Chapter 31
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍
Chapter 31
Jinjina kai Aminu Dutse ya yi bayan yaji bayanin Laminu sannan ya ce.
"Nan gaba a wane ƙarni kenan za'a iya samun makaran baƙin tsafi, zan so ace ba a wannan zamanin bane a zamanin gaba ne kafin nan an samu wasu sababbin cigaba ta yanda za'a shafe labarin karewar baƙin tsafi koda kuwa mutanen sun bayyana?."
Wannan karon Ƙwaro ne ya yi magana.
"Indai zamuci gaba da samu mutane masu baƙar zuciya irinta Abdullahi Makafa tofa muna gab da cimma nasara, tun farko na shigo da shi rayuwata ne saboda ɗunbin hasken dake baibaye da shi, sannan allon tsafi ya bani nasara ta hanyar haska min amfanin da zai yi a rayuwata musamman a siyasa, yanzu haka da nike maga wannan maganar ta sanadiyyar shi ne na samu cikar burina, yanzunma shi zai zama silla, daga cikin ku du wanda ya shirya to yazo ayi wannan tafiyar tare da shi."
A wannan rana rayuwa Abdullahi ta sauya gaba ɗaya kamar yanda suna shi ya tashi daga Abdullahi ya koma MAKAFA, tun yana jin ƙiyayyar sauyin da ya samu daga gangar jiki da ruhin shi, har ya daina ji, tun yana jin ƙyamar ɗanyan aiyukan da ake saka shi aikatawa harya daina ji tun yana ganin kamar bakan daidai yake ba har ya sadaƙar yayi amana tare da ture kowane tunani yaci gaba da tabka ɓanna a ban ƙasa babu imani bare tausayi nan take ya ke cika du wani aiki ko umarni da oganin shi su Ƙwaro ke ba shi.
Akwai wani babban aiki da ya gagari su Ƙwaro yasha musu kai, bama iya su kaɗai ba du wani matsafi a wannan lokacin sai da duniyar shi ta girgiza, wani aljani ne yayi butulci wa dodonsu na tsafi ya musulunta sannan ya saci wani ɗan ƙaramin akwati me daraja wanda aka ƙera shi da zallar gold ya kaiwa wani babban malamin addini, shi kuma malamin yayiwa ƙanen shi kyautar shi, ganin sun gaga amsar akwatin ikon su yasaka suka sakawa matar ƙanin lamin cuta, akaita magani amma a banza hakan ya saka ya fitar da akwatin ya sayar ba tare da sanin yayan shi ba, lamarin da yasa suka bi akwatin har kasuwa domin su ɗauka amma akai rashin sa'a wani ya siya, inda suka bi bayan wanda ya saya suka gano gidan da yake, amma kuma sai ya sauya wasu abubuwa tare da tsarin akwatin wanda yasaka suka daina ganin inda akwatin yake, koda suka je gidan shi basu same shi ba haka suka kashe shi shida matarsa da ƙaramar ƴarsu, kafin su fice wani haske ya bayyana tare da tarwatsa su, wanda hakan sosai ya taɓa Makafa ya raunata tsafin shi ya jima yana jinya kafin ya dawo daidai, a lokacin kuma ɓaƙaƙen aljanun shi suka fice daga jikin shi, Ƙwaro na sane ya ƙi tankawa akan lamarin yaja bakin shi ya yi shiru yana jiran ganin iyakar Makafa, aiko ko cikakken sati ba'a rufa ba ya jewa Ƙwaro afujajan yana neman taimakon.
