ƊAURIN ZUCI

Chapter 33

by @maryamstar248

***


END OF BOOK ONE

𝘿𝘼𝙐𝙍𝙄𝙉 𝙕𝙐𝘾𝙄🔐
         𝘽𝙔
𝙈𝘼𝙍𝙔𝘼𝙈 𝙎𝙏𝘼𝙍

Chapter 33.
    "He is fine, dagaske nike Muhammad." Junaid ya faɗa cike da tabbatarwa.
    Wata iriyar sufa Unclr yayi tare da rungumar Junaid da Saminaka ke kwance a ƙirjin shi yana fitar da numfashi a wahale.
  "Alhamdulillah ya rab Alhamdulillah rabil'aalamin." Uncle yaita jero handala cike da maɗaukakin farinciki.
   Har lokacin Fahad na nan a sume sai da suka gama murnar Daddy Junaid har da ɗauke ƙwallar data cicciko idanuwansa sannan ya tuna da Fahad, da sauyi yayiwa Uncle nuni da shi, dan bai jin zai iya fitar da shi daga ƙirjin shi a yanzun.

  Ruwa Uncle ya ɗauko tare da shafawa Fahad ɗin a fuska har sau uku, nan ya saki ƙaƙƙarfar numfashi, kafin daga bisani kuma ya fara surutai idon shi a rufe.
   "Mommy,,,,,,Mommy please kice min ba ke ba ce kika aikata hakan Pleaseeeee." ya faɗa kuka na ƙwace ma shi me ƙarfi.


MOMMY
   A sukwane ta haura samanta tare da shigewa room ɗinta ta danna key a jikin ƙofa tana maƙyarƙyatar tsoron ganin da Fahad ya yi mata, ajiye jakar hannunta ta yi tare da soma tuɓe kayanta ta yi tsirara tana sambatu, goran jini ta ɗauko tare da kwarara shi akanta yana saukowa jikinta, bakinta na furta wasu kalmomi  babu tsaitsayawa.
         Sannu ahankali hayaƙi ya soma tasowa ta jikin bango yana zagaye da sauri, ya ɗauki sakanni kafin ya tsaya cak, a hankali suffar mutum ta soma bayyana kafin daga bisani ya washe tarrrr tsoho Ƙwaro ya bayyana zaune cikin baƙa ƙirin ɗin shiga hannuwansa riƙe da sandar tsafinsa idanuwansa sun rikiɗe sun sauya kala zuwa jajaye sosai.
    Faɗuwa ƙasa Mommy ta yi tare da soma jeranto kirari cike da ƙwarewa.
     "Haƙiƙa wajen da  kike akwai kiyayyar Allah ki gaggauta faɗa mana abin da kike so domin kuwa bazamu iya ɗaukar lokaci anan ba."
    "Dodo ya ja da ranka ina cikin firgici da tashin hankali, yau na je domin incika aikina amma anyi rashin sa'a ɗana ya ganni, kuma kwalbar jini me daraja ta faɗi ta fashe jinin ya soye alamar da  ke alamanta min akwai gagarumar  matsala."
    Sake murtuke fuska Ƙwaro ya yi kin abin da ta faɗa, sannan a taƙaice ya ce da ita.
   "Dodo da muƙarrabansa na fushi da ke akan hakan, kuma za ki fuskanci hukunci akan abin da kika aikata munbada aiki kin amsa mun baki sharaɗi kuma kin amince yanzu kiyi gaugawar  barin wannan gidan domin kuwa yana cike da tsoro da kariya idan kika bar gidan zamusan abin da zamuyi." yana gama faɗin hakan ya ɓace ɓat kamar bai taɓa wanzuwa a wajen ba.
    A kiɗime Mommy ta tattare tarkacen tsafinta ta bi ta cikin ginin wajen ta ɓace ɓat bayan ta ɓatar da motarta, tana fatar kar wanda yasan da ta zo gidan bare kuma a zargeta akan abin da ta aikata.
   Sai de kuma abin da Mommy bata sani ba shine ta manta abubuwa masu muhimmanci a gidan da kuma ɗakin Saminaka da ta shiga, ta sanadiyar wannan abin rayuwarta zata shiga tazku.

