Sai a yanzu nasan daɗin rayuwa, bayan lokaci ya kusa ƙure min, ina son gyara abinda na ɓata ina so in rayu tare da ke Zunaina ina so ki haifa min kyawawan yara masu tarin yawa waɗanda zasu kore min yanayin kewa da kaɗaicin dana taso a ciki, please kiyi wani a cikin ƙuntataciyar rayuwata."
Ya faɗa wasu ruwa masu kama da hawaye na taruwa a cikin idanuwansa.
Duda yanda jikinta ke amsawa da tsananin azaba haka ta yunƙura ta tashi zaune, tare da matsar da fuskarta a daidai saitin fuskar Muhammad ta yanda har numfashinsu ke haɗuwa tare da cakuɗewa waje ɗaya cikin muryarta data ƙara sanyi fuye da baya ta ce.
"Indai har inada iko da abinda kake so to bakada shamaki komi kake so zan baka, kamar yanda kake ji nima haka nike ji agame da kai abaya sam ban damu da ya rayuwata zata kasance ba amma a yanzu daka kasance atare da ni sai nike jin kwarin gwuiwar gyara rayuwata inkuma faɗaɗata ta yanda zatayi yaɗo ta bazu a sassan duni."
Sai ta kama hannunshi ta ɗora akan cikinta ta danne tare da nata hannun sannan taci gaba da faɗin.
" Bakai kaɗai ba nima ina son tara zuri'a wacce zata zamanto mallakina ne, ina son gina ahali wanda zasu kafu har bayan rayuwata, indai har wannan cikin nawa zai ɗauka to zai haifa maka daga ɗa ɗaya har ƙwaya ɗari bazan taɓa gajiyawa ba."
Ta faɗa idanuwanta a cikin nashi, ta yanda yake karantar zallar gaskiyarta a cikin idanuwanta wanda hakan ke ƙara gwarara shi akan abin da yake shiryawa.
Rungumeta yayi completely a cikin ƙirjinsa yana jin tsananin ƙaunarta na lunkuwa a jininshi, ji yake da ace yanada dama daya haɗiyeta kawai ya huta tsabar yanda yake jinta a ranshi.
Luff Zunaina ta lafe a ƙirjin shi tana sauke numfarfashin gaba ɗaya tausayin rayuwarsu ita da shi na lulluɓeta du yanta take tausayawa kanta jin labarin shi da tayi yasake tabbatar mata lallai yasha gwagwarmayar rayuwa.
Da ace sun san ƙalubalenda yada tunkarosu gadan-gadan da sun sake sakewa da junansu kuma da sun yi wani abu akai wanda zai sauƙaƙa musu zugin dake tafe zuwa garesu.
Suna a wannn yanayin wani barci me nauyi yayi awon gaba dasu lokaci ɗaya batare da sunsan abin da zai faru zuwa gaba ba.
Ɓacin rai kwance akan baƙar fuskar makafa wanda har halittun kan shi ke hayaniyar ɓacin ran da yake ciji, hannun shi riƙe da sandar tsafin shi daya watsa ma su Muhammad tsafin daya saka su barci ba tare da sun sani ba.
Daga gefen shi kuma ƙwaro ne tsaye ya harɗe hannayen shi yana ƙarewa kariyar da Aljani Kanzul ya yi musu.
"Tunda dai munangab da samun cikar burinmu kawai mu farraƙa su ta suyi nesa da juna ta hakane kawai zamu samu abin da muke so cikin sauƙi, ɗaurarrun zukatansu muke so da su zamuyu amfani gangar jiki da ruhinsu bashida wani amfani ka sake su kawai bayan ka tabbatarda ka raba su da juna nasara tamu ce."
Ƙwaro ya faɗa yana zagaye bangon kariyar tare da tunanin ta inda zasu bi su fasa abin, nan take ya gama gane muddin ya taɓa farin bangon tsafin shi zai raunata dan haka sai yaja da baya ta saman iska tare da kallon makafa yace.
"Ka aiwatar kawai na tsananta buncike babu wani matsala nasara tamuce." Ya faɗi tare da bin iskar wajen ya ɓace dan muddin Makafa ya fasa wannan katangar hasken shima nashi tsafin zai raunata shiyasa yayi dabara ya zame kan shi.
Cikin ƙosawa da hayaniyar da halittun kan Makafa ke yi ya tunkari Bangon haske gadan-gadan tare da tattaro duka ƙarfin tsafinsa ya saka wajen rushe shi, sai de kuma abin mamaki ko gezau bangon bai yi ba, haka ya ƙara tattakewa akaro na biyu ya sake aika tsafin shi, ya daddafe da duka ƙarfin shi har sai da yayi nasarar tsaga bangon gida biyu.
Yaraf ya faɗo akan ƙafafuwan shi yana haɗa gumi ya fara maida numfashi kenan ya sake miƙewa a razane ganin Bangon na ƙoƙarin sake haɗe kan shi.
Bai da yayi dagaske har yana haɗa uban gumi sannan ya samu ya ƙara girman ƙofar, bai jinkirta ba wajen saka tsafi ya fito dasu Muhammad dake duniyar barci ya raba su da juna ya tura Muhammad bangon kudu ita kuna Zunaina ya turata bangon arewa, akuma daidai lokacinne bangon hasken ya tarwatse, wanda ya ɗauki Makafa yayi sama da shi can ƙoli sannan ya samo shi ƙasa ya baje a wajen cikin ficewar hankali....
*****
RIMSHA.
