NUFIN ALLAH

35

by @anisamuhammadyah897



💕 NUFIN ALLAH 💕 
By
Anisa Muhammad yahaya 


 YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA

Page 3️⃣5️⃣

Wani irin abune ya caki zuciyar ta gaba ɗaya ganin ta taji ya ɗauke Saida Abhie ya rike ta

Da kyar ya iya zaunar da ita, ta jima a haka kafin ta kalle shi tace

"Abhi ka kaini gida Papi na Papi wayyo Allah!!! shikenan mun koma marayu ta ko ina"

"Kiyi shiru Rukayya addu'a ake ba surutai ba kidena wannan ihun kiyi addu'a"

"Nidai ka kaini gida kawai kakaini gida"

Kuka take sosai mara sauti irin me cin rai ɗin nan

Mukullin motan shi ya ɗauko ya ce ta taso suje shima gaba ɗaya jikinsa yayi weak ga rasuwar Papi ga yanda take kuka me taɓamai zuciya, riƙo ta yayi suka fito, har side dinta ya zaga da ita ya bude ya saka ta acikin suka fito daga gidan 

Kasa gane inda kanta yake tayi Saida ta tashi taga hannunta saƙale da drip, hannun tabi da kallo har inda aka saƙale drip din, ɗakin ta fara bi da kallo, kwance taganta akan gadon asibiti,mamaki ne ya kama ta, to ita me take yi a nan ba gidan Papi zasu ba, kodai mafarki ne, da alama ma mafarki ne 

Yinƙurin tashi tayi Juwaira tayi saurin riƙe ta tana faɗin 

"Sannu Adda, yi ahankali"

"Ina Abhie, a kaini naga Papi na d
DanAllah akaini inganshi, nasan duk wannan mafarki ne amma a ƙira mun shi ko a waya ne inji muryarsa tunda nasan baya gari, yace gobe ze dawo"

"Kiyi hakuri Adda addu'a zakiyi kinji, ki kwantar da hankalin ki dan Allah kiyi shiru"

"Juwaira ki kaini naga babana dan Allah me nake yi wai anan, ina Aliyu ina miji na, ina Abhie a kira mun shi, so nake inga Papi in tabbatar da mafarki nake kawai ba gaske bane, akaini naga baba na danAllah"

Anty Zuhura da shigowar ta kenan cikin ɗakin asibitin tace

"Kiyi hakuri Rukayya, yanzu zamu koma gida ai ki kwantar da hankalin ki, kiyi hakuri, kiyi shiru kafin wani abun ya ƙara samun ki, ki kwantar da hankalin ki dan Allah ki ɗauki ƙaddara a yanda yazo Miki kinji"

"Adda ina Aliyu ba tare muke ba, ko dayake na tuna wannan ai duk mafarki ne, amman dai ina yake, wai ba gidan Papi zamu je ba ya nagan ni anan, ohooo ashe fa mafarki nayi wai ance Papi ya rasu zamu je gidan shi nida Abhie amman duk da haka a ƙira mun shi inji muryarsa"

"Juwaira je ki kira mana doctor yazo yaji in zamu iya tafiya da ita"

Da to ta amsa ta, ta tashi ta fita dan kira doctor din

Suna zuwa daya ga yanda take ta faman kuka yace

"Hajiya kiyi hakuri ki daina kukan haka, ki kwantar da hankalin ki dan zai iya affecting babyn dake cikin ki tunda da kyar yayi surviving accident ɗin"

"Baby!! Wani baby Kuma aina, wani kalan accident" sai Kuma ta tuna 

Sanda suka fito daga gidan yanda take ta kuka tana kiran ya ƙara sauri, yana tuƙin yana juyowa side ɗinta Yana lallashin ta, sun zo shawo kwanar titin gidan papi kenan wani mai adaidata ya shawo ba horn, Sam daga me adaidaitan har Papi ba wanda ya kula da pole din wutan da ya kusa faɗuwa

A ƙoƙarin kauce mai ne lokacin da Abhie ya kula da pole din ya daki jikin wani bishiya dake gefen gangare glass din suka farfashe suka cake shi, pole din ma ya Zubo kan adaidaitan, har wasu ma na faɗuwa kan motar ta wajen side din shi, itama wani glass din ya same ta a cinya tun lokacin da pole din ya faɗo kan motar bata ƙara tuna me ya faru ba se yanzu da ta tashi ta ganta a gadon asibiti, wai daman ba mafarki bane, yanzu da gaske ta rasa Papi, to ina Abhie kenan?? Ina Aliyun ta??

Muneef ne sanda abun ya faru suna baƙin Kofar gida ya kasa shiga dayake gidan banisa daga titi a na iya hango bakin titin

Da sauri matasan gurin suka taso ciki harda shi saboda gani yake kamar yasan motar

'' Tun jiya ake maganar a saukar da pole wiren nan kafin yayi ta'asa tunda masu wutan sunƙi zuwa su gyara kar yayi barna amman baayi hakan ba gashi nan''

Wani matashi a cikin su yake maganar, suna ƙoƙarin ɗaga pole din daga kan motar, side din rukayya ya nufa ita da pole din baya kan gefen ta ya fito da ita, tsabar ruɗani da tashin hankali yasa har ta fara fitar da jini ta ƙasan ta,

Da kyar aka iya ciro Abhie saboda yanda kofar tashi ta hade da jikin bango ga bishiya taƙara tokare ƙofar 

sai da suka kaisu asibiti sannan ya kira su Anty Zuhura ya sanar da su

Bayan an gama dudduba su aka tabbatar Abhie ya rasu amman ita tana da rai saidai bata hayyacin ta ga kuma jini dake bin ƙafarta 

Sun ceto cikin wanda baifi 1 month ba da kyar, wanda mahaifinsa baisan dashi ba a duniya itama kuma haka

Tayi kusan 4 days a asibitin kafin ta farfaɗo dan doctor din yace da alamar lokacin da incident din ya faru tashi shock sosai

'' Anty Zuhura! ina Aliyu?, juwaira maisa ban gan shi ba ne anan??, shi wani ɗakin aka kai shi, muje in duba shi...''



______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺 
***