ƊAURIN ZUCI

Chapter 29

by @maryamstar248

***

𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
         𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍

    Chapter 29
Da taimakon wasu samari biyu dake wajen aka sakata a mota, kuma kamar ɗaya daga cikinsu yasan bazai iya tuƙin ba sai ya kalle shi tare da faɗin.
    "Oga naga kamar a rikice kake kawo inyi driving ɗin akwai wata ƙaramar privet asibiti anan sabon layi SAHEL CLINIC sai muje can kawai."  Babu musu ya sauka tare da yiwa matashin godiya ya koma mazaunin me zaman banza ya dafe kan shi da hannuwa bibbiyu.

Emergency aka nufa da ita direct tare da soma bata taimakon gaugawa har aka samu aka cetota ta farfaɗo daga suman da tayi.

      Waya Junaid ya ɗauka tare da turawa Uncle guntun massage.
   'Karkujini shiru ina hospital na kaɗe wata and nima bana jin daɗi.'
   Bayan ya tura ya nemi ganin likita jiri na kwasar shi, yasan de ya zauna akan kujera bayan wanda ya tuƙo shi ya taimaka ma shi ya riƙe hanun shi gani kamar yana jin jiri, daga nan bai sake sanin inda yake ba.



  UNCLE
"Wallahi Fahad na soma gajiya da halin Junaid ana tausaya ma shi amma sam shi baya tausayawa kan shi, ka duba ka gani sarai yasan halin da muke ciki shi ne yake ƙoƙari ƙara jefamu a wani yanayi."  Ya faɗa ɓacin rai na bayyana a muryar shi.
   Nisawa Fahad ya yi tare da jinjina al'amarin Junaid sannan cike da son fahimtar da Uncle ya ce.
    "Dani da kai duka munsan waye Junaid, baya taɓa yadda yayi abin da yake kuskure ko cutarwa ba tare da wani babban dalilina.
    Mi yasa idonka zai rufe akan abin da kasan gaskiya ne, ka fi kowa sanin waye shi, kamar yanda kafi kowa sanin hali da ɗabi'ar shi, kasan ba zaka goya ma shi bayaba akan abin da ya saka gaba mi yasa zaka saka ya dawo ƙasar nan, ƙasarda yayiwa kan shi alƙawari akan bazai sake waiwayarta ba, ƙasardata zama silar ɗaure zuciyar shi da tarin raunuka, ya kamata ka dinga waiwayen abubuwan da suka faru a baya, shin ka mance tarin abubuwa da muhimman aiyukan daya baro acan Dubai yazo nan duda yayiwa kan shi alƙawarin bazai sake takowa Nigeria ba???."
     Fahad ya faɗa shuɗaɗɗun lamurran da suka faru a baya suna dawowa dalla-dallah a kwanyar shi.
    "Lock Fahad wannan ba hujja bace da zai yi amfani da ita wajen cusa kan shi a abinda ya kasance hatsari ga rayuwar shi, shin kasan maganar wa yake, kasan shirin shi ana tunkarar azzalumin mutumin can ne, ko kasan har yanzu  bai cire Muhammad daga ran shi ba."
    Ya faɗa a ɗan hasale.
    "Wane mutumi ne zai tunkara?
    Sannan akan wane muhammad kake magana, and minene shirin shi na gaba da ni ban saniba?."
     Fahad ya faɗa aɗan rikice yana ƙoƙarin daidaita nutsuwar shi waje ɗaya ta hanyar hana kan shi yarda da tunanin da ke yawo a kwanyar shi.
     "No Fahad ka gazkaga tunani da zuciyarka abin da kake ƙoƙarin ɓoyewa shi nike nufi shin har yanzun  kana ganin laifin ko har yanun kana tunanin banyi ma shi adalci ba, shifa ɗan uwanmu ne tare muka taso tun ƙuruci miyasa bazanji zafi ba idan ƙaddara mummuna irin wacce ta auku a rayuwar shi, kana tunanin zai iya haƙura da bibiyar abin da ya faru tun shekarun baya, kana tunanin shiru da kuma nisan da yayi zasu tashi a banza, to tabbas kayi kuskure domin kuwa ni nasan waye Junaid kuma nasan abin da zai iya aikatawa, na tsani alaƙar shi da wannan yaron Muhammad na tsani du wani abu da zai dangantasu da juna na tsani shaƙar numfashin da yake yi a doron ƙasa shiɗin annoba ne kuma fitina ne."
      Uncle ya fad'a ran shi na kuma 'baci."
"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'um, Allah kai kad'ai muke da a wannan yanayin Allah ka karkatar da hankalin d'an uwanmu daga fuskantar abinda ya ke 'kalubale a rayuwar shi, Allah ka sau'ka'ka zuciyar shi ka sassauta ma shi rad'ad'i da azabar da ya kwashe shekaru a cikinta." Fahad ya fad'i hawaye na gangarowa daga idon shi saboda tuna mummunan abin da ya faru da su a shekarun da suka shud'e.


