RABO DA KADDARA

Page 7

by @mrsclassywrite


Jazzeelah ta fara. Daya... kafarta na rawa. Biyu... skirt dinta na roba mai launin coffee brown ya taso sama kadan, ta ja shi da sauri. Uku... gumi ya fara keto mata duk da kwai sanyi.

Abidah ma haka. Doguwar rigar ta pencil da duwatsu masu sheki na jan kasa, amma tana kokarin tsalle.


part din Hajiya Aisha Miemie wani  labari daban yake faruwa. Baka Jin Karan ko mai sai na AC guda biyu da suke aiki, kamshin turaren wuta na oud da sandal na ratsa falon, kujerun dakin kana gani ba sai a baka irin labarin kudin da suka saye su ba, labule masu tsada, komai na a tsari. daya daga cikin kujeran Hajiya Aisha Miemie ce a zaune. Mace ce mai shekara 50, amma duk wanda ya ganta sai ya ce 38 ko 40 take Fatar ta na haske, da sheki. Ta saka wata atamfa mai tsada ta Exclusive, an yi mata dinkin zaman, .

A gefen Hajiya Aisha Miemie, a kujera daya, Aunty Amarya tana zaune da alama suna magana ne.


A kujera 3 sitter, Hajiya Jumai na zaune. Hajiya Jumai mace ce mai shekara 45, kyakkyawa, mai son kwalliya, fatar ta fara, tana da sheki. Amma yaran ta  suna kiranta da Umma Ita ce mahaifiyar Bahayurah.

Kuma kusa da ita  Bahayurah ne zaune, tana buga kafa, sai faman tauna  chewing gum take.

Bahayurah, idan aka kalle ta, za a iya cewa kyakkyawa ce ta fuska. Fuskarta fara tas, idanu manya masu kyau, hanci dogo, lebe ja, gashi dogo da ta yi masa kitso kalaba. Amma idan aka sauka kasa, jikinta... siririya ce sosai, kwata-kwata bata da shape. Siririya ce kamar maduki, kamar tsinke. Ba ta da hips ba ta da kirji mai cika duwawunta a shafe yake, kafafunta sirara, hannunta ma haka suke. Doguwa ce, Shekarunta 24  amma kwata kwata ba ta da tarbiya,

An haife ta a Kano, amma tana da shekara 8, mahaifinta, Alhaji Bashir, ya dauke ta zuwa Dubai ita da mahaifiyar ta. Alhaji Bashir, mahaifin Bahayurah, mutum ne mai shekaru 58, mai kudi ne sosai. Shi ne mai kamfanin Bashir & Sons Oil & Gas, da kuma shagunan sayar da zinarai a Dubai Gold Souk da kuma a Kano. Mutum ne mai kudi, amma mai hakuri, mai natsuwa, mai daraja. Yana zaune a Dubai sama da shekara 20, yana hada kasuwanci tsakanin Dubai da Nigeria. Ya auri Umma (Hajiya Jumai) tun tana yarinya yar shekara 18, ya dauke ta zuwa Dubai. Umma kuma, duk da mijinta mai kudi ne, ita kanta tana da sana'arta - tana da shagunan lace da atamfa a Dubai da Kano, sunanta Baha Fabrics. Ita ce ta koyawa Bahayurah duk wani abu na kwalliya, amma tarbiyyar  bata koya mata wan nan ba, saboda Bahayurah ta girma a makarantar turawa a American School of Dubai.

Saboda haka, Bahayurah ta girma da halin turawa. Magana daya, sai ta hada da turanci. Tarbiyya babu, kunya babu, shiga babu. Duk abin da take so, shi take yi.

Yau, ta saka wata karamar riga ta crop top black haryana nuna fatan cikinta, da wando Jean mai matsewa wanda ya nuna siririyar kafafunta, da takalmi mai tsini na Steve Madden, sai mayafi  a wuya kawai, kirjinta kadan da ke akwai a waje. tana ta faman tauna chewing gum, tana wasa da iPhone 15 Pro Max dinta, tana snapping.

