RU'UYAA (The dreams we never lived)

35. ...His life line...🖊️

by @autum17



Washegari da rana ina tsaye a kitchen Roman ya shigo hannun shi riƙe da waya yana video call da Yaren su yake magana ban masan mai yake cewa ba...suna guda naji yana maimaitawa 'Lucita' can ya ajiye wayar saman counter ya ɗaura apron yana cigaba da magana...

Daga cikin wayar naji ance


(Sei entrato in cucina... cosa stai facendo?)  
Kashigo kitchen... mezakayi ne?

Lasagna... voglio sentire la tua presenza qui vicino a me. 
(Lasagna... ina so in ji ta a kusa da ni...) fuskar shi tayi duhu daya faɗi koma meye hakan ke nufi... Ya nufi fridge ya ɗauko kaza da wuƙa 

(Andrà tutto bene...)
Komai zai yi daidai...
 
''Hmmm, babu abinda zai sake kasancewa iri ɗaya har ƙarshe Lucita.''
(Hmm... niente sarà più lo stesso fino alla fine, Lucita.) Yayi maganar tsakanin haƙoranshi...yana bin kazar da wani irin kallon daya sa zuciyata bugawa da ƙarfi..yanda ya riƙe wuƙar duk jijiyoyin shi sun fito hannunshi ya ƙara fari kamar ƙasusuwan zasu karye


''Romano, kayi rayuwa kamar mai rai, kada ka rayu kamar matacce.''(Romano, vivi come un vivo, non vivere come un morto)

''Na' daɗe da mutuwa Lucita... sau biyu na mutu... har yanzu ban farfaɗo ba!''(Sono morto da tempo, Lucita... sono morto due volte... e non mi sono ancora ripreso!)ya ɗauke kanshi gefe daya faɗi hakan... fuskarshi tayi ja,laɓɓanshi na rawa... maƙogwaronshi sai kai kawo yake kamar tayar dake gaba da baya...amma nashi da sauri 


Shiru akayi daga can gefen na ɗan lokaci kafin aka sake magana''Shikenan ka yi lasagnar ka." (Allora fai la tua lasagna..) 




Ya fara yankan kazar da ƙarfi kamar zai haɗa da hannun nashi..kamar kazar itace ciwon dake zuciyar shi da ba'a iya gani...kamar hakan zai sa yaji sauƙin koma meye... idonshi suka sauka akaina na rabin second ya ɗauke idonshi kamar bai ganni ba...ɓoyayyar ajiyar zuciya na sauke...ina cigaba da kallon shi... wanke kazar yayi ya zuba cikin kwando sannan ya kunna gas 

Ya zuba man zaitun a pan. Sautin *tssss* ɗin ya cika kitchen ɗin, kafin ƙamshin albasa da tafarnuwa suka gauraye kitchen...

Kazar daya yanka ƙanana ƙanana ya zuba cikin wata tukunya daban,ya zuba magunguna da Black pepper..ya ɗaura saman gas...yanayin komai da sauri ne kamar idan ya ɗan dakata abinda ke tafasa daga cikin zuciyar shi zai fito ne da ƙarfi 


A wata tukunya, butter ya narke. Ya zuba gari. Ya motsawa. Ya motsawa. Har saida ya zama paste... sannan ya dinga damƙar madara yana zubawa hannu a sama,kamar yana barbaɗar da ciwon dake zuciyar shine..

Ya ɗauki lasagna(lazanya) sheet ɗin. Ya ji ta a hannunsa ya shimfiɗa saman wani flat plate

Layer ya zuba Sauce a ƙasa don kada ta ƙone.  
ya sake shimfiɗa wani a saman na farko ya ƙara zuba farar sauce, sai kaza, Sai cheese yana faɗuwa kamar dusar ƙanƙara. ...ya maimaita wannan kusan sau biyar sai da abin yayi tsawo...

