19
*_BAYA TA HAIHU_*
19
_*Ummu Maher (Mrs green)🍀*_
_My channel_
***
*MATA!MATA!!MATA!!!*
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️
***
*_Mu ta shi mu farka mata_*
*Ina mata masu son yin tallan kaya ana biyansu? Ko da ba ki da jari a hankali za ki samu na ki, ta hanyar tallatawa Ummufadeel FOODMART*
*_Wannan dama ce wacce ke da kanki za ki san cewa zama bai kama ce ki ba, musamman matan da suke zaune babu sana'ar yi, UMMUFADEEL ta zo muku da wane take me sunan MU TASHI MU FARKA inda za ta dinga baku tallah ana fitar dake bayan an siya ba da son zuciya ba, za ta fitar dake riba wacce za ki samu abin adanawa duk wacce ta shirya tallata mata hajarta ta kayan fruit, da irinsu doya, dankalin turawa, dankalin Hausa, fiya, dankalin Hausa, da duk kayan lambu kai har ma da tsirrai, ka ma daga tsiron da ake shuka wa a samu kayan binci da kuma tsiro na flowers wanda ake sanyawa a gida, in sha Allah ba zaku yi nadamar shiga grp ɗinta ba. Ga lambarta a neme ta ta wannan lambar *** ko kuma ta group ɗinta da ke sama_*
Yi join domin ka da a barki a baya ki zama ƴar kallo, ki ga mata na samun riba ke kina zauna, domin yanzu azumi zai zo kuma ba a siyan komi idan ba kayan su nau'ikan doya, dankali, dankalin Hausa, kayan fruit, latas, kabeji, kwakwamba, apple, grapes, strawberry, duk tana siyarwa ke har ma da abin da ke baki sansa ba sai ƴan gayu.
*Wanda ya iya ya huta*💃🏼
_MERO_
Sam ranar bana jin daɗin jikina amma a haka na tashi na ɗora girki ga ciwon marar da yake damuna tun da watan haihuwata ta kama yanzu tun da watan ya kama nake ta rashin lafiya ga kuma matsalar Hammah, sosai nake tuna irin rayuwar da muka shimfiɗa a baya, yadda idan ya dawo yake rungume ni tsam a ƙirjinsa ya yi ta shafa gashin kaina, ni kuma ina jin daɗi ina ƙara shigewa jikinsa a haka har na yi barci, sai na kwanta barci kullum sannan yake kwantawa shima amma yanzu ko ta kaina ma ba ya bi, dana yi magana kuma sai zagi da hantara amma a haka ko mahaifiyarsa ban bari ta gane abin da yake damuna ba, na dai yi shiru da bakina saboda son da nake wa Hammah Habibu.
Ammi ta kula dani sosai dani, saboda haka har ɗakina ta zo ta same ni ta kalle ni sosai ta ce"Mero wai ni kam me yake damunki ne? Sannan alamu sun nuna ba ki da lafiya, bayan hakan akwai abin da kuke ɓoye min domin na ga Habibu duk ya canja ko zama a gida bai san yi shi yasa nake so na ji me yake faruwa?.
Fashe mata da kuka na yi, ina son na faɗa mata kuma ina tunani domin zuciyata ta fara bani cewar na faɗa wani halin da nake ciki ko zai taimake ni amma sanin hakan ke zai haifar yasa nake barin duk wata damuwata a raina.
Ganin ina kuka duk sai Ammi ma ta ruɗe, ta fara rarrashina gami da faɗa min abubuwan da zasu kwantar min da hankali, sannan ta ce na kwanta na yi barci.
Haka na bi umarninta na kwanta ɗin amma ciwon da nake ji ya hana na yi barci tun ina yi a ɗaki Ni kaɗai har dai Ammi ta fara juyi numfarfashina, ai kuwa sai ga ta kamar an jeho ta duk ta bi ta ruɗe baki ɗaya, ta sa aka kira mata Habibu a waya aka faɗa masa Mero tana naƙuda.
A lokacin yana gidan Hafsah, Hafsah na kwance akan ƙirjinsa tana barci ya ɗan janye taa hankali ga mi da kai mata sumba a fuskarta, ai kuwa da sauri ya tashi ya yi wanka ya sanya kayansa sannan ya tashe ta.
Ai kuwa tana ji ance tana naƙuda tuni ta ruɗe amma duk da ta ruɗe ba ta so Habibu ya gane plan ɗinta, ta kira wata likita dama da ita duk suka shirya komi tana gama wayar ta ce su je Surbajo clinics za ta biya kuɗin komi.
Habibu ya ji bati ai tuni ya dinga yi mata godiya gami da yi mata zafafan romance kiss sannan ya tafi, ai kuwa ta kusan sumar da Hafsah saboda a duniya sai ta ga kamar duk mazan duniya ba su iya kiss ba idan ba Habibunta ba.