Bin parlorn ta dinga yi da kallo, ɗaurariyyar zuciyarta na saƙa mata wani abu, wani abu me kamanceceniya da rayuwar data baro, tana a wajen zaune kalar gunki ta hanki innuwa na bin bangwaye, gabanta yai wata iriyar mummunar dokawar, zuciyarta ta yi tsalle tare da matsewa a ƙirjinta, a razane ta miƙe tsaye tare da isa wajen bangon da innuwar ta bi ta ɓace, kasa riƙe kukanta ta yi sai kawai ta durƙushe a wajen tare da soma rairo kukanda ke tsaye a maƙoshinta tun lokacin data farka, tsabar yanda ta ke kukan har jikinta ya soma jijjiga saboda sautin na fitowa ne daga can ƙasan ruhinta, sulalewa ta yi a wajen a sume rumfashinta ya ɗauke ɗiffff....


****
MARYAM
     A hankali ta buɗe idanuwanta da suka yi mata nauyi, irin nauyin nan da yake saka bata son koda buɗe su, domin idan fatar idonta ta haɗe a yayin ƙyaftawa tana jin kamar an ɗaurawa idanuwanta dutse me nauyi, ba iya kwanyarta ba hatta da ƙoƙon kanta ya gagara tantance asalin tunanin daya kamata ta yi a lokacin.
      "Noor mu ba mutane bane....bane...mutane bane..."
   Sune kalaman da ke amsa kuwwa a kunnuwanta.
    "Mu jinsin fararen Aljanune ni da ɗan uwana da yayi basaja a matsayin tsohon kakanki." 
    Kalam Hamzalul keta maimaita kansu a cikin kunnuwanta.
    Yunƙurawa ta yi da ƙyar tare da tashi zaune ta dafe kanta da ke yi mata ciwo sosai gashi yayi mata wani irin nauyi, bin ɗakin ta soma yi da kallo kamar me son gane wani abu a cikinsa, sai de kuma bata iya gane komi ɗin ba, bayan ɗaki falle ɗaya ɗan ƙarami ginin ƙasa sam bata ga komi ba.
    Sai de kuma da ace ta aje hankalinta waje guda zata gane ɗakin ba kamar ko wane ɗaki yake ba, a maimakon a samu ɗakin da rufi sai ya kasance kurman gini bashi da rufi ko kaɗan, kamar an tona dutse haka ɗakin ya ke, kuma ba wani girma gare shi ba kamar yanda bai da haske sai hasken da ke fitowa daga ƙofa.

  

Ƙasan teku.
    Ruwa ne ke tsalle tare da tartsatsi suna dukan junan su suna fitar da wani irin sauti me ban tsoro da firgitarwa, ga wani haske na musamman da ruwan ke da shi daga sama zaka iya hangen abin da ke ƙasan ruwan du kuwa da tsurfin ruwan.
      A tsakiyar tekun a nan tafar Sarkin jinsin fararen Aljannu wato Kabisatul ƙamaru ta ke, shi da fadawa da bayinsa na musamman tare da kuma sauran jinsin Aljanun da yake mulka.

    Zaune ya ke a saman kujerar da aka ƙera da narkakken ɗanyan gold, baka iya ganin komi daga siffar shi sai hasken da ke ya ke gudana a cikinsa.
     Cikin muryarsa me ƙarfin amo gami da kaifi ya ce yana maida akalar haskensa zuwa sashen da Kanzul ke durƙushe.
    "Ya kai wannan bawa me aminci ka yi sani cewa lokaci ya yi da zaka baro waccan rayuwar wa'adain dana ɗibar maka ya cika na rayuwa tare da ƴan adam ka zo ga jinsinka muna da buƙatarka"
 