Hawaye ne suka 'ballewa Saminaka lokacin da yake jiyo firar su, tunda maganar shi ta d'auke bai ta'ba jin takaici da damuwar hakanba sai a yau da aka zo wajenda maganar shi keda muhimmanci amma kuma babu baki, da ace yana da ikon magana daya kirasu sun matso kusa da shi sannan ya ce musu.
    "Muhammad  da Fahad ku rabu da  Junaid yayi abin da ya dace a lamarin nan, domin kuwa yafiku gaskiya da hangen nesa, shi zai iya hasashen abin da zai faru saboda yanada basira, ko babu komi yana fafukar neman warken maganin dam'bareren ciwon da ke zubda jini ba dare ba rana a zuciyar shi, ni da shi muna cikin wani yanayi da ba kowane zai gane hakan ba sai mu da abin ya shafa, ku daina shiga ralurran shi kuna yin kane-kane kawai kubi shi da addu'ar fatan alkairi da fatan nasara."
    Amma yanzu ba hali babu yalin da zai yi musu bayanin da zai gamsar da su.

Tunanin sanda rayuwar shi ta fara ya soma yi da kuma yanda ta kai shi matakai mabanbanta har zuwa yanayin data dawo da shi a yanzun.
WANENE SAMINAKA?
   MIYE ABINDA YA FARU DA RAYUWAR SHI CAN BAYA???.
ku cigaba da kasancewa tare da ni domin warware muku asalin zaren labarin.

****

Numfashi haɗe da huci Ƙwaro ke saukewa yana jin tsananin buƙatuwar son kasancewa da abin da yake ba halilinsa ba.
    Wata arniyar dariya ya saki tuna abin da zai iya faruwa da MAKAFA muddin ya tarwatsa wannan bangon sihirin, da hannun shi yayi amfani wajen yi tsafi ya hasko MAKAFA.

    Kwance ya ke yanata faman tari wanda ke fita tare da baƙin hayaƙi, da alama ba iya shi kaɗai ba hatta da halittun kan shi suma sun taɓu wanda hakan ke nuni da tabbas akwai ƙalubale a lafiyar makafan.
    Nishaɗi ne ya bayyana a kan fuskar Ƙwaro yana ji a ran shi ankusa isa matakin da yake jiran a je, ya kusa nunawa MAKAFA har yanzu yana ƙasa da shi.
   "Yanzun wasan zai Fara Abdullahi Makafa ganinka a haka na bani nishaɗi tare da tunatar da ni yanda na shigo da kai rayuwata."
     Ya faɗa hotunan abubuwan da suka shuɗe na dawowa tar akan shi kamar yanzu ne abin ke wakana.
             TUNA BAYA
        WAYE ƘWARO
  WAYE MAKAFA?

