Chapter 1
*_The Amazing Pen_ ✍️...*
*Bani da Madogara*
(Sai Allah...)
001
*Kwanar faru k'wai Kaduna State,Nigeria*
•••••••••••••••••Gida ne babba mai kyau da tsari daidai gwargwado,idan kaga gidan baza kayi tunanin a k'auye a kayi ginin ba.Mata ne zaune a saman bencina tuna murza flawa,wasu kuma na yanka kwab'abb'an flawan k'ananu,wasu bangeren matan na tuyar cincin ,kowacce kana ganinta kaga ƴar k'auye saboda shigar da ke a jikinsu ba wata shigar kirki bace,riga daban ɗan-kwali daban haka suketa faman aikin tuya.Wata ce a cikinsu ta dubi ƴar uwarta ta ce
"Wai in tambayeki Harira"
Wacca aka kira da Harira ta ce
"Ina sauraranki Balki"
Balki ta ɗan nisa sannan ta ce
"Wai ina Hujayrah mai idon mujiya take ne,naga tun da aka fara shirye-shiryan bikinsu Maryamu bana ganinta"
Taɓe baki Harira tayi sannan ta ce
"Yooo ke kuwa Balki ina zaki ga mai idan mujiya,baƙin hali ya hanata kataɓus! Bata nan bata can,ita ce bin Kakulle dauji samun saiwar ƙasa da gayayyaki na magunguna,ita ga mai bada magani Mtws! "
"Wai da gaske Kakulle Hujayrah mai idan mujiya taba laƙanin magani yanzu,bayan Baba Audu ya makance? "
Gyara zama Harira ta yi don ta ji daɗin ba da labarin da kyau ta ce
"Hmmmm ke dai bari,na ji takaicin hakan wallahi,maimakon Kakulle taba Babana ko su Baba Zubairu,Baba Musa ko kuma ƴaƴanta mata kamar su Gudidi amma ta ɓige da ba Hujayrah laƙanin bada magani, daman tun fil-azal tafi ƙaunar Baba Audu sama da su Babanmu,ai gashi yanzu ya makance ƙila ita ma d'iyar tashi mai idan mujiyar tana gab da makancewa"
"Da na ji dad'i kuwa" cewar Balki tana dariya
"Ku ta laƙani kuke,da kun ƙyaleta kun daina saka mata ido don abin duniya ya gama isarta yanzu ,kalla mu sa'aninta duk munyi aure mun hayayyafa amma ita ko mashinshini ta gagara samu,sai shegen iyayin zuwa boko,wallahi na ji dad'i da su Baba Zakari suka hanata kammala makarantar " cewar takusa da Balki
"Nima na ji dad'in hanata karantun da Baba yayi,ai sai muga yadda za ta yi,wallahi har islamiyar da take zuwa naso Baba ya hanata amma Kakulle ta ce babu wanda ya isa ya hanata zuwa karatun addini" cewar Harira tana k'ara gyara goyon yarinyarta
"Ya akayi kika sani?" Balki ta tambaya.
Sai da ta kai cincin bakinta tana taunawa sannan ta ce
"Ai ranar na taki sa'a ne,su Baba sun saka shegiyar a gaba suna mata fad'a akan bazaka sake zuwa boko ba,wanda tayi ya isa haka,sai na ma mama rad'a a kunne a kan ta cema Baba har da islamiyar ma a hanata, ai kuwa itama rad'an tayi ma Baba a kunne,sannan ya ce har da islamiya ta daina zuwa daga yanzu,to a nan ne Kakulle ta ce atafau babu wanda ya isa ya hana Hujayrah zuwa koyan addini, su Baba sunyi-sunyi su fahimtar da Kakulle amma tak'i fahimta, kuma ta ce tana akan bakan dole sai Hujayrah ta ci gaba da zuwa islamiya, haka suka k'yaleta,ni yanzu abinda yafi min dad'i rashin auranta,shegiyar dama ta dawamma a gidan tana bada maganin,mu kuma mu yi ta haihuwa abunmu"
Dariya suka tuntsire suna yi hankalinsu kwance,ba a fi mintuna ashirin da kammala hirarsu ba sai ga sallamar wata dattijuwar mata da wata budurwa 'yar kimanin shekara 22 a duniya sun shigo gidan,matan da suke aiki ne naga suna gaida dattijuwar,ita kuma budurwar ko kallon inda matan suke batayi ba ta ƙarasa cikin gidan,wani buhu ne cike da gayayyaki da sassaƙe-sassaƙen bishiyu a bisa kanta,sauke buhun tayi a ƙasa sannan ta nufi wani ɗaki daga cikin ɗakunan gidan ,ɗan madaidaici ne ɗakin,yasha fenti da sumintin ƙasa,gadaje biyu ne a cikin ɗakin,akwai gado mai rumfa sai karamin gado,a ta gefan ɗakin ɗan akwatin ƙarfe ne irin na da babba,a saman shi kuma Ghana-must-go ne ƴar k'arama.Wuri budurwar yarinyar ta samu a gefan ɗan k'aramin gadon ta zauna tare da cire hijabinta ta linki.
Dattijuwar matar ce ta shigo ɗakin da sallama,amsa mata budurwar tayi,sai dattijuwar ta ce
"Hujayrah bazaki je ki taya ƴan uwanki aikin biki ba,kinzo kuma kin zauna a nan kamar bakisan da bikin y'ar uwan naki ba"
Wacca aka kira da Hujayrah na kai dubana gareta,baƙa ce ko kuma in ce kwankan tarwatsa sannan baƙin nata zan ita cewa ba a cika samun irin kalar baƙin ba domin kuwa har wani irin sheƙi fatar jikinta take,kasancewar babu hijab a jikinta,sai a nan na ƙare mata kallo tsaf! Mace iya mace amma black beauty ,ba za a kirata da mai dogon hanci ba domin kuwa hancinsa bai da