RU'UYAA (The dreams we never lived)
34. ... Bewitched...🖊️
by @autum17
34. ... Bewitched...🖊️
muna tsaka da juyi Mufeedah ta turo ƙofar ɗakin saye da wasu tsinannun kayan da suka kamata musamman daga ƙirji da hips...mazaunan ta shape ɗinsu ya fito sak sannan skirt ɗin shara shara ana ganin komai..haka ma rigar jar breziyar dake jikinta shatin taya fito...wani banzan turare mai ƙarfi tasa daya mamaye ɗakin lokaci guda disrupting the mild scent dake ɗakin kafin ta shigo...hannunta riƙe da laptop kanta ba ɗankwali
murmushin dake fuskata ya ɓace... Khalil ya sauke ni Batareda ya sake kallon Mufeedah a karo na biyu ba...
share kallonta tayi akaina wanda harara ne cike da tsana,ta maƙe murya '' ya IB dan Allah ina buƙatar taimakon ka akan wani mathematics assignment da aka bamu.. pls '' ta matso ta tsaya kusa dashi kamar zata shige cikin shi,ji nayi zuciyata na tafarfasa,kamar in haɗa kanta da bango
'' oh...okay'' Khalil ya faɗa hesitantly..'' yeeey mutafi parlor!" Ta juya tana tafiya kamar hawainiya tana tsammanin ya biyo ta..hmm badai a gabana za'ayi wannan ba...
'' Khalil ku tsaya a cikin ɗakin nan,nima ina so in koya amma kaga har yanzu jikina ba ƙwari pls...'' nayi maganar ina wani lanƙwashe kamar taliyar data jiƙu cikin ruwan xafi tare da turo baki kamar yanda yara suke idan suna son sweet...
'' Whatever you say!" Maganar ta ƙwace daga bakin shi like someone bewitched idonshi a kaina
'' wait, WHAT!!!!!" Mufeedah tayi juyin 360 baki sake fuska yamutse...bayan Khalil na ɓoye na sakar mata murmushin nasara..nizata nunawa ta'addanci? tana tunanin ita babbar macece and she could dress to seduce him ina nan tsaye babu abinda zan yi ko?
hannun shi ya zagayo a kafaɗuna ya tayani zama na jingina bayana da bangon gadon...ya zauna gefe....kamar zata kama da wuta tazo ta zauna da gangan nake wasa da pillow na jefa shi tsakaninsu yanda bazata haɗa jiki dashi ba...kamar zata kashe ni datse haƙoranta tayi saman lips ɗinta ta gyaɗa kai irin zaki sani ɗin nan ko a slippers ɗina...
wani banzan mathematics ne mai sarƙaƙiya yake koya mata sauraren shi kaɗai yasa ni ciwon kai...sai cewa take bata fahimta ba..dan kawai ta ƙara kasancewa dashi... turarenta shaƙe ni yake shigar jikinta na sani ciwon ido...
idan idon mu ya haɗu sai mu sakar ma juna harara...oh ni Abeedahtuwo na canja sosai fa,ba kamar daba da yanayina kesa ni inaji kowa ya fini dan haka dole in ƙanƙantar da kaina a gaban kowa...idan ma so samu ne in ɓace...yanzu akwai wannan ƙaramin ƙwarin guiwar da nake ji tattare dani...idan badan haka ba,taya na iya shishshigewa Roman duk da nasan sama tayi wa yaro nisa? Taya na iya sakin jiki da Khalil? Taya na iya tasarwa masu cimin mutunci...saɓanin da danake yin shiru inyi ƙasa da kaina cikin ƙasƙanci...
nayi farin ciki sosai da wannan cigaban dana samu koda bakoda yaushe nake jin confidence ɗin ba, at least akwai shi!
'' Khalil yunwa nake ji...'' Batareda yace komai ba ya zaro wayarshi ya kira kitchen yan mintina kaɗan sai ga Leonardo ya shigo ɗauke da farantin abinci karɓa Khalil yayi ya ajiye gabana '' na gode...'' na furta...kafin na fara cin abincin dayayi daɗi sosai...har lokacin Mufeedah na nan
'' kai ma kazo muci..''
'' bana jin yunwa...''
'' okay...amma abincin yayi daɗi ɗanɗana kaji...'' na ciko cokali na kawo saitin bakinshi... Mufeedah take karkaɗa halshe cikin baki irin lalala ɗin nan tana kallona
riƙa hannu na yayi yakai abincin bakin shi '' ni banji daɗin da abincin yayi ba...''
'' wai ma bakaci da kyau ba...ƙara kaji..' cigaba da bashi abincin nayi...tana goga haƙoranta tace '' har yanzu ban fahimta bafa ya IB...''