Kwance ta ke tana barci, bakinta na motsawa gami da fitar da sauti can ƙasa sosai "Subahanallahi wabihamdihi Subahanallahil azeem."
(Ƴan uwa ku lazimci yin wannan zikiri ako wace rana domi ita cw kalma mafi soyuwa ga Allah kuma mafi nauyi akan ma,auni kuma me sauƙin faɗa akan harshe.)
Can cikin barci ta soma jiyo kamar ana shafata, da farko ta share bata maida kaiba amma jin anci gaba ya saka ta zabura tare da faɗin a razane, "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un."
Da sauri Ƙwaro ya rufe mata baki da tsafinsa yana jin tsigar jikin shi na tashi, yayinda ya sake kwaɗaituwa da siffarta.
Sake ja da baya ta yi tare da ƙanƙame jikinta waje ɗaya tana karanto dukanin addu'ar da tazo bakinta babu ƙaƙƙautawa.
Huci Ƙwaro ya saki tare da shafa sili-silin furfurar kan shi da muryar shi da tsufa ya bayyana ya ce da ita.
"Ki gama gudun amma dole ki zama tawa, hatta Makafa bai isa ya hana ni cimma wannan ƙudurin ba zan waiwayo kine idan na gama cimma burukuna daga nan zanga ƙarshen gudun ruwanki."
Ya faɗa yana ƙarewa siffarta kallo.
Wani tuƙuƙin bacin rai ne ya lulluɓe Rimsha gami da takaicin abin da Ƙwaron ke nufi.
Tattaro duka ƙarfin gwuiwarta ta yi wajen tofa ma shi yawu akan fuskarsa taci gaba da faɗin.
"La'antar Ubangiji da tsinuwarsa su tabbata agareka tsohon banza munafuki."
Sai kuma ta rushe da kukan bain ciki tana jin inama rayuwarta ta tsaya iya nan inama mutuwa ta sauƙaƙa mata tayi awon gaba da ita a yanzu kafin wani abin ya sake ɓullowa, ji take kamar ta ɗora hannu akai taita rusa ihu tsabar gajiya da tai da rayuwa.
Sai de abinda bata saniba shine asalin gwagwarmaya yanzu aka fara, yanzune wasu shafukan zasu buɗe mata wanda bata shirya buɗuwarsu ba.
Ƙwaro kuwa tuni ya yi ɓatan dabo tun lokacin data tofe fuskarshi da yawu ashe yaji ciwo, saboda yawunta akwai iskar azkar ɗin da take kanyi hakan yayi tasiri wajen ƙone fatar wajen wanda hakan ke nuni da ya raunata daga tsafinsa.
****
MALAM
Tun lokacin da Maryam ke tafiya akan hanya yayi nasarar ganinta, bayan tsayin lokaci daya shafe yana nemanta sai gashi asanga yau daya fidda rai yayi tozali da ita, hakan ya saka yacigaba da binta cikin iskar tsafi yana bin bayanta adu inda ta saka ƙafa.
Kamar almara haka yaga tayi ɓatan dabo cikin wani haske, sosai ya ɓata lokaci kafin ya yi nasarar gano inda wannan hasken ya kaita, lokacin daya gane kuwa sai da ya ƙara tsanantawa kanshi tsaro sannan ya tunkari inda take gadan-gadan yana jin ƙarshen wahalar shi ya zo.
Sai de yana gab da cimmata kawai yaga ta shige cikin wani shuri dake wajen, sosai ya tsorata da ganin abin da ta yi wanda lokaci ɗaya ya gane tabbas ba mutum bace aljana ce ita ɗin, dan kuwa saida yayi ƙoƙarin kusantar shurin amma kuma aka saka haske aka dawo da shi, daga nan ya nemi shurin ya rasa.
A mugun razane ya zauna wajen kamar ya ɗora hannu akai ya ɗirma ihu saboda tsabar takaicin kuɓuce ma shi da tayi, sai de ya dake ya tashi ya tafi gudun tonuwar asirin shi, gaba ɗaya ya gaji akan wannan aiki yana buƙatar ganin Huwaila suɗan zanta ga kewarta data addabe shi a ƴan kwanakin da suka yi basa tare, gashi yanzu basuda masauki ako ina saboda an baza hotunan shi ana neman shi yasan idon shi idon mutane sai de wani ba shi ba, ko abinci baya samunci sai de ya yi tsafi ya ɗauka a wajeb wasu, hakama jini ya daina samun wanda zaisha sai de yasha na dabbobi, gashi Makafa yaƙi yafe mashi saima ƙara jadadda ma shi da yayi lallai ya nemo yarinyar aduk inda take dodo nada buƙatarta.
Yanzunma sai de yayi tsafi ya kwana akan itace cikin daji shi kaɗai kamar maye, sau uku yana yunƙuri zuwa gidansu amma abu ya gagara da zarar ya kusanci gidan sai hankalin shi ya tashi, wani zafi me tururi ya dake shi har sai ya matsa nesa da gidan sannan yake samun nutsuwa.....✍🏻
A'ah to ai kaɗanma ka gani Malam inde rayuwace yanzu zaka fara fuskantar ƙalubalenta, yo bakayi cuta da zaluncibama ya aka cika bare kuma harda kisan kai, ai se abinda ka gani.
Allah ya kyautata mu'amalarmu da junanmu ya kwar da tunaninmu da zukatanmu akan zalunci ya ƙarfafa imaninmu ya haskaka zukatanmu Allahumma ameen.
MARYAM STAR CE