Kai tsaye asibitin aka kai Mero, wannan likitan ita ce ta karɓi haihuwar Mero sun yi kusan awa biyu suna abu ɗaya sannan likitan ta fito ta cewa su Ammi Mero ta haihu amma yarinyar ta zo ba rai saboda wahalar da ta sha.
Ammi ta ce "amma ita tana lafiya ko?.
Likitan ta ce"Yes mah za ki iya shiga ba". Da ita da Habibu suka shiga kana ganin Mero kasan tasha wahala ga jaririyar can a gefe cikin wani babban abu kamar dai kwali.
Duk da ƴar ta zo ba rai sai da Habibu ya yiwa ƴar huɗu ba da suna Hafsah. Duk da Ammi tana son magana amma sai ta yi shiru ta kyale sa tun da ƴarsa ce yana da zaɓin da zai sanya mata duk sunan da yake so.
A ranar da daddare aka sallamo ni tuni har an je an binne yarinyar sai da yamma na farka da nannauyan barcin da ya ɗauke ni. Sosai na ji kaina ya yi nauyi bayan na farka, na tabbatar da na haihu yanzu sai dai me? Ban ga ɗana a kusa dani ba, alhali lokacin da aka yi min allurar barci na jiyo kukan jariri amma yanzu kuma sai sautin kukan yake dawo min, irin na jaririn da yake neman taimakon a kula da shi tun da aka yi mata wannan allurar ba ta ƙara sanin inda kanta yake ba har sai da ta tashi yanzu.
Ammi ce ta shigo take ce min"sannu Mero kin ta shi? Ya jikin?.
Babu wata kunya irin ta Fulani na ce"Ammi ina yarona?. Ammi ta kasa magana sai kuma ta ga alamar na tsare ta da ido sai ta ce"Allah ya yiwa jaririyar da kika haifa rasuwa yanzu ma haka har an kai ta, tun da kin ga ba za a jira ki har sai kin ta shi ba an dai yi miki adalci an ɗaukar miki hotonta".
Ta faɗa tana mai ƙara rarrashina, na danne zuciyata ba tare da na yi kuka ba amma dai na yi kukan zuci.
***
_HAFSAH_
Dariya suke sosai ita da Billy, Hafsah ta ce"uhum yanzu dai na mallake Habibu sai yadda na yi da shi wallahi ko gidansa sai na lallaɓasa yake tafiya saboda ya ce min wani irin wari take yi, ko kallon fuskarta ma baya son yi saboda yadda take masa muni tamkar dai goggon biri".
Tafawa suka ƙara yi suna dariya, Billy ta ce"yo ai dama na faɗa miki mutum biyu za ki mallaka a lokaci ɗaya sannan kuma sai yadda ma kika yi da su, yi me aka yi da Mero idan ana batun Hafsah".
Dai_dai lokacin ne Humairah ƙanwar su Mero ta koma da baya sosai, ta jingina da jikin bango hawaye Masu zafi suka fara zubo mata, Allah sarki Addah Mero ashe mummunan cin amanar da ake mata kenan? Tabbas Addah Hafsah ta zama azzaluma sawun farko a duniya tun da take a rayuwarta ba ta taɓa jin wannan mummunan abun ba, tabbas dai BAYA TA HAIHU domin kuwa yanzu ne asirin su zai tonu domin ko me za a yi sai ta faɗawa Addanta.
Wasu zafafan hawaye suka zubo mata, ta goge su tana da sauri ko waiwayen gabanta ba ta yi da sauri ta nufo hanyar get da zummar fita.
Sai ta ga an rufe get ɗin ta waje, sosai hankalinta ya ta shi ta zaro ido to waye kuma? Waye ya ganta ko ga ji ta? Ta dinga ambaton innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
Tun daga nan ba ta ƙara sanin inda kanta yake ba, amma dai ta ji kamar saukar wani abu a kanta sai kuma ta faɗi ƙasa jini ya fara bin jikinta nan da nan.
A lokacin da Humairah ta laɓe, Hafsah ta hango gefen mayafinta sosai ta fara murmushi domin tasan koma waye ya ji duk abin da suka tattauna saboda haka tilas ta yi maganin mutum, tuni ta yi saurin fita ta waccan ƙofar ta baya ta rufe get ita kuma Billy ta kwaɗa mata wata ƙatuwar sandar Baba me gadi kafin Hafsah ta kore shi.
Janta suka yi a hankali cikin nutsuwa har zuwa saman benen gidan, suka kai ta wani ɗaki suka ajje ta ga mi da ɗaure ta akan kujera suka sanya mata salatif a bakinta, hannayenta, ƙafafunta, duk sai da suka ɗaure tamkar dai akuya sannan suka fito suka baro ɗakin.