   "Umarninka abin bi ne a gare ni yakai adalin shugaba da izinin Ubangijin dukkanin halitta zan bar waccan rayuwar indawo cikin jinsina inci gaba da rayuwa kamar yanda aka saba."
   Wannan maganar da Kanzul ya yi ita ce ta kawo ƙarshe  dukanin alaƙar su shi da Noor wato Maryam, yarinyar da suka rayu tare da ita shayin shekaru sha takwas wacce bayan su bata san kowa ba, bata saba da kowa ba su kaɗai ne a cikin rayuwarta, sune farinciki da walwalarta, bata saba da kowa ba sai su, su kaɗai take tarayya da su.

Daga ta saman kan shi Hamzalul ya tsaya tare da raɗa ma shi.
    "Yakai ɗan uwana ka amince min inje insada Noor da ƙaddararta bazan lamunci ganin rayuwarta na walagigi ita kaɗai a haka ba, na maka alƙawarin bazan jima ba zan dawo gareka." Hamzalul ya faɗa cike da rauni da kuma tausayi.
    "Yakai ɗan uwana Hamzalul ka yi sani cewa ni me aminci ne agareka akan dukanin abin da ya ke daidai, Ubangijin halittu yayi maka jagora ka faɗa mata zan yi kewar rayuwa tare da ita." ya faɗa yana ɗaura silken shi tare da shiryawa cikin ainahin kayan shi da yake amfani da su a baya.
    Cikin abin da bai fi daƙiƙa ɗaya ba Hamzalul ya ɓace ɓat daga kogin, tare da bayyana a daidai saitin wannan shuri da ke cikin garin Katsina unguwar Shinkafi.
     Tsayawa ya yi cikin iskar wajen yana ƙarewa shurin kallo, rayuwar da suka yi shekaru sha takwas baya na dawo ma shi shi da ɗan uwan shi da kuma yarinyar da suka tsinta wacce yake kiranta da Noor.

 FLASH BACK
A ranar da Kanzul da Hamzalul suka ceto wannan jinjirar, sai suka rasa yanda zasu yi da ita bayan sun baro ƙasan teku.
   "Yakai ɗan uwana shin bazan baka shawara ka ɗauka ba." Hamzalul ya faɗa yana kallon fara tas ɗin fuskar yarinyar.
    "Kai ɗin ɗan uwana ne ba ina maraba da shawararka ako da yaushe." Kanzul ya faɗa shima yana kallon yarinyar.
    "Akai cutarwa idan muka rayu da ita cikin siffa irin tamu, zai fi kyau mu rayu da ita tamkar jinsinta bil adam saboda gudun juyewar kwanya da tunaninta, Sarki ya lamunce mana mu rayu da ita na tsayin shekaru kafin nan sai mu idasa ladarmu mu taimaka mata ta hanyar inganta rayuwarta."
    Wannan kuma shawarar da ita Kanzul ya yi amfani suka ci gaba da rainon Maryam wacce Hamzalul ya raɗa mata suna Noor acewar shi.
   "Tun da nike ganin ƴan adam ban yaɓa ganin mutum wanda baiwar shi ke haskakawa ba irin wannan yarinya, da ace ita ɗin ba haske ba ce ba lallai ta jure rayuwa yare da mu ba tana ganin yanda muke ɓacewa muna kuma shawagi amma bata taɓa firgita ba, gashi sam bayada rigima."
     Buɗar bakin Kanzul a lokacin sai cewa ya yi.
   "Tunda haka ne mu rage yawan abubuwan da muke yi, mu riƙi siffa ɗaya  da zata sanmu da ita kafin wa'adin ya cika."
   Daga wannan rana a kuma wannan lokacin suka sauya siffarsu suka zaɓi siffar tsofafi sai Kanzul ya zaɓi tsufa sosai fiye da Hamzalul.

