Chapter 33
by @barista
BIYU A ƊAYA
(Don't judge a book by its cover)
Page 33
Sayyada barrister
***
YOTA 13
ALAJA ta mik'e ta daidaita tsayuwar, ko kunyar kayan da yake jikinta ba ta ji ba, ga shi ko'inanta rawa yake, ta ce
"Da gaske bana jin daɗin abin da kike yi wa ƴata, za mu saka ƙafar wondo ɗaya da ni dake"
"Kin san yadda nake son Bilqees ko kaina bana so haka, ina ji da ita, ina so na inganta rayuwar ta, ina so ta yi alfahari dani, sai dai naga ita ba haka bane cikin ranta"
"Ki kwantar da hankalin ki babu abin da zai kanja tare da ita, har yanzu tana nan a Angel nata"
"Um ALAJA har wani zurfin ciki take yi min yanzu"
"To ai hakan yana nuni ne da alamun ta girma ta fara yin hankali"
"Ai duk ke ce kika ɓata min ƴa"
"A'a ni dai na gyara ta, kuma da kike cewa ƴar ki ai ni ma ƴata ce"
"Haka ne, sai na sauƙo zan saurareta"
"Ba damuwa zata zauna tare dani, amma ki sani ta kai ta zaɓawa kanta rayuwar da take so"
Girgiza kanta Maman Bilqees ta yi ta ce
"A'a har yanzu da saura"
"To ni dai kin ga tafiyata"
Ta fice, Maman Bilqees ta sauke numfashi da ƙarfi tare da jan tsaki ta kwanta..
****
Bilqees tana zaune a palourn Alaja ta rafka tagumi, sai zancen zuci ta ke yi, Mamanta ta sauya mata lokaci guda kamar ba ita ba, yau ko tausayin da ta ke nunawa a gare ta babu shi, dubi yadda ta cilla mata kayan ta waje, a hankali hawaye suke zubo mata, damuwarta ta ƙaru, haka ma ciwon kanta...
"Angel"
Cewar ALAJA ta zauna a kusa da ita, ta ci gaba da cewa
"Ba ki kwanta bane?"
"Eh Maa, ina jiran shigowar ki ne ko mamata ta sauƙo"
Sauke numfashi ALAJA ta yi tare da cewa
"Kin san mene ne, kawai ki kwanta ki yi bacci zuwa safe sai mu je, don har yanzu bata sauƙo ba"
Kuka Bilqees ta saka, ta ce
"Don Allah Maa ki bata hakuri"
"Mun yi magana, kuma ta sauƙo amma ki kwanta a nan da safe sai ki koma side naku"
Bilqees ta sauke numfashi tare da share hawayen da yake fuskarta ta ce
"To Maa"
"Yawwa Angel, wai ina ki ka je ne?"
"Maa Yallaɓai likita ne yazo"
"Don't tell me angel!"
"Da gaske Maa shi ne"
"Mamaki na yi, amma me ya kawo shi?"
"Cewa ya yi kwana biyu ban yi serving nasa, kuma ma baya ma ganina"
"Oh! So nice"
"Shi ne na fita Mama bata sani ba, da naje kuma ya ce na yi masa rakiya, ashe siyayya zai yi min"
"Me ya saya miki?"
"Maa tsire ne da drinks"
ALAJA ta janyo ledar ta buɗe taga sire da abin sha, ta buɗe ƙamshi ya baɗe su ta ajiye ta ce
"Zauna ki ce abin ki rabu da Mamanki"
Bilqees ta zauna, ALAJA ta damƙo ta saka a bakinta ta ce
"Kai an yi gashi anan, wai tab ya yi daɗi"
Bilqees ta yi murmushi ta ce
"Maa sai kin ga mutane da yawa fa a wajen sai saya ake yi"
"Ba dole ba, kina jin tsire me daɗi haka"
Murmushi Bilqees ta yi suna ci suna shan drinks nasu Abeedah ta shigo ta zauna ta saka hannu ta kai baki ta ce
"Yau soyayyar uwa da ƴarta ne ya tashi?"
ALAJA ta ce
"Eh mana, ko kina da matsala da hakan?"
