MATAR GIDA

MATAR GIDA PAGE 77

by @maimunabala209

*MATAR GIDA BOOK* 2

*SHUUKRAN*


*YOTA ASSOCIATION*


P77


Alhamdulillah an yi taro an watse lafiya safiyar Lahadi Anty Nazaaha da kawo Abubakar tare da tawagar su sun kama hanyar komawa ƙasar Maroco,kamar yadda Anty Nazaaha ta tsara can ƙasar Maroco zata karasa sauran bukukkuna irin ta al'adarsu,misalin ƙarfe sha ɗaya na safe da yawa yawan ƴan biki sun koma gidajensu wa'inda suke nisa kaɗai suka rage,wa'inda suke ƙwayukan Kano tun jiya sun fara tafiya,tuni Amirah da sauran ƴan biki tare da Husnah sun gama gyare gyaren gida,ko ina tsaf kamar ba a yi taro ba ita dai Unaisa tun safe ta shirya jakarta tana zaman jiran Ɗalha, ɗazu da safe kafin ya fita ya faɗa mata yau za su koma Kaduna hakan yasa take Allah Allah ya dawo gaba ɗaya garin Kano ya fita ranta ji take kamar ta yi tsinstuwa zuwa Kaduna tun safe ta shiga ɓangaren Ammi ta gaida Ammi Ammi ta amsa mata kamar kullum fuskar dai babu yabo babu fallasa a parlourn Ammi ta haɗu da Husnah tana shirin gaida Husnah Husnah ta dauke kai ta yi shigewar ta kitchen,Unaisa ta taɓe baki kawai ta fita daga ɓangaren Ammi bayan fitarta daga ɓangaren Ammi kai tsaye ta wuce ɓangaren Amirah inda ta tadda Amirah na gyaran kitchen ɗinta,gaisawa suka yi daga haka Unaisa ta koma nata ɓangaren ta yi kwanciyarta bayan tashinta ta shiga haɗa kayanta,ganin sha biyu ta wuce yasa Unaisa ɗaga waya ta kira Ɗalha bugu ɗaya ya dauka bayan ya amsa kiran ne Unaisa ta yi masa magana kai tsaye ta ce ''ba ka dawo ba sha biyu ta wuce'' shiru Ɗalha ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya ce ''me ke faruwa?" Unaisa ta rasa abinda zata faɗa masa kawai ta ce ''babu komai kawai dai ina son mu tafi da wuri ne ina jin kamar zazzaɓin na son dawowa'' sauke numfashi Ɗalha ya yi tare da yin shiru na wasu ƴan sakanni ƙafin ya buɗe baki da ƙyar ya ce ''ok'' daga haka ya katse kiran ba'a dauki lokaci ba Unaisa ta ji karar motarsa wani irin farin ciki ya ziyarce tana nan zaune cikin ɗaki tana jiran shigowar Ɗalha ga mamakin ta har a ka kira sallar azahar Ɗalha bai shigo ɓangarenta ba,Unaisa na zaune kan darduma hannunta riƙe da carbi, misalin karfe biyu Ɗalha ya tura kofar ɗakinta ya shigo bakinsa dauke da sallama da sauri ta waigo tana kallonsa shima ita yake kallo yana tsaye daga bakin kofa ya ce ''kin gama?" gyaɗa masa kai kawai ta yi ba tare da ta ce komai har sannan idanunsa kanta ya ce ''ok ki fito zamu fara biya gidan su Amirah kafin mu wuce'' da to kawai Unaisa ta amsa daga haka ta shafa addu'a cikin ɗan kanƙani lokaci ta fito sanye da wata farar doguwar riga egyptain ta yi rolling da pink veil hannuta riƙe da madaidaicin travelling bag ɗinta ta fito daga ɓangarenta bayan ta rufe kofar ɓangaren nata,Amirah da yara ta gani tsaye jikin mota Amirah ta sakar mata murmushi ita ma ta mayar mata da murmushi,Amirah ta cewa Sudais ya je ya karɓi jakar Unaisa babu musu ya ruga a goje Unaisa na daf da shiga ɓangaren Ammi ta jiyu muryar Sudais ya ce ''hi Anty wai ki kawo jakar na riƙe maki in ji Mumyna'' ya ƙare magana fuskarsa