   Sun raineta cike da gata, kulawa, da ɗumbin soyayya, hakazalika sun san ba lallaine rayuwarta ta ɗore tare da su ba, sai suka ɗorata akan turba me kyau, suka reneta ta taso a yarinya me riƙo da addini da ibada, acewarsu ƴan Adam mugaye ne wasu daga ciki, suna sutar da kawunansu da ƴan uwansu ta hanyar amfani da jinsin aljannu masu cutarwa.


CIGABAN LABARI

Kaɗa jelar shi Hamzalul ya yi tare da shigewa ta ɗaya daga cikin ƙofofin shurin bakin shi na fitar da amon sautin sallama kamar yanda ya saba yi adu lokacin da zai je gidan.

     "Da sauri Maryam ta ɗaga kanta gabanta na faɗuwa, rawa jikinta ya soma yi lokacin da ta tashi tsaye, da sauri ta fita zuwa tsakar gidan don tabbatar da abin da kunnuwanta suke jiye mata.
    "Kaakkakak Kaka Abu!!!." ta kira shi cikin rawar murya cike da ƙarfin hali.
      Ta nufe shi gadan-gadan da niyyar ta rungume shi kamar yanda ta saba, amma sai wani abu ya faru, wani abu wanda ke neman tabbatar mata da mafarkinta.
   Kakanta Abu da take gani ne ya ɓace ɓat daga suffar shi ya koma kan iska yana fitar da wani irin haske mw kaifi, wanda ganin hasken kawai yana ƙara ƙarfin ciwon kan da take yi, da kyar ta ɗaga rinanun idanuwanta izuwa sama tana kallon hasken dake zagaye da wata halitta a cikin shi, halittar daya kamata ace ta bata tsoro harta nemi wajen fakewa da ganinta, amma kuma sai zuciyarta data cika fal da mamaki ta tsaya ƙyam tana haska mata gaskiyar da taketa faman ƙaryatawa tun jiya gaskiyar da take fatan ta kasance ƙarya ce ko kuma mafarki, gaskiyar data zama abar gudu a wajenta.
     "Haba mana Noor karki kasance daga cikin mutane masu taurin kai, ba wannan tarbiyar muka yi miki ba ki kasance cikin mutane masu yarda da ƙaddara tare da amsarta hannu bibiyu, kar kiyi jayaya da gaskiyar data ɓoyu gareki tsayin shekaru, shin ba zaki godewa Ubangijin gaskiya ba daya nufe ki da sanin komi tun da sauran lokacin ki, bana son kafiya da taurin kai ki, kasance yanda Kakan ki Kanzul mujulu ke buƙatar kasancewar ki, ina yi miki umurni akan ki yi shiru da komi na tsayin lokaci har sai bayan kin samu abin da kike muradi sannan ki magantu, ƙorafi ba naki bane a yanzu, ki adana tambayoyin da ke bakin ki domin kuwa ke da kanki za ki nemo amsoshin shi, daga  yau kuma a yanzu da ikon Ubangiji."
    Ya faɗa yana aiko da haske zuwa saitin zuciyarta.
    "Tsak komi nata ya tsaya na ɗan lokaci, kai tsaye ba tare da jayayya ba ta ji ta amince da dukanin maganganunsa ta kuma manta da maganganun da ke kaiwa da kawowa daga ƙirji zuwa zuciyarta.
    "Ki yafe ni Noor ban ɗaure zuciyar ki ba don wata manufa sai dan in sauƙaƙa miki abubuwan da ke tunkaro rayuwar ki, zanci gaba da bibiyar rayuwarki amma ban yi miki alƙawarin koda yaushe ba saboda zan kasance tare da ɗan uwana acan nahiyar mu, Ubangiji ya albarkaci rayuwar ki da yarin ni'imomi ya kawo miki ɗauki sannan ya taimakeki akan abin da kika saka gaba, ina miki fatan nasara Maryam Noor kiyi rayuwa me kyau da inganci."
    Yana gama faɗin hakan ya kanannaɗota da jelar shi me haske yayi sama da ita suka fice daga cikin gidan, ajeta yayi ƙasa tare da saita ganinta akan gidan da lokaci guda ya rikiɗe ya sauya mata, daga wannan gidan me ƙaramar ƙofa zuwa wata ƙasa wacce ta taru me hudoji da ramuka wati shuri.
     Ita ɗin me jin magana ce bata kuma iya musu da jayayyaba, kuma tana gaugawar barin du wani abu da waɗanda suka rayu tare da ita suka haneta, shi yasa ta danne ɗaurariyar zuciyarya  bata matsawa kanta da tambayar ta yanda ta rayu a cikin shuri ba ta soma saƙa yanda zata fuskanci rayuwarta da kuma hanyoyin da zata bi su sadata da jininta ƙwalli ɗaya jal da Kakaninta suka tabbatar mata da yana raye amma kuma basu bata wata ƙofa ba da zata gane inda wannan jinin nata ya ke.

