Chapter 32
***
***
𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼R
Chapter 32.
JUNAID
Yana iya jin yanda numfashin shi ya soma dawowa sannu a hankali, har ya daidai zuwa lokacin ne kuma ya dawo hayyacinsa, sannu a hankali ya soma buɗe idanuwan shi da yake jin sun yi ma shi nauyi sosai, ya sauke shi akan ya sauke su akan fankar sama da ke jujjuyawa tana bada iska, iskar da yake ji tana shigar har cikin ƙofofin gashin jikin shi, tana saukar da sanyi.
"Sannu Junaid, mike maka ciwo ne, bara in inje in kira Doctor ya ƙara dubaka." Uncle ya faɗi yana juyawa ya fice da sauri.
"Sannu Brother."
Fahad ya faɗa tausayin halin da yake ciki kwance akan fuskar shi.
Kallon shi Junaid yayi da idanuwansa da suka ɗan shige ciki, a hankali cikin sassanyan sauti ya ce.
"Fahad wa kuka baro wajen Abeey naga kai da Uncle a nan??." Ya faɗa yana kafe Fahad ɗin da idanuwansa da suka yi rauni sosai.
"Ai Mommy ta dawo gida jiya, and ta tabbatar min da zata kwana biyu bata fita ba, kuma a wajen Daddyn na barta kafin infito." sai kuma ya ƙara da faɗin "Yanzu na zo babu jimawa dama ina son duba yanayin da kake ciki, amma yanzu zan koma gidan in sha Allah."
Junaid nan take gaban shi ya faɗi jin Fahad ya ambaci Mommy, laluben dalilin da zaisaka abarota ita kaɗai wajen Abeey ɗin shi ba, kai tsaye ya ce da Fahad.
"Fahad tashi ka koma gida please nima yanzun zan taho."
Babu musu Fahad ya miƙe tare da faɗin.
"Get well soon bro, bye." ya faɗa tare da miƙewa ya ture kujerar baya ya doshi ƙofar fita.
Kusan karo suka ci da Uncle daya sanyo kai biye da shi Doctor ne.
"Yauwa Fahad gida zaka koma ko?." Unle ya tambaye shi yana shigowa ciki.
"Ih Uncle yanzu zan koma, Allah ya bashi lafiya."
Ya faɗa a taƙaice tare da ficewa.
Motar da yazo ya ita ya kunna ya shiga, sai ga ɗora kan shi a kan setiyari ya yana jin zuciyar shi na ƙunci akan abin da Junaid da Uncle ke yi na rashin yadda da Mommy, kai tsaye basa nunawa amma yanda sam basu yarda da ita ba abin na sosa zuciyar shi kuma yana jin babu daɗi sosai, koba komi ai mahaifiyar shi ce kodan yanda yake son su tsakani da Allah bai dace ace sun riƙe abin da ta yi shekara da shekaru ba, wanda zuwa yanzun ya kamata ace ya wuce.
Tada motar yayi ya fice daga asibitin, tun kafin ya isa gida ta soma nuna ma shi alamun babu wadatacen mai, hakan ya saka ya rage gudu sosai ya dinga tuƙi a slow har ya iso ƙofar get ɗin gida, kasheta yayi tare da yi mata key ya durfafi get ɗin yana rayawa a ran shi dole yayiwa Uncle magana akan ƙarewar da mai yake da wuri yanzu kuma ba'a cika lura ba wannan shi ne karo na biyu daya fita da mota mai ya ƙare ma shi a hanya.
Da mamaki ya ke knocking amma still ƙofogin duka da ƙarama da get ɗin a kulle, ganin zai ɓatawa kan shi lokaci sai ya janyo waya ya dannan kiran layi security ɗin da ke gadi, a ran shi yana mitar yanda Junaid ya tarkato su suka dawo Katsina, Katsinar da tsarin gidajenta sam basu yi ma shi ba.
Wani tsaki ya doka sanda me gadin ya tabbatar ma shi ai Mommy ce ta aike shi, shi da driver, a fili ya ce.
"Kai Mom ko problem daga dawowarta zata sa a fara issue tafi kowa cika ciki wallahi."
Ya faɗa yana lalibo key ɗin daya amsa tare dana mota a hannun Uncle, cikin sa'a ya samu Extra key wanda Uncle ɗin baya rabo da su, ya buɗe ƙaramar ƙofar yana jinjina nauyin da take da shi da kuma ƙoƙarin da Security ke yi wajen buɗewa da kullewa.