dauke da murmushi kallon yaron Unaisa ta yi ta ga babu inda ya baro Ɗalha har murmushinsa kamar babansa abinda ya bambanta sa da Ɗalha hasken fata ce kawai wacce ya dauka wajen Amirah,Unaisa ta ji kaunar yaron har cikin zuciyarta gashi tsaf tsaf sai baza ƙhamshi yake abinsa, a hankali ta miƙo masa jakar cikin sakin fuska ta ce ''thank you'' Sudais ya ƙara faɗaɗa fara'arsa ya ce ''you are welcome Anty'' ya faɗa cikin jin kunya,da wani irin sauri ya bar wajen ya nufi inda Amirah da sauran yara ke tsaye yana ta sakin murmushi tare da rufe fuska da hannusa ɗaya a dole kunya yake ji,bayan ya ƙaraso inda Amirah da ƴan uwansa ke tsaye, Rayyan ne ya fara yin magana inda ya ce ''she cover her hair today i want to see it'' ya kare magana yana toshe baki Afef kuma ya ce ''she is so white and beutiful'' ya yi magana yana murmushi Suhail ya taɓe baki ya ce ''yes she is''daga haka ya waigo tare da kallon Amirah ya ce ''amma Mumy me yasa ki ke hana mu zuwa site ɗinta kullum cewa ki ke zamu sa ta magana ko ki ce zamu ɓata mata gida but we like her Mumy and kin ce ita ma Mumyn mu ce to me yasa ba ki barin mu muna zuwa site ɗinta?" Ya ƙare magana yana kafe Amirah da ido duka yaran sunyi shiri suna jiran jin abinda Amirah zata faɗa numfasawa Amirah ta yi kafin ta ce ''kamar yadda na faɗa maku baza kuna zuwa ɓangarenta ba saboda za ku sa ta magana sannan za ku ɓata mata gida'' shiru ta yi na wasu ƴan sakanni daga haka ta mayar da dubanta ga Rayyan ta ce ''ina sane da laifin fasa min Tv da ka yi kai kuma Suhail kofar saif ɗina daka ɓalla zamu koma gida sai na yi maganin ka'' daga haka ta ja bakinta ta yi shiru suma kuma duk suka yi shiru tunawa da ɓarnar da suka yiwa Mumyn nasu,tabbas Amirah tana jin dadin yadda yaranta ke kaunar Unaisa sai dai bata barin su suna zuwa ɓangaren Unaisa ne saboda ɓanna su tana da yawa in ita tana hakuri da ɓanna ɗa ɓata waje da suke mata ba lallai Unaisa ta yi hakuri ba ko bata yi magana tabbas baza ta ji daɗi ba duk sanda suka mata mammunar ɓanna,sannan maganar dogon gashin Unaisa da bai fita bakinsu kullum cikin maganar dogon gashin Unaisa suke sanin Amirah in Unaisa ta sakar masu fuska to wata rana cewa zasu yi zasu mata kitso,bayan shigar Unaisa ta tadda Ammi zaune tare da Ɗalha da alama sallamar ta yake cike da girmama Unaisa ta raɓa jikin kujera cikin sanyi murya ta ce ''Ammi zamu wuce'' Ammi ta mayar da dubanta ga Unaisa ta ce ''to Unaisa Allah ya tsare hanya Ubangiji ya sauke ku lafiya,dan Allah ki kula sosai ki daure kina cin abinci sosai da shan magunguna,da kuma motsa jiki banda yawan bacci barkatai in kina yawan motsa jiki naguɗa zata zo maki da sauƙi'' a hankali Unaisa ta ɗago tare da kallon Ammi fuska cike da mamaki kawai ta taɓe baki sai kuma ta yi magana cike da girmamawa ta ce ''insha Allah Ammi nagode daga haka ta yunkura tare da miƙewa tsaye Ammi ta dakatar da ita ta hanyar faɗin ''dauki waccan ledar ki tafi da shi'' Unaisa ta dauki leadr kamar yadda Ammi ta faɗa tana ƙara yiwa Ammi godiya daga haka ta fita daga parlourn mamakin Ammi fal zuciyarta