Da daddare Habibu ya zo, Hafsah tana ganinsa ta ji wani abu yarrrr a jikinta, Habibu ya yi mata kyau fiye da kullum son shi a cikin jinin jikinta yake, ba kunya ba tsoron Allah ta tashi ta rungume shi ta shiga aika masa da hot romance tuni ya ɗauke ta tamkar ƴar tsana suka shige ɗaki suka ma manta da zaman Billy a wajen.
Sosai wani irin imani ya shige ran Billy, ta dubi agogon hannunta 11 dai_dai na dare ya baro matarsa ta sunnah ya zo ya tare wa ƴar bariki wacce ta ɗauki zina ba a bakin komi ba, ita dai Billy duk iskancinta wallahi ba za ta yi abin da Hafsah ta yi ba, ƙanwarki uwa ɗaya uba ɗaya amma kuma ace ki rasa wacce za ki ci amanarta sai ita?. Tabbas a yau ba sai gobe ba za ta nunawa Hafsah kuskurenta na yarda da ita a yau za ta kira Mero ta shaida mata komi.
Wayar Hafsah ce a kusa da ita, tasan password ɗinta saboda haka ba ta sha wahala sosai ta danna kiran Mero kira na biyu ta ɗaga saboda dare ya yi a wannan lokacin.
Na ɗaga cikin tsoro ganin lambar Addah Hafsah ce ina ce wa Allah dai yasa lafiya domin ba ta taɓa kirana a wannan lokacin ba.
Ina ɗagawa sai na ji muryar wata, jikina ya fara tsuma hankalina kuma ya tashi na nasan dai cikinta a wannan lokacin bai isa haihuwa ba, to meye matsalar? Allah dai yasa lafiya? Duk a cikin zuciyata nake wannan karanta wasiƙar jakin.
"Nasan baki sanni ba ko? To ki buɗe kunnuwanki ki ji ni kin taɓa ganina a gidanku sau ɗaya shima lokacin Hafsah ce ta aiko ni gidan mijinki, tabbas mijinki da yayar Hafsah suna cin amanarki a bayan fage..."
Da wata irin tsawa na tashi tsaye ina mai ganin duhu-duhu jikina ya fara rawa harsunana suka fara kaɗuwa na ce"ke! Ka da ki ce za ki faɗa min maganar banza wallahi ƙarya kike yi ba ki faɗa min haka idan gaske ne ki kira mana da wayarki sannan idan da gaske ne ki nuna min na gani da idona".
Billy ta ce"idan har wayarki babba ce shiga Whatsapp zan turo miki wani abu".
Ai kuwa nan da nan ta turo min wasu mahaukatan hotuna waɗan da suka kusa haukatae dani, na koma gefa yaf kamar kayan wanki, idanuwa suka ƙafe, zuciya ta bushe sai kukan zuci. Wato wannan shi ne abin da yasa Habibu ya ƙaurace min? Rabon ta da shi yanzu sun kai wajen wata huɗu tun kafin ta haihu ga shi yanzu har ta yi arba'in don ma ƴar ba rai.
Billy ta ƙara kiranta, ta ɗauki wayar tana ji kamar ma ta fara wayar ta kowa ma ya huta tabbas da mutuwarta za ta zo ta same ta tabbas da ta ji daɗi wallahi, saboda wannan ba ƙaramar mummunar ƙaddara bace ace yayarka uwa ɗaya uba ɗaya suna cin amanarka, tabbas abin ya yi muni.
"Nasan kina cikin ɗimuwa da kuma ruɗu amma ki mayar da hankalinki yanzu haka suna gidan Hafsah ɗin kuma a gidanta zai kwana".
Tuni na dafe saitin zuciyata da hannuna, hawaye masu ƙarfi da zafi suka fara fita, ban san lokacin da dana ta shi ba na ɗauki hijabina na sanya shi da ƙer ko takalmi ban sanya ba na buɗe gidan na fice ƙarfe 11:20 dai-dai lokacin ba tsoro ba fargaba tun daga gidanmu har gidan Hafsah sai dana je ranar duk da dama G R A ɗin unguwarmu ne amma da ƴar tazara a ƙalla a mota tafiyar minti ashirin a ƙafa kuma zai kai tafiyar minti arba'in.
Bana ko duba gabana kawai sanya ƙafata nake a ko'ina saboda lukutar masifar da nake ciki wacce ko a tarihi ban taɓa jin ƙazamar rayuwa irin ta Yayata da mijina ba.