    Juyawa ta yi ita kaɗai a wajen shurin da take hange  mutane na wucewa nesa kaɗan ta shi, bakinta da zuciyarta na ambatar sunayen Allah tsarkaka ta durfafi gabanshi ta soma takawa da ƙafafuwanta, tana jin yanda komi ya sauya ya zame mata daban, daga gefe ɗaya kuma tsoro da zullumi ne cike fal ranta na yanda zata rayu alhalin bata saba rayuwa da mutane ba.....
   Alhamdulillah 🤲 yau Allah ya nufe ni da kammala littafina na ɗaya ƊAURIN ZUCI BOOK ONE.
     Ina roƙon Allah yaci gaba da bani iko, dama, lafiya da rayuwa me albarka da zanci gaba daga inda na tsaya.

Littafi na ɗaya ya ƙare a daidai inda cakwakiya zata fara, shin mine ne makomar rayuwar Noor Maryam, taya zata ci gaba da gudanar da rayuwa a haka bayan bata saba mu'amala da jinsin mutane ba, shin wannan jinin nata da ke raye zata ci nasarar gano inda yake kuwa, mizai garu da ita a lokacin da gaskiya ta buɗe mata?????.

     Makafa, du abin da ya aikata ba yin kan shi bane, an ɗaure zuciyar shi da baƙin tsafi yanzu kuma ya shiga wani yanayi sakamakon fasa bangon kariyar da Kanzul yayiwa Muhammad da Zunaina yayi nasarar tarwatsa su inda daga nan kuma wani yanki daga cikin ƙarfin ikon shi ya zagwanye, shin mi zai faru da rayuwar shi nan gaba bayan tsafin shi ya raunata???

Wane yanayi Muhammad da Zunaina zasu kasance idan suka farka suka samu kan su a rabe wani waje na daban????

Shin wai mine ke faruwa da rayuwar Junaid da Saminaka????

 Wacece Mommy, kuma mi ta aikatawa Saminaka wanda ɗanta Fahad ya ganta????

Wannan dama sauran amsoshin du zaku same su ne a littafin ƊAURIN ZUCIYA BOOK TWO wanda zai fara sauka nan bada jimawa ba a whatsapp groups na dandalin arewapen akan account ɗin MARYAM STAR, da Hausa novel app shima akan account ɗin MARYAM STAR.

Littafin Ɗaurin Zuci free book ne daga farkon shi har ƙarshen shi, wanda ya kasnace kyauta daga ni zuwa ga masoyana masu siyan litattafaina musamman littafin.

RAYUWAR SAMHAD

ZAFIN WUTA

MABANBANTAN ZUKATA.

MUHASEEN.

Ina matuƙar godiya agareku jarumai kuma zaƙaƙuran fans ɗina Allah yabar zuminci.



Allah kajiƙan mahaifina da ƴan uwana musulmai baki ɗaya ka gafarta musu ka haskaka makwancinsu kasa aljannace makomarsu alllahumma ameen yah Rahaman🤲.


MARYAM STAR⭐WRITER....✍🏻 CE

***..