Lokacin daya kama handle ɗin gami da buɗewa sannu a hankali cikin nutsuwar da ta kasance adu wani aiki na shi, sam baya da hayanida da kwaramniya barshi dai da surutu amma ko wajen magana baya da ɗaga sauti, komi na shi a sauƙaƙe kuma asanyaye ya ke, da ace yasan abin da zai gani kenan da tun farko ya fasa shigowa nan ɗin ya haura sama ya watsa ruwa, saboda abin da yake ji na saka ma shi tashin zuciya wato warin asibiti warin Izal da sam baya so.
Ba iya jinin jikin shi ba hatta da ɓargon dake tsakiyar ƙashin shi yana jin yanda yake daskarewa da tsananin tashin hankalin abin da ya gani, Mommy, Mommyn shi daya rasa dalilin Junaid na tsanarta bayan babu abin da ta aika ma shi, idan ma abin da ya faru ne a baya ai ba laifinta bane ita kaɗai kuma ai kuskure ne aka samu.
A yanzun da yake kallonta tana aikata mummunan abu sai ya tsinci zuciyar shi da fatan ba wannan bane dalili, kar wannan abin ya zama dalilin tsanarta da Junaid yayi.
Zai iya rantsewa da ba akan ƙafaguwan shi yake takawa ba, saboda sam baijin wani abu na motsi a jikin shi, kawai de ya tsinci kan shi yana tafiya kamar akan iska tsabar ruɗani da tashin hankalin daya shiga.
Duka hannayensa biyu ya saka, ya ture kwalbar glashin da take zuƙar jinin shi tana zubawa a ciki, nan take kwalbar ta faɗi ƙasa ta tarwatse jinin cikinta ya soma malalewa yana sauya siffa daga kalar shi ta jah zuwa baƙin hayaƙi ya soma tashi yana sama, yayinda kwalbar ta shiga narkewa a ƙasan wajen.
Da wata iriyar razana Mommy ta saki allurar hannunta sanda ta juyo da nittar ɗura jinin data zuƙo na ƙarshe, sai ta yi tozali da Fahad tsaye a bayanta cikin wani kalar yanayi me wutar fassarawa....
Baya kaɗan.
Yau tun asubahi Mommy ta dawo daga tafiyar kasuwancin da tayi, lokacinne kuma Fahad ya fito da zummar fita masallaci anan suka yi clash shi da ita, da tsananin mamaki ya ke kallonta tare da faɗin. "Mommy saukar yaushe, karde kice min yanzu kika iso?." ya faɗa da mamaki yana kallon motarta dake fake a harabar.
"Ih Son yanzun nan na sauka wallahi kwanan hanya muka yi ai, ina sauran ƴan uwan naka ne?." ta faɗa tana leƙen bayan shi kamar tana neman su a wajen.
A taƙaice ya ce da ita, "Ya Jay ba lafiya yana hospital Uncle yaje ya kwana da shi nima dana dawo sallah zanje na dubo shi kafin Daddy ya tashi tun jiya naso zuwa amma Uncle ya hana ni saboda Daddy." ya faɗa a gaggauce jin an haramar tada sallah.
"Okay yanzu ai zaka iya zuwa ni sai in kula da Daddyn naku tunda na dawo Allah ya bashi lafiya." Ta gaɗa wani yanayi na gilmawa ta cikin idanuwanta.
Bin bayan Fahad ta yi da kallo har sai da ya fice sannan ta koma motarta da sauri ta ɗauko wata jaka ranta ƙal zata aiwatar da aikinta cikin sauƙi ba tare da zullumi ba.
Sai da ta tabbatar da Fahad ya ɗauki mota ya fice daga gidan sannan ta ɗauki kayan aikinta ta shige ɗakin Saminaka ta taradda shi kamar yanda aka haska mata shi, hankali kwance ta soma gudanar da aikinta kiran wayarta da aka yi ne ya tsaida ita, ko kusa bata tsammaci dawowar Fahad nan kusa ba bare da aka ce Junaid ne ba lafiya, kuma sai da ta ɗauke hankullan duka ƴan gida bayan ta aiki driver da security saboda bata son kowa ya shigo gidan sai ta gama aikinta....
Cigaba.
Wata iriyar jijjiga Saminaka ya soma yi baƙin hayaƙi na fita daga bakin da hancin shi, lamarin da ya ɗauke hankalin Fahad kenan daga kan Mommy ya koma wajen Daddynshi da ke fizge-fizge yana wani irin nishi da gurnani me tsoratarwa.
Da wannan damar Mommy ta yi amfani taja jakarta ta fice ba tare da saninta ba tayi mantuwa, mantuwar da zata kawo ƙarshen wani abu, abu abu me muhimmanci a rayuwarta.
