BABI NA TAKWAS
by @zainabb
Zaren Rayuwar Mu
TUN LOKACIN da muka fara soyayya da Temi nake cikin farin ciki marar misaltawa. Tana faɗa min abubuwa da dama game da harkar Law wanda ni ban sani ba tunda tana final year nata ni kuma ina aji uku. Tana bani labarin wasu ƙasashe da ta tafi; yadda take son al'adu da dabi'u mabanbanta na ƙasar North America. Tana kallo na a cikin idanu take faɗa min zanyi mamaki idan tace Turkiye na ɗaya daga cikin ƙasashen da ta fi so akan yadda suke tafiyar da al'amuran rayuwar su. She told me they have a very rich culture that's so outstanding. She told me that she loves their tea and their coffee. Tace ƙamshin su na nishaɗantar da rayuwar ta. Ta faɗa min yadda take kusanci da mahaifin ta akan mahaifiyyar ta kuma yadda take son mahaifin ta akan mahaifiyyar ta. Ta faɗa min mahaifin ta yana da wasu yara daga first wife nashi kafin su rabu ya aure mahaifiyyar ta kuma ta kan ce yadda take son step siblings nata idan nagan su tare ba zan ce ba mahaifiyyar su ɗaya ba.
Ta kan gayyaceni a apartment nata dake wajen makaranta ita ba hostel take zama ba. Ɗaki ne ɗaya nata me duk wani abu da take buƙata na rayuwa har ƙaramin fridge tana da. Gadon ta medium sized da lush carpet me laushi sosai idan ka ɗaura kafar ka akai. Tana da ƙaramin plasma TV ƙarami sosai an ɗaura a bango. Bana son tana cewa zata dafa min abinci duk naje inda take shiyasa bana son zuwa amma kuma idan na tafi zata dafa min abinci bana zama tashi nake yi nace muyi tare. Zata tambaye ni “You know how to cook Baffa?” Kaina nake gyaɗawa nace “Yes of course. I'm a barracks boy” Dariya take yi tace “Your mom let you cook? That's impressive. I love it” “I and Ahmad cook whenever we're home. We help her.” Murmushi take yi wanda baya barin fuskar ta har mu gama girkin.
Temi ta waye fa, ta waye sosai duk wani abu da take so ko riƙa min hannu ne se ta fara tambaya na. “Can i hold your hand?” Kallon ta nake da murmushi na gyaɗa kaina. Bata taɓa ɗaura min jikin ta ba ba tare da izini ba. We have never kissed each other. Sometimes I see her wanting to do it but she'll just brush it off and I never go for it first.
Tafiya muke tare da ita zan raka ta zuwa apartment nata. Hannun ta na cikin nawa muna tafiya tana bani labari. “I wanted Science class initially. But see me here, a finalist in Bachelor of laws”
“A doctor?”
“Yes, a doctor. What else if not a doctor? Here in our society, some people believe it's medicine or nothing”
Dariya nayi saboda gaskiya take faɗa “It is true to some extent. And lecturing too. People get respected for it”
“I believe you. I'd want to leave Nigeria when I'm done”
“You'll leave me?”
Dariya tayi sosai tace “Jokes apart”
“It is easier for you. If I ever dream of going somewhere, then I'm taking my mom with me”
Tsayawa tayi tana kallona da murmushi akan fuskar ta. Na gyaɗa mata kaina.
“I love how you look out for your family, especially your mom. What about Dad?”
“It is mom before anyone else”
“I think it's a study. Boys love their moms more and girls loves their Dads more”
“That's really how it is for me. I have seen her trying for us. She deserves better”
“I hope you'll give her the life she deserves”
“Yes, one day” na faɗa muka cigaba da tafiya.
Shiru muka yi bamu ƙara cewa komai ba har muka kusa karasowa apartment nata. Tsayawa tayi tana kallona tare da cire hannun ta a cikin nawa. “Look, go back to your hostel it's getting dark or will you spend the night here with me?”
Ahankali na girgiza mata kaina.
“So you quickly go back. Thank you for having me”
Hannuwan ta biyu na riƙe ina kallon cikin idanun ta as I move closer to her. Hannuwana na fara cirewa a nata na kai a gefen fuskar ta and I move my face very close to hers and she helps by coming close to my own face too and we got into a kiss so intense and passionate.