BABI NA GOMA
by @zainabb
Zaren Rayuwar Mu
CASE NA FARKO da na fara handling a matsayin Barrister dake aiki a Ministry of Justice dake nan Abuja shine na yarinyar da kishiyar mahaifiyar ta take mata azaba mafi munin da zaka yi tunani. Zuciya ta naji tana tafarfasa akan irin ciwon dake bayan yarinyar.
Ƙaramar yarinya ce wacce zata yi shekaru goma a duniya. Mahaifiyarta ta rasu shi kuma mahaifin ta baya so a raba mishi kan ƴaƴan shi shiyasa da ƙanwar mahaifiyyar tace tana so a bata ita ya hana. Matar da ya auro a matsayin wacce ya damƙawa amanar yarinyar ce tayi mata azaba a bayan ta. Wurin yayi muni sosai ansa wuƙa a cikin wuta tukuna aka dasa mata a bayan ta saboda ta zubar da ruwa a cikin bokiti, ruwan da suka rage a dafa abinci dashi.
“Dan Allah ku duba muna. Ku kwatowa yarinyar nan ƴancin ta marainiya ce bata da uwar da ta haife ta” ƙanwar mahaifiyyar ta ta faɗa tana kuka. “Wata biyu kawai nayi ban taho na duba ta ba saboda bani da kuɗin mota daga Dutse zuwa nan Habuja. Shine koda na taho matar ubanta tayi mata wannan azabar kuma mahaifin ta shima baya nan yana Legas wurin nema”
Wani irin abu nake jin ina haɗiyewa wanda ban san meye ba saboda ɗacin da nake ji. “Kun tafi asibiti?” na tambaya ina kallon bayan yarinyar
“A'a bamu tafi ba. Hali se de hamdala amma bamu da kuɗin zuwa asibiti”
Hannah, colleague ɗina tace “Wannan wace irin mata ce yake aure? To wallahi duk uban da ya tsaya mata se anyi hukunci tsakanin ta da wannan yarinyar”
“Baaba, kuyi haƙuri ki dena kuka. Zan sa a kaita asibiti. Duk abinda ya dace shi zamu yi”
“Nagode Allah ya saka muku da alheri. Mun gode sosai”
Makullin mota ta na jawo daga desk ɗina muka fita tare dasu. A police station muka fara zuwa na ɗauko ɗan sanda tukuna muka wuce asibiti. A chan da sauri aka amsa yarinyar. Likita da nurses da suka taimaka aka gyara wurin da taji ciwo suna ta mamakin abinda wata mata zata iya yiwa ƙananun yara saboda kawai wani ra'ayi nasu wanda hankali ba ze ɗauka ba.
“Try your best and make sure that woman is put behind bars” likitan ya faɗa bayan sun gama. Nodding kaina na mishi na musu godiya muka fito. A restaurant na fara biya wa na siyowa yarinyar abinci kuka kawai take akan zafin da take ji.
“Yaya sunan ta Baaba?”
“Sunan ta Nana Asma'u”
“Kiyi shiru kinji Nana Asma'u. Cikin kwana biyu zaki ga wurin ya dena ciwo. Kukan ya isa” na faɗa mata tare da sa kanta a jikina.
Kuka ta cigaba da yi nima nasan ba zata iya denawa ba. Ƙaramar yarinya ce bata san inda kanta ke mata ciwo ba. Ta de san an ji mata irin wannan ciwon kuma ba zata iya yarda akan ta zubar da ruwan dafa abinci ne akayi mata irin wannan azaba ba.
Documenting komai nayi a cikin desktop ɗina ina tunanin irin yaran nan da ake yiwa irin wannan azabar. Wanda aka kawo mana domin hukunci su muka sani bamu san wanda ba'a kawo ba duk da they all exist.
Babu wani abu da yake ƙona min rai sama da zalunci. I detest it with everything in me. Ko a cikin dangi na ne ake zalunci, ni zan tashi tsaye akan shi. Koda mahaifiya ta ce ko mahaifina Allah yasa suka sa kansu a cikin zalunci, ba zan taɓa jin tsoron yi musu magana akai ba kuma ba zan ji tsoron tsayawa against them in the court of law.