FADIANA

Chapter 1: The Night everything changed

by @hauwajaywrites

Daren ya yi shiru, amma ba irin shiru na dare da ke sa mutum samun nutsuwa ba, shiru ne mai nauyi, wanda yake sa kowane ƙaramin sauti ya zama kamar gargadi, yayin da iska ke ratsa dogayen bishiyoyin da suka kewaye gidan tana girgiza rassansu a hankali. Labulen windows din beni na sama yana motsi kaɗan-kaɗan, hasken fitilar cikin gida yana ratsawa ta cikinsa yana zana siraran layukan haske a ƙasan ɗakin


A ɗakin da ke ƙarshen corridor, wata ƙaramar yarinya tana barci cikin natsuwa, hannunta ƙarƙashin kumatunta, numfashinta yana fita a hankali irin na wanda ba ta da wata damuwa a duniya. Blanket ɗin da aka rufe ta da shi ya zame daga kafadarta, gashinta ya ɗan watse a gefen pillow, fuskarta kuwa babu wata alamar cewa tasan wani abu wai shi tashin hankali


Can other side na gidan kuma, wani mutum yana tsaye a gaban taga, kusan mintuna goma kenan bai motsa ba


Wayar da ke hannunsa ta haska fuskar da damuwa ta mamaye, sannan ta sake duhu, ya kalli screen ɗin sau ɗaya, ya ɗan cije leɓensa kafin ya danna wani number nan take..


Ya fara ringing ya ɗaga wayar zuwa kunnen sa, haka wayan take ringing yana jira a ɗaga amma shiru, zuciyarsa ta cigaba da bugawa, ya sake dialing but what? Har sannan ba’a ɗaga ba, yayi hakan kusan sau biyar amma babu amsa


Ya sauke wayar daga kunnen sa yana kallon screen ɗin kamar yana jiran ta fara ringing da kanta, sannan ya kashe wayar gaba ɗaya. Hannunsa ya shiga aljihun wando kafin ya ɗaga idanuwansa zuwa agogon bangon da ke gabansa


1:47 na dare. Ya sauke numfashi a hankali, sai wani motsi ya jiyo daga wajen window, ya yi saurin matsowa kusa da gilashin, ya yaye labulen kaɗan yana rarraba ido


Sai kawai wani haske ya bayyana a can nesa, ya wuce tsakanin bishiyoyi na ɗan lokaci kamar hasken touch light da ta yi juyi a backyard na gidan, sannan ya ɓace


Fuskarsa ta canza “Ba zai yiwu ba,” ya furta a hankali, yana ci gaba da kallon wajen kamar idanunsa za su iya gano abin da yake ɓoye a cikin duhun


Ya sake ɗaukar wayarsa ya danna number ɗin da ya kira ɗazu, har yanzu babu amsa


Sai wata ƙara yaji daga sama, ya ɗaga kai da sauri, na ɗan lokaci ya tsaya yana sauraro, sai ya fara hawa matakala da sauri


“Ke ce?” Yayi maganar kamar whispering, amma babu amsa


Ya kai hannu kan handle ɗin ƙofar ɗakin, ya buɗe ta a hankali, yarinyar tana kwance a gadonta kamar yadda ya bar ta


Ya tsaya a bakin ƙofar yana kallonta na wasu seconds, damuwa da ke fuskarsa ta ɗan sauka, sai ya matsa kusa da gadon ya gyara blanket ɗin da ya zame daga jikinta


“Ki yi barci” ya rada


Ya juya zai fita, wayarsa ta yi vibration a hannunsa, ya kalli screen


Unknown Number ya gani, fuskarsa ta canza nan take, ya buɗe saƙon


‘Ka samu isasshen lokaci’ Ya karanta shi sau biyu, kafin ya samu damar ɗaga kai, wani saƙo ya sake shigowa


‘Ba za ka iya ɓoye ta har abada ba’ kallon sakon yake babu kiftawa, hannunsa suka yi sanyi sosai 


A hankali ya ɗaga kansa ya kalli yarinyar, wannan karon, ba shi da lokacin yin tunani ya sunkuya ya ɗauke ta daga kan gadon


Yarinyar ta motsa a hannunsa, ta buɗe idanunta a hankali “Daddy…”


Ya matse ta a jikinsa “Shhh…”


Ta ɗan ɓata fuskarta tana ƙoƙarin farkawa gaba ɗaya “Me ya faru?”


“Babu komai” ya faɗi hankali tashe, Cike da sangarta ta ce “Me ya sa ka tashe ni?”