"Ah wane ni"
Suka cinye tas sannan Bilqees ta wanke hannu ta kinkimo akwatin zuwa ɗakin da Alaja ta ce ta shiga ta kwanta. Ta shigo ta ajiye kayan ta, ɗakinta ne a lokacin da take wajen Alaja daga baya Mamanta ta maida ta wajenta.Ta hau kan bed ta kwanta, da kyar bacci ya ɗauke ta...
WASHE GARI
Zaune take akan dardumar sallah, tana lazimi ta jima a haka sannan ta tashi ta shige toilet dake ɗakin ta watsa ruwa ta fito ta shirya cikin uniform na restaurant ta tuna jakarta na ɗakinsu, ta sauke numfashi ta zauna a bakin bed.
ALAJA ta turo ƙofar ta shigo, tare da cewa
"Good morning my Angel"
"Morning Maa"
Cewar Bilqees ta mik'e tsaye, suka fito ALAJA ta ce
"Tun da kin shirya kawai mu wuce restaurant acen za mu yi breakfast"
"To Maa amma jakata tana ɗakin mu"
"To mu je sai ki ɗauka"
Abeedah ta fito daga ɗakin ALAJA tana hamma ta ce
"Wai har kun shirya?"
Da mamaki Bilqees ke dubanta yaushe Aunty Abeedah ta fara kwana a ɗakin ALAJA?
"Eh Abeedah yanzu ma tafiya za mu yi"
"To sai kun dawo"
Suka fito taga ALAJA bata rufe ƙofa ba haka suka wuce side nasu Bilqees, suna zuwa ALAJA ta ce
"Ki bamu jakarta"
Maman Bilqees dake zaune bata da niyyar tashi, ta ce
"Wane jaka?"
"Mama barka da safiya"
Bata amsa ba, ALAJA ta ɗauko jakarta ta bata suka fito tana ce mata kada ta damu Mama zata sauƙo suka tafi restaurant...
******
Dr Waahab yana tsaye a gaban mirror ya shirya cikin black suit ya yi kyau sosai sai ƙamshi yake yi. Tun da ya tashi yake tunanin Angel ko ciwon kanta ta warke, ya zauna a bakin bed ya saka takalminsa, wayarsa ta yi ringing ya ɗauka ganin Sa'eed ne ya ce
"Sa'eed kamar ka san kana raina kwanakin nan"
"Bro ka kini fah"
"A'a na isa, ya Egypt?"
"Fine fah ya Ghana?"
"Ga shi nan muna cikinta"
Dariya Sa'eed ya yi ya ce
"My man nayi kewarka fah"
"Ya jikin Mommie"
"Da sauƙi, don yanzu tana ɗan iya yin wasu abubuwan da kanta"
"Ah ma sha Allah, ina Suhaima"
"Suna nan lafiya"
Sun ɗan yi hira sannan su ka yi wa juna sallama, Dr Waahab yana shirin mike wa aka yi nocking kofar ya bada izinin shigowa, ya koma ta zauna, Dr Faisal ne ya shigo ya tsaya tare da cewa
"Mu wuce ko"
"Barka da safiya"
Murmushi Dr Faisal ya yi ya ce
"Sorry Sir, morning"
"Kai ka sani"
Dariya Dr Faisal ya yi ya ce
"Bab ce duk ta sa na koma haka"
"Shiyasa na ce kai ka sani"
Murmushi Dr Faisal ya yi suka fito, suka wuce mota, babu jimawa suka bar farfajiyar hotel ɗin...
******
Bilqees suna shigo cikin restaurant kai tsaye ta wuce kitchen ta haɗa musu breakfast ita da Alaja, ta kawo su ka ci, sannan ta koma ta shirya abincin customers, aikin da yawa su Laraba suka taimaka mata, suna aiki suna hira Majada ta ce
"Friend naga an buga invitations card na birthday ki"
Da mamaki Bilqees ta ce
"Yaushe?"
"Um bakina ba ƙanin ƙafata ba, a ɗakin Aunty Abeedah na gani"
"Wai da gaske ne taron?"
Cewar Jumma, Laraba ta ce
"Ni ma naji ana hiran, na ce to akwai chasu"
"Aiko za mu ceshe"
Suna hira Bilqees bata soma baki ba, tunanin Mamanta take yi, ko ta ci abinci ko bata ci ba..
