ƘYAURE KARIYAR GIDA

BOOK ONE CHAPTER ELEVEN

by @hindatuauwal

Kafin ta fahimci abinda yake shirin yi, sai taji laushin leɓunansa a goshinta.


Yayi mata kissing.


A hankali. Cikin kulawa.


"Good night, Aunty"

Sai yamiƙe.

Jamila ta tsaya cak.


Kamar an dakatar da duk wani abu dayake motsi a cikin ɗakin.


Ta kasa motsawa. Ta kasa magana. Ta kasa ko binsa da kallo.


Amma tana jin zuciyar ta. Tana jin yadda take bugawa dasauri.


Yayi min kissing a goshi?


Ta ɗaga hannunta a hankali zuwa goshinta. Wurin da leɓunansa suka taɓa. 

Ta ɗan lumshe idanunta.


Wani irin yanayi ya mamaye ta, wanda bata iya tan tan cewa ko farin ciki ne, ko mamaki, ko kuma wani abu daban.


Taji wani abu yana motsawa a cikin zuciyarta.


Wani abu data daɗe tana ƙoƙarin kauce ma tunanin sa.


Raihan ya kai bakin ƙofa. Ya juyo ya kalleta.


"Good night, Jamila"


A wannan karon, bai kirata Aunty ba.

Sai dai yakira sunanta. A hankali. Kamar yana son tuna mata itace Jamila.


Jamila ta ɗaga idanunta.


"Good night."


Ta amsa cikin wata murya mai laushi.


Yayi murmushi. Sannan ya fita. Ƙofar ta rufe.


Shiru ya mamaye ɗakin.


Jamila ta sauke hannun ta daga goshinta.


Ta kalli ƙofar. Sannan ta sake kallon talabijin ɗin.


Film ɗin yana cigaba da tafiya, amma hankalin ta ya riga yabar wurin.


Ta ɗanyi murmushi. Sai kuma murmushin ya ɓace.

Ta sunkuyar da kanta..Me ya sa nake jin haka?

Ta sake taɓa goshinta.

Me ya sa wannan ƙaramin abu ya sa na kasa samun nutsuwa?

Ta ɗan yi shiru. Jiki a matukar mace ta miƙe ta kashe talabijin din. Ta dawo ta kwanta.

Sannan ta ja bargon gadon ta rufe ƙafafunta.

Amma duk yadda ta yi ƙoƙarin kawar da tunanin, sai ta sake tuna yadda ya sunkuyo gare ta.

Yadda ya tambaye ta ko tana lafiya. Yadda ya zauna yana ba ta labari. Da kuma yadda ya kira ta da sunanta kafin ya fita.

Jamila ta lumshe idanunta.

A hankali ta furta"Raihan..."

Sai ta yi shiru.

Domin ita kanta ba ta san abin da take son faɗa game da shi ba. 



ALIYA

Zaune suke suna kallo. Wani scene a kazo da jarumin ya jawo jarumar sa zuwa bedroom din su dake cike da flowers, kan gadon ma an musu decorations na flowers.



"Wow! Ɗa kinan nan yai kyau. Ustaz kalli moment din."


Kansa ya ɗago daga littafin da yake nazari. Ya kalli talabijin yai wani murmushi yace



"Kar Ki soma wannan mafarkin. A India kawai ake irin wannan soyayyar."



Harshen sa ya datse kalmar ƙarke ta 'soyayya' da wani irin ni san taccen yanayi mai ciwo.


Baki ta buɗe za tai magana se kuma tai shiru. Ta maida dubanta ga talabijin zuciyar ta na soma saƙe-saƙe.


*


Har alla-alla ta dingiyi gari ya waye taje gaida Ummu su haɗu da Ammar abokin katoɓarar ta.



Aikam Ustaz Rayyan na fita ta silale taje gaida Ummu cikin sa'a kuwa taga Ammar zaune yana danna wayarsa.



"Yaya Ammar ina kwana."


"Lafiya ƙalau Aunty Aliya."



Bai cin uzurin dake gaban ta da sai tayi masa raddi akan Auntyn daya kirata dashi.



"Yaya Ammar decorations na keso aimin irinna couples din India a first night ɗin su."



Jin abinda tafaɗa ya sanya Ammar waro idanu yana kallonta.



"Yaya Ammar mana....! Kaga so Ni keyi na burge Ustaz."



Tai ƙasa da muryanta wajen fadi kar Ummu taji.



"Okay akwai wata class mate ɗina da take yi bari na kirata naji."


Tana kallon sa yai dialing numbern ta yakira cikin sa'a kuwa ta ɗaga.


Bayan sun gaisa ya gaya mata dalilin kiransa sai tace insha Allah tana nan zuwa nanda la'asar.



Daga yanda sukai magana zuwa yanda yake tambayar ta kudin da zai bata taƙi fadi ya sanya Aliya gane ba ƙaramin sabo bane atsakanin su.



Dubu ashirin ya tura mata ta opay dinta da guntun sakon tai kudin mashin dashi.



Aliya tai mai godiya tana cewa ta ɗora mai ɗawai niya haka kurum.