“Za mu fita ne”


Ta ɗaga kai tana kallonsa “Yanzu?”, Kai kawai ya samu ya gyaɗa mata, “Da daddare kuma?”


“Fadi… kiyi shiru” Ta yi shiru na ɗan lokaci, Idanunta suka bi fuskarsa a hankali, kamar tana ƙoƙarin gano abin da yake ɓoye mata


“Daddy… kana tsoro ne?”, Ya kasa amsa nan take sai ya ɗan mannata jikinsa “Ki yi shiru, sweetheart”


Ya ajiye ta a gefen gadon ya ɗauki wata jaka da ke kusa da ƙofar, ya buɗe ta da sauri yana cusa wasu files da envelopes a ciki, ya ɗauki wata ƙaramar akwatin ƙarfe, ya tsaya yana kallonta na ƴan seconds, kamar akwai wani abu mai nauyi a cikin abin da ke ciki, sannan ya saka ta cikin jakar ya rufe ta


Yarinyar ta kalle shi “Za mu yi tafiya ne Daddy?”


“Eh”, Kallonsa ta tsaya yi “Ina za mu je?”, Ya ɗaga jakar ya rataya a kafaɗarsa “Wurin da ba za su same mu ba”


“Su waye?”, Yana kallonta, bai samu amsar da zai iya ba ta ba


“Zo,” kawai ya ce, ya miƙa mata hannu, ta kama shi, suka fito daga ɗakin


Da suka isa corridor, wata mata ta fito daga ɗayan ɗakunan, fuskarta ta nuna cewa ba ta buƙatar tambayar abin da ke faruwa kafin ta gane


“Sun zo ne?” ta tambaya cikin sanyin murya


Mutumin ya kalleta sannan ya gyada kai “Ban sani ba, kawai mu samu mu bar nan dan akwai hatsari”


“Ka kira shi?”


“Na kira bai ɗaga ba, kin san dare ne dole yana bacci” Ya kare maganar cikin tashin hankali


Idanunta suka sauka kan yarinyar “Ya zamu yi da ita?”


“Rayuwarku tafi nawa, musamman ita d nake son ta yi gadon komai, gwara na fitar da ita daga kasar nan ko da zasu kashe ni


Matar ta rufe idanunta na ɗan lokaci, ta sauke numfashi mai nauyi “Allah…”


“Ba mu da lokaci” ya katse ta, Ta ɗauki ƙaramin jakarta daga kan kujera “Mu tafi”


Suka fara sauka daga stairs, suna kusa da ƙarshen stairs din sai suka ji wani sauti daga can ƙasan gidan


Krrrrrr…


Dukkansu suka tsaya cak, Mutumin ya ɗaga hannu “Shhh”


Matar ta matse hannun yarinyar tana zare idanuwa


Sautin suka sake ji, kuma wannan karon ya fi na farkon Kara sosai, Kamar an buɗe wata ƙofa ne


Duk sun fahimci sun riga da sun riske musu, Mutumin ya sauke jakar daga kafaɗarsa a hankali, ya kalli matar, sannan ya yi mata alamar ta shiga ɗakin da ke gefen corridor “Ku shiga”


“Amma….”, Ya katse ta “Ku shiga kawai”


Matar ta kama hannun yarinyar ta ja ta cikin ɗakin “Daddy fa?” yarinyar ta tambaya da ƙaramar murya


“Shhh, ki yi shiru”, Yarinyar ta shagwaɓe fuska “Amma Daddy yana can” Tayi maganar Duk da bata da wani wayo balle ta fahimci abu 


“Ki yi shiru” Matar ta rufe ƙofar, Mutumin ya tsaya a corridor shi kaɗai yana son ya tabbar inda suke


Fitilar ƙasan gidan ta mutu, duhu ya mamaye komai


Ya ɗan matsa baya ya mannu da bango yana sauraron motsin da ke ƙasa


Ya kai hannu cikin drawer ɗin da ke kusa da shi ya ɗauki wani ƙaramin abu, ya riƙe shi a hannunsa kafin ya sake kallon agogon hannunsa


1:56am na dare, ya san ba shi da lokaci ya juya ya koma cikin ɗakin da suke, da ya buɗe ƙofar, matar ta taso da sauri “Me za mu yi?”