'' baki ga yana cin abinci ba,ki dawo wani lokaci..ko ki tafi wurin Farzan na tabbatar shima ya iya!"jinjina kanshi Khalil yayi. kamar akuyar data sha ruwan zafi Mufeedah ta finciki laptop ɗinta tana taku kamar zata ruguje ɗakin ta fita ta banko ƙofa...na raka bayanta da harara
'' ban san kina da kishi har haka ba...'' yayi baya ya kwanta yana min wani irin kallo mai ma'ana ɗage kafaɗa ta nayi '' wayace kishi nake?''
'' your actions did!" Taɓe baki nayi '' uhm bari inzo in tafi...''
na sauka daga gadon tare da ɗaukar plates ɗin ya biyo bayana bayan ya ɗauko min hijabi ash color daga ɗakin shi
'' yanzu wake nuna kishi?"
'' Ni!" Ya amsa...banyi tsammanin hakan ba..na ƙifta several times
'' what? Kina tsammanin nima in ɓoye kamar yanda kike yi?" gira ɗage baki a sama yayi tambayar...tsuru tsuru nayi da ido...ya nuna min hanya muka fita tare zuwa kitchen...
Sannan ya rako ni zuwa sashen mu a bakin ƙofar yace '' zaki iya kwana a sashena idan kina so...''
'' awwn.. ɗan wani na tsoron kwana shi kaɗai ...''
'' ba haka bane...'' ya sosa ƙeya
'' toh meyasa ka bari muka fito kafin ka faɗa?"
'' oh..it slipped my mind..''...'' idan baki son taka ƙasa ne,zan iya ɗaukar ki!" Yayo gaba nayi baya...
'' rufa min asiri kada su seratena su cinye ni ɗanya..''
'' ban san kina da tsoro har haka ba!'' yayi murmushin gefen baki '' wai ma...''
'' amma fa gara in zauna a sashen mu...zan zo gobe kafin in tafi makaranta...''
Ya jinjina kanshi...muka sakar ma juna murmushi sannan ya tafi...
Ina shiga ɗakin mu sabuwar wayata na ciro na kunna,tana kawowa na shiga play store nayi Installing abubuwa harda Whatsapp nayi sign in..number Jay d ta fara fitowa nayi mata text...amma bata online bata amsa ba
Sauran ranar ta wuce da sauri... washegari bayan na shirya cikin uniforms ɗina nasa guntun hijabi fari na wuce sashen Khalil..tun daga dining nake jin yanda ake jefo min kallon tsana da zagi amma ban juya ba...
na ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin shi tunda bai nan parlor...nan ma ba amsa na leƙa ciki bai nan..zama nayi na ɗan lokaci ina jin ɗumi a tsakanin ƙafafuna amma ban wani maida hankali ba can na miƙe na fita
Ina tafiya a hall way ƙamshin Romo ya daki hancina...kaɗan kawai na ganshi ya jefo min baƙar rigar shi a fuska..jaye rigar nayi da sauri.. ya jingina da bango ƙafa ɗaya tokare ta baya hannun shi cikin aljihu kallon da yake min yasa na tuna abunda ya faru jiya,da busassar muryar shi dake haifar min da sanyi har cikin ƙashi yace '' ke baki iya kula da kanki bane?...'' ban fahimci abinda yake nufi ba,shima baiyi min bayani ba...ya juya yayi tafiyar shi,to me zanyi da wannan rigar daya jefo min yanzu? rungume rigar nayi... at least yanzu ina da wani abu nashi...na kai rigar saitin hancina na cigaba da tafiya
Zirrr! Naji wani abu mai ɗumi na fita tsakanin ƙafafuna kamar fitsari sai dai wannan yana da zafi da kuma kauri... lokaci guda idona suka buɗe...na ɗaura hannu saman kai '' lailaha illallahu... shike nan ya ganni...'' da sauri na jawo bayan rigata sai lokacin na fahimci amfanin jacket ɗin,da sauri na ɗaura ta a ƙuguna.. jikina ya ɗau zafi...naji kamar ƙasa ta haɗiye ni...
'' yar matsiyata kin zo kin kanainaye su yaya IB kina cinye musu kuɗi baki ji kunya ba?" Seraphina ce tayi maganar murya ɗauke da guba
'' dama talakawa ina suka ga kunya? har take tunanin dan kawai ya Khalil na favoring ɗinta zata iya shiga da fita a duk sanda taga dama....'' Khaleesat take hararata da jajayen idonta
'' ni na rasa me maxan gidan nan suka gani tattare da mummunar yarinyar nan da suka haukace mata!" Mardiyya ta faɗa
'' sihiri tayi masu mana...dama kin san ya'yan talakawa dabin bokaye,kin kuwa ga yanda yaya Khalil keyi da ita!" Mufeedah ce tayi maganar tana riƙe haɓa
Nayi tsaye ina sauraren su,suna cimin mutunci...da farko rashin sanin abinda zan faɗa yasa nayi shiru.. can nace
'' come on girls..say the words!" suka kalleni da rashin fahimta
'' wane kalamai?" Heedayah ta tambaya
'' yanda zaki sa namiji ya zauce,ya susuce yayi yanda kike so... batareda kin yi magana ba,simply saboda kina da gray eyes,that look like Galaxy of Stars at night!...'' na gwalalo masu idona ina nuna masu ƙwayar ciki da murmushin gefen baki....