Shi kam Ammar farin cikin da yagani akan fuskar ta kadai ya wada ceshi. And ko ba komai ta yine don yayansa.



Maganar gaskiya ba abinda zasu yi su biya Aliya halaccin da tai musu na auren Ustaz.



✨✨✨


Da la'asar mai decorations tazo. Aka shimfida zanin gadonta fari sai akai decorations din flowers red and white. Aka sanya net red color. A ka sanya baloons a ɗakin sannan akai decorating din red and white flowers a tsakar ɗakin da shape ɗin heart.




Kafin Ustaz yadawo zuciyar Aliya har tsallan farin ciki ta keyi.



Yana sallama ta tare sa a falo.


"Welcome my love"


Murmushi yai mai sanyi yana kallon reaction din ta.


"Yau action din India zamuyi dan haka duk abinda nace maka kayi kawai kayi banda gardama"


Tai maganar cikin sanyi da wani side na umarni a muryanta kamar wacce take magana da yaro ɗan shekara uku.



Ustaz ya kalleta ya girgiza kai. Aliya bazata taɓa daina kashe shi da mamaki ba. A baya idan akace zatai duk wadannan abubuwan kai tsaye zai ƙaryata sabida rashin hangota awannan matsayin. Amma yanzu tagama dashi, gajiyar da yakeji ya hanashi magana. Ya....



"Rufe idanun ka"


Maganar Aliya ta katse mai tinani.



Da muryanta mai sanyi daya ƙara narkewa da gajiya yace "idan na rufe idanuna taya zanga hanya?"


"To ai zan maka jagora "


Ai shikenan sai kawai yarufe idanuwan nasa. Ta saƙala ƙaramin hannun ta cikin nasa. Suka soma ta kawa atare.

Aliya kuwa zuciyarta na bugawa da sauri saboda farin cikin da take ji.

Ba ta san sunan wannan yanayin da zuciyarta take ciki ba. Ba ta san dalilin da yasa take jin kunyar kallon fuskarsa idan ya kalleta ba. Ta dai san abu guda ne kawai—tana son ganin ya yi farin ciki da abin da ta shirya masa.

A hankali ta ja shi zuwa cikin ɗakin.

"Kar ka buɗe idanunka!"

"To."

Ta tsaya.

Ta kalli ɗakin, sai murmushi ya bayyana a fuskarta.

Ko da ba wani babban gida bane, akwai kyakkyawan rufin asiri da ya sa komai ya yi kyau.

An kawata ɗakin da furanni masu launin ja da fari, an jera balloons a wurare daban-daban. Kayan furniture ɗin da suke da su, duk da ba na alfarma bane, sun ƙara wa ɗakin kyau.

Aliya ta duba komai.

A zuciyarta ta ce "I hope he likes it."

Sai ta kalli Rayyan.

"Yanzu ka buɗe."

Rayyan ya buɗe idanunsa. Ya tsaya cak.
Kamar an kafeshi a wurin.

Idanunsa suka zagaya cikin ɗakin.

Furannin...

Balloons...

Tsarin da aka yi...

Sai ya sake kallon Aliya.

Wata irin nutsuwa ta mamaye fuskarsa mai cike da farin ciki mai nauyin gaske.

"Aliya..."

Muryarsa ta fito ƙasa-ƙasa.

Aliya ta fara murmushi, tana kallonsa cikin tsammani.

"Ka ji daɗin shi?"

Rayyan bai amsa nan take ba. Ya maida duban sa zuwa ga ɗakin akaro na biyu. Wani abu ya motsa acikin zuciyar sa.

Ba saboda kayan ado ba. Ba saboda balloons ba.

Sai saboda ƙoƙarin da aka yi domin faranta masa rai.

Ya ji zuciyarsa tana bugawa a hankali. Ya sauke numfashi yana furta 

" Saboda kisanya Ni farin ciki, Ki kai duk wannan?!"

Aliya ta ɗan sunkuyar da kanta tana amsawa.


"Eh."

"Ke kaɗai?"

Ta gyada kai.

Rayyan ya yi shiru.Ya runtse idanunsa na ɗan lokaci.

A shekarunta, ba ta fahimci ma'anar abin da take yi ba.

Ba ta san cewa irin wannan kulawar za ta iya zama abu mai nauyi ga zuciyar sa ba.
A gare ta...faranta masa rai kawai take so.

Ya san hakan. Shi ya sa ya yi ƙoƙarin daidaita motsin zuciyarsa.

Ya kalli Aliya cikin tausayi. Da zai iya daya manta komai ya aiwatar da abinda zuciyar sa ke muradi akanta. Sedai yanada buri sosai akan Aliya. Zai....


"Ba shi da kyau?"

Tambayar Aliya ya katse mai zancen zucin da yake yi.

Rayyan ya yi saurin girgiza kai. Yana murmushi mai zurfi. Yana amsa ta.

"A'a. Yayi kyau sosai."

Fuskar Aliya ta haskaka. Murmushinta ya bayyana kamar yarinyar da aka yaba wa aikinta na farko.

"Da gaske?"

