MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 76

by @maimunabala209

*MATAR GIDA BOOK* 2


*SHUUKRAN*/022


*YOTA ASSOCAITION*


P76


Karfe biyar da wasu mintina na yammacin wannan Unaisa na zaune ɗaki gaban madubi tana shirin zuwa kamu Nailah,kusan rabin jama'a duk an tafi wajen kamu Unaisa bata dade da tashi daga bacci ba tun karfe biyu ta kwanta sai yanzu ta farka,zuwa yanzu ta samu saukin jiri da ya addabe ta ɗazu dalilin rashin cin abinci da wuri da ba ta yi ba,body lotion da hoda kaɗai ta shafa fuskarta,turarukan humra masu sauƙin ƙhamshi ta shafi jikinta da su, sabuwar karamar hand bag da sabuwar takalmi da ta siya dan bikin ta dauko ta sa,kallon kanta ta yi cikin madubi ta ga ta fita rass da ita wata doguwar ajiyar zuciya ta sauki daga haka ta fita daga ɓangarenta,cike da jureya take tafiya tana jin yadda ƙugu da kafafunta suke riƙe mata har ɓangaren Amirah ta shiga bakin ta dauke da sallama nan parlour ta tadda Amirah tana shirya yara daga can gefe Ɗalha na zaune saman kujera one siter yana riƙe da Fauziyya hannunsa riƙe da waya ya kunnawa Fauziyya carton,wasu daga cikin relatives ɗin Ɗalha dake ɓangaren Amirah sai kaiwa da komuwa suke su na shirin zuwa kamu,Ɗalha dan ba yadda ya iya ne kawai yasa zai zauna da yara amma ko kadan bai so zaman gidan ba,kasancewar mata ƴan biki dake cike gidan jiya bayan zuwan su Kano babu kowa ɓangaren Amirah har safen nan hakan yasa ya saki jiki ya yi zaman sa,sai dai tun azahar ya lura wasu daga relatives ɗinsa sun tattaro kayayyakin su ba ki ɗaya sun dawo ɓangaren Amirah hakan yana nufin nan za su zauna har sai an gama biki,kasancewar Ɗalha na zaune parlourn yasa relatives ɗinsa suka gaisa da Unaisa cike da mutuntawa,ita dai ta yi ta mamaki a zuciyarta,tun shigar Unaisa parlourn Ɗalha  ya ƙureta da ido sai bin ta yake da ido,waje ta samu ta zauna bayan ta gaisa da Amirah a natse ta mayar da dubanta inda yake zaune murya ƙasa ƙasa ta gaishe sa,amsa mata gaisuwar ya yi yana ƙara kallonta,ita dai tunda suka gaisa bata sake kallon inda yake ba,tana nan zaune har Amirah ta gama shirya yara duka ta shirya kanta,Ɗalha zai zauna da yara a gida da ƙyar Amirah ta shawo kansa tun daren jiya ta yi ta masa magiya da ƙyar ta samu ya amince,tare da Husnah suka tafi kamu cikin motar Husnah,Husnah ce ta tuƙa su tare da wasu cousin ɗin Ɗalha,a hanyar su ta zuwa wajen kamu haka suka yi ta hira da junan su Unaisa ta koma kamar bare cikin su da ta yi magana sai su yi shiru Amirah ce kaɗai ke amsa ta,ko a wajen kamu Amirah na riƙe da hannu Unaisa haka ta yi ta nuna ta cikin dangin amma kaɗan daga cikin dangin Ɗalha suka sakarwa Unaisa fuska da yawa yawan su yi suke kamar basu ganta ba sai su yi ta magana ta Amirah ita dai tana tsaye kamar marainiya ko ta yi ƙokarin shiga cikin su a yi komai tare da ita haka zasu ware ta sarai Amirah ta fahimci abinda