A gurguje suka biya ta gidan mahaifin Amirah sun yi sa'a yana gida nan dai suka gaisa kafin daga bisani sun kama hanyar Kaduna lokacin karfe uku da wasu mintina,basu suka shiga Kaduna ba sai karfe bakwai na dare lokacin ana ruwan sama sosai,a hanya Ɗalha ya yu masu take away duk sun gaje musamman Unaisa da kafafuwanta sun ƙara kumbura,bayan saukowarsu,a bangaren Amirah Ɗalha yake ba tare da ɓata lokaci ba Amirah ta ba yara abincin da Ɗalha ya siyu masu ta yi masu wanka daga haka ta umurci su ta je su kwanta,bayan yara sun kwanta ne ta dauki ledar da Ammi ta ba ta ta buɗe ta ga cincin ne da su alkaki sai dubla da nakiya an zuba su cikin wasu fararen robobi masu matsakaici girma ɗaya robar kuma soyayyar nama ce cike ciki,Amirah ta yi murmushi daga haka ta sa su inda ya dace,a can wajen Unaisa bayan shigarta ɓangarenta ta buɗe leadr da Ammi ta ba ta,ta ɗan ji dadi ganin abubuwan da ke cikin ledar waje ta samu ta ajiye su daga haka ta shiga bathroom ta yi wanka ta kwanta,bayan sati biyu da dawowarsu daga Kano cikin Unaisa ya shiga wata bakwai da sati biyu zaune take cikin parlour ta kara waya kunnenta waya take da Mama inda Mama ke tambayarta ya zaman ta Ɗalha a yanzu numfasawa Unaisa ta yi kafin ''lamarin dai da sauƙi Mama'' Mama ta ƙara bata shawarwari, yammacin wannan ranar Unaisa na zaune ɗaki bayan ta idar da sallar isha'i hannuta riƙe da waya tana kallon flim saƙo ya shiga wayarta daga whatsApp group ɗin matan gida cigaba da kallon ta yi sai kuma ta ga an yi taging ɗinta hakan yasa ta tsayar da kallon ta shiga whatsapp ta buɗe saƙon,a firgice Unaisa ta yunƙura ta zauna tana ƙara kallon sakon,nan take jikinta ya shiga rawa cikin ɗan kankanin lokaci ta jiƙe da zufa shakaf,harda fanka da A C dake aiki ɗakin hakan bai hanata zufa fa,wani rawa jikinta ke yi gaba ɗaya ta fita hayyacinta tsoro da firgici kwance cikin idanunta a hankali take ƙara karanta sakon,dogon rubutu Hajiya Bilƙisu ta yi da fari ta fara da godiya ga Allah (S W A) daga haka ta yi rubuta kamar haka an je gidan kowacce an yi taro kamar yadda aka saba Unaisa ce kaɗai ba a je taro gidanta ba saboda haka karshen wannan sati za a yi taro gidan Unaisa,Unaisa ta karanta saƙon ya fi a ƙirga hankalinta ya yi mugun tashi cike da kiɗima ta fita daga whatsapp ta kira layin Hajiya Bilƙisu bugu biyu Hajiya Bilƙisu ta amsa kiran babu ko sallama Unaisa ta ce ''Hajiya me ki ke nufi da sakon da ki ka tura cikin ƙungiya?" Unaisa ta kare magana cike da tashin hankali wata iriyar shu'umar dariya Hajiya Bilƙisu ta yi kafin ta ce ''abinda na rubuta shi nake nufi'' cikin rawar murya Unaisa ta ce ''me yasa ki ke son kashe min aure har gida fa na same ki na faɗa maki iyayena da mijina basu son kasancewata ƴar kungiya,tsakanin ki da Allah wani taro kuma za a yi gidana bayan wanda aka yi kwanakin baya?" Unaisa ta kare magana cikin ɗan ɗaga murya wata iriyar murmushin mugunta Hajiya Bilƙisu ta yi kafin ta ce ''taron da aka yi gidan ki taro ne na shigarki kungiya da tabbatar dake ɗaya daga cikin mu wannan kuma da za a yi taro ne da ake zuwa gidan kowacce daga