Kuka Fahad ya fashe da shi tare da ɗaga Daddy ya rungume shi yana kuka kamar ran shi zai fice zuciyar shi na matse a irƙin shi, yayinda kwanyar shi ke hasko ma shi yanayin da yaga Mommy ɗin da kuma zarginta daya ɗarsu a ran shi.
'Sanye ta ke da jajayen kaya, gaba ɗaya jikinta inka cire hannuwanta da suka fito ta cikin faffaɗan hannuwan rigar, hatta da fuskarta a rufe take sai bayan da ta juyo zata zuba jinin sannan ya ganta gaba ɗayanta.
Ba wanna bane babban abin da ya firgita shi, kalaman da ya ji tana ambatar kamar me karanto wani abu, kalamanda lokaci ɗaya suka tayar da tsigar jikon shi, wannan kalaman nata sune suka ƙarfafa zargin shi, sannan kuma ɗibar jinin da take ba abisa ƙa'ida ba taya zata ɗibi jinin Daddyn da yawa har hakan bayan jiya Doctor ya ce jinin jikin shi ya ƙone da yawa gana buƙatar a dinga ƙara ma shi jini after two days, kuma a lokacin sai da ya kirata ya sanar da ita kawaide besan zata dawo ba a yau.'
Kukw ya ci gaba da yi cikin kullewar kai babu abin da yake sai sake matse kan Daddy a ƙirjin shi akamr zai maida shi cikin shi, sam bai damu da amai me warin da Daddyn ke zazzaga ma shi ba.
Sannu a hankali yake takawa bayan sun sauka daga motar, juyawa baya yayi tare da yi ma matar alama akan ta shiga gaban.
Cikin tafiyarta a hankali ta ɗan matsa kusa da su amma bata shiga gabansun ba kamar yanda ya so.
Lumshe ido Junaid yayi, sannan ya buɗe suka cigaba da tafiya shi da Uncle, a main parlor Uncle ya yi mata alama data zauna, shi kuma yabi bayan Jay daya nufi ɗakin Saminaka.
Cak su duka biyun suka tsaya ganin abin da ke faruwa a wajen, kafin suka zabura lokaci ɗaya zukatan su na harbawa suka doshi wajen su Fahad a zafafe.
"Subahanallah." Jay ya furta tare da tsugunawa a wajen ya na kama ƙafar shi ɗaya da yaji wata arniyar azaba na huda shi, ƙurrr ya bi ƴar ƙaramar farar kwalbar data daki lallausar fatar tafin ƙafar shi, nan take ta soma narkewa tana ɓacewa, baƙin jini nayo tsartuwa daga wajen.
Azabure ya miƙe tare da sanne ƙafar ya ƙarasa wajen Abeey ya taimakawa Uncle suka ɓanɓare kan shi da ƙyar daga Ƙirjim Fahad, suna raba su Fahad yayi luuuu baya tare da faɗuwa kamar marar rai.
"Ruwa please Uncle." Junaid ya faɗa tare da kallon Fushar Saminaka da wani baƙin jini keta fitowa ta hancin ci, wani hayaƙi kuma na fita daga bakin shi.
A kiɗime Uncle ya ɗauko goran ruwan zamzam wanda aka tofe da ayyatush shifa ya kawowa Jay a rikice.
Da bisimillah Junaid ya kafawa Samminaka goran ruwan a baki wannan duda wannan baƙin hayaƙin bai daina fitowa ba.
Caraf saminaka ya soma haɗiyar ruwa domin kuwa a yahayin zafin da yake ji a cikin jikin shi babu abin da yake da buƙata irin ruwa wataƙila ya sassauta ma shi azabar data addabi gangar jiki da ruhin shi.
Da janye robar ruwan da Junad ya yi da kuma tahowar wani ƙaƙƙarfan amai da Saminaka ya yi, bai wuce ƙyastawar ido ba.
Riƙe a cikin hannayen Junaid ya dinga kwarara wani irin baƙi ƙirin ɗin amai me tsananin wari, kuma marar kyawun gani.
Idasa rikicewa Uncle ya yi du dauriya irin ta shi ya gagara riƙe kukan daya taho ma shi sai kawai ya duƙe a wajen tare da soma rera kukan shi da dukanin ƙarfin sautin shi.
Lumshe ido Junaid ya yi tare da jingina Saminaka da jikin shi yana jin yanda hucin da naman jikin shi ke yi ke dakar fatar shi da sam bata son zafi.
"Its okay Uncle, finaly ya amayar da komi by now he is fine."
Ya faɗa cike da comfidance.
Yunƙurowa Uncle yayi da azama yana zare idanuwan shi tubarikallah ya ce. "Are you sure, stop ...."
MARYAM STAR...