BABI NA UKU
by @zainabb
Zaren Rayuwar Mu
KWANA BIYU haka muke zama dashi a cikin gida gashi har sati na ƙoƙarin juyowa. Bana son yana min magana amma kuma idan ya min ba zan iya share shi ba. Amma a yanda nake bashi amsa ya kamata ya ɗago I'm simply not interested but Zaid won't just leave.
Ina zaune a parlour tare da waya ta ina dannawa ya shigo. Da sauri na tashi tsaye ina yi kaman zan je na duba abu amma nasan ba dawowa zanyi ba, avoiding nashi kawai ne nake yi.
“Diza, come back here. Why are you avoiding me?” ya faɗa ya kuma riƙe hannuna.
“Zan shiga ciki inaso zan duba wasu takardu na”
“Idan baki dawo ba, zan biyo ki”
“I'll be right back. I promise”
Jin abinda nace yasa ya sake hannuna ya zauna. Ni kuma ba wasu takardu da zan duba amma dai zan dawo tunda yace idan ban dawo ba, ze biyo ni a a ɗakin. Shiga ta a ɗakin da fitowar be yi minti biyar ba.
“Glad you kept your promise” Zaid ya faɗa da dawowa ta.
Murmushi nayi na dole na zauna se ya dawo a kusa dani. “Why are you avoiding me?” yace yana kallo na. Ba tsoron shi nake yi ba kuma ba kunyar shi nake ji ba se nasa idanuna a nashi.
“I'm not avoiding you”
“Of course, you are”
“Ba haka bane. Kasan yanda auren namu yazo. Komai ya faru a gaggauce”
“Baki so irin wannan faruwar ba?”
“Bamu ma fa san juna ba”
“Bamu san juna ba kika ce? Ke da nasani tun muna yara, like teenagers?”
Rufe idanu nayi na buɗe na cigaba da ɗaurawa akan nashi “Mutane suna chanjawa. Baka taɓa sani ba? Shekara nawa yanzu?”
“Zaki cigaba da zama irin wacce nasani tun wancan lokaci”
“Ya kamata ka goge wannan Hadizar kuma. We are now adults not teenagers. Besides, ƴan gidanku basu san na girme ka ba? Mesa bamu haɗu da Muhammad ba?”
“Me ruwan ƴan gidanmu da shekarun matar da na amince na zauna da? Yace min yana tahowa yau”
“Muhammad yasan ni ka aura?”
Girgiza kai yayi “Be sani ba”
Ban sake ce mishi komai ba se waya ta da nake dannawa. Muna zaune haka tare dashi naji sallama. Muryar Muhammad ce tare da wata na mace. Gabana ne ya fara duka se nayi sauri na tashi daga kusa da Zaid ina ji kaman na gudu tun kafin ya ganni amma duk yanda nayi se mun haɗu tare dashi kuma wannan zuwan ganin amaryar Zaid aka zo yi ba Zaid aka taho gani ba.
Amsa musu sallama nayi cikin fara'a. Bayan Muhammad ya gama sauke idanun shi akaina cikin mamaki da kuma murna yace “Hadiza Tahir!”
Murmushi nayi na ɗan kalla Zaid se kuma na maida idanuna akan Muhammad Liman.
“Ko kece amaryar Zaid ban gane ba” Muhammad ya faɗa ya kalle ni kuma ya kalla Zaid.
“Bismillah zauna” na share abinda yace nayi wa wacce ya shigo da ita tayin zama ina jin kamar ƙasa ta buɗe na shige.
Hannuwan shi yayi folding a kirjin shi yana kallon mu nida Zaid “Allah ban gane ba. Zaid, Hadiza ka aura?”
“Ya laƙe min, yaya zanyi?" Na faɗa cikin wasa amma kuma maganar gaskiya ce.
“Ah ah!" Muhammad yace duk mamaki ya ishe shi
“Yaya ka zauna mana. Idan ka zauna se kuyi magana” Zaid yace
“Mamaki ne duk ya ishe ni" Muhammad ya ƙara faɗa se kuma ya zauna. “Dama Hadiza kake so ko yaushe.... menene ya faru?”
Zama nayi daura dashi muka fara hira dama classmate ɗina ne. Zaid shi kuma ya shiga kitchen ya ɗaukowa matar shi desserts da ruwa.
“Kasan ƙanin nan naka fa muna SS3 ya fara cewa yana sona. Na ɗauka duk wasa yake ashe da gaske yake”
“Lokacin yana SS2 ko?"
"Eh, yana SS2”
“Dama kinsan ɗaliban SS2 sun fi na SS3 rashin jin magana. Amma ni ban taɓa sanin ke yake so ba. Ko a gida ban taɓa ji ba. Kuma lokacin da aka ɗaura auren ku, kin san yanda ya taho kuma bana gari. Ai da da naji sunan ki zan gane kece ko kuma nace ji me irin sunan Hadiza Tahir Zaid za shi aura”
Murmushi nayi ina kallon Muhammad. Zaid yace “Ai duk ajin su babu kamar irin ta. Kuma ka gan ta nan Yaya kafin na samu ta yarda dani na sha wahala sosai. Bata ɗauka da gaske nake akan ta ba”
"Da ka taho ka faɗa min da tun yaushe na shawo maka kanta”
Murmushi matar shi tayi. Itama tana da tsawo kyakkyawa da ita amma bata da fuskar fara'a ko kaɗan.
“Ya rayuwa bayan rabuwa kuma? Kin cigaba da karatu? Koda yake nasan ba irin ku ne ake yiwa aure da kun gama secondary ba”
Dariya nayi wacce ban taɓa yi ba tun lokacin da na shigo garin Abuja da maganar zaman aure ya kawo ni.
