36
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad yahaya
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA
Page 3️⃣6️⃣
Bayan sun dawo gida ne Uncle Munir ya zaunar da ita ya fara mata nasiha sosai
"Kiyi hakuri Rukayya kiyi hakuri, nasan ke macece mai juriya da hakuri, kiyi tawakkali karkiyi tunanin dan kin rasa mijin ki da mahaifin ki lokaci ɗaya Allah baya sonki ne, ko baya ganin halin da kike ciki, duk son da kike musu ya fiki sonsu, lokacin da zasu zauna dake a duniya ne ya ƙare, ke ma wata rana haka lokacin da wasu zasu zauna dake zai ƙare, bazance ki daina kuka ba dan kuka rahama ne idan kika yi zai sauƙaƙa Miki zuciya, zai rage Miki wani miki, Allah ya amshe mijin ki amman ya bar miki ɗa ko ƴar da zaki ringa tunawa dashi, inda yaso zai iya haɗawa gaba ɗaya, ya ɗauke miki mijin da kuma a binda ke cikin naki amman se ya bar miki wanda zaki ringa kalla kina jin sanyi a ranki, ya dauke miki mahaifi amman ki na da ƴan uwanki, wanda suma kika gansu zaki tuna shi har ki mai addu'a, kina da wasu iyayen duk da ba'a maye gurbin uwa da uba amman muna tare daku a kowani lokaci, kiyi hakuri ki ƙara hakuri kinji Rukayya ba abinda zai faru a rayuwa batare da wani nufi na Allah ba, sai kiga wani wuyan ƙarshen shi yayi daɗi, kagama shan wahala amman sai kiga duk ya koma labari, ko a Yanzu ke kanki misali ce, danAllah kiyi hakuri kiyi tawakkali, karki sawa ran ki damuwa da yawan da zai cutar da lafiyar ki ko ɗan dake cikin ki"
Kuka take yi sosai so take ta yi juriyar da Abba Munir ke faɗa amman takasa, hannunta takai cikin ta tana tunanin da ace Abhie yana raye sai yafi Kowa farin ciki da haka
Ada itace me damuwa, shi ke kwantar mata da hankali yace da ita
"Indai muna da rabon ganin jinin mu Rukayya zamu gani, ki daina damuwa Allah na sane da mu bayinsa a koda yaushe"
Bayan rasuwar da Wata biyu ne su Juwaira suka dawo Kano da zama dan cema Baba tayi bazata iya zama a wani ƙasar ƴar uwarta na wani waje daban ba
Tunda yanzu ba wanda ta ke da yaƙinin zai kula mata da ita yanda ya dace
Da farko Baba so yayi Ammi ta dawo gurin su da zama amman ta ce bazata koma gidan ƙanwarta da zama ba itama tana da gidan mijinta
Yanda Amma ta tada mai hankali yasa shi dawowa Kano saboda akwai branch dinsu acan
Koda suka dawo juyin duniya Amma tayi ta dawo su zauna gida ɗaya amman taƙi lokacin Ammah na goyon Jalila da bata wuci 10 months ba
Itama lokacin Anty Muneefa nada Nabila ita kuma kusan 7 months
Ran Ammah ne ya ɓaci jin yanda Ammi taƙi yarda, ta kira Daddy ta faɗa mai shine ya nemi gida a Kano kusa da inda Ammah take ya siya
Shima dai da kyar ta koma Kanon dan da cewa tayi tafison ta zauna Kaduna gidan da mijinta yake
Saida suka nuna mata ɓacin ran su har Anty Zuhura suka haɗa ta da Abba Munir tukuna kafin ta amince ta koma
Ammah na zuwa dubata akai akai dan kusan kullum tana gidan, shi yasa Ahmad sukayi sabo da Ammi sosai dan duk weekend Yana gidan anan yake ma zuwa tahfeez, Ammah tana hakan ne saboda kar a ringa Barin ta ita kaɗai a wannan halin
A haka wani ziyara da su Daddy suka kawo ne bayan sun je Kano ya siya wani fili dake kusa da gidan Ammi ya haɗa da gidan da ya zama shine ya shiga tsakanin filin da gidan Ammin ya gyara gidan yace idan sun zo hutu sai su riƙa sauka a gidan
Da suka zo tafiya ne Umar ya sa kukan ba zai je ko ina ba, shi so yake ya zauna a wajen Ammi, kuma daman sun shaƙu da abokin sa Ahmad dan shine babban abokin shi tun kafin su bar Egypt
Itama Ammi rokon su tayi subar mata shi dan Umar yana da shiga rai
Mommy ce tace ta riƙe shi har sai ta gaji dan itama a lokacin tana fama da kanta tanada tsohon ciki kusan 6 to 7 months
Bayan ta haihu akasa ma jaririyar suna Anisa Wanda Umar ne ya zaɓa mata sunan
Saboda yanda tun sanda aka haife yarinyar yake sonta kullum tana ƙanƙame a hannun shi duk rashin son shi da yara, banda ita yanda yake hade rai kuwa idan za'a amshe ta se kayi mamaki, bacci ko cin abincin kawai ke rabashi da yarinyar, ko abincin zata ci yana zaune har tagama a dawo mai da ita