Hajiya Aisha Miemie ta kalli Umma, ta ce, "Hajiya Amma zuwa yanzu Bahayurah ta kammala university din ta ko, gashi kuma har yanzu bata yi aure ba Allah be kawu ba tukunna,


"Eh wallahi kuya Hajiya A'I lamarin Bahayurah sai ita kwata kwata ba ta so a mata maganan aure,


Tabba haka nake fama da Muhammad kin ga da zasu dai dai ta tsakanin su aida munsha biki, 

Umma ta yi ajiyar zuciya, ta kalli Bahayurah, ta ce, "ita ma Bahayurah Umma ta kalla, kafin cikin shagwaba tace wallahi ina so.

Aunty Amarya (Murshida) da ke gefe, ta daga kai kadan, ta kalli Bahayurah, ta ce a hankali, "Umma, gaskiya ne, yarinya ta girma masha Allah kamar ba ita ba,



Cikin shagwaba ta sake fadin,"Wait, what? Like, are you guys talking about me and MD? Oh my God! Are you serious?" Ta ce da karfi, muryarta na dauke da turanci sosai, tana murmushi mara sauti Dan ita sai yanzu ta tabbatar da akan MD suke magana ba Jameel ba, dan ita kallo daya ta musu lokacin da suka hadu a bangaran Mommy gane ko da tace tana son shi to da wahala ta same shi saboda kwata kwata ba taga sassauci ba,

"Yes! Umma, Miemie, I want him! Like, seriously, I'm obsessed with MD! Wallahi, since the first day I saw him a gidan Daddy, like, last Sallah, I couldn't sleep! I swear! His swag, yadda yake tafiya, yadda yake magana, his voice, even when he's angry, like, it's so hot! So attractive!"

Ta mike tsaye, siririyar jikinta babu shape tana bayyana, ta cigaba da magana, tana cin chewing gum.

"I swear, Umma, I can do anything for him! Anything! Wallahi, ko ya ce in gurfana a kasa, I will kneel down! Ko ya ce in bar Dubai, in bar degree dina, in bar komai, I will leave everything! I don't care! I love him! I love him so much! , I know I'm flat, but I swear, I will do anything! I will cook, I will clean, I will do anything for him! Like, I'm so in love!"

Umma ta bata harara, " mara kunya


Hajiya Aisha Miemie ta ce, "Bahayurah, ki rage sauti. Kuma ki ja mayafinki. MD ba ya son irin wannan shigar. Idan kina son shi, ki nuna dole, ki gyara. Shi mutum ne mai tarbiyya."

Bahayurah ta yi dariya, ta ce, "Miemie, please! This is fashion!! I know I'm skinny and I don't have shape, but I'm sexy! I have flat tummy! I want MD to see me! I want him to notice me! Like, I want him to see my body!"

Aunty Amarya ta girgiza kai, ta ce a hankali, "cikin zuciyarta aiko akwai matsala."

Ana haka MD ya shigo cikin falo kai tsaye corridor ya nufa zai shiga part din shi Jameel biye dashi hannu shi rike da system Miemie tayi kiran shi, sai da yayi Jim ka mar minti uku kafin ya juya yana kallon Jameel da idanuwan nan nashi a tsaitsaye kamar wanda yake gaya mishi ya sanar da Miemie bashi da lokaci a yanzu lokacin shi kurare ne, shiko Jameel kau da kan shi yayi ya wuce ta gefan shi falo ya shiga kafin ya zauna kusa da Miemie cikin gajiya ya bude bake ya gaisar dasu kafin ya kalli Miemie, kauda kai tayi kafin tace na kira ka ne ga Bahayurah ina so ku dai dai ta kan ku sai mu ajiye lokacin biki, wani irin kallo yake ma Miemie kamar be san me take fadin ba, ita ma cikin tsare gida ta daga mishi kai take fadin ko baka ji bane, shima daga mata kai yayi yana mikewa kuma dai dai lokacin da Jameel shima yake fitowa jin kamalaman Miemie sai yaga Lion din na nufar kofan fita shima fridge ya bude ya dauki ruwa ya bishi