MADARASATUL TA'AZIMUL ISLAM.
    Shahararriyar makaranta ce ta addini wacce tai fice da suna a cikin garin Katsina unguwar Malan Niga, makaranta ce data kafa tarihi me tsawo, domin kuwa anjima ana yin karatu a cikinta kasancewarta makarantar allo ta almajirai.
    A wata ranar lahadi da marice wani baƙi ƙirin ɗin almajiri ne rakuɓe jikin bango yana share gwalla, yayinda ƙafar shi ke fitar da jini jikin shi kuma du ƙasa da alama faɗa suka yi.
    Wata ƙerarriyar mota ce ƙirar golf da ake ji da ita a zamanin tayi parking kusa da rumfar makarantar da almajirai keta haramar shirin zama karatun bayan sallar azahar.
    Cak wannan almajirin ya tsayar da kukan da yake yi tare da yin wani irin yunƙuri ya nufi wajen motar kan shi tsaye ya saka hannu ya buɗe jikin shi na ɓari.
     Kallon daga sama har ƙasa Senator Mansur Ashiru yabi baƙin matashin yaron da shi, zuciyar shi na ƙissima ma shi wani abu na daban game da matashin yaron.
   "Ranka ya daɗe dan girman Allah ina neman taimakonka, ko aikin kakkaɓe motocinka ne ka bani."
    Almajirin ya faɗa idon shi kafeM akanMM Senator Mansur Ashiru.
     Isowar malaminsu ne ya saka yaron tashi tare da ja da baya har lokacin bai daina kallon sanata ba.

Sun ɗauki lokaci suna tattaunawa tsakanin malam da Sanata Mansur wanda suke magana yana hangen wannan yaron.

   Almajirin da ake kira da Audu ya koma gefe ya rakuɓe yayinda ya kafe motar da ido ko ƙiftawa baya yi.
      Kuma da Malaminsu yazo ma shi da wani batu wanda ya wanke zuciyar shi fes, saboda tsabar zumuɗi ko jakar kayan shi bai tsaya ɗaukaba kamar yanda Malam ya ce, duda yace ma shi aikin naɗan lokaci ne zai dawo, amma ya saka a ran shi idan ya tafi ya tafi kenan yanda baya ƙaunar wannan karatun baiga abin da zaisa ya dawo makarantarba bayan ya samu fredom, shi ko baiyi aiki a gidan sanata ba indai har yabar makarantar nan tofa buƙatar shi ta biya.
    Ya so ya tsaya sanda wani daga cikin yaran sanatab ya fincike shi tare da janyo shi baya, amam sai tattaurar zuciyar shi taƙi bashi haɗin kai sai ya bangaje matashin ya faɗa cikin motar yana zare ƙananun jajayen idanuwan shi dakw ƙara ma shi muni.
     Nan matashin yahau zagin shi yana tada jijiyoyin wuya kamar zai kai ma shi mangari amaa sai Sanata ya hana ya tada motar tare da saita madubi a saitin Audu yana kallon shi time to time.

Koda suka isa gidan Sanata Audu ya sauko bai wani tsaya ƙarewa gidan kallo ba saboda hakan baya gaban shi, babban burin shi shine ya aiwatar da ƙusurin shi cikin gaugawa ya ƙarawa wandon shi isa, idan yana waje aka yi ajiya bai sata ba hannayen shi sun dinga ƙaiƙayi kenan bai samun salama sai yayi dabara ya sace abun nan, inyaso daga baya bai damuba du irin hukuncin da za'ayi ma shi.....

Kaɗan kenan daga cikin tarihin MAKAFA DA ƘWARO yanzu zamu soma asalin labarin kuci gaba da kasancewa tare da ni.
Wannan page ɗin na masoya novel ɗina ne masu like da comnent harma da masu taya ni da share ina mayuƙar godiya sannan ina alfahari da ku💪🙏🏻.

MARYAM STAR.