Ta fadi cikin ɗoki. Sannan tayi ƙaramar dariya tana cigaba da cewa 

"Na yi tunanin ba zai burge ka ba."

Rayyan ya kalle ta yace"Why wouldn't it?"

Sai ya sake kallon ɗakin. Bai jira amsar taba ya sake cewa

"Kin yi tunanin yadda zan ji ne kafin ki yi tunanin yadda ɗakin zai kasance."

Aliya ta yi shiru. Ba ta fahimci zurfin kalamansa ba.

A gare ta, kawai tana farin ciki ne saboda ya ce abin ya yi masa kyau.

Ta kalli balloons ɗin. Sai ta ce:

"Na so idan ka shigo ka yi farin ciki."

Rayyan ya ji kalmar ta shiga zuciyarsa. Hakan ya haifar mai da bugun zuciya. Muryarsa ta narke da yanayin da yake ciki yace


"Allah ya saka miki da alheri."

Aliya ta yi murmushi.
"Ameen."


Ya yi mata murmushi mai taushi.

"Ki ci gaba da kasancewa yarinya mai kyakkyawar zuciya."

Aliya ta kalle shi, ba tare da ta fahimci dalilin da yasa kalmar ta yi mata wani irin daɗi ba.

Sai kawai ta ce "To."

Rayyan ya sake kallon ɗakin. Furannin ja da fari suna rawa kaɗan saboda iska. Balloons ɗin suna cike da ɗakin.

Amma a zuciyarsa...abin da ya fi komai girma shi ne ƙoƙarin Aliya da ta so ta ga murmushi a fuskarsa.

Ya numfasa.

"Sometimes, the simplest things carry the deepest meaning."


Aliya ta kalle shi na ƴan daƙiƙu. Sai ta ɗan karkatar da kanta.

"Ustaz..."

"Hmm?"

"Har yanzu akwai abinda bai kammala ba"

Rayyan ya ɗaga gira.

"Me kike nufi?"

"Idan akai irin wannan decorations din. Couples su kanyi wani abu na musamman kamar rawa... watching movies ko shan ice cream."


Tafaɗi kalmar ƙarke idanunta na haskawa da wani yanayi da yafi duk sauran soyuwa azuciyar ta.


Ustaz ya gyara tsayuwa yana kallon ta da kyau. 


Yace"yanzu kina expecting din zan miki rawa kenan?"

"Eh. Mana"

Rayyan ya girgiza kai yana ƙoƙarin danne dariyarsa.

"Aliya..."

"Ustaz..."

"Ba zan iya rawa ba."

Aliya tayi dariya cikin tsokana tace"zaka iya"

"Ina Ustaz din da girmana za kice nai rawa! No impossible "


"Haka fa....waya ga Ustaz na rawa!"


Sigan da tai amfani wajen yin magana yasa suka fashe da dariya.


Wata irin dariya ce mara nauyi, wadda ta cika ɗakin ba tare da ɗayansu ya damu da komai ba.

This is the first time cikin kwanakin nan, dariyarsa ta fito ba tare da tilastawa ba.

Aliya ta kalle shi na ɗan lokaci.

A wannan daren, karon farko tun zuwanta gidan, ta ji kamar ba baƙuwa ba ce a wurinsa.

Sai ta juya ta fita.

Bayan ƴan mintuna ta dawo ɗauke da ruwan wanka.


A zaune ta sameshi a bakin gado yana waya.


Kafin ta shiga bayin tajiyo sa yana cewa"Please, yanzu-yanzun nan zaka siya. Ina jiran ka.”


“Ga shi nan. Ka je ka yi wanka ka fito mui dinner."

Rayyan ya amsa ta yana danna wayarsa daya shiga Vidmate ya soma downloading din Film.


Se daya gama yai copyn film din a system dinsa. Ya mike ta shiga wanka.

*

Bayan ɗan lokaci, Rayyan ya fito cikin kayan bacci. Kai tsaye ya nufi ƙofar falon da ake knocking.

Kamar yadda yai tsammani a tsaye yaga Ammar. Cike da girma mawa ya russuna ya miƙa mai ledan hannun shi.


Ustaz ya karɓa yana mai godiya. Shi kuma Ammar ya juya ya tafi.


Rayyan ya buɗe ledar.Sai ga kwantena biyu na ice cream.

Ya kalli ɗaya daga cikinsu na ɗan lokaci, sannan murmushi ya bayyana a fuskarsa.

A hankali ya ɗaga murya.

“Aliya.”

Daga ɗakin ta amsa.

“Na'am?”

“Zo.”

Ta fito tana gyara hijabinta. Jikinta sanyeda kayan baccin data sauya.

Da ta ga abin da yake hannunsa, sai ta tsaya.

“Wannan fa?”

Rayyan ya ɗaga ɗaya daga cikin kwantenan.

“Kin ce kina son ice cream ko?”

Ta kalle shi cikin mamaki.

“Ni?”

“Eh, ke.”

“Yaushe na ce?”

Ya yi murmushi. Yace "ƙwayannin idanuwan ki suka faɗamin lokacin da kike maganar ice cream"