A saman, ya zuba cheese mai yawa...ya daɗe yana kallon abinda ya haɗa ɗin kamar ya shiga duniyar tunani kafin ya ɗauka ya saka shi cikin oven. Ya rufe bayan yasa timer na 35 minutes... fuskar sa a tamke fiye da koda yaushe...motsin shiya rage sauri...yanda ƙirjinshi ke sama da ƙasa ya ragu...tap ya kunna ya shiga wanke hannayen shi slowly kafin yayi ƙasa da fuskarshi ya watsa ruwa...sanda ya miƙe ranar data shigo ta window ta bugi fuskar shi ta haskaka ruwan dake maƙale a fuskar shi kamar Lu'lu'u...lips ɗinsa sukayi ja na musamman... idonshi dangerously sharp...yan tsirarun gashi suka sauka a kan idon shi....Ahhh! ji nayi bugun zuciyata ya sauya sanda ya kalle ni... ba tsoro bane, soyayyar sace tamun kamun kazar kuku...kasa dena kallon shi nayi...sai shi daya ɗauke kanshi saboda tsayawar oven ɗin,gloves yasa ya buɗe ya ciro abinda ban san Meye Shiba...abun yayi kyau a ido ga ƙamshi dake tashi daga gani zai yi daɗi har yawu na sun tsinke cikina ya bada ƙarar daya sa naji kamar ƙasa ta haɗiye ni...

    "Wannan duniyata ce... inda nake wanzuwa kai kaɗai."( `Questo è il mio mondo... dove esisto da solo.`) ya furta yana gyaɗa kai cikin tabbatar wa...

Wurin da ake ajiye plates na tafi na ɗauki ɗaya na tura gaban shi ina tsaye ta bayan shi...bai ce komai ba..ya ɗauki wuƙa ya yanka min gefe ɗaya... 

'' akwai daɗi?" Na tambaya daga bayan shi..'' akwai ɗaci!" Ya amsa min tareda matsawa daga wurin...ɗaukar plate ɗin nayi ina kallon abinda ke ciki kafin na wanke hannu na zauna akan ɗaya daga cikin kujerun kitchen ɗin na fara ci after much hesitation... saboda abin ƙazanta yake ban... amma duk wannan ɗar ɗar ɗin ya fece sanda abun ya sauka a bakina... idona har ƙyalli suke..da sauri na haɗiye na bakina na ƙara wani...abun yayi daɗi sosai...

'' kai bazaka ciba?" Ɗagowa yayi daga wayarshi da yake daddannawa ya kalleni kaɗan ya cigaba da danna wayar


Diyaam ta fara shigowa kitchen ɗin,wurina tazo da murmushi a fuskarta tace '' Lazanya?"..ashe hakane sunan abun...zama tayi muka cinye wanda ke plate ɗina ta sake ɗauka ta tafi wurin Roman '' Hamma nima ina so...''

Wayarshi yasa a aljihu ya yanka mata wanda yafi nawa girma,juya ido a nayi wato yafi sonta fiye dani...wani irin kishi naji araina..data kawo saura kaɗan ince banci tuna daɗin abun yasa na haƙure naci..muna tsaka daci sai ga Khalil...da hannu nayi mashi alamar ya ƙaraso..ya zauna gefen Diyaam

'' party kuke ashe?" Ya tambaya...

''ci kaji abun baiyi daɗi ba,turawa kawai nake saboda yunwa!" taune leɓenshi yayi.. amma naga murmushin dayake ɓoyewa..yasa hannun shi a plate ɗin muna ci tare... Diyaam tayi ƙasa da kanta fuskar ta kamar tumatur.. meyake damun yarinyar?

Ya kalli Roman yace '' Rome...da gaske Abuja zaka tafi ranar Friday?" batareda ya ɗago kanshi ba yace '' hmm..''

'' yaushe zaka dawo?"

'' Monday...'' ya mayarda wayarshi cikin aljihu..ya ɗauki plate ya yankawa kanshi ya zauna yana ci elegantly... Kafe shi nayi da ido Batareda Nasan nayi hakan ba

'' you're choking me with your eyes!" ƙatuwar muryarshi da a wannan lokacin tafi komai daɗi a kunnuwa na ta karaɗe kitchen ɗin... Diyaam da Khalil suka kalleni

Ɗaure fuska nayi nace '' oh...bansan cewa ido suna da hannu ba da har suke shaƙe mutum batareda mai su ya sani ba!" Dariya Diyaam tayi..bakinta rufe,bakin Khalil a ɗage alamun murmushi...

.Roman bai sake cewa komai ba..Nima ban sake kallon inda yake ba...