Murmushi me cike da manufa Ƙwaro yayi tare da kallon Makafa dake durƙushe a gaban shi bashida banbanci da wancan zamanin illa na shekaru da sauyin rayuwa, yana kallon wannan yaron kuma almajiri daya tsugunna a gaban motar shi da kaya gaje-gaje yana neman ɗauki daga gare shi, a yanzunma haka yake kallon shi yana juya ƙudurin da ke can ƙasan ran shi agame da Makafa sai de wani yanki na zuciyar shi na gargaɗin shi akan hakan, musamman da binciken shi ya tabbatar ma shi bazai taɓa samun abin da ya ƙwallafawa rai ba, ture tunanin da ke yi ma shi zarya ya yi tare da murmusawa sannan ya ce.
"Muddin zaka cigaba da kasancewa a ƙarƙashin sarrafawar ikona tofa ba zan gajiya ba wajen tabbatar maka da cikar burukanka ka je, zanyi maka aiki daga nan zuwa gobe ko jibi aikin da zai kasance tare da kao har abada zan kafe maka jajaye da baƙaƙen aljanu wanda zasu kasance tare da kai suna bautata maka ba zasu taɓa nuna gajiyawa ba matiƙar zaka cigana da shan jini."
Tsananin murna ta kama Makafa ba tare da ya sani ba ya idasa janyo aukuwar ƙaddarar dake bibiyar shi tun soma tarayyar shi da Ƙwaro, batare da yasan asalin gaskiyar abin da Ƙwaro ya shirya ma shi ba ya amince kamar yanda ya saba amincewa da abubuwanda idan za'a tona zuciyar shi sam baya son su.
Wannan shi ne tushe kuma mafari aukawar Makafa ga halaka ƙiri-ƙiri yayinda Ƙwaro ya maida shi sama sosai ta yanda yake jin kan shi kamar yafi kowa yake kuma aikata abubuwan da shi kan shi bai san ta yanda aka yi ya saba aikata su ba, yanzun baya jin komi dan ya kashe rai baya jin kunyar kowa idan zai aikata ɓarna.
Sannu ahankali Ƙwaro yacigaba da cimma muradan shi ta hanyar amfani da Makafa a zahiri Makafa ne babban amma a baɗini yana ƙarƙashin sarrafawar Ƙwaro shi ne me tsarawa yayinda Makafa kuma ke aiwatarwa....
Wannan kenan kaɗan daga labarin asalin alaƙar Ƙwaro da Makafa kuci gaba da biyo ni don jin yanda zata kaya a gaba.
****
CIGABAN LABARI.
Da zoben sihiri Ƙwaro ya yi amfani wajen sanar da abokan ɓarnar shi buƙatar haɗuwar gaugawa domin su tattauna, cikin ƙanƙanin lokaci suka turo da amsar amincewa tare da bin tsafi suka isa wajen da suke haɗuwa domin su tattauna.
A kallon farko da zaka yi musu zasuyi kama da kamillan datijjai, amma kuma akwai wani abu da basu da shi ba iya imani da bushewar zuciyar su ba, harda kwarjini da kamala da kamewa irinta salahan bayi basu da, a kallon farko mutum me kamala zai gane su ɗin ba cikakkun mutanen kirki bane du kuwa da ƙwarewar su wajen iya pritending, badan farin gashin furfura da kuma tsufan da ya bayyana akan fatansu ba tofa da ko kallo ba zasu ishi wasu mutanen ba, amma dayake sun yarda da kan su kamar yanda suka yarda da baƙin tsafinsu ɗari bisa ɗari sai suka kasance ababen girmamawa daga al'umma.
Ƙwaro ne ya fara magana ta hanyar faɗin. "Bayan gaisuwa da jinjina wa dodonmu, haƙiƙa yau ɗin rana ce ta farinciki agare ni, wadda na daɗe ina jiran dodo yayi min irinta amma bata samu ba sai yanzu, kai tsaye bari inje ga abin da ya tara mu yanzu anan wajen, batu ne akan rugujewar wani yanki daga cikin tsafin Makafa saboda yayi jayayya da ɗaya daga cikin jinsin fararen aljannu, ba wannan bane maƙasudin zama ina me farincikin shaida muku yanzu haka na sami wano haske game da mutanen da zasu iya haɗuwa su kawo ƙarshen baƙin tsafi, sannan kuma na samu haske dangane da akwatin da ke aje da ruhin baƙin tsafi."
