MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 75

by @maimunabala209

*MATAR GIDA BOOK* 2


*SHUUKRAN* /022


YOTA ASSOCIATION



P75


bayan sati biyu da faruwar haka Unaisa ta sake kiran Ammi, dalilinta na kiran Ammi shine Amirah ta faɗa mata duk sati take kiran Ammi wannan dalilin yasa Unaisa sake kiran Ammi bayan sati biyu,bugu ɗaya Ammi ta amsa kiran cike da girmamawa Unaisa ta ce ''barka da safiya Ammi'' ga mamakin ta Ammi ta amsa gaisuwar sai ta cigaba da hira a gefe tare da ƙawarta Unaisa na jin hirar da Ammi ke yi wanda hirar bikin Nailah ne,jikin Unaisa ya yi sanyi amma sai ta daure ta ce ''hello Ammi..hello Ammi'' Ammi bata amsa ba sai hirar ta take wata doguwar ajiyar zuciya Unaisa ta sauke kafin daga bisani ta kashe wayarta zuciyarta cike da ƙunci,bayan wasu ƴan mintina ta sake kiran layin Ammi,bayan Ammi ta amsa kiran kai tsaye ta ce ''yi hakuri Unaisa ina tare da baƙi ne''daga haka ta aji waya ba tare da ta kashe wayar ba,Unaisa ta yi shiru bata ce komai can ta kashe wayarta ko kaɗan bata ji dadin abinda Ammi ta yi mata ba ina laifin ko gaisuwa ne su yi,zuciyarta babu ɗaɗi ta dauki mayafi daga haka ta shiga ɓangaren Amirah,bayan shigarta ta tarar Amirah da Aina'u kitchen suna aikin abinci,gidan ya yi shiru su Sudais sun tafi makaranta,sallama dauke a bakinta ta shigo ɓangaren Amirah ta amsa mata sallama daga can kitchen bayan Unaisa ta zauna ne Amirah ta shigo parlour suka ƙara gaisa,wayar Amirah dake daure saman center table ta yi ƙara alamar shigar kira daukar wayar Amirah ta yi ganin Ammi ke kira yasa ta faɗaɗa murmushi ta kalle Unaisa kafin ta ce ''Ammi ce ki kira'' ta faɗa fuskarta dauke da murmushi kafin ta amsa kiran ita dai Unaisa bata ce komai ba kawai ta gyaɗa kai,Amirah ta ɗauki sama da mintina goma tana waya Ammi da yawa daga hirar hira kan bikin Nailah ne yanda Ammi ta cewa Amirah ta sama masu mai lallai da kitso Amirah ta ce babu damuwa,bayan sun gama waya ne Amirah ta kira Rumaisa ta ce ta sama mata mai lallai da kitso da zata masu lallai da kitso kafin bikin Nailah,haka unin wannan ranar Unaisa ta yi shi jiki mace,kwanaki sun ja lokaci ya tafi kwana a tashi asarar mai rai cikin wannan satin za a yi bikin Nailah da angonta Vahid ɗan kasan Maroco,a can Kano gidan Dady za a yi bikin Nailah,ranar Lahadi kawu Abubakar da matarsa Anty Nazaaha tare da  tawagar ango da amarya suka diro Nigeria,ɓangaren dangi Dady kowa tun ranar asabar wasu daga ƴan uwa da abokan arziki na birni da ƙyauye suke gidan Dady babu laifin gidan Dady yana da girma sosai,kawo Abubakar ya so a yi bikin a sabuwar gidansa da ya siya a unguwar giɗaɗo road sai dai ba a gama aikin gidan ba wannan dalilin yasa za a bikin gidan Dady,a ranar Alhamis da dare Ɗalha da iyalansa suka diro garin Kano gida ya cika da ƴan biki a gajiye suka sauko garin musamman Unaisa da yanzu cikinta ya shiga wata bakwai ko kaɗan bata so zuwa bikin ba harda cikin bai wani fito sosai ba dan in ba faɗa ta yi ba za a dauka