“Eh, maganar gaskiya mana. Wane field kika je? Nasan de art class kika yi”
“Ahmadu Bello University na Zaria naje bayan mun gama. Kasan na cika Law a chan lokacin rubuta JAMB nawa”
Kallo na Muhammad yayi wholly yace “The Barrister! I know you delivered well”
"Yes, I did” na faɗa mishi tare da motsa jikina da murmushi me faɗi akan fuska ta.
“Kina aiki a Kaduna ne?”
“Eh, ina yi”
“Yanzu kuma fa da kika dawo Abuja?”
“Gani nan dai, we'll sort it out” na faɗa tare da kallon Zaid saboda har yanzu be min maganar aiki ba kuma ina ciki dashi.
“Yes that's good. Zaid knows how to fix that and he will. I'm really happy for you. Congratulations Hadiza Tahir”
“Thank you Muhammad Liman. Now enough about me, what's happened in your life?”
Ruwa ya fara zubawa ya sha yace “I work in NNPC here in Abuja. I recently got married. This is my wife” ya nuna matar dake kusa dashi “Her name is Zainab and she's a student in Baze University studying Radiography”
“Ma Sha Allah, that's great. Nice to meet you Zainab”
“Nice to meet you too Hadiza Tahir. Congratulations on your marriage”
“Congratulations too. Muhammad is a nice guy”
Murmushi tayi ta kalla Muhammad ta mishi fari da idanu. Daga gani suna son junan su har cikin zuciyoyin su.
Bayan sun tafi ne Zaid yake tambaya ta akan aiki.
“Se bayan ka ji ina faɗa” na amsa shi cikin jin takaici da haushi
“Ki yi hakuri ba haka bane ba. Baki tsayawa muyi magana da juna. Yau ne kawai na taɓa ganin kinyi magana me tsawo irin haka”
“Oh really?” na faɗa se kuma na tashi tsaye da sauri na fara tafiya. Tun kafin na isa cikin ɗaki na tsinkaye muryar shi yana cewa “I'm going to be in Port Harcourt this week, Hadiza”
Tsayawa nayi duk haushi ya ishe ni. Da yake faɗa min wannan bayani me zan yi dashi. Ko an faɗa mishi zan tsaya ina kuka ko ina ɓata rai saboda ze tafi Port Harcourt bada jimawa da auren mu? Ni fa idan akwai ya wuce Port Harcourt, to ya tafi ban damu ba. Juyowa nayi nace “And what about it?”
Cikin kamar nuna gajiya ba tare da ya tashi tsaye ba yana nan zaune yana kallo na ɗauke da kallon tausayi amma kuma ba nuna gajiyar halaye na ba yace “We have been married for quite a number of days now, Diza. And we don't act like we are married. We're humans”
“Can you please just cut it and be straight?”
“I'm talking about intimacy”
Tsayawa nayi maganar tana digesting a cikin kaina ina kallon shi. Ni wannan abubuwan duk ban damu da faruwar shi ba. Ko yanzu ya nuna min he want to be really close, I'll let him. “Whenever you are ready, I don't mind” na amsa shi ban jira abinda ze faɗa ba na wuce cikin ɗakin da nafi zama yanzu.
Da dare Zaid ya shige min a jiki sosai saboda na bashi dama. Be saka min gaggawa ga duk abinda yake ba. Na bashi dukkanin haɗin kan da mutum ze buƙata a cikin irin wannan yanayin saboda kawai sunan aure kuma nasan hakkin juna. Ƙoƙari nake yi kar nayi kuka amma jin tsoro duk ya rufe ne yasa ma bugun zuciya ta ya ƙaru sosai. Ina jin muryar Zaid yana faɗa min “are you okay, Diza?” “I'm okay” na amsa shi dashi.
Bayan mun gama abinda muke yi, yana so ya taimaka min a cikin banɗaki na hana shi duk da ina jin wani irin kamar zazzaɓi da yanda ƙafafuwana suke min ciwo amma bana buƙatar taimakon shi. Chanja ɗaki nayi saboda ko kallon shi bana son yi.
Bayan wannan abun ya faru, ya zama very clingy to me Kuma bana so babu yadda zanyi ne. Kuma ina mamakin da yanda yake laƙe min a jiki duk da yana ganin yanda nake ɓata fuska amma wayasani ko baya lura tunda bana yi ta yanda ze gane.
Bayan kwana biyu hutun sati ya shigo kuma a lokacin yake faɗa min ze yi tafiya jirgin su ze tashi da rana. Kallon shi kawai na dinga yi da idanuna nayi shiru ina nazarin me ze je yayi a Port Harcourt kuma wani irin aiki yake.
“Subsea engineer ne ni” ya faɗa min kamar yasan abinda nake tunani
“Oh” nace
Nodding Kai yayi sau ɗaya yace “Nayi magana a wani law firm, ranar Laraba bayan na dawo zamu tafi da takardun ki”
“Private? I don't want to work in a private firm. I prefer government”
Kallo na Zaid yake da mamaki amma be ce komai ba. Chan kuma yace “Zan duba gwamnatin”
Anan parlour muka rabu dashi ko Allah ya tsare ban mishi ba ko rakiya daga fita daga cikin harabar gida ko kuma nayi mishi waving hannu se motar shi ta ɓace kamar yadda naga anayi a cikin finafinai.
Ina nan zaune a parlour riƙe da waya ta saƙo ya shigo. Daga chan sama naga sunan Zaid se na buɗe “Ko Allah ya tsare babu?”
“Allah ya kai lafiya” na rubuta kuma na tura mishi. So nayi na share saƙon nashi amma kuma bana so ya gano wasu halaye na shiyasa na tura. Nasan ko fita daga gate din be yi ba amma kuma ba zuwa zan yi na zama lovey-dovey to him. Abu ne wanda ba zan iya ba.