BABI NA UKU
son, ai Kaine yanzu da auren ka da ka samu Mai maka ko da tausa ce am, ka ki kayi aure, ni kam Ina ga ma wajen ruqiyya zan Kai ka, da sauri ya dago ya zauna mum, ruqiyya fa?
Yes, of course, Dan naaga kaman baka da lafiya,
Sa annin ka duk sunyi aure Amma Kai ka ki kayi, ka duba fa Dan Allah kaga Salim Yanzu har Yara biyu da shi, Amma Kai Kuma ka zauna sai Kara tsofe min kake yi a gida, mum Dan Allah ki bar maganan Nan, nifa ba mace bane zan yi aure
A duk San da naga wacce nake so, Auu dama
Wai baka ga wacce kake so bane?
Ehh, ya fada Yana tashi Dan shi baya son wannan
Maganan sam, Ah lallai ma son,. Ma haifin ka zan samu a daura maka aure da Yar Kawata kawai,
Dan Allah mum kiyi hakuri wallahi zan fitar da matar da nake so kwanan Nan, yafada Yana shagwabe fuska, ni dai na gaya maka, nabaka 2 month Dan wallahi na gaji da yi maka magana,
Ta, tashi ta hau sama, ajiyar zuciya yayi shima yayi bangaren shi, washe gari tashi yayi ya shiga ,
Bandaki, wanka yayi ya dauro alwala, yazo kan darduman dakin shi, ya tada sallan Dan ya makara da zuwa masallaci, sallah yayi a nitse, ya idar
Daga hannu yayi ya fara Jero addu'oin, sa na Allah ya sa iyayen nasa su dai na yi masa maganan aure.
Tashi yayi ya nufi word drupe, kayan sa ya dau ka, yau ma irin na jiya, kananan kaya am yau rigan fari mai guntun hannu, wandon ne Baki ya dauko tsiririyar glass din sa yasa yayi kyau sosai,
Sauko WA yayi daga benen ya fito Palo, mum, da dady, kannen sa mata biyu, Nadiya, da hapsat, zaune suke a kan dinning table, suna jiran sa,
Da murmushi dukkan su suke kallon sa, Amma Banda, mum fuskan Nan Bata ba yabo ba fallasa
Amma taki ta yi masa yadda ta Saba, good morning dad, morning, Babana, Dan dady kam
Baya Kiran shi da wani suna da ya wuce Babana,
Dan Mai sunan Baban dadyn ne, Good morning, mum morning tace, ta kauda kan ta tace Nadiya
Ki zuba mishi, to tace ta fara zuba mishi,
Suka ce Ina kwana Yaya Faruq, daga Kai kawai
Yayi Bai yi musu magana ba.
Abincin suka faraci, yaci kadan, ya tashi yace musu, am living, dagowa dukka suka yi daddy yace, yanzun, yace Ina da patient ne a hospital, I have to leave, At least you have to eat, yadda zaka
Duba patient da kyau,. No dad zan ci a office idan naje office. allah ya kiyaye suka yi masa.
MASHA ALLAH WANNAN KENAN DAGA LITTAFIN, (NANA ASMA'U) NICE TAKU A KULLUM KHAREEMAH USMAN BOBBO.
dan Allah🙏 kuyi min like, da comment, ta yadda zan samu karfin gwaywan cigaba da labarin, dan Allah🙏 ku taimaka, kuyi wa yar uwan ku, like da comment.