10:00 am na yi, Bilqees ta lallaɓa ta ɗauko jakarta ta fito zuwa islamiyya, ta bayan restaurant ta saka after dressing da niqabinta ta fito a wata makaranta dake kan hanyar shigowa cikin gari anan take zuwa ɗaukan karatu, a wajen wata Malama, tana isowa babu jimawa ta ƙara mata, don ma tana da ƙoƙari sosai a take take iya haddacewa, kasancewar ɗalibai suna da yawa yasa ta nemi alfarma a dinga ƙara mata saboda aiki da take yi.
Tana barin islamiyya ta dawo bakin hotel, sai da ta saya musu Alawa da biscuit sannan ta ƙaraso ta tadda yaran suna nan zaune kamar kullum suna zaman jiranta ta iso tare da cewa
"Barkan ku da safiya abokaina"
Da murna suka taso gare suna
"Oyoyo kyakkyawar Aunty"
Ta yi murmushi tare da cewa
"Kun ga ku sake ni ka da ku kadani"
Su ka yi dariya suka sake ta, ta zauna tare da cewa
"Ko ku fah"
Suka zauna ta raba musu Alawa da biscuit suna murna suna sha, Dr Waahab ya iso ƙamshinsa ne ya ankarar dasu isowarsa da murna su ka yi masa oyoyo, ya shafa kansu ya zauna suka gaishe shi ya amsa, Angel ta ce
"Barka da safiya Uncle"
Da murmushi ya amsa da
"Yawwa barka kyakkyawar Aunty"
Ta sudda kai ƙasa, ya rabawa yaran BOBO da biscuit, suna sha ya sake dubanta ya ce
"Ba zan jima ba, zan tafi muna aiki ne"
"Ok ba damuwa"
"Ya ciwon kan?"
"Da sauƙi"
"To Malama bye na tafi"
Yaga qur'an a cikin jakarta yasa ya ce da ita Malama, ta sauke numfashi suka haɗa idanu ta ce
"Allah ya taimaka"
"Amin, a shirya min special dinner"
"In sha Allahu"
Ya bar wajen, ita ma yaran suna barin wajen ta koma restaurant.
*******
8:00 pm daidai Dr Waahab ya iso cikin restaurant, ya zauna a teburin sa, Bilqees ta fito ɗauke da madaidaicin tray da ta shirya masa dinner akai ta kawo, ta fahimci shi ba mutum bane me son cin abinci me nawi musamman ma abincin dare.
Ta jera masa a nutse sannan ta ce
"Uncle ya aiki"
"Da godiya Mommie nah"
Ta ɗan kalle shi ta ce
"Na gode da siyayya"
"Ba siyayya bane kayan dubeya ne"
"Siyayya ne"
Ta faɗa a hankali"
Ya yi murmushi ya ɗauki shayin gargajiya da ta zuba masa ya karɓa sannan ya ce
"Ina Mama?"
"Tana nan lafiya kalau"
"To ya yi kyau, ki gaishe ta"
"Za ta ji in sha Allahu"
Ta bar wajen ta dawo kitchen, ta ɗan jima sannan ta koma dining area ta tadda ya kammala cin abinci, ta ce
"Uncle kana buƙatar wani abu kuma?"
"A'a"
"To zan koma kitchen"
"Ba damuwa ni ma yanzu zan koma hotel duk na gaji"
"To Uncle sai gobe"
"Bye"
Ta koma ciki, bata fito ba sai da lokacin tashin su ya yi sannan suka dawo gida, ɗakin su ta nufa, a hankali ta shigo ta yi sallama Mama ta amsa ba tare da ta ɗago ba, ta zauna kusa da Mamanta ta ce
"Mama don Allah ki yi hakuri"
"Kin girma Bilkisu, ki yi abin da kike so"
"A'a Mama zan faɗa miki komai da komai"
"Ki koma wajen ALAJA tun da ta fini kulawa dake"
"Mama don Allah ki yi hakuri ba zan jure fushin da kike yi dani ba"
"Waye yake zuwa wajen ki?"
"Mutumin da nake yi wa aiki a restaurant ne yazo dubani ya ce kwana biyu bai ganni ba ko lafiya"
"Bayan wannan?"
