Nikaah marriage for rent 27
by @hanaady
NIKAAH
(Rental Marriage)
By
Rahama Aminu Bala
HANADY
HE HAD THE COURAGE TO REMARRY?WILL HE FIND THE COURAGE TO LOVE AGAIN?
Page 27
Ramadan ya daɗe tsaye a wajen library ɗin.
Idonsa na kallon ƙofar da Karime ta shiga.
Sai dai zuciyarsa tana wani irin yanayi da bai taɓa jin irinsa ba.
Jealous.
Cikin mota ya nufa ransa na kuna
Dafe steering motarsa yayi da ƙarfi har jijiyoyin hannunsa suka fito.
"Who is Yusuf?"
Tambayar ta sake dawowa cikin kansa.
Bai san dalilin da ya sa sunan saurayin yake masa yawo a rai ba.
Shi kansa bai san dalilin da ya sa ganin Karime tana murmushi ga wani ya sa kirjinsa ya ke masa ciwo ba.
Dogon numfashi yaja
"No..."
"This is wrong."
Ya tada mota a hankali.
Kai tsaye office ya nufa.
...
A office kuwa...
Sadiq yana duba wasu files ne lokacin da Ramadan ya banko ƙofa ya shigo.
Dago kai yayi yana kallonsa.
"Any problem?"
Ramadan bai zauna ba.
Kai tsaye ya tsaya a gabansa.
"Who is Yusuf?"
Sadiq ya ɗan ɗaga gira.
"Wanne Yusuf?"
"Wanda yake makarantar Karime."
Sadiq ya yi murmushi kaɗan.
"Ohh yauma kaje makarantar kenan."
Tamke fuska Ramadan yayi .
"I asked you a question."
Jingina da kujerar office Sadiq yayi cikin yanayin nishadi
"He's just a student."
"Just a student?"
"Yes."
"Then why was he talking to her?"
Sadiq ya ɗan yi dariya.
"Ramadan..."
"You're asking too many questions for someone who wanted to divorce his wife."
Kawar da kansa gefe yayi domin bashi da ansar maganar Sadiq .
Sadiq ya ci gaba.
"Ko kana tunanin duniya za ta tsaya saboda kai?"
"Karime tana da rayuwa."
"Tana da buri."
"Tana da mutane da za su yi magana da ita."
Ramadan ya dafe goshinsa.
"I don't like it."
Sadiq ya yi shiru na ɗan lokaci.
Sannan ya ce cikin nutsuwa,
"You don't like it because..."
"...you're in love with your wife."
Ramadan ya ɗago kai da sauri.
"No."
Sadiq ya yi murmushi.
"Kai ka san abin da kake ji."
"Amma daga yau..."
"Ka daina gudun gaskiya."
Ramadan bai sake cewa komai ba.
Ya juya ya fice.
Amma kalaman Sadiq sun ci gaba da yawo cikin kansa.
"...you're in love with your wife."
...
A bangaren Karime kuwa...
An kammala lectures
Dalibai sun fara fita ɗaya bayan ɗaya.
Karime tana tattara books ɗinta cikin nutsuwa.
Yusuf ya ƙaraso.
"Excuse me."
Ta ɗago.
"Yes?"
Ya yi murmushi cikin girmamawa.
"I noticed you're alone."
Karime ta ɗan yi murmushi.
"I'm okay."
"Actually..."
"Ina da wasu notes na course ɗinmu."
"If you don't mind, I can share them."
Karime ta girgiza kai.
"Thank you."
"But I already have mine."
Yusuf ya fahimci ba ta son tsawaita magana.And ta d'an fi bashi attention idan suna tareda Memi
Murmushi yayi had'i da cewa
"No problem."
"See you around."
"You too."
Ya juya ya tafi.
Karime ta kalli bayansa.
Ta fahimci Yusuf mutum ne mai tarbiyya.
Amma zuciyarta...
Ta rigada ta fad'a soyayyar wani.
Mutumin da bai damu da wanzuwar taba.
Sai dai har yanzu...
Ita ce take ƙaunarsa.
Ta yi murmushin takaici.
"Move on, Karime..."
Ta rada wa kanta.
"You have to."
...
Da yamma...
Karime tana hanyar dawowa gida.
Wayarta ta yi ringing.
Ta ciro daga bag d'in ta
Mijin Sa'ada Calling...
Ta tsaya cak.
Gabanta ya faɗi.
Numfashinta tsayawa yayi na wasu sec .
Ta kalli screen ɗin na wasu sakanni.
Zuciyarta tana bugawa da sauri.
"Don't answer."
Wani sashe na zuciyarta ya faɗa.
"But what if it's important?"
Wani sashe ya mayar.