aka riƙa yiwa Unaisa  sai ta yi ta jan Unaisa da hira wannan dalilin ya sa Unaisa ta iya zama wajen kamu har lokacin tashi,bayan komawarsu gida wanka kawai Unaisa ta yi bata iya cin komai ba ta yi kwanciyarta kawai,ko kaɗan bata jin cin abinci fruit take son sha,wayarta ta dauko ta riƙa juya wayar, Ɗalha take son kira sai dai ko kaɗan bata son ya yi tunanin buƙatarsa take ɓangarenta yake yau amma har karfe tara bai shigo ba ita kaɗai ce ɓangarenta babu wacce ke son zuwa ɓangaren nata,bayan dogon nazari ta tura masa saƙo inda ta roƙe sa tana son fruit,Ɗalha bai shigo ba har karfe goma da wasu mintina lokacin Unaisa ta yi bacci hannayensa riƙe da leda cike da fruit ya shigo ɓangaren shiru ɓangaren nata na yi babu motsin komai sai ƙarar AC dake aiki sanin kansa ne zuwa yanzu ta yi bacci hakan yasa ya wuce kitchen ya buɗe firiji dake kitchen ya sa ledar fruit ciki,tun karfe takwas ya dawo yana ɓangaren Dady a can ya ɓata lokaci bayan dawowarsa Dady ya haɗasa da wasu daga abokan kawo Abubakar da suka zo daga ƙasar Maroco ya kai su hotel,ɗakinsa ya wuce ya yi wanka ya shirya kansa cikin wasu riga da wando nigth wear daga haka ya shiga ɗakin Unaisa sallama dauke a bakinsa ya shigo ɗakin ganinta ya yi kwance tana bacci hankali kwance ta rufe jikinta da bargo tsayawa ya yi bakin kofa yana ƙare mata kallo bayan wasu mintina ya shiga ɗakin,bayan shigarsa zama ya yi bakin gado yana ƙare mata kallo can ya kai hannu goshinta ya shiga wasa da sumarta da ya fito daga hula,can ya fara kiran sunanta a hankali,a cikin bacci Unaisa ta ji ana kiran sunanta kamar a mafarki a hankali ta buɗe idanunta dake cike da bacci ta sauke su fuskar Ɗalha murmushi ya sakar mata Unaisa ta gyara kwanciya har sannan idanunta kansa bata tanka sa ba a hankali ya kai bakinsa kunnenta ya ce ''sleeping beuty'' ya faɗa tare da manna mata kiss a kunci,shiru kawai ta yi ta masa banza kamar ba da ita yake ma magana ba, har sannan hannunsa goshinta ya ce ''fruit ɗinki na firiji na kawo maki?" kallon sa ta yi na wasu ƴan sakanni kafin a hankali ta juya masa baya fuskarta tana fuskantar window ɗakin a hankali ta ja bargo tana ƙara rufa jiki tare da gyara kwanciya murmushin gefen baki Ɗalha ya yi can ya kai hannu bargo da ta yi rufa da shi ya yaye bargon da sauri Unaisa ta waigo da niyyar magana sai dai bai bata damar hakan ba ta buɗe baki da niyyar magana ya kwanta samanta bai sakar mata nauyinsa ba ya kai bakinsa daidai nata yana son haɗe su waje guda sai dai bata damar hakan ba,har yanzu haushin sa take bata manta rashin mutunci da ya mata ba sanda ta yi rashin lafiya tun kafin su zo Kano ta fahimci yana son shiri amma sai ta yi kamar bata fahimta ba ta yi ta share sa ba za ta iya yafe masa lokaci guda ba,kawar da kai gefe ta yi tana ɓata fuskar fuskarsa dauke da murmushi ta riƙe fuskarta tare da kai baki kunnenta 