Billy ce ta buɗe min gidan, tun da ina tafiya ta ƙars kirana ina kusa da gidan ina shiga ta buɗe min ɗakin su Hafsah ai ban san lokacin dana fito da gudu daga ɗakin ba, riƙe da saitin zuciyata ina haki da neman agaji, Billy ta yi saurin ɗebo min ruwa ta bani nasha. Hafsah da Habibu suka kiɗime a yanayin da na gansu tabbas idan wata macen ce mutuwa za ta yi ma a wajen saboda tsabar masifar dana ke ciki.
Ai kuwa Mero ba ta yi wata-wata ba ta ɗakko wuƙa a kitchen ta yi hanyar ɗakinsu Hafsah Billy tana riƙe ta da ƙarfin tuwo ta warɓar da ita a ƙasa domin burinta dukansu ta kashe su kowa ma ya huta.
Suna ganinta ko wannensu ya shiga taitayinsu ba ta yi wata-wata za ta lumawa Hafsah sai Habibu ya riƙe mata hannunta daga shi sai gajeren wando ina kuka ina tsine musu albarka, yaƙi sakina tuni Hafsah ta kira emergency a wayar Habibu. Dama kuma wajen ba headquarter ɗin ƴan sandan ba nisa, ai kuwa nan da nan suka zo wuƙa a hannun Mero sai ihu take tana cewa "ku barni na kashe su tsinunnu la'anannu in sha Allah ba za ku tsere min ba sai na kashe ku".
A haka ƴansanda suka zo nan da nan suka yi gaba dani, ina ihu ina komi suka kwace wuƙar a hannuna.
Bayan sun tafi dani na shiga tashin hankali idan na tuna yadda na samu Hafsah da Habibu a ranar ne na fara aman jini a police ɗin na faɗi tamkar gawa a cikin sell suka kai ni asibiti nan da nan kuwa likita ya fara gwada ni, ya tabbatar musu da ina da ciwon zuciya zai ɗan riƙe ni kaɗan.
A daren Billy ta yiwa Hafsah ta ƴan bariki ta ce ai wannan ƙanwartata ashe tuni ta faɗawa Mero, ta goge kiran da ta yi saboda kada ta gane domin kuwa ta sha alwashin sai ta ruguza rayuwar Hafsah kamar yadda ta ruguza rayuwar ƙanwarta.
Bayan na samu sauƙi aka shiga kotu, da yake ba ni da wani gata sai Allah Hafsah ta cunkusa musu kuɗi aka ce wai saboda ina baƙin cikin ƴar uwata tana da kuɗi ni ba ni dashi shi yasa naje gidanta domin na kashe ta.
A lokacin na fashe da kuka me ƙonu, na ce"na barku da fitowar rana da faɗuwarta na barku da Allah domin shi ne zai tsaya min saboda haka duk hukuncin da za a yanke a kaina a yanke na ƙwammace ma na yi gidan yari dana dinga ganin mutanen cen biyu".
Na fashe da kuka ina riƙe d saitin zuciyata, tuni alƙali ya yanke min hukuncin zaman gidan yari bisa yunƙurin kisa domin har ƴansanda sun tabbatar da har suka je ina riƙe da wuƙa kuma ina cewa sai na kashe su.
Hukuncin gidan yari life in prison wai saboda na yi yun ƙurin kisa, shi kuma yunƙurin kisa kamar kisa ne.
****
Back to labari
Dai dai Mero ta share hawayenta sannan ta ce"wannan shi ne labarina labarin da ya canja komi na rayuwata tabbas idan na tuna ina jin zafi a zuciyata kuma wallahi ko yanzu da zan gansu sai na kashe su".
Ta faɗi hakan tana kuka.
RABI'ATU DA MAMA suka share hawayensu sannan RABIATU ta ce"tabbas labarin ki ya yi kama da nawa amma nawa ya fi na ki cin amana kafin Mama ta bada na ta bari na baku na wa....
RABIATU
_Garin kano_
Kash! Laifin daɗi karewa, anan na tsaya d book 1 sai ku jira fitowar book 2 anan ne zaku ji labarin RABIATU da wannan tsohuwar Mama.
Wanda labarin Mama d Rabiatu har ya fi na Mero.
Shin Mero za ta fito daga yari kuwa? Shin yaya labarin RABIATU da Mama ya ke? Kun san dai labarin su har ya fi na Mero cin amana? Shin wani irin labari ne? Duk amsar ku sai a book 2 da 3.
Idan kin shirya karanta cigaban tura kuɗinki ta wannan opay ɗin.
7068606171
Opay
RABIATU BASHIR ABDULLAHI
Sai ki tura min shaidar biya ta wannan lambar
***
Ta ku Ummu Maher Mrs green.🍀💃🏼 masu yin arewa ma za a ɗora musu na su.