"Babu komai Mama, kuma duk fitan da nake yi wajensa nake zuwa"
"A ina kuke haɗuwa?"
"Nan dakalin shagon John ne"
"To in kina so mu shirya duk abin da za ki yi sai kin sanar dani sannan ki aiwatar"
"In sha Allahu Mama"
"Je ki taho da kayanki"
"To Mama"
Ta mik'e ta fito zuwa side ALAJA ta taddata zaune, ta iso tare da cewa
"ALAJA Mama ta sauƙo ta ce na dawo bangaren mu"
"To ita ta sani ga nan invitations card na birthday party ki, sai ki gayyaci duk wanda kike so, akwai gate pass ma"
"To Maa na gode sosai"
"Kwashe ki tafi dasu, ni ma na ɗauki nawa"
Bilqees ta ɗauka sannan ta shigo ɗaki ta ɗauki akwatinta ta dawo ɗakin Mamanta tana murna, ta nuna mata katin gayyatar da Alaja ta bata, Mamanta ba ta ce komai ba, har suka kwanta....
******************
Bayan kwanaki
Bilqees ta saki ranta, tana aikinta ta rabu da ciwon kai tun da Mamanta ta sauƙo shirye-shiryen birthday party su ke yi da Alaja, sai gyara Tumbin Giwa ake yi, sun raba katin gayyata, kowa jiran ranar yake yi yaga wainar da za a toya, mamaki suke yi, wai ALAJA ta shirya bikin cikan shekaru ashirin da biyu na Bilqees...
Duk da ana shirye-shiryen hakan bai hana su maida hankali a kan restaurant ba, Bilqees tana zuwa aiki kuma tana zuwa ɗaukan karatun Alqur'ani, sannan tana zuwa aiki hotel a kowanne sati.
Yau ma haka kasancewar Sunday ne, bayan sun zo restaurant ne ta shiryawa Yallaɓai likita abin breakfast ta a food carrier ta ɗauko ta kawo masa hotel, ta yi nocking shiru, ta tsaya na wani lokaci sannan ya buɗe, sanye yake da jallabiya baƙa tayi masa kyau, ya ɗan dawo ciki, ta shigo ta ajiye food carrier ta ce
"Barka da safiya Yallaɓai likita"
A hankali ya zauna a bakin bed ya amsa da
"Sannu Mommie nah"
Yadda taji muryar sa yasa ta ɗago suka haɗa ido, kamar baya jin daɗi, amma ta sudda kai tare da cewa
"Ina zan fara gyara wa?"
Shiru da yayi ne yasa ta kalle shi, ya sauke numfashi ya ɗan ɗaure ya ce
"Yau kuma tambaya ta za ayi in da za a fara gyarawa"
Ta kasa magana, ya mik'e tare da cewa
"Ki kawo min abinci na palour"
"To"
Ta faɗa ta gyara jakarta dake maƙale a abayanta, ta iso palour ta ajiye, tana ƙoƙarin barin wajen ya ce
"Ki zuba min na ci"
Ta dube shi taga ya langwaɓe jikinta kujera yana kallon ta, ta duka ƙasa ta buɗe shayin gargajiya ta zuba masa a mug da tazo da shi sannan ta zuba masa Farfesun kayan ciki da dafa masa, da soyayyar doya, ta ajiye amma ya ce
"Miƙo min"
Ta miƙa masa, yasa hannu ya karɓa, yana kallon uniform dake jikinta, ganin duk ya fito mata da shapes nata yasa ya ɗan ɗauke kansa ya kurɓi tea ya ce
"Kamar kullum daɗin da"
Tana wasa da siraran yatsun hannunta, kanta a ƙasa bata ce komai ba, har ya kai Farfesun kayan cikin bakinsa ya tauna ya haɗiye sannan ya ce
"C'est délicieux"
It's delicious ya faɗa ya yi daɗi, ta kasa ɗagowa, kwarjini yake yi mata, tana jin nawinsa, she doesn't want to make eye contact with him, ya sauke numfashi tare da cewa
"Yau bana jin daɗi"
Da sauri ta ɗago cikin tausayawa ta ce
"Sannu"
"Yawwa"
Ya faɗa ta mik'e ta fito ta gyara masa ɗakinsa, ta jima a toilet sai da ta tsaftace sannan ta fito ta tadda yana zaune bakin bed ta wuce palour ta tattare wajen sannan ta gyara ko'ina, tana ƙoƙarin maida kayan cikin food carrier ya shigo palour ya zauna kan kujerar dake kusa da ita, ta ɗan yi baya amma ya yi mata nuni da ta zauna, ta zauna..