“Window” Ya fada dakayr saboda tashin hankali, ta kalli window ɗin sannan ta kalli ƙasan beni “Beni na biyu ne fah Dear”


A hankali ya ce “Na sani” Ta kalli Babynta “Yarinyar fa?”, “Zan sauke ku”


Ya ɗauki yarinyar ya riƙe ta, Matar ta buɗe window, Iskar dare ta bugi fuskokinsu


A ƙasa akwai ƙaramin terrace da zai iya taimaka musu su sauka “Ki fara”


Matar ta kalli ƙasa cike da tashin hankali “Idan na faɗi fa?”, Ya girgiza Kai “Ba za ki faɗi ba”


Ta haɗiye sauran maganar, ta hau kan ledge ɗin window ta sauka a hankali zuwa terrace


“Ba ta motsa ba?” mutumin ya tambaya, Ta ce “Na sauka”


Ya ɗaga yarinyar ya miƙa mata “Riƙe ta da kyau, idan da rabo zamu hadu”


Matar ta ɗauke yarinyar tana girgiza masa Kai “Ka zo kai ma, kar ka basu kanka hakanan pls” Ya ce “Zan zo”


Ta ce “Ba zan tafi ba sai ka zo”Ya kalleta tsoron da ke idanunta ya bayyana a sarari “Ki kula da ita pls” Sai ya rufe windown


Nan take suka ji ƙarar gilashi ya fashe daga wani ɓangaren gidan


Matar ta firgita hawaye suka fara zuba mata, gashi dare ne ko tayi ihu sai dai ta tonawa kansu asiri amma daga waje babu me zuwa cecansu “Sun shiga!”


Ya leko kansa “Ki gudu nace!”


“Amma kai fa?”, Ya danne kansa ya sake cewa “Ki gudu!”


Ta kama hannun yarinyar ta fara gudu hawaye na zu ba


A ɗakin kuma, mutumin ya juya da sauri jin motsi a sama inda yake, kofar ta girgiza Bang!


Ya ja baya yana kallon wajen, yana iya ganin shadow dinsu, aka sake bugawa Bang!


Sai wata murya ta fito daga wajen “Ka daina ɓoye mana bcos Yau ba zaka tsere mana ba”


Ya rufe idanunsa na ɗan lokaci, ya ɗauki numfashi mai karfi, sannan ya buɗe ƙofar ƙaramin storage room da ke bayan ɗakin, a ciki akwai wata ƙaramar ƙofa da ba ta da sauƙin ganewa


Ya buɗe ta ya fito ta bayan gidan, ya fara gudu


Meanwhile matar nasa itama tana gudu da yarinyar tana goye da ita a bayanta


“Ki riƙe ni sosai” ta ce tana ƙoƙarin kar yarinyar ta zame daga bayanta “Daddy fa?”


Tana haiki ta ce “Zai zo”, “Ammah me zai faru ?”


“Nothing dear”, Yarinyar ta sake tmbyrta “Daddy zai zo?”, Matar ta yi shiru na ɗan lokaci, ta kalli bayanta


“Zai zo” Ta furta kalmar kamar alkawari, ko da yake ita kanta ba ta san ko za ta iya cika wannan alkawarin ba


Suka isa bayan babban gidan nasu, Matar ta buɗe ƙaramin gate ɗin sai ta tsaya cak, Motar da suka shirya amfani da ita ba ta nan


“Ya Allah…” Ta kalli titi babu kowa, ta kalli dama shiru ta kalli hagu


Sai hasken mota ya hasko su, ta ja yarinyar da sauri ta koma bayan wani pila suka buya, Motar ta wuce


Da motar ta yi nisa, matar ta sake goya yarinyar “Mu tafi” nan suka cigaba da gudu, suna bin hanyar da zai fitar da su titi


Ba su yi nisa ba sai suka ji murya daga bayansu “Tsaya!”


Matar ta juya, kawai gani tayi wani mutum yana tsaye a bayansu,


Ta sauke yarinyar ta matse ta a jikinta, “Ki gudu!” ta ce mata cike da dauriwa 


Yarinyar ta fara kuka “Amma Mama…”


“Ki gudu! Allah zai kare ki” Matar ta ja ta baya, Mutumin ya fara matsowa ya ce “Ba za ki iya gudu ba”


Cike da tsoro ta ce “Me kuke so?”, Yayi dariya “Kin san abin da muke so”


Ta girgiza kai “Ban san komai ba”, Ya ce “Amma shi ya sani”


Matar ta yi shiru, Idanunta suka cika da tsoro “Don Allah” ta ce cikin raɗaɗi “ku bar yarinyar”


Mutumin ya yi wani murmushi mara daɗi “Ba ita muke nema ba”


Suna cikin haka, a wannan lokacin wata mota ta tsaya a gefen titi


Mutumin ya juya kansa yana son sanin waye ne a cikin motar, hakan yasa Matar ba ta jira komai ba ta ja yarinyar ta gudu


Suka shiga wata ƙaramar hanya tsakanin gidaje “Da sauri” ta ce tana jan ta


“Mama…” Bata amsa mata ba, “Daddy zai same mu?”


“Zai same mu” ta daga ta suka ci gaba da gudu


Ba su wani daɗewa ba matar ta fara jin numfashinta yana nauyi, ta tsaya ƙarƙashin wata bishiya tana ƙoƙarin daidaita numfashinta


“Shhh” ta ce, tana ɗaga yatsa zuwa bakinta, Yarinyar ta kalli fuskarta “Me ya faru?”


“Ki yi shiru kawai”, Sautin mota ya bayyana a bayansu, Matar ta matse yarinyar a jikinta


Motar ta wuce still tana zaune, bata motsa ba sai ta tabbatar da cewa motar ta yi nisa sannan ta sauke numfashi


A lokacin ne ta ji yarinyar tana sosa hannunta, ta kalli ƙaramar hannunta, akwai ƙaramin rauni a hannun “Ya Allah…”


“Yana ciwo Mama” yarinyar ta ce tana shafa wurin


Matar ta ɗauke ta a hannunta “Ki yi haƙuri” Ta fara tafiya da ita


Sai suka sake jin ƙarar mota, wannan karon ta zago ta tsaya a gabansu


Ƙofar aka buɗe wani Mutum ya fito, Matar ta rungume yarinyar da ƙarfi


Ta san gudu ba zai ƙara taimaka musu ba “Ki rufe idanunki” ta rada


“Me ya sa?”,


“Do so, please my baby” Yarinyar ta rufe idanunta, Matar ta matse ta a kirjinta tana ƙoƙarin kare ta da jikinta


Mutumin ya matso “Where is it?”, Matar ta yi shiru tana kallonsa


“Na san kina da shi”


“Ba ni da komai”


“Kin tabbata?”


Ta ƙara rungume yarinyar “Ku kashe ni idan kuna so”


“Ba ke muke so ba”


Ta ɗaga idanunta “Ba za ku taɓa samun ta ba”


Mutumin ya ɗan karkatar da kansa “And?”


Matar ta yi shiru a lokacin ne ta fahimci cewa ta faɗi abin da bai kamata ta faɗa ba


Idanun mutumin suka sauka kan yarinyar “Shin…” Bai ƙarasa ba


Wata ƙara ta tashi daga can nesa, Matar ta rufe yarinyar gaba ɗaya da jikinta tana Jin bugun zuciyarta na tsananta


Meanwhile , mutumin da ya bar gidan dan tsira da ransa yana kwance a ƙasa, numfashinsa yana fita dakyar


Jini ya jika gefen rigarsa, ya motsa hannunsa da ƙyar


Wayarsa tana can yashe, ya ja jikinsa a hankali, yatsunsa suka kai ga wayar


Screen ɗin ya haska ya danna wani number, amma har ta yanke ba’a daga ba, ya sake kira


A karo na uku aka ɗaga, ya yi ƙoƙarin magana, amma muryarsa ta fito can kasa saboda wahala “Ta… tsira…”


A ɗayan ɓangaren aka yi shiru, ya rufe idanunsa na ɗan lokaci sannan ya sake matsar da wayar kusa da kunnensa, dakayr ya ce


“Ku… kare… min.. ita…” Wayar ta zame daga hannunsa, ya ja numfashin karshe sannan idanunsa suka rufe


A can kuma, wayar ce ta fara ringing wani mutum da ke zaune shi kaɗai ya ɗaga kansa zuwa wayar kafin ya miƙa hannu ya ɗauke ta, ya kalli screen ɗin


Unknown Number, kawai ya amsa “Hello?”


Ba’a amsa ba, sai wani irin numfashi mai nauyi ya fito daga ɗayan ɓangaren “Hello? Who is this?”


Still babu amsa, sai wata kalma ta fito a hankali, kamar wadda mai kiran yake ƙoƙarin fitarwa da sauran numfashin da ya rage masa


“Fadiana…” Wayar ta katse


Mutumin ya tsaya yana kallon screen ɗin, bai motsa ba sannan bai sake kiran number ɗin ba, ya kawai riƙe wayar a hannunsa yana kallon duhun ɗakin


Hello lovelies idan har kum shiryawa wannan tafiyar kuyi liking na book din dan na sani! sannan ayi following account dina for daily updates dan samun notifications