Jazzeelah, bayan tsalle na 13, ta fadi kasa gabadaya. Kafafunta sun yi sanyi, sun kasa daukar ta. Ta fadi akan gwiwata  kuka mai karfi ya kwace mata, "Abidah! Kafa na! Kafa na!"

Abidah ta rike ta, ita ma tana kuka, "Jazzee, ki tashi, wallahi MD zai kara fushi!"

Salim da ke tsaye a gefe, ya kasa jurewa, ya juya kai.

A daidai wannan lokacin, motar Alhaji Ma'awiyya, Baba ta shigo gidan  tun kafin yayi part ya hango yaran a kasa, suna kuka, gwiwowinsu sun kumbura, ya tsaya cak, ya ce, "Subhanallah! Me ke faruwa anan? Salim! Me take faruwa ne?"

Salim ya sunkuyar da kai, "Baba, MD ne ya ce su yi tsallen kwado 20, saboda sun fita walima da irin wannan kayan."

Alhaji Baba ya yi shiru, fuskarsa ta canza, " Ku tashi! Ku tashi ku shiga ciki yanzu! Zanga Mahmmadun ai?"

Ya rike su biyu, suna tafiya ker suna kuka, gwiwowinsu na ciwo, ya kai su kai tsaye part din Hajja Kaka.

. Tana zaune a babban falonta, tana karanta Alkur'ani, tana da tasbihi a hannu. Ta ga Alhaji Baba ya shigo da yaran suna kuka,  ta ajiye Alkur'anin da sauri, ta ce, "Wayyo! Me ya same ku? Wayyo Abidah! Jazzeelah!"

Abidah ta fashe da kuka, ta fada mata komai, "Kaka, wallahi mun je walimar Farida ne, Hamma Muhammad ya ce mu yi tsallen kwado 20 zuwa tankin ruwa!"

Hajja Kaka ta dauki sandarta, ta mike da sauri duk da tsufanta, ta fita daga part dinta, tana tafiya da sauri, tana cewa da murya mai karfi, "Muhammad! Muhammad! Ka fito ka ina ne! Ina dan iskan nan yake? Wato yanzu ya zama uban gidan har yana hukunta yara haka? Yaran da bai haife su ba?  Wallahi sai na nuna masa shima haihuwan shi a kayi! Wane irin zalinci ka nuna musu? Ka sa yara mata suna tsallen kwado a gaban gida? Meye laifin su? Sun je walima! Ko a gidan nan an hana zuwa walima ne? Ni ce na ce musu su je! Idan zaka hukunta, ka hukunta ni!"

A wannan lokacin, MD ya dawo daga masallaci. Yana cikin farar jallabiya, hula fara, takalmi kamshi na turaren oud mai tsada na fita daga jikinsa, gemunsa a gyare. Yana tafiya cikin natsuwa, kafada a bude, amma fuskar sa a hade take.

Hajja Kaka ta tsaya a gabansa, ta daka masa tsawa, "Kai! Wane irin yaro ne Kai, kayi da kirji kamar allon manya,  Ka sa yara mata suna tsallen kwado  Meye laifin su?"

MD ya tsai da idanun shi kanta"Hajja, sun saba doka. Sun fita da kayan da na hana su. Sun fita ba tare da driver ba."

Hajja Kaka ta ce, "Doka? Wace doka? Doka ta nuna ka wulakanta su? Ka duba kafafunsu, sun kumbura! Ka duba idanuwansu, sun kumbura da kuka! Ka kira likita yanzu! Ka kira likita