Washe gari da zazzaɓi Unaisa ta tashi,ko kaɗan ɗaren jiya Ɗalha bai sarara mata ba,da ƙyar ta yi sallar asuba yanzu haka karfe sha ɗaya da wasu mintina amma tana nan kwance bata iya tashi ba,ganin yanayin da take ciki yasa Ɗalha bai fita ba sai da ya haɗa mata breakfast,da wuri ya fita dalilin kiran da Dady ya masa baƙin kawo Abubakar da suka kwana a hotel jiya suke buƙatar wanda ya san gari a tare da su,sai sha biyu Unaisa ta iya tashi ta yi wanka da brush abin kari da Ɗalha ya haɗa mata kafin ya fita ƙasa ci ta yi karshe tea kawai ta sha ta sha magungunanta daga haka ta kwanta amma bata iya bacci ba dalilin hanayiyar jama'a ƴan biki,a can wajen Amirah kuwa gaba ɗaya bata da sukuni kusan gaba ɗaya ragamar bikin Ammi ta sakar mata,Amirah ta zama ita ce kirjin biki tun safe bata haɗu da Unaisa ba duk da aiyuka ta tarɓar baƙi da ta uni ta na yi tunanin Unaisa na zuciyarta,ita a tunaninta Unaisa ta shiga cikin ƴan biki bata san tana ɗaki kwance ba lafiya ba,rashin ganin Unaisa ranar ba ƙaramin tayar da kura hakan ya yi ba wajen dangin Ɗalha kowacce da abinda take faɗi kan Unaisa,a tunanin su da gangan Unaisa ta ki fitowa kuma babu wacce ta yi tunanin zuwa ɓangaren Unaisa ta duba ko lafiya,har aka tafi daurin aure Unaisa bata fito ba nan ma suka yi ta surutai marasa dadi kan Unaisa,a can wajen Unaisa kuwa ba ita ta samu sauƙi ba sai misalin ƙarfe biyar na yamma wanka ta kuma yi bayan fitowarta daga wanka tsayawa ta yi tana ƙarewa ankon uni wanda ya kamata ta sa yau,sai dai baza ta  iya sanya su ba,tun safe ta tsinci kanta cikin rashin son sanya kaya masu nauyi, wannan dalilin yasa ta shirya kanta cikin wasu riga da wando na Pakistan marar nauyi sosai ta ji daɗin jikinta,zuwa yanzu zazzaɓin ya sauko sai ciwon kai shima kuma ba sosai take jinsa ba kaɗan kaɗan yake mata,jiki babu kwari ta ja ƙafa zuwa kitchen inda ta daura farar indomie bata sa komai cikin indomie ba daga ruwa sai indomie haka ta tafasa bayan ya dahu ta kashe gas kafin ta dauki plate ta juye indomie ciki,a nan parlour ta samu waje ta zauna ta fara ci a natse tana ci tana lumshe ido sosai ya yi mata dadi cikin ikon Allah ta ci da yawa ta ci kusan rabi daga bisani ta dauke sauran ta kai kitchen,sai da ta wanke plate ɗin kafin ta fita daga kitchen,kai tsaye ɗakinta ta wuce,bayan shigarta ɗaki zama ta yi bakin gado tana mayar da numfashi kamar wacce ta yi babban aiki,tunawa ta yi yau gaba ɗaya bata fito ba dalilin zazzaɓi sanin kanta ne ƴan biki za su yi ta surutu kan rashin fitar ta harda basu san halin da ta uni ba,wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke murya can ƙasa ta ce ''bara na je na gaida Ammi sai na faɗa mata zazzaɓi ne ya hanani fita'' cike da juriya ta miƙe tsaye tana jin yadda mararta ya ƙulle duk sanda ta ci abinci hakan cikin ke mata riƙewa yake na wasu mintina daga bisani kuma ya sake babies su yi ta motsi suna wasa a cikin ciki,sosai Unaisa ke jin dadi duk sanda babies ɗinta ke wasa ciki sai ta yi sakin murmushi ita kaɗai Allah ya sani tana mutuƙa son cikin da rayuka da ke ciki, wata green hijab har ƙasa ta zura daga haka ta fita daga ɓangaren zuwa ɓangaren Ammi,tun fitowarta ƴan biki suka rinƙa maganganun ƙasa ƙasa suna binta da ido zuwa yanzu gaba ɗaya Unaisa ta gaji da lamarin su wannan dalilin yasa ko kallon inda suke bata yi ba, gaisuwar ma da jiya ta rinƙa binsu tana gaida su suna ƙin amsawa wasu kuma su amsa amma sai su riƙa mata kallon raini da rashin sani yau bata gaida kowa ba,a yanda take jin kanta yau bata son damuwa ko abin da zai ɓata mata rai hakan yasa ta yi masu banza kai tsaye take tafe har ta isa ɓangaren Ammi lokacin yamma ta yi sosai an kusa kiran sallar magrib hakan yasa parlourn Ammi yin duhu kaɗan,Unaisa ta ratsa cikin jama'a kai tsaye ta shiga ɗakin Ammi bakin ta dauke da sallama,bayan shigarta ɗakin Ammi na tsaye daga kofar bathroom dattawan mata biyu da Unaisa ta gansu ɗakin