cikin baifi wata uku ba,ko kaɗan bai nuna alamar girma ba sai ɗan tauri tauri da ya yi,ita kaɗai ta san halin da ciki kusan kullum da ciwon ƙafa da ƙugu take kwana da uni,bayan saukowarsu kowacce ta yi ɓangarenta dan Ammi bata bari an buɗe ɓangarorin su ba,a wannan dare. Unaisa bata iya cin komai ba daga abincin da Ammi ta aiko masu,karshe fruit ta sha shima dan zata sha magani ne,Allah ya taimake su Ammi ta sa an gyara masu bangaren hakan yasa bayan saukowarsu ba su yi wahalar shara ba ko ina tsaf,washe gari tun asuba da Amirah ta farka bata koma bacci ba,da yaranta ta fara ta yi masu wanka ta shirya su kafin ta fito tsakar gida ta hau aiki tare dangin Ɗalha suna aiki suna wasa da dariya kusan duk wata shawara da ita Ammi ke yi kasancewar Uwar amarya da tawagarta suba gefe guda an ware masu komai nasu ko abinci su ke dafawa kansu,auren kawu Abubakar da Anty Nazaaha kusan shekaru talatin amma har yanzu Anty Nazaaha taƙi sakin jiki da dangin mijinta hasalima ba su cika burgi ta ba Ammi ta yi iya yinta dan ganin sun saba amma fir Anty Nazaaha ta nuna bata son alakar dan dole Ammi ta hakura,Ammi na tare da yan uwan Dady na birni da ƙyauye yayin da Anty Nazaaha na tare da ƴan uwanta ƴan kasan Maroco a ɓangaren ɗaya,misalin ƙarfe goma aka gama dafa abin kari wanda Amirah ce ta jagoranci aiki baki ɗaya,Unaisa na can ɓangarenta kwance ciwon ƙugu ya sata gaba tun karfe uku da ta tashi sallar nafilah ta ƙasa komawa bacci dalilin ciwon ƙugu,da kyar ta samu ta yi sallar asuba,duk wani man zafi da ta saba amfani da shi ta shafa amma duk a banza ta so fita ta yi aikin safe saboda tana jin sanda Amirah ta fito amma ko tashi baza iya ba a wannan lokacin,haka ta kasance sai misalin ƙarfe tara da wasu mintina bacci ya dauke ta,ganin bata fito ba Amirah ta samu flask ta zuba abinci ta bawa wata couise ɗin Ɗalha mai suna Na'ima ta ce ta kaiwa Unaisa ɓangarenta nan sauran ƴan uwa suka hau magana ita mai ya hanata fita ta yi aiki tare da sauran mutane da za a dafa abinci a aiki mata wasu ganin suke girman kai ce wata couise ɗin Ɗalha daga gefen Dady ta taɓe baki ta ce ''mai ku ke tunani shuwa ce fa kuma kun san su da shegen girman kai ga mugun son jiki ƙilah tana can manne da miji Maman Sudais na nan tana cin aiki'' haka dai suka yi ta aibata Unaisa,duk wannan surutan da suke Amirah bata sani ba tana can wajen Ammi,wasu ƙawayen Ammi sun zo shine Ammi ta kirata su gaisa bayan sun gama gaisawa ne ta dawo inda ake aikin ta tarar ƴan uwan Ɗalha na zagin Unaisa bil hakki gani suke girman kai da son jiki da kuma mugun ƙazanta da ake bada labari kan shuwa su suka haka Unaisa fita ta taya su aiki,Amirah ta riƙe baki tana mamakin yadda suka haƙiƙance kan abinda basu da masaniya a kai wata Unaisa ce ta maƙalewa miji wani mijin? saurin dakatar da su ta yi ta hanyar faɗin ''dan Allah ya isa haka yarinyar nan ciki gareta baku san ya ta kwana ya ta tashi ba kawai kun zauna kuna ta zaginta,a ɓangare na abban Sudais yake tun jiya dan Allah ku yi mata uzuri'' Hajara ta buɗe baki ta ce ''lallai Maman Sudais kishiya ki ke kare amma kuwa da sauran ki,kishiyar ma shuwa kin kowa san su da asiri?" dafe kai Amirah ta yi gaba ɗaya ta gaji da zantukan su har ta buɗe baki zata yi magana sai kuma ta ga rashin amfanin maganar kawai ta kama aiki dake gabanta da suka ga ta yi masu banza sai suka bar zagin Unaisa