Ta lumshe idanu.
A hankali...
Ta ɗaga.
"Assalamu alaikum."
Shiru.
Sai numfashinsa kawai take ji.
Bayan wasu sakanni...
Muryarsa ta fito.
"Karime..."
Muryar ta tayi sanyi
Daurewa tayi tace .
"Na'am."
"Kin isa gida?"
Ta yi mamaki.
Tambayar kenan?
"Ban kai ba."
Shiru ya sake ratsa tsakaninsu.
Ramadan ya dafe idanunsa.
A karo na farko a rayuwarsa...
Bai san yadda ake kula da zuciyar mace ba.
Ya san yadda ake yin business.
Ya san yadda ake yanke hukunci.
Amma bai san yadda ake cewa,
"I miss you."
Ba.
Kalmar ta gagare shi.
Sai kawai ya ce,
"Be careful."
Karime ta lumshe ido.
Hawayenta suka cika.
Ta yi tsammanin ta riga ta fara mantuwa da shi.
Amma jin muryarsa kaɗai...
Ya sake karya duk ginin ƙarfin halin da take ginawa.
Ta haɗiye kukanta.
"In sha Allah."
Katse wayar ta yi.
Rungume jakar ta tayi
Had'i da rufe baki da tafin hannu.
"Ya Allah..."
"Why is it so hard to stop loving him?"
A ɗaya ɓangaren kuwa...
Ramadan ya ci gaba da riƙe wayar a kunnensa duk da kiran ya katse.
A hankali ya furta,
"I miss you..."
Sai dai...
Ba ita ya faɗawa ba.
Shi kaɗai ne ya ji.
Kuma wannan ne karo na farko da Ramadan ya faɗi gaskiyar da zuciyarsa ta daɗe tana ɓoyewa.
"I miss my wife."
Karime ta daɗe tsaye a bakin hanya.
Wayar har yanzu tana hannunta.
Screen ɗin ya mutu, amma zuciyarta har yanzu tana jin sautin muryarsa.
"Be careful."
Kalma biyu kacal...
Amma sun sake tarwatsa duk ƙarfin halin da ta shafe kwanaki tana ginawa.
Ta lumshe idanu.
"No, Karime..."
"Don't do this to yourself."
Ta share hawayenta da bayan tafin hannunta.
A hankali ta ci gaba da tafiya zuwa gida.
...
A gida kuwa...
Mama tana zaune tana gyaran shinkafa.
"Kin dawo?"
"Eh Mama."
Mama ta lura da yadda idanunta suka yi ja.
"Kin yi kuka ne ?"
Karime ta yi saurin girgiza kai.
"A'a Mama, iska ne ya shiga idona.
Mama ta kalleta na ɗan lokaci.
Ta san ƙarya take yi.
Amma ba ta matsa mata ba.
"Wuce ki ci abinci."
Kai ta gyada.
Ta nufi d'akin Maimunatu.
Tana rufe ƙofa ta saka kuka.
Had'i da zamewa kasa.
Rungume gwiwowinta tayi.
Hawayen da take dannewa tun daga hanya suka fara zuba.
"Why?"
Ta furta cikin rauni.
"Why do you keep pulling me back..."
"...when you're the one who pushed me away?"
...
A wani ɓangaren kuwa...
Ramadan yana zaune shi kaɗai a balcony.
Dare ya fara ratsawa.
Iska mai sanyi tana bugun fuskarsa.
Coffee cup yana hannunsa.
Amma tun da aka kawo masa bai sha ba.
Idonsa na kallon sararin sama.
Tun lokacin da Karime ta katse wayar...
Zuciyarsa ta ƙara rikicewa.
Ya buɗe gallery ɗinsa.
Hotunan Sa'ada suka bayyana.
Ya daɗe yana kallonsu.
A da...
Waɗannan hotunan sukan ba shi nutsuwa.
Yanzu kuwa...
Ko kallonsu yake yi...
Fuskar Karime ke faɗowa cikin tunaninsa.
Yadda take murmushi.
Yadda take masa dariya.
Yadda take kiransa...
"Mijin Sa'ada..."
Ya rufe idanu cikin sauri.
"This is not happening..."
Ya furta.
Amma zuciyarsa ta riga ta ba shi amsa.
It is happening.
...
Washegari da safe...
Karime ta sake komawa makaranta.
Ta yi niyyar mayar da hankali kan karatunta.
"Education first."
Ta faɗa wa kanta.
Bayan lecture ta shiga library.
Ta zauna a wani lungu mai shiru.
Books buɗe a gabanta.
Amma ko layi ɗaya ba ta karanta ba.
Sai ji ta yi an ja kujera a gabanta.
Ta ɗago kai.
Yusuf ne.