"Angel"
Bata ɗago ba ta ce
"Na'am"
"Ba haka Angel take ba, wannan fuskar Bilqees ce, yau fuskar Angel nake so za mu yi hira"
A hankali ta ɗago suka kalli juna, ta ce
"Ya jikinka?"
"Da sauƙi"
Ta ɗauko jakarta ta fiddo da katin gayyata ta miƙa masa ya karɓa ya karanta sannan ya ce
"Um birthday girl"
Ta yi murmushi, ya sake cewa
"Ko lady ce"
"A'a girl ce"
"To ya za ayi ni ban cika zuwa irin wannan gayyatar ba"
Suna kallon juna ta ce
"Ba komai"
"Ba ki ji daɗi ba?"
"A'a Uncle ai baka zuwa ne"
"Gaskiya bana zuwa, amma me ya haɗa Malama da bikin birthday?"
"ALAJA ce ta shirya min"
"Ok na fahimta, na gani ma next week ne"
"Eh to Allah yasa ayi taro lafiya"
"Amin"
"Kwanaki na ce ina so na haɗu da mahaifinki"
Ƙirjinta ya buga, ta ɗago tana kallon sa, ya ci gaba da cewa
"Yanzu zai yu mu haɗu?"
Idanunta suka ciko da kwalla, ta ce
"A'a"
Da mamaki ya ce
"Don me sa?"
"Baya raye"
Jikin Dr Waahab ya yi sanyi, yana kallonta ganin ta sudda kai ƙasa yasa ya ɗan dawo kusa da ita ya kira sunanta, ta kasa ɗagowa, tana jin ya cika ta da yawa, tana ganin girmansa, ga wani ƙamshin turare da yake yi, ya yi magana cikin sanyin murya
"Ki yi hakuri, ban san cewa baya raye ba, na takura sai na haɗu da shi"
"Ba komai"
Ta faɗa kanta still a ƙasa, hannu ya saka karo na farko yaji yana so ya ɗago da fuskarta, bata hana shi ba, sai dai kirjinta ya sananta bugu, ya kurawa fuskar ido yaga hawaye take yi, a hankali ya ce
"I'm sorry Angel"
Da ƙyar ta sauke ajiyar zuciya, ta ji ya ce
"Yaushe ya rasu?"
"Ina ƙarama"
"Ok ba ki taɓa ganinsa ba?"
"Eh bana iya tuno komai da yake lokacin"
"Shikenan, kin ji I'm with you"
Ta gyaɗa masa kanta alamun to, ya sauke hannun sa, sannan ya ce
"Kina tare da Mamanki, what i mean ku biyu ku ke rayuwa"
"Eh sai kuma ALAJA"
"Ita ma ƴar'uwar ku ce?"
"Eh"
"Ok na fahimta, ina takura miki ne?"
Suna kallon juna ta ce
"A'a"
"Kada ki yi shakkar komai, duk abin da ki ke so ko ki ke buƙatar, ko ya shige miki duhu ki tunkare ni kin ji"
"To na gode"
"Ba komai, za ki iya tafiya"
Ta mik'e za ta ɗauki food carrier ya rigata ɗaukawa ya yi gaba, tabi bayansa har ƙofa, ya buɗe mata, sannan ya miƙa mata tare da cewa
"Take care"
"Thanks"
Ya dawo ciki, ita kuma ta wuce restaurant....
Ayi hakuri da typing errors. Masu yin comments ina godiya kuma ina samun ƙwarin gwiwar yin rubutu. Masu yi min addu'oi ma ina godiya Allah ya bar zumunci.
Duk me son yi min gyara ko shawara ko wani abu kai tsaye ayi min magana ta number na dake saman page.
Comment and share fisabilillah