A can wajen Unaisa ba ita ta farka ba sai karfe sha ɗaya da wasu mintina zuwa yanzu ta samu sauƙin ciwon ƙugun harda bai daina gaba ɗaya ba amma da sauki sosai, wanka ta fara yi ta yi brush ta shirya kanta cikin wata ɓakar egyptain abaya mai matsakaici ado,abayar ta ƙara fitar da hasken ta sosai ta yi ƙara kyau da haske ita dai kyau ciki ya sa ta saɓanin wasu mata da suke muni in suna da ciki,bata shafa komai fuskarta ba ta gyara sumarta ta naɗe ta daura da reborn ta fita ras da ita kamar balarabiya,bayan ta gama shirya kanta ta gyara gado da ta kwanta kai kafin ta fita daga ɓangarenta gaba ɗaya gidan cike yake da jama'a ƴan biki,tun fitowarta mutane ke binta da ido dake da yawa basu waye ta ba sai binta kawai suke da ido har wa inda suka waye ta ma duk basu iya shedata ba saboda yadda ciki ya canza ta gaba ɗaya,a natse take tafiya in ta zo wucewa ta inda mutane suke sai ta yi masu sallama kafin ta ce ''ina kwanan ku'' duk sai su amsa mata da lafiya harda da rawar baki suna ƙara binta da ido,ba ƙaramin canzawa Unaisa ta yi ba dalilin cikin jikinta in ba wanda ya santa da can bane ba lallai ya gane ta ba wanann dalilin yasa da yawa daga dangin Ɗalha basu shidata ba,can ta hango Amirah tana baɗa umurnin abinda za a daura da kuma wanda za a kaiwa abinci,wani irin nitsuwa ne ya ziyarci Unaisa nan take ta ƙara sauri kaɗan gaba ɗaya ta tsargo da irin kallon da Ɗangin Ɗalha ke mata tana daf da zuwa wajen Amirah idonsu ya haɗu nan take Amirah ta sakar mata murmushi ita ma ta mayar mata da murmushi Unaisa na kallon Amirah kawai ta ga Husnah ta tsaya gefen Amirah ta kai bakinta kunnen Amirah tana yiwa Amirah magana da wani irin sauri Amirah da Husnah suka bar wajen kai tsaye suka wuce babban site din gidan inda Ammi da sauran jama'a suke lokaci guda annurin fuskar Unaisa ya dauke amma haka ta daure ta rasta cikin jama'a ta shiga ɓangaren,bayan shigarta kai tsaye ta wuce ɗakin Ammi ta tarar Ammi bata ɗakin sai wasu dattawan mata su biyu zaune cikin ɗakin ɗaya daga ciki tana shafa mai da alama daga wanka ta fito ɗaya kuma tana cin abinci,har ƙasa Unaaisa ta durkusa ta gaishe su suka amsa mata duk suka mata kallon rashin sani,parlourn Ammi cike da jama'a wanda da yawa Hajiyuyi ne dattawan gaske masu class ba irin su Hajiya Bilƙisu ba,duk Unaisa ta gaishi su wasu suka amsa wasu kuwa ko kallo bata ishi su ba,ɗaya parlour ta shiga inda ta tarar da family Dady cike ciki parlourn sai hayaniya da surutai ke tashi parlour ga kukan yara,nan ma dai ta gaida su tana ratsa cikin su,ɗakuna uku dake wannan parlourn Unaisa ta duba bata ga Ammi