Kitchen ɗin yayi shiru...miƙewa yayi da plate ɗinshi ya buɗe ƙofar baya ya fita...


'' do you want to go out too?" Khalil ya tambaya..nida Diyaam muka gyaɗa kai...

'' follow me!" Muka bi bayanshi hannuna riƙe da ruwa cikin cup, sassanyan iska ne ke kaɗawa...ruwan cikin swimming pool ɗin sunyi blue sosai...iska na kaɗa su a hankali... bishiyoyin dake zagaye da wurin suma suna rawa da iska

'' ka iya ruwa?" Na tambayi Khalil

'' a'a!" Ya bani amsa...duƙawa daga baki baki Diyaam tayi tana wasa da ruwan...can na hangi Roman zaune a ɗaya daga cikin kujerun yana wasa da wayarshi..barin Khalil da Diyaam nayi na isa wurin shi...koda na leƙa wayar game yake bugawa yana ganina na ya kashe wayar ya mayar cikin aljihu


'' Abeedah zoki ga wani abu...'' Diyaam ta kira Ni,barin wurin nayi na isa inda take...wasu flowers masu kyau ta nuna min ranar dana ke zagaye wurin ban kawo har nan ba...wata pink na tsinko na jaye ɗan kwalinta baƙar sumar ta,ta sauko har rabin bayanta..
''.kin yi kyau ma sha Allah..kamar ɗaya daga cikin wa'yannan Disney princesses ɗin!" Ta sadda kanta ƙasa,fuskarta ta ɗanyi ja kaɗan


'' wai ke daga an maki magana sai fuskar ki tayi ja a'a!" Dariya tayi tace '' fuskar take yin ja da kanta bani nake sata ba!" 

'' hakan na ƙara maki kyau sosai...''

'' na gode...bani ɗan kwalin''ta miƙa hannu zata karɓa,ɓoye ɗan kwalin nayi baya na...

Ta zaro ido '' ki bani mana...''

'' bamu kaɗai bane a nan,ki barshi kawai...'' ɗaure fuska tayi ta miƙa hannu zata karɓa na kwasa da gudu ta biyoni

Ina gudu ina dariya ko gabana bana kallo...Roman na tsaye daga bakin swimming pool ɗin hannunshi saye cikin aljihun wandon shi...nayi lattin ganin shi,koda nayi ƙoƙarin taka birki kasawa nayi sai dana tura shi cikin swimming pool ɗin ya faɗa tsumbul!!!

Allah ya taimake ni ƙafafuna kamar suna da ikon kansu sukayi tsaye daga bakin wurin batareda na bishi ciki ba...sama yayo ya sharce ruwa daga fuskar shi yana hararata kamar idonshi zasu zubo


'' LORD GIVE ME THE PATIENCE!!!?...'' yayi maganar yana riƙe matattakalar fita daga wurin yayo kaina da jajayen ido ruwa na sauka daga jikinshi ta ko ina...na fara matsawa baya

''.uhm..ba..bada ga...n..''riƙo hannu na yayi da alamu nima wurga ni zai yi cikin ruwan


'' KHALIL!!!!" na kira da ƙarfi tare da runtse idona ina turjewa...da sauri ya iso wurin ya ƙwace ni daga hannun Roman da yake jefamin banzan kallo.. da alamu na kaishi maƙura...cusa hannunshi yayi cikin jiƙaƙen gashin shi yabar wurin kamar zai kama da wuta...

'' why did you push him into the pool?" 

'' ban lura dashi ba...'' na faɗa ina turo baki idona cike da hawaye

'' it's okay kada Kiyi kuka!" Ya riƙe ni muka bar wurin...

Slowly Diyaam ta fito daga inda ta ɓoye tun sanda Abeedah ta jefa Roman cikin ruwa ta laɓe a wurin...tsayawa tayi kusa da ruwan once more sai ta zuƙunna.. seems like sun manta da ita... Hawaye da suka ciko idonta suka ɗiga cikin ruwan,fuskarta tayi ja...kafin ta fara sniffling da ƙarfi tana kallon reflection ɗinta


Tsoma hannun ta tayi cikin ruwan ta zaro,iska na kaɗa gashinta sanyi na ratsa ƙasusuwanta...da muryar kuka tace '' "An min maa... waɗi nyalnde maa a heɓan anndude ɗum? A maa yiɗi yi'ude am?(Nima...akwai ranar da zaka damu sani irin haka? Zaka taɓa gani na?)

