Babi na biyu
by @maryamlitee
CANJIN BA ZATA
MARYAM IBRAHIM Litee
Babi na biyu
Ni ma na bi ta tana mamutse da ita suka shiga ɗakin, murna yaya Azima take sosai, ita kuma ta faɗa kan Innarmu tana kuka. Mutanen gidan ma kan ka ce me sun cika ɗakin sai da aka natsa kowa ya kama gaban sa sai mu kaɗai. Labari take ta ba ta na bayan bata, zuwa can sai ta zura min ido, "Wai Shuhainar Inna ce ta zama haka? " Jawo ni ta yi, "Ba ki gane ni ba ko? Na ce "Da dai a hanya na hadu da ke zan rinƙa tunanin ina na san ki, dan ko hotunanki da ke akwai ba haka haka kike ba". Ƴar dariya ta yi. Ni kuma mamakin irin kyan da ta ƙara nake, duk da dai dama mutane suna cewa ba me kyanta a ɗakin mu, gata doguwa ce ita, kuma bata da jiki amma tsananin jin dadi yasa fatarta ta murje ta yi lukwi-lukwi kyan fuskarta kuwa ya isa. A ɗakin da Yusuf kaɗai na ga take kama, dan dai shi ba fari ba ne Ita kuwa kalar jikinta wani yallow yallow ta koma dan tsananin kyan da tayi, ɗakinmu kuwa tunda ta shigo tamkar kana a cikin birnin paris tushen turaren saboda tsabar kamshin da yake, wani danƙararren less ne jikinta wanda kallo ɗaya kai masa ya wadatar da kai gane ba na me ƙaramin karfi ba ne. Yaya Azima ta dubi Yusuf amma dai ɗan Ƙanina tafiyar nan ba yau ba ko? " Ya murmusa. Ga fa sister ta iso wane tafiya sai dai kuma lokaci yana kurewa ". Amina ta nemi jin inda za su aka faɗa mata ta ce; jiya bayan mun isa Kaduna na tsaya na saya mata kayan daki ". Yusuf ya ce Kaduna kuka sauka? Ta girgiza kai . Abuja muka sauka. Mun samu mahaifin shi ya gyara ma shi ɗaya daga cikin gidajen shi, kwanan mu biyu, jiya muka isa Kaduna ya ga wani dan uwan shi, ni kuma sai nayi sayayyar anjima kaɗan kayan za su iso, har da kayan kitchen da na saya mata a Dubai dan sai da muka biya ta can har da su kafet su zannuwan gado da labulayya duk an yi sayayyar su. Yaya Azima ta ɗaga hannu sama Allah kai ne Almusawwiru Mun gode maka bisa ga wannan rufin asiri da kayi mana Allah ka kara rufa mana. @@@@@@@@@@ Innar mu kuwa sai dai muka ga ta fadi tayi sujjada kafin ta dago tayi ta sa mana albarka Ta dubi Anty Amina "An tsinke da labari ba'a tanbaye ki mijin na ki ba. Gyara zama tayi "Tare muke sai dai ya ce ba zai shigo yanzu ba
Ta ce "ke baki da saurayi ne? Ummu da ke ta kwalliyar tafiya wajen angon ta , ta tabe baki "Wannan, ai ta dai yi aikin gida, amma duk wanda ya zo , ya ma gaji ya kama kansa, bata sauraron kowa. innar mu tana ganin ta fara kuka, idan aka aiko kiran ta, za ta ce a rabu da ita akwai sauran time. "Amina tayi 'yar dariya, ita kuma ta fice. Innar mu tana tsakar gida in da mutanen gidan ke shan iska. Aminar ma ta fita tsakar gida, shigowar ta naji tana magana. "Inah ka bar Abdullahin?? Ya ce" zan zo wajen matata kuma sai na dakko shi." dai-dai yana zama wata carpet data shimfida masa, ta ce "Amma dai gari ya gari ka dauko shi? Ya ce "kin manta jihar shi ce nan, yanzu haka ya isa katsina." Ta ce "ka hana in maka girki, to me kaci? Ledar dake hannun sa ya miqa mata. cire ma su mama leda guda, ki aje mana guda. "Suna ci tana jan shi da fira, wanda dama magana bata dame shi ba, ban san lokacin da suka tashi