ba haka Amirah,kusan ko ina sai da ta duba amma bata gansu ba ɓangaren Dady da wani ɓangaren da tun zuwanta Kano sanda take amarya take ganin ɓangaren a kulle su kaɗai ne bata duba ba,har ta juya da niyya komawa ɓangarenta sai kuma ta ce bara ta duba ɗaya ɓangaren wata ƙila su Amirah suna can bayan shigarta parlour mai dauke da ɗakuna uku tun daga parlour wani irin ƙhamshi da bata taɓa jin irinsa ba ya dake hancinta har ta kai tsakiyar parlourn ta je muryar mutanen suna magana amma da wata yare kamar Larabci sai dai ba Larabci ba ce ɗakin farko ta buɗe ta ga Nailah da wasu ƴan mata zaune Nailah na riƙe da waya tana vidoe call tana magana da yarensu sallama dauke bakin Unaisa ta shigo ɗakin duk suka mayar da dubansu gareta sarai Nailah ta gane Unaisa dan Husnah ta taɓa tura mata hotun Unaisa kafin bikinsu da Ɗalha haka ma sanda Unaisa take asibiti Amirah ta bata waya sun yi vidoe call saboda haka sosai ta gane Unaisa amma sai ta yi mata banza ta cigaba da wayar da take,ɗaya daga cikin ƙawayen Nailah ta faɗaɗa murmushi tare da yiwa Unaisa magana da harshen turanci ta ce ''please  take a set'' ta faɗa tana tura wata kujerar roba resting chair gaban Unaisa sauran ƙawayen amarya kuwa hirar su suke hankali kwance ko kallo Unaisa bata ishe su ba ganin haka yasa Unaisa saurin faɗa ''no tnxs l will take my leave Ammi nake nima'' ga mamakinta sai ta ji wacce ta bata kujerar ta ce ''ok suna ɓangaren Dady'' Unaisa ta faɗaɗa murmushi ta ce ''ok nagode sosai'' daga haka ta fita daga ɗakin cikin sauri harda harɗe kafa Nailah ta bi bayan Unaisa da harara,bayan fitar Unaisa ta ji Nailah ta magana cikin harshen turanci ta ce ''shegiyar yarinya marar kunya kawai'' ɗaya daga cikin ƙawayenta ta ce ''wacce?" cikin ɗan ɗaga murya Nailah ta ce ''kishiyar Maman Sudais ce shegiya a kanta Yaya Ɗalha ya saki Maman Sudais,kafin ya aurota babu kalar wulaƙanci da yaya Ɗalha bai yiwa Maman Sudais ba,ko kaɗan bani son yarinyar shegiya buzuwa ko shuwa ce oho'' ɗaya daga cikin ƙawayen Nailah ta ce ''kar ki ga laifin sa ba a taɓa raba ƙabilar shuwa da sihiri ta iya yiwuwa duk abinda ya yi ba a cikin hayyacin sa ya yi ba'' duk cikin harshen turanci suke magana wanda haka ya bawa Unaisa damar fahimtar abinda suke faɗi,haka dai Nailha da ƙwayenta suka yi ta zagin Unaisa,jiki babu kwari Unaisa ta fita daga ɓangaren,zuciyarta cunkushe da baƙin ciki sai yanzu ta fahimci dalilin ƙarar tsana da dangin Ɗalha suka daura mata,kenan su gane suke ita ta sa Ɗalha ya sake Amirah sakin da bata goye baya ba ''innalillahi wa innalillahi raji'un'' ita ce kalmar da ta rinƙa maimaita a hankali har ta kai ɓangaren Dady tun daga kofa ta fara jiyu muryar Ammi da Husnah daga wata ɗaki dake parlourn Dady  magana suke kan abubuwan da za a raba wajen kamu, hannu ta kai handle ɗin kofar ɗakin zata buɗe Husnah ta buɗe kofar ta fito hannuta riƙe da wani baban kwali,wani mugun kallo ta watsa wa Unaisa kafin ta matsa gefe cikin sanyi jiki Unaisa ta buɗe baki a