Ya yi murmushi cikin ladabi.
"Sorry."
"All the other seats are occupied."
Karime ta kalli sauran kujerun.
Hakika babu ko ɗaya a buɗe.
"No problem."
Ya zauna.
Ba su yi magana ba.
Kowa ya maida hankali kan littafinsa.
Bayan kusan rabin awa...
Yusuf ya miƙa mata wata takarda.
Ta karɓa cikin mamaki.
A rubuce yake.
"You look sad these days."
Ta ɗaga kai ta kalle shi.
Ya yi saurin cewa cikin ƙaramar murya,
"I'm sorry if I'm crossing the line."
"I just thought maybe..."
"...you needed someone to remind you to smile."
Karime ta yi murmushi kaɗan.
Murmushi mai natsuwa.
"Thank you."
"I'm okay."
Yusuf ya fahimta.
Bai ƙara matsawa ba.
Sai ya ci gaba da karatunsa.
A zuciyarsa ya ce,
"Whoever broke her heart... must have been a fool."
...
A lokaci ɗaya...
Ramadan yana cikin meeting.
Managers suna ta gabatar da reports.
Amma shi...
Hankalinsa baya jikinsa.
Phone ɗinsa ya ɗauka.
Ya shiga WhatsApp.
Ya tsaya kan chat ɗin Karime.
Last seen.
Dogon shiru.
Ya fara typing.
How are you?
Ya tsaya.
Ya goge.
Ya sake rubutawa.
Have you eaten?
Ya sake gogewa.
Ya yi ajiyar zuciya.
Sannan ya ajiye wayar.
Sadiq wanda ke zaune a gefensa ya lura da komai.
Bayan meeting ta ƙare...
Ya bi Ramadan zuwa office.
"Har yanzu ba ka tura mata message d'in ba?"
Banza yayi dashi ..
"Me yake hana ka?"
Ramadan ya sauke numfashi.
"I'm afraid."
Sadiq ya yi mamaki.
"Ramadan..."
"Kai?"
Ya ɗan yi murmushi mai ciwo.
"Yes..."
"I'm afraid she'll ignore me."
Sadiq ya daɗe yana kallonsa.
Sai ya ce cikin nutsuwa,
"Ka san abin da ya fi ciwo?"
Ramadan ya ɗaga kai.
"Mutum ya ƙaunaci wani..."
"...ne bayan ya riga ya karya zuciyarsa."
Kalmar ta shiga zuciyar Ramadan kamar kibiyar da ba ta kuskure .
Ya lumshe idanu.
A karon farko...
Ya fara gane cewa...
Ba wai shi kaɗai yake shan azaba ba.
Karime ma...
Tan shan tata.
Kuma watakila...
Fiye da nasa.
Ya dafe ƙirjinsa a hankali.
Muryarsa ta fito cikin rauni.
"I've hurt her..."
Sadiq ya gyada kai.
"You did."
Shiru ya biyo baya.
Sai Sadiq ya ƙara da cewa,
"But if your love is real..."
"Don't just miss her..."
"Fight for her."
Ramadan ya ɗaga kai a hankali.
Kalaman Sadiq sun tsaya masa a zuciya.
A karo na farko...
Ba wai yana son Karime ta dawo ba.
A'a.
Yana son shi ne ya je ya nemo ta.
Da dare...
Karime tana zaune saman katifa.
Books buɗe a gabanta.
Assignment take son yi.
Amma duk lokacin da ta karanta layi ɗaya...
Sai ta sake tunawa da muryarsa.
"Be careful..."
Ta rufe littafin da ƙarfi.
"No..."
"I can't keep doing this."
Ta miƙe tsaye.
Ta nufi window.
Iskar dare tana bugun fuskarta.
Ta ɗaga kai sama.
Taurari sun cika sararin sama.
A hankali ta rada,
"Ya Allah... Ka bani ikon mantawa."
"Because every time I think I'm getting better..."
"He comes back into my mind."
Sai hawaye ya zubo ba tare da ta shirya ba.
...
A wani ɓangaren kuwa...
Ramadan bai koma gida ba.
Har ƙarfe goma na dare yana office.
Sadiq ya fito daga office ɗinsa ya tarar da shi yana zaune shi kaɗai.
Laptop a buɗe.
Amma ba aiki yake ba.
"Har yanzu baka tafi ba?"
Ramadan ya girgiza kai.
"I don't feel like going home."
Sadiq ya zauna a gabansa.
"Because she's not there?"
Ramadan bai musa ba.
Bai kuma amsa ba.
Sai dai shiru da ya yi...
Shi ne amsar.
Sadiq ya yi murmushi kaɗan.
"You know..."
"Gida ba bangaye bane."