Wata iriyar zabura Aminu dutse ya yi har sandar hannun shi na faɗuwa cike da mamaki yake faɗin. "Ka gano akwatin ruhi tayaya a ina kuma???."
Shima Alhaji cike da mamaki ya saki baki yana ƙara gyara glashin dake ƙarawa idanuwan shi ƙarfin gani ya tsurawa Ƙwaro ido yana sauraren amsar da zata fito daga bakin shi.
"Hummm bana faɗa muku Abdullahi Makafa shi ne tsanin da zan hau ya kai no matakin nasara ba tun a baya, yanzu haka maganar da nike muku na gabatar da wannan aikin ne cikin sauƙi ta sanadiyyar amfani da shi, shi ɗin ya kasance innuwa da nike fakewa a cikinta, ina sarrafa tunanin shi cikin sauƙi ya yi min aiki komi wahalar shi, anashi tunanin yana ganin kamar ni nike taimakon shi, yayinda a zahiri shi ne yake matuƙar taimakona, ina amfani da lafiya da zuciyar shi dana daɗe da ɗaurewa da baƙar sarƙar tsafi ina cimma muradaina a yanzu haka amfanin shi na gab da ƙarewa a gare ni."
Ya faɗa cikin rashin damuwa.
Jinjina kai Alhaji Laminu yayi tare da faɗin.
"A'a ba ayi haka ba idan ka gama da shi nikam ina so ka bani nima injarraba tawa sa'a tunda na lura shi ne ƙarfinka a yanzu."
Wari baƙin kallo Ƙwaro ya wurgawa Alhaji Laminu tare da faɗin "Kama daina wannan tunanin domin kuwa ni kaɗai ke da iko da shi kamar yanda na samo shi tun yana yaro ya sauya ma shi rayuwa na ɗora shi a turbar da nike so dan haka ni kaɗai zan mori kayana."
"Yanzu dai mu nutsu ayi magana, shin wane haske ne ka gano dangane da baƙin akwatin tsafi, sannan kuma ka gano mutanen da zasu iya karya alkadarin baƙin tsafin su wayene, a ina zamu iya samunsu."
Aminu Dutse yayi tambayar cike da zaƙuwa.
Nuni da sandar shi wacce ta sauya Ƙwaro yayi tare da haska wani hayai daya soma bayyana yana zana siffofin mutane.
"Waɗanda suke da alaƙa kuma baƙin tsafi ya dangani wani daga cikin makusantansu har hakan ya taɓa rayuwar su sune zasu zasu karya alƙadarinmu, abu mafi sauƙi dana gano shine akwai mutane biyu wanda suke hannunmu kuma suma baƙin tsafi ya dangance su, yanzu haka mun ɗaure zukatansu da baƙaƙen saraƙuna mun kuma killace su a cikin kwalbar sihiri da su zamuyu amfani wajen cimma nasarar mallakar ɗaukaka da arziki marar yankewa.
Su huɗu ne zaƙaƙuran jaruman wanda yanzu haka biyu daga ciki sun bayyana kuma suna gab da haska mana saura biyu wanda da zarar sun bayyana daga lokacin aiki zai soma gadan-gadan."
Ya faɗa yana goge zanen hayaƙin da sandar shi, daga haka suka ƙara tattaunawa kaɗan sannan suka watse kowanen au cike da farincikin jin wannan labarin....✍🏻
Akwatin baƙin tsafi????
masu karatu shin kun tuna da akwatin da Abdul ya bawa abokinsa Ahmad, kodai.....
Mutane huɗu masu alaƙa....shin suwaye wannan mutanen????
Kuci gaba da kasancewa tare da ni domin jin ƙarashen labarin nice taku...
MARYAM STAR
@all