Sai ta haɗa kanta da guiwarta tana kuka sosai...

(Ashe Dee Dee ta iya fulatanci 🤭)
***
Washegari nayi kwance a saman gadona cikina na tsananin ciwo wurin ƙarfe ɗaya na shirya zan tafi makaranta sashen Khalil na fara zuwa amma bai nan...na ɗan zauna na lokaci har Saida ciwon ya sassauta sannan na fito daga sashen.. runtse idona nayi tareda dafe inda ke ciwon...sai na miƙe tsaye na fara tafiya da sauri na kawo wurin elevator naci karo da mutum...nayi baya baya zan faɗi na damƙo wuyan rigarshi..hakan ya tilasta mashi riƙe kafaɗuna badan yaso ba,Roman ne, expression ɗin fuskarshi kamar kunun aya daya lalace...idon mu ya haɗu...ya haɗe fuska '' idan baki tsaya da kyau ba xan sake ki!" Ya furta da murya mai zurfi...taɓe baki nayi sai nayi murmushin gefen baki duk da ciwon da nake ji...

'' da gaske? Kyawawan Idanuna basa tuna maka da komai?'' taune leɓenshi yayi ya cire hannuna daga colar rigarshi...'' you're too bold for your own good!" Ya matsar dani gefe yayi tafiyarshi nabi bayanshi da dariya mai rauni...

Tafiya a hankali na shiga elevator,yau ban taka ƙasa ba abun hawa na hau ya sauke ni har gaban makarantar mu...na shiga ciki na isa ajin mu na zauna...ciwon cikin na ƙara hauhawa...kwantar da kaina nayi saman desk na juyar da kaina gefe ina hango waje ta taga..idona sunyi jawur zuciyata tayi nauyi...babu rana a can wajen hakan yasa yanayi na ya ƙara ɓaci...surutun mutanen dake ajin yayi nesa dani...akwai wani emptiness a zuciya ta...nake ji ajin yamin faɗi...kowa nada wanda suke hira dashi..ni kaɗai ce mara aboki hakan yasa nake ji kamar ban cancanci in kasance anan ba...i don't belong with them...babu wani irina..babu wanda ya damu dani....

Lumshe idona nayi ban sake buɗe suba sai da aka shigo ana kiran lambobi....bayan wani lokaci aka kawo kaina...da ƙyar na tashi na karɓi tawa paper...na zauna akan table ɗina ƙasan marata na ƙara ɗaurewa....


Can aka fara rubuta jarabawa...baƙin cikina ya ninku..na farko bana jin daɗi,na biyu babu abu ɗaya dana karanta daya fito a jarabawar...wani malami ne cikin wa'yanda ke karɓar cin hanci yazo ya tsaya akaina yana min ihu wai inyi rubutu ...mai zan rubuta bayan ban san komai ba?


Hankalina ya ƙara tashi...ajin yake ƙara ƙarancewa a idona...duk da kuwa faɗin da yake dashi...nake kuka sosai... mutane sai kallona suke wani invigilator ne ya shigo yace ma Malamin ya rabu dani...

Ina sheshsheƙar kuka..ina ƙoƙarin tilasta ma kaina inyi ƙoƙarin tuna wani abu...nake so inyi addu'a amma zuciyata tariga da ta yarda da cewa babu abinda zai canja..kamar baya..haka ma wannan addu'ar itama zata kasance babu amsa...


lokaci tafiya yake sai ƙara tunatar damu suke akan hakan...hannu na rawa na ɗauki pencil ɗina na fara shading amsa batareda Nasan abinda nake shading ba...essay ɗin ma abinda ban sani ba na rubuta...

Wurin ƙarfe huɗu muka gama jarabawar...mutane suna zuwa wurina suna bani haƙuri...hakan ya ƙara sa hawayen da suka tsaya na ɗan lokaci suka sake ƙwace min...

Na tafi wurin masallaci na zauna...iska na kaɗawa a hankali...ranar ta faɗa saman bangon dake gabana... further making me feel worse... ni kaɗaice a wurin..babu kowa...dama wazai kasance tare dani? badan Allah ya kawo Jadeedah a rayuwa taba,nayi imanin daga jss har ss zan kasance ne babu ƙawa...