cikin mu saboda haka ki shirya in Allah ya kaimu ranar asabar muna nan zuwa'' daga haka ta katse waya tsabar tashin hankali wani irin zazzaɓi haɗe da jiri ya saukowa Unaisa lokaci guda da kyar take iya furta kalmar innalillahi wa inna'ilahi raji'un a hankali ta samu waje ta zauna bakin gado gaba ɗaya kanta ya kulle ta ƙasa kwakkwarar tunani daren ranar bata samu isasshen bacci ba haka ma washe gari gaba ki ɗaya ta zama wata iri kamar wacce bata da lafiya wata zuciyar ta bata shawara ta fita kawai daga kungiyar wata zuciyar ta karanto mata ta yi ta addu'a kawai Allah ya kawo mata mafita,bayan sallar isha'i tana kwance ɗaki jikinta ya yi sanyi sosai tunanuka kala kala zuciyarta Ɗalha ya shigo ɗakin bakinsa dauke da sallama ganin ta kwance shiru ya sa ya yi tunanin bata jin daɗi ne hakan yasa ya samu waje ya zauna tare da mayar da dubansa gareta ya ce ''jikin ne?'' Unaisa ta kallesa kawai ta gyaɗa masa kai alamar eh tambayarta ya yi ko ta sha magungunanta nan ta ce masa eh ta sha,bayan wasu ƴan sakanni ya tashi ya fita daga ɗakin tare da ja mata kofa,ko bangaren Amirah bata samu damar shiga ba cikin wannan kwanakin tsabar tashin hanklai,kwanaki nata tafiya lokaci na ja Unaisa na ƙara shiga damuwa da tashin hankali yau saura kwanaki biyu a yi taro gidanta safiyar Alhamis kwance take ɗaki ta yi nisa cikin tunani,Ɗalha ya shigo ɗakin hannunsa riƙe da wata karamar jaka travelling bag da alama tafiya zai yi da sauri Unaisa ta yunƙura tare da zauna tana kallon Ɗalha shima ita yake kallo gyara tsayuwar sa ya yi kafin ya ce ''tafiya ta kamani ɗazu bayan sallar asuba Director ya kirani yake sanar mani cewar da akwai wani program me mahimmaci da aka gayyace sa a Legas amma ba zai samu damar tafiya ba yana so ni da Muhsin mu wakilce sa'' shiru ya yi na wasu ƴan sakanni kafin ya ce ''bayan sallar azahar zamu tafi Kano a can zamu hau jirgi,and jirgin karfe takwas na dare zamu bi,ranar asabar za a yi program ɗin Lahadi zamu dawo'' tsabar farin ciki Unaisa ta rasa inda zata sa kanta kawai ta shiga sakin murmushi, kuɗi Ɗalha ya ciro daga aljihun rigarsa naira dubu ashirin ya miƙo mata yana faɗin ''ki riƙe wannan'' a hankali Unaisa ta miƙe tsaye ta sa hannu ta ƙarɓi kuɗin tana masa godiya tsabar farin ciki bata san sanda ta rungume sa ba tana jero masa addu'o'i Ɗalha bai kawo komai zuciyarsa ba ya sa hannu ya rungumeta tare da manna mata kiss daga haka ya raba ta da jikinsa yana gudun kar ta sa ya makara,Muhsin na waje yana jiran sa, daga office za su wuce Kano,sai da Ɗalha ya sallame Amirah suka sha soyayyar su kafin ya shiga ɓangaren Unaisa,bayan fitar Ɗalha cike da farin ciki Unaisa ta yi shujudud shukur tana yiwa Allah godiya lokaci guda ta ji ta dawo hayyacinta wani karfi da kwarin gwaiwa ya ziyarce ta lokaci guda,bata san sanda hawaye ya shiga zubawa daga idanunta ba tsabar farin ciki,cikin rawar jiki ta dauki wayarta ta shiga whatsapp ta shiga chat ɗinta da Hajiya Zulfa'u ta tura mata saƙo cewar tana so ta yi mata order abincin taro da za a yi gidanta daga haka ta tura mata saƙon,unin ranar cikin farin Unaisa