Shine da ake tambayar Ammi wani suna takeson a sa mata tace ya zaɓar mata suna
Kallon jaririyar yayi duk da ba fara bace amma black beauty ce, be taɓa Ganin black Jaririya ba, sai akanta ya saba da ganin yaran Larabawa farare, amma ita wannan baƙa ce, gata kuma kyakkyawa, yana son abu mai kyau kuma special, kuma tun lokacin yaji ta shiga ranshi
A hankali sanyayyar Muryar shi ta furta Anisa!! ya kalla Ammi yace
"Ammi a saka mata Anisa"
"Kasan meaning din sunan" Ammi ta faɗa tana kallon shi dan itama sunan ya mata
Kai ya jinjina mata alamar eh yace
"Yana nufin friendly and affectionate"
"Are you feeling so affectionate to her"
Anty ta tambaye shi tana ɗan dariya
"Ehmana Anty shiyasa naga ta dace da abunda nike ji akanta sunan yaje da ita"
Dariya sukayi duka Amma tace
"Anisa ba nickname bane"
"Aa suna ne me zaman kanshi buh mutane suna sakawa a nickname amman suna ne na gaskiya"
Faɗin Mommy wadda duk tare suke harda su Momma Zuhura, suma su Usman na zaune gefen shi ya hana su jaririyar ko su Antyn ma suna ɗauka ba jimawa zai je ya amshe ta kamar shi kaɗai aka haifa mawa
Ko da yaushe yarinyar na hannun shi, da mutum ya ɗauke ta ze koma kusa da kai ya zauna ya kafe ka da idanu har se ka gaji ka bashi idan kuma ya ga baka da niyyar bashi ita se ya kai hannu ya amshe ta, shima idan baka bashi ba yayi ta ƙunci kenan yana haɗe rai, ko kula shi akayi baze tanka mutum ba ranar, in ko tana hannun shi ai ko su Ahmad ɗin ma baya biye mawa suyi wasa, har ta fara wayo kodayaushe suna tare, duk rashin son yara na zuwa inda yake wai shi a lallai babba banda ita
Amman wani abun mamakin duk yanda yake sake mata ita kuma tsoron shi take, kuma hakan ya samo asali ne da tun sanda sukayi wani taro suka haɗu yaran suka je suna taɓa mai kayan shi, suka mai ɓar na sosai, gashi suka shigar mai ɗaki abinda ya tsana, sun mai kaca kaca da ko ina,
Kowannen su seda ya bi ya zane yasa su punishment ranan yaran ba karamin wahala suka ci ba gashi iya sune a part din ba me ceton su, amman da ita, jalila, fareedah da nabila suka gudu suka buya ƙasan gado shi
Da ya gansu kuwa yace sai sun koma kasan gadon kuma ba zasu ci koda abinci ba sai sanda yaga dama sannan zasu fito, yana ji ana neman su amma yayi biris seda suka kusan awa 3 a kasan gado sannan yace su fito, sun wahala sun gama kukan sauro, ga duhu ga zafi har ɗan baccin wahala sukayi,
Tun sannan ta fara tsoron shi dan sun wahala a ƙasan gadon nan ba kaɗan ba, kuma dalilin da yasa suka haɗe kansu su hudu kenan suna kiran kansu the P quadruplets, lokacin suka ba kansu suna, ita Anisa pixie, Jalila pickles, Nabila pebbles, se Fareedah pookie
Shiyasa da taji ance ga babban yayan ku zata nemi guri ta ɓoye daman gashi Allah ya mata shegen tsoro to balle da ya haɗu da yaci zalinta
Shi kuma gudun da take mai ba ƙaramin harziƙa shi yake ba, dan duk cikin ƙananan shi yana ji da ita amma take mai haka shiyasa shima yake share ta
Shekaru sun ja, Faruq ya samu soja ya fara daga rank din lieutenant yanzu currently Yana rank din Major General (MAJ GEN UMAR ADAM BAFFAYO), and Yana aiki a Companyn Daddy dake kaduna dan kafin ma ya samu aikin soja a Company ɗin yake aiki kuma har yanzu yana aiki a Company ɗin kawai dai dan yafi son aikin sojan ne ma yafi karkata hankalinsa a can
Usman ke kula da Company ɗin tunda she ke zaune a Kaduna kuma architecture shima ya karanta, sai dai ko idan Daddy yazo ya ke zuwa ɗan duba wa,
Shi kuma Ahmad medicine ya karanta, kuma yana ɗan taɓa business, yanzu ne ma da baba ya buɗe nashi a Kano yake kula dashi amman da shi duk wani business be dame shi ba akan aikin shi kawai yayi forcusing
Jama'a baku tambaye ni ya shaheeda, abida da Umma sahura suka ƙare ba,
Se mun haɗu a page na gaba idan naga comment
Follow and like my account on arewapen ba dan halin wannan marubuciyar ba dan Allah 🥹🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
______________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺
***