Fuskokinsu kamar kashin da ruwa ya duka har hayaƙi yake fita daga hancin su tsabar yanda na fusata su...
'' Ni ɗin yarinya ce mai sauƙi,bana bin bokaye abu guda nake yi...'' sai na turo baki tareda ɗan buɗe idona kaɗan ina kallonsu nacigaba da faɗin '' sai in kalli cikin idon mutum... shikenan duk abinda nake so na samu! Simple no?"
'' Hah! You're seducing them with your stupid ugly eyes?" Khaleesat tayi busassar dariya ..dukansu suka dafe ƙirji...na ƙifta idona cutely
'' wannan ba jacket ɗin yaya Roman bace?" Khadeejah ta nuna rigar dake ƙuguna..nayi narai narai da ido kamar wacce ake bullying
'' shi ya bani da kansh...''
'' ƘARYA KIKE!!!!" Seraphina tayi min ihu tayo gaba tana jan rigar daga ƙuguna sauran na ƙara taya ta...nima damƙe rigar nayi kamar rayuwata ta dogara da rigar...taya zan bari ta karɓi abinda Roman ya bani?
ganin ta kasa cire rigar ta ture ni da ƙarfi cikin fushi...sauran na cheering ɗinta...kafin in kai ƙasa hannaye masu ƙarfi suka taro ni,ƙirjina ya shiga harbawa zazzafan hucin sa na sauka a fuskata
Ɗagowa nayi na kalleshi Khalil ne ya fito daga elevator daidai Seraphina na ture ni yayi saurin riƙo ni...suka yi tsaye wurin kamar an ɗasa su
'' are you okay?" Ya tambaya da kulawa..jinjina kaina nayi.. batareda ya kalleni ba ya kalli Seraphina da sauran
'' KU BATA HAƘURI YANZUN NAN!" ya faɗa da ƙarfi fuskarshi ɗauke da fushi...sakin baki sukayi kafin suka kalli juna da mamaki
'' Amma ya IB...''
'' Now!" Ya katse Heedayah...
'' kiyi haƙuri...'' suka faɗa a tare... Seraphina ta tsere tana share hawaye suma sauran idonsu kamar garwashi
'' I'm so...''
'' meyasa zaka bani haƙuri bayan bakai kayi min abu ba?" Na ɗaura hannuna a haɓa ta kamar mai tunani...
ya girgiza kanshi...'' oh bari in tafi muna da jarabawa fa...''
'' let me drop you off...''
Na gyaɗa kaina daidai nan Diyaam ta ƙaraso shirye cikin uniforms ɗinta a girmame ta gaishe da Khalil sannan ni..muka shiga elevator tare..har muka fita kanta a ƙasa...tana da kunya sosai...
Sashen mu na shiga na sauya kaya..ina neman pad idona ya sauka akan baƙar ledar da Khalil ya bani shekaran jiya...ina dubawa naga Pad... runtse ido nayi kafin da sauri na ɗau ɗaya na shiga Baye nasa na fito muka wuce
cikin motar nida Khalil kaɗai ke hira Diyaam tana duba littafin ta kamar babu ita a motar har muka iso..ya bamu kuɗi da ƙyar muka karɓa yayi mana bye ya tafi
Yau Jay d dasu Asma'u basu da paper hakan yasa basu zoba... Da ƙarfe goma da rabi muka fara jarabawar muka gama ƙarfe biyu, duk na gama gajiya...kowa faɗa yake jarabawar tayi wahala nima na yarda itakam Diyaam cewa tayi bataji wahalar paper ba...
da ƙarfe uku muka bar makarantar muna tafiya tare da wasu yan ajin mu muna hira da farin ciki.. duka munga nawar a gama jarabawar mu huta...
Da ƙarfe huɗu muka isa gida...
Ma'aikatan babu kowa...duk suna wurin aiki,kayana na canja nayi sallah ko abinci ban nema ba na kwanta bacci... Da daddare kaɗan naci abincin na shige ciki da wuri...
***
RU'UYAA…📖
₦500 ne idan ya kammala zai koma 800
Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay
Shaidar biya ta ***
Autumn writes 📖🖋️