hankali ta ce ''barka da safiya'' taɓe baki Husnah ta yi kafin ta ce ''yauwa barkan ki dai''daga haka ta yi wucewarta ta bar Unaisa tsaye kofar ɗaki kamar wacce aka dasa wajen kanta ƙasa zuciyarta na mata zafi ta ji ina ma bata zo bikin ba nan da nan idanunta suka ciciko da ƙwallah,daga cikin ɗaki Unaisa ta jiyu muryar Amirah Amirah ta ce ''shigo mana'' a hankali ta ɗago tare da mayar da dubanta ga Amirah dake zaune saman wata kujera daga gefenta kuma Ammi ce tsaye cike da juriya ta hana hawaye dake shirin zubo mata ta saki murmushin yaƙi daga haka ta shigo ɗakin,Amirah ce ta amsa mata sallamar Ammi na tsaye tana ƙare mata kallo cike da girmama ta gaida Ammi,Ammi ta amsa fuska babu yabo babu fallasa daga haka ta mayar da dubanta ga Amirah ta ce ''ki hanzarta yanzu sai kiga an kira sallar azahar'' Amirah ta ce ''insha Allah Ammi'' ta faɗa tana zuba turaren wuta cikin wasu robobi inda take haɗa kowanne robar turare da kasko da lallai ja da baƙi bayan fitar Ammi Amirah ta ɗago ta kalle Unaisa fuskarta dauke da murmushi ta ce ''Amarya zo ki tayani na samu na gama da wuri'' cikin sanyi jiki Unaisa ta ja kafarta zuwa inda Amirah ke zaune ta zauna Amirah ta tura babban robar turaren wuta gaba Unaisa tare da robobi ta ce ''bismillah'' ta faɗa tana dariya ita ma Unaisa dariyar ta yi daga haka ta kai hannu cikin robar ta fara zuba turaren kamar yadda ta ga Amirah ke yi,har karfe sha biyu da wasu mintina na rana Unaisa da Amirah na ɗakin basu gama zuba turaren ba suna ɗan taɓa hira sama sama,zuwa wannan lokacin jiri ya fara ɗibar Unaisa dalilin rashin cin abinci da bata ci ba,abincin da Amirah ta baiwa Na'ima ta kai mata bata kai mata ba,wani ɗaki ta kai abinci ta ɓoye da gangan, Unaisa ta ɗago lumsansansun idanunta ta zubawa Amirah dake faman bata labari da ƙyar ta iya furta ''Maman Sudais'' jin yadda ta kira sunan ta yasa Amirah kallon fuskarta da sauri tana faɗin ''na'am'' ganin yadda idanun Unaisa sun sauko sun yi ja jawur kamar barkono yasa Amirah ajiye robar turaren da take riƙe da tashi yunƙurawa ta yi tare da miƙewa tsaye ta nufi inda Unaisa ke zaune ta kai hannu ta dafe kafaɗunta cikin kwantar da murya ta ce ''lafiya ki ke kuwa me ke damun ki?" da kyar Unaisa ta iya furta ''yunwa..yunwa tun safe ban ci abinci ba'' cike da mamaki Amirah ta zaro idanu waje ta ce ''subhanallah yunwa kuma ba ki ci abincin da Na'imah ta kai maki ba ne?"  shiru kawai Unaisa ta yi bata iya cewa komai ba sai kwanciya ta yi saman gado da take zaune,ganin haka Amirah bata tsaya ɓata lokaci ba ta fito daga ɗakin cikin saurin ta nufi ɓangaren Ammi bayan shigar ta ta wuce kitchen inda ta haɗawa Unaisa tea hannunta riƙe da kofi ta fita daga kitchen kai tsaye ta wuce ɗakin Ammi ta buɗe kolar da aka sawa Ammi da jama'arta abinci ta diɓe abinci daga kolar daga haka ta koma ɓangaren Dady ɗakin  da Unaisa ke kwance daga shigarta ta ɗaga Unaisa ta bata tea ta sha,babu laifi ta sha da ɗan yawa abinci dai bata ci sosai ba 





*SHUUKRAN*