ta yi shi amma can ƙarƙashin zuciyarta tana sane dole wata rana zata bar ƙungiyar duk yadda ta kai ga son zama cikin kungiyar ko dan samun madauwamiyar zaman lafiya a gidan mijinta da kuma iyayenta,washe gari juma'a misalin karfe biyu na rana Unaisa ta shiga ɓangaren Amirah ta tadda Amirah zaune Aina'u na gefenta suna cin gyaɗa dafaffiya waje Unaisa ta samu ta zauna,bayan sun gaisa da Amirah,Amirah ta tura farantin gyaɗa gaban Unaisa tana faɗin bismillah murmushi Unaisa ta ce ''a'a nagode''daga haka ta gyara zama tare da mayar da dubanta ga Amirah ta ce ''Maman Sudais wata alfarma nake nema wajen ke da Aina'u'' daga haka ta ja bakinta ta yi shiru da wani irin expresion Amirah da Aina'u suka kalle Unaisa ita dai Aina'u bata ce komai ba sai Amirah ce ta yi magana inda ta ce ''alfarmar me amarya?" Unaisa ta gyara zaman tare da sunkuyar da kai ƙasa ta ce ''daman in Allah ya kaimu gobe zan yi baƙi''..shiru ta yi na wasu ƴan sakanni tana tunanin yadda zata fidda zancen can dai ta daure ta ce ''daman da akwai wata kungiya da nake ciki ƙungiya ce ta mata da muke taimakon junanmu muna haɗawa juna kuɗi kamar dai adashi haka muke yi,ko na ce meeting'' ta kare magana fuskarta dauke da murmushi sannan ta yi shiru a karo na biyu,Aina'u da Amirah duk suka zuba mata ido musamman Amirah tana sauraran Unaisa cike da mamakin Unaisa kenan bata fita kungiyar ba ko me hakan ke nufi,muryar Unaisa ne ya katse mata tunanin inda Unaisa ta ce ''duk karshen wata muke zuwa gidan ɗaya daga cikin mu yanzu dai in Allah ya kaimu gobe zasu so nan gidan taron ya zagayu kaina'' gyara zama ta yi ta lanƙwasa murya ta ce ''dan girman Allah Maman Sudais ina son ki rufa min asiri kar Abban Sudais ya samu labarin an yi wata taro nan gidan wallahi baya son zama na a kungiyar ki rufa min asiri dan Allah'' da fari ƙasa magana Amirah ta yi  tsabar mamakin Unaisa da ya lulluɓeta, baki sake take kallon Unaisa har Amirah ta buɗe baki da niyyar yiwa Unaisa nasiha ta kuma nuna mata hakan ba daidai bane sai kuma ta fasa tunawa ta yi duk tsawon zaman ta da Unaisa ko sau ɗaya Unaisa bata taɓa mata hirar wata kungiya ba,kenan in ta yi mata nasiha yanzu Unaisa zata fahimci Ɗalha ya faɗa mata rikicin mota da kuma maganar kungiya da suka yi kwanakin baya,ba lallai hakan yawa Unaisa daɗi ba kila ma su samu saɓani da Ɗalha hakan yasa Amirah faɗin''insha Allahu ba zan faɗa masa ba'' ta kare magana cike da tsantsan mamakin Unaisa sosai Uniasa ta ji dadin amsar da Amirah ta bata nan ta shiga jerowa Amirah godiya,bayan komarta ɓangarenta ne ta dawo hayyacin ta sai a sannan ta gane ta aikata baban kuskure,wata tunani ne ya faɗo mata cikin zuciyarta a zahiri ta ce ''da na sani ban faɗawa Maman Sudais maganar kungiya ba,da na ce mata ƴan uwana ne ba matan ƙungiyarmu ba'' ta ƙare magana tana cizan yatsan hannunta manuniya,me yasa bata yi wannan tunanin tun da wuri ba sai yanzu murya can ƙasa ta shiga furta kalmar innalillahi wa inna ilaihi raji'un cikin zuciyarta tana addu'ar Allah sa Amirah ta cika alƙawarin da ta dauka kar ta faɗawa Ɗalha 







*SHUUKRAN*