NUFIN ALLAH

33

by @anisamuhammadyah897

https://www.arewapen.com/book?id=6aa58fbdf7af357fd59c9f87

***

💕 NUFIN ALLAH 💕 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA

Under team yota's amazing pen

Page 3️⃣3️⃣


Bayan auren malam Ali da rukayya papi ya bashi gida da aiki a Company ɗin shi saboda yana da diploma a computer engineering 

Wannan lamarin sai da ya haifar da ƙaramar fitina tsakanin papi da sahura, da kyar ya iya yiwa idon shi kwalli ya tsaya kan ƙafarshi baza'a karɓa gidan ba, dan ita aikin da ya bashi ne kai gidan daya bashi tayar mata da hankali ba, koda tace ayi auren nan ba wai dan rukayya ta ji dadi bane, so take taje ta cigaba da shan wahalar rayuwa a gidan ma ba wai so take taje taji daɗi ba

lamarin da har gurin hajja Saida yaje, ita ce ta tsawatar wa abun dan badan tsufa ya cinye ta ba da ta daɗe da ma lamarin sahura tufka, dan itama ba daga nan ba, ba ta ɗaukar shirme da shiritita ko kaɗan, rashin lafiyar da take fama dashi ga hawan jini ga kuma ciwon ƙafa, ƙaramin hauka ne sahura kawai bata ma papi ba akan wannan lamarin, kuma ba yanda ta iya dan tana bala'in tsoron ƴar tsohuwar nan, shiyasa tana ji tana gani, Ahaka dai zancen ya lafa,

Bayan shekara biyar da auren su, abubuwa na tafiya daidai, sun samu daidaito da fahimtar juna da shaƙuwa tsakanin ta da mijinta,

Rayuwa suke cike da jin daɗi da walwala,suna son junar su, Amman har lokacin Allah bai basu haihuwa ba 

A lokacin juwaira ta gama secondary ta fara zuwa kasu, tana level 4 sauran 1 year ta gama

Suma su muneefa da muneef suna level 2 

Adam da hafeez kamar wasa suka cike wani scholarship na studying a Cairo university, Kuma duk su biyun sun samu tare da wani abokin su shima, su kusan bakwai suka yi applying Amman su uku suka samu, dan suma dai basuyi tunanin zasu samu ba

architecture Adam yayi applying Kuma shi ya samu, shi kuma hafeez mechanical engineering, duk course ɗin nasu 4yrs course ne 

Yanzu sun ci 2 yrs da ƴan kai baifi 1 and a half ya rage su gama su dawo ba

Suna zuwa gidan uncle abdallah idan suna free anan Adam ya saba da jannat ƴar gidan uncle abdallah Wanda itace ta biyu a gurin shi bayan Yusuf babban ɗan shi, su biyu ne yaran shi kawai 

Wani rana ne sunje gidan gaida umma da Ganin sauran ƴanuwanta dan tun sukayi aure baifi sau huɗu taje ba saidai ko idan sun zo

Suna zuwa tayi sama hanyar parlourn umma , maganganu take ji da alamar shashsheƙar kuka kuma Muryar shaheeda ne umma ita kuma nata balai 

shiga tayi, taga shahida zaune kan kujera jikinta du shatin duka, umma na kanta sai masifa take kamar ta auri baki ita kuma sai kuka take zubawa

"Ai wallahi Bazan yarda Ba ai ba cewa nayi bana sonki ba da zasu jibgeki kamar jaka ba ko wata mara gata, wallahi bazata saɓu ba, kuma wallahi sai ya sake ki tunda shi bai da ta ido baida daraja, bai.."

Ganin zancen nata ba ƙarewa zai yi ba yasa ta ƙara yin sallama tana cewa

"Umma ina wuni, meya faru haka, shaheeda meya faru"

"Wannan laanannen mijin nata ne mana, dukanta yayi kamar wanda ya aike jaka da ta kai ƙara itama uwar shi da ƙannen shi suka haɗu suka mata duka wai tana musu rashin kunya, jaka suka samu da zasu dakar mun ƴa, ko saboda ba su suka haifar mun ita ba basu san ciwon rasa ta ba, idan suka kashe mun ita zasu iya mun madadin ta ne"

Duk zuban nan da take wa rukayya ta manta ita wani hali ta saka yaran wasu abaya Amma yanzu tazo tana tada jijiyar wuya dayake nata ne

Akace ranar naka se naka, duk abinda shahida da umma suka mata abaya Saida taji tausayin shahidar Dan ta koɗe ta rame ga fuskarta wurin gefen idonta ya loma alamar naushinta akayi ga bakinta ya kumbura

Kamar ba wannan ƴarkwalisa masifaffiyar yayarta ba, itama zama tayi tana ƙara bata hakuri umma tace

"Daman fa ba tun yau ya fara ba, ashe ɗan giya ne sai yayi maƙil yazo ya mata zagin ƙare dangi wai dan kudin shi kawai ta aure shi da sauran su, yanzu kuma harta kai ƴanuwansa ma su daketa, dan ban taɓa magana ba, to wallahi bazai yuba"

Mamaki da tsoron Allah ne suka cika ran rukayya dan wannan abinda ta shuka ne ta fara girba akan ƴarta kaɗan da kaɗan....

follow and like for more update 🥰


______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***