ba na dai farka naga innar mu da amina suna ta fira, ba alamar barci, Aunty ummu ce kusa da ni, itama barcin take, da asuba tunda nayi sallah na kwanta, Ina karanta addu'oi'n da ke cikin (hisnul Muslim). Sai da 7:00 tayi, na dora koko. Yusuf ya kawo kosai ( Enough) har da bread. Innar mu ce ta dubi Amina data shigo lokacin tayo brush, ta ce"zaki iya shan kokon kuwa? dan murmushi tayi "ka ji innar mu, ke ki ka sha, 'yan uwana suka sha, sai ni ce ba zan iya ba. Shuhaina zubo min." na ce To, sallamar da aka yi a bakin kofa ne , ya samu saurarawa. Na san ba ni kadai na shiga mamaki ba, kuma ba sallamar na ke mamaki ba, me muryar. Watau baba ya'u Kanin mahaifin mu shi ke bi masa, dan sanin da nayi masa baya hulda da mahaifiyar mu, tun auren su Azima daya kawo wani tsohon mai kudi, ta ce bata san shi, Sai ya ce innar mu ke zuga ta , tun daga nan bai kuma sake bi takan mu ba, balle abinda ya shafe mu. wai tunda an nuna masa iyakar shi. Alhali lokacin da baban mu ke raye, yana cikin wadanda suka fi kowa cin moriyar shi, wai yau shi ne har dakin mu Fakare na yi, in ji da wadda ya zo. Bayan sun gama gaisawa da innar mu, muka gaishe shi "Ashe Amina kin zo? Ta ce "Eh baba." Ya ce " Ai jiya ban shigo gidan da wuri ba, don na je mani, da na dawo kuma na tsaya hira a layin barankaci." Ta ce "mun same ku lafiya? Lafiya kalau, ya mai gidan da iyayen shi? "Ta ce duk suna Lafiya lau, tare ma muka zo." To.to madallah , ai ladi ta bani tsaraba, har da ita dani da yara duka. "Ta ce "Ai bako mai Baba. Ta sa, ummu ta miko mata jakarta ta hannu ta amsa ta zaro Bandir din 'yan Dari biyu ta mika ma baba, "Ga shi ba yawa, baba ayi cefane Godiya ya shiga yi har yana 'yar kwalla, wai ya tuna dan-uwan shi mahaifinmu , niko dariya nake a zuciyata, Ina cewa "kudi masu gida rana, ba wuya sun ruda mutum. Allah ya dora mu kan kudi, kowa san su yake kamar me, dan idan baka da su, sai ka karan rogo ma ya fi ka amfani. Sai na tuna wani malamin mu da ke mana karatun tauhidi a islamiya in da yake ce mana yana daga cikin hikimar Allah ta'ala da ya turo kowane manzo zuwa ga mutanen sa da mu'ujiza. Ga abinda manzon ya zo da shi kuma mu'ujizar manzon tayi dai-dai da abinda mutanen sa suke akai, dan mutanen su gaskata mu'ujizarsa, dan bijiro da imaninsu da cewa lallai wannan daga Allah ta'ala yake, kamar Annabi musa (A.S) mafi yawanci a zamanin sa sihiri ne kuma suna gasgata masu sihiri, sai Allah ya aiko shi da mu'ujizar data ruda duk masu sihiri, kamar kuma Annabi isa( A. S). Allah ya aiko shi ne a zamanin likitanci da ma'abota ilimin dabi'a Sai ya zo masu da mu'ujizar data dace da wannan , ya kasance yana warkar da makafi da kutare da tayar da matattu da izinin Allah, amma manzon mu Annabi Muhammad (S.A. W) an aiko shi a lokacin fasaha da balaga ta magana , sai ya zo masu da mu'ujiza dawwamamma, ita ce Al-kur'ani. Sai malamin namu ya ce da ace a yanzu za'a sake turo Annabi, da me kudi za'a turo, dan mutanen yanzu ba abinda suka fi ganin kimar shi irin naira To haka dai baba ya gama matse-matsen shi, ya tafi , ni kuma na tashi na gyara dakin. Ummu ta kwashe wanke wanke za tayi. [1/13, 5:25 PM]