Harɗe hannayena nayi saman cinyoyina na ɗaura kaina a sama...ina kuka a fili kuma da ƙarfi...

Bayan lokaci mai tsawo na wanke fuskata...idona ya sauka akan sarƙar dake yawo a wrist ɗina...mai ɗauke da silver chain da kyakkyawan saphire blue pendant a saƙiya da kunburarrun idona na ɗago zuwa fuskata...ina na samu? Kamshin turaren jikin abun ne ya sanar dani ko na waye...Roman...

share Hawayen da suka taru a idona nayi... suddenly naji babu wanda nake so in haɗu dashi sai... KHALIL...miƙewa nayi da ƙyar,hannu na dafe da cikina na shiga tafiya..

Makarantar har an tsiyaye...ni kaɗaice...daga ni...sai iskan dake kaɗa ni a baya...da kuma ranar dake tausayamin da hasken ta daya kasance orange...sai kuma shirun dayake abokina tun ba yau ba...

Nake kallon yaran dake gabana,su huɗu ne suna tafe suna dariya a tsakaninsu..sai dariyar su ta kasance...mafalkin da baxan taɓa kasancewa a ciki ba ...

Ƙasa nayi da kaina na danne leɓena da haƙorina...baza Kiyi kuka ba Abeedah...kina da Jay d ko?

Dogon numfashi naja takuna na ƙara zama slow...hannuna ya ƙara ƙarfi wurin riƙe cikina...

****

Roman na tsaka da shafa lotion a jikinshi bayan ya fito daga wanka... idonshi ya ƙanƙance bayan bai ga pendant ɗin dake hange a wuyanshi ba a koda yaushe....


Da sauri ya bar gaban madubi ya isa toilet duk da yasan abune mai wahala ya kasance wurin don baya cire wannan pendant ɗin ko wanka zai yi...a koda yaushe yana maƙale da wuyanshi... Ɗaya daga cikin abubuwan dasu ka rayar dashi kenan na tsawon lokaci...

Cusa hannayenshi yayi cikin sumar shi yana numfashi sosai yayi tsaye wuri ɗaya hannu a ƙugu...

Can ya buɗe idon shi da suke a lumshe...'' Damn!" Ya furta a gaggauce ya jefa baƙar t shirt da baƙin wando ya fice daga ɗakin bayan ya wasgi mukulli..a parking lot ya haɗu da Leonardo jefa mashi mukullin yayi ... Leonardo ya caɓe Roman ya shiga baya shi yana a gaba a mazaunin driver da gudu ya fita daga gidan....



Tafiya nake batareda Nasan inda nake saka ƙafafuna ba,ba wai na damu bane da koma ina nake a wannan lokacin...wata hanya ce da babu kowa sai ganyayyakin dake faɗuwa da kuma ranar data kusa faɗuwa...sai kuma ni tare da ƙawayena...shiru da kaɗaici da kuma Hawayen dake zarya a fuska ta..na gaji da tafiya...duƙawa nayi a wurin cikina kamar zai fashe...ban taɓa yin ciwon ciki mai tsanani irin wannan ba...

Miƙewa nayi iskan na ƙara tura ni gaba dan ƙarfina ya ƙare...kamar xan suma...jinayi na kasa cigaba da tafiya kamar an riƙe ƙafafuna wuri ɗaya...idona ya fara ganin duhu duhu..wata baƙar motace ta parka gaba dani kaɗan...gani nayi Roman ya fito yana share gashin shi da iska ke kawowa saman fuskarshi baya..yayo kaina daidai ƙafafuna suna shirin jefar dani...gaban rigarshi na sake riƙowa kamar wancan lokacin, duka maɓallan sukayi ta kansu, na tabbatar da lafiya ta kau ƙila har suma sai nayi wai Romo ne riƙe dani


hannun shi riƙe da ƙuguna wannan lokacin saɓanin ɗazu daya riƙe kafaɗuna...


Da ƙyar nake iya ganin fuskarshi...'' c...cik..ina...zan..mut..uu.. Khalil...'' ban sake sanin mai ya faru ba bayan wannan...



***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️