"Gida mutum ne."
Ramadan ya ɗaga kai.
Sadiq ya ci gaba.
"Da Karime tana nan..."
"Ko ba ta yi magana ba..."
"Ka kan ji gidan yana da rai."
Ramadan ya haɗiye wani abu da ya tsaya masa a maƙoshi.
Ya tuna...
Kowace safiya idan zai fita...
Karime za ta fito da gudu.
"Mijin Sa'ada..."
"Breakfast first."
Ko da ya ce baya so...
Sai ta matsa.
Ko da ya yi mata tsawa...
Sai ta yi dariya.
Yanzu...
Table ɗin dining babu kowa.
Kitchen babu ƙamshin girki.
House ɗin ya yi shiru.
Ya sauke numfashi.
"I miss home..."
Ya furta a hankali.
Sadiq ya kalle shi.
"No..."
"You miss your wife."
...
Washegari...
Karime ta gama lecture.
Tana fitowa daga Faculty...
Rumaisa ta hanga tsaye bakin mota.
Fuskarta ɗauke da murmushi.
"Anty!"
Karime ta yi saurin zuwa ta rungume ta.
"Na yi missing ɗinku."
Rumaisa tayi murmushi sosai take jin Karima kaman kanwar ta domin Karime akwai dad'in zama had'i da biyayya idan zama ya had'a ku
"Na zone domin muje shan mu ice cream."
Dariya Karime ta saka a karon farko cikin kwanaki nan.
"Really?"
"Yes."
"You need fresh air and a little fun
Mota suka shige.....
...
Bayan mintuna kaɗan...
Suna zaune a wani quiet café mai suna Ice Hup
Hjy Karime ice cream d'in take ci hankali kwance.
Rumaisa tana kallonta.
"Kin rame."
Karime ta yi murmushi.
"I'm okay."
Rumaisa ta girgiza kai.
"No..."
"You're surviving."
"Not living."
Karime ta yi shiru.
Rumaisa ta kama hannunta.
"Tell me the truth."
"Do you still love him?"
Idanun Karime suka cika da hawaye.
Ta yi ƙoƙarin murmushi.
"But love alone isn't enough, Anty."
Rumaisa ta yi shiru.
Karime ta ci gaba.
"I've decided..."
"If Allah didn't write him for me..."
"I won't force destiny."
"I'll pray for him..."
"...from afar."
Sosai Rumaisa taji tausayin Karime.
Ta san kalaman nan nata daga zuciyar ta suke kuma iya gaskiyar ta take fad'i.
...
A wannan lokacin...
Ramadan yana parking motarsa a wajen café ɗin domin ya haɗu da wani client.
Tafiya yake yana ansa waya
Idanunsa ne suka sauka kan wani familiar hijab.
Tsayawa yayi cak.
Karime ce.
Tana dariya tare da Rumaisa.
Wata irin nutsuwa ta bayyana a fuskarta.
Ba irin dariyar da take yi masa ba.
Amma dai tana dariya.
Ramadan ya kasa ɗauke idonsa daga kanta.
A hankali murmushi ya bayyana a fuskarsa.
"She's smiling..."
Ya ji wani irin daɗi.
Sai dai...
A daidai lokacin...
Yusuf ya shigo café ɗin.
Ya hango Karime.
Ya ƙaraso cikin girmamawa.
"Assalamu alaikum."
Karime ta amsa cikin girmamawa.
Rumaisa ta ɗaga kai tana kallonsa.
Yusuf ya ce,
"I forgot to give you the textbook I promised."
Ya miƙa mata text book d'in.
"Thank you."
Karime ta fad'a tana mai karɓa.
Ba su wuce minti biyu suna magana ba.
Ya yi mata sallama ya tafi.
Amma...
Abin da Ramadan ya gani kenan.
Ya ga murmushin ta.
Ya ga suna magana.
Bai ji abin da suka faɗa ba.
Sosai zuciyarsa ta shiga bugawa da ƙarfi.
Wani irin kishi ya sake mamaye shi.
Ba tare da ya sani ba...
Ƙafafunsa suka fara tafiya zuwa ƙofar café ɗin.
Rumaisa ce ta fara hango shi.
Idanunta suka buɗe.
"Ramadan?"
Bin inda Rumaisa ke kallo Karima tayi
Idanunta suka haɗu da nasa.
Lokaci ya tsaya.
Ba wanda ya motsa.
Ba wanda ya yi magana.
Sai iska mai sanyi da ta ratsa tsakaninsu.
Ramadan ya kalli idanunta.
Ita kuma ta kalli nasa.
Wannan shi ne karo na farko da suka sake haɗuwa ido da ido...
Tun bayan barinta ta gidan aurensa.
Hmm