Ammi jiya su ta kuma gani yau zaune kan gadon Ammi sai wasu ƙawayen Ammi biyu zaune kan kujera two siter sun sha gayu sosai sun baza gold a jiki hannayen su riƙe da manyan wayoyi da disigner bags,cike da girmama Unaisa ta gaida dattawan matan da ƙawayen Ammi duk suka amsa mata fuska sake,a hankali ta tako inda Ammi ke tsaye ta gaida Ammi fuska babu yabo babu fallasa Ammi ta amsa mata gaisuwar daga haka Unaisa ta samu waje saman carpet dake shimfiɗe parlourn Ammi ta rukuɓe ta zauna,gaba ki ɗaya a takure take rashin samun sakin fuska daga Ammi yasa gaba ɗaya ta takura kanta,cikin zuciyarta ta ji da ma ta yi zamar ta ɓangaren ta,ta yi nadamar zuwa gaida Ammi da ta yi,shiru ne ya biyo baya a hankali Unaisa ta ɗago tare da mayar da dubanta ga Ammi cikin kwantar da murya ta ce ''Ammi ya aka ji da jama'a?" kamar baza ta amsa ba sai kuma ta ce ''alhamdullilah'' Unaisa bata ji dadin yadda ta ba ta amsa ba amma sai ta daure ta ce ''tun asuba nake kwance ban ji daɗi ba sai yanzu na samu sauki'' a gatse Ammi ta ce ''ayyah Allah ya sauwaƙa'' daga haka ta cigaba da hira da ƙawayenta,ita dai Unaisa ta yi shiru tana sauraron hirar can Ammi ta shiga bathroom ta dauro alwalah kasancewar an fara kiran sallar magrib Unaisa na nan zaune har Ammi ta fito daga bathroom,daidai sanda Ammi ta zo wuce kusa da Unaisa ne Unaisa ta kai hannu da niyar gyara hijab ɗinta daga hanyar da Ammi zata wuce ga mamakin Unaisa Ammi ta sa ƙafa ta shure hijab ɗin kadan ya rage ta taka hannu Unaisa,da wani irin sauri haɗe da mamaki Unaisa ta ɗago ta kalle Ammi ko kallon inda take Ammi bata yi ba,ta wuce wajen saif ta buɗe tare da ɗaukar hijab da zata yi sallah,sosai Unaisa ta yi ƙokarin saita nitsuwarta kafin ta yi magana cike da nitsuwa ta ce ''Ammi zan tafi sai da safe'' ta faɗa tare da miƙewa tsaye ba tare da kallon inda Unaisa ke zaune ba Ammi ta ce ''to Unaisa nagode'' Unaisa ta sa kai ta fita zuciyarta cike da ƙunci ta isa ɓangarenta ta dauro alwala ta gabatar da sallar magrib,bayan ta idar da sallah zama ta yi kan darduma tana kai kukanta ga mahaliccin ta,sai a sannan ta samu damar kuka,kuka ta yi sosai mai isarta tun zuwanta garin Kano dangin Ɗalha ke ƙuntata mata bata masu laifi komai ba kawai sun daura mata karar tsana,sai da ta yi sallar isha'i kafin ta tashi daga darduma,har bayan sallar isha'i Ɗalha bai shigo ba,Unaisa na kwance ɗaki ta kunna wani horrow flim cikin wayarta tana kallo, kamar wasa har karfe goma Ɗalha bai shigo ba ganin haka yasa Unaisa tashi ta fita parlour ta kashe wutar parlour da kitchen daga haka ta koma ɗaki,bayan shigar ta ɗaki bathroom ta wuce bata dauki lokaci ba ta fito ta rage wutan ɗakin ya rage iya hasken bedside lamp daga haka ta yi kwanciyarta tare da karanto addu'ar bacci,a cikin bacci ta ji Ɗalha ya buɗe kofar ɗakin ya shigo ya kwanta bayanta tare da janyota jikinsa ya manna mata kiss a kafaɗa,bakinsa ya kai daidai kunnenta ya yi magana kamar mai raɗa ya ce ''ya ku ke?" Ya faɗa yana kai hannunsa shafaffan cikinta shiru ta masa kamar tana bacci ƙara haɗeta ya yi da jikinsa cikin wata iriyar murya ya ce ''zazzaɓin ya sauko? na ji jikin babu zafi sosai'' ko kaɗan bata yi miyar tanka sa ba amma sai ta tsinci kanta da faɗin ''ya yi sauƙi'' ta faɗa a hankali wani kiss ya kuma manna mata a gefen fuska daga haka ya shiga bata labarin abubuwan da ya yi yau,Unaisa ta yi shiru tana sauraran sa har ya gama bata labari bata ce komai ba,jin ta yi shiru yasa Ɗalha tunani ta yi bacci hakan yasa ya ja masu bargo yana manna mata kisses a bayanta,bayan ya gama shafe shafensa ya karanto masu addu'a ya tofa mata da shi kansa,cikin ɗan kankanin lokaci bacci ya dauke sa ba ƙaramin gajiya ya yi ba,Unaisa ta yi lamo jikinsa tana jin yadda numfashinsa ke sauka a bayanta wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke daga haka ta rintsa idanunta ba tare da ɓata lokaci ba bacci ya dauke ta









*SHUUKRAN*