FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Hey there! I'm Hauwa Jibrin, aka Hauwajay writes. Anxiously waving at you! I'm a bookworm who loves reading and writing, which is why I'm here. *** journey began as a reader, and now I'm thrilled to be a writer too! A little about me: - Avid reader - Avid writer - D...
Sample · Chapter 1: The Night everything changed
Daren ya yi shiru, amma ba irin shiru na dare da ke sa mutum samun nutsuwa ba, shiru ne mai nauyi, wanda yake sa kowane ƙaramin sauti ya zama kamar gargadi, yayin da iska ke ratsa dogayen bishiyoyin da suka kewaye gidan tana girgiza rassansu a hankali. Labulen windows din beni na sama yana motsi kaɗan-kaɗan, hasken fitilar cikin gida yana ratsawa ta cikinsa yana zana siraran layukan haske a ƙasan ɗakinA ɗakin da ke ƙarshen corridor, wata ƙaramar yarinya tana barci cikin natsuwa, hannunta ƙarƙashin kumatunta, numfashinta yana fita a hankali irin na wanda ba ta da wata damuwa a duniya. Blanket ɗin da aka rufe ta da shi ya zame daga kafadarta, gashinta ya ɗan watse a gefen pillow, fuskarta kuwa babu wata alamar cewa tasan wani abu wai shi tashin hankaliCan other side na gidan kuma, wani mutum yana tsaye a gaban taga, kusan mintuna goma kenan bai motsa baWayar da ke hannunsa ta haska fuskar da damuwa ta mamaye, sannan ta sake duhu, ya kalli screen ɗin sau ɗaya, ya ɗan cije leɓensa kafin ya danna wani number nan take..Ya fara ringing ya ɗaga wayar zuwa kunnen sa, haka wayan take ringing yana jira a ɗaga amma shiru, zuciyarsa ta cigaba da bugawa, ya sake dialing but what? Har sannan ba’a ɗaga ba, yayi hakan kusan sau biyar amma babu amsaYa sauke wayar daga kunnen sa yana kallon screen ɗin kamar yana jiran ta fara ringing da kanta, sannan ya kashe wayar gaba ɗaya. Hannunsa ya shiga aljihun wando kafin ya ɗaga idanuwansa zuwa agogon bangon da ke gabansa1:47 na dare. Ya sauke numfashi a hankali, sai wani motsi ya jiyo daga wajen window, ya yi saurin matsowa kusa da gilashin, ya yaye labulen kaɗan yana rarraba idoSai kawai wani haske ya bayyana a can nesa, ya wuce tsakanin bishiyoyi na ɗan lokaci kamar hasken touch light da ta yi juyi a backyard na gidan, sannan ya ɓaceFuskarsa ta canza “Ba zai yiwu ba,” ya furta a hankali, yana ci gaba da kallon wajen kamar idanunsa za su iya gano abin da yake ɓoye a cikin duhunYa sake ɗaukar wayarsa ya danna number ɗin da ya kira ɗazu, har yanzu babu amsaSai wata ƙara yaji daga sama, ya ɗaga kai da sauri, na ɗan lokaci ya tsaya yana sauraro, sai ya fara hawa matakala da sauri“Ke ce?” Yayi maganar kamar whispering, amma babu amsaYa kai hannu kan handle ɗin ƙofar ɗakin, ya buɗe ta a hankali, yarinyar tana kwance a gadonta kamar yadda ya bar taYa tsaya a bakin ƙofar yana kallonta na wasu seconds, damuwa da ke fuskarsa ta ɗan sauka, sai ya matsa kusa da gadon ya gyara blanket ɗin da ya zame daga jikinta“Ki yi barci” ya radaYa juya zai fita, wayarsa ta yi vibration a hannunsa, ya kalli screenUnknown Number ya gani, fuskarsa ta canza nan take, ya buɗe saƙon‘Ka samu isasshen lokaci’ Ya karanta shi sau biyu, kafin ya samu damar ɗaga kai, wani saƙo ya sake shigowa‘Ba za ka iya ɓoye ta har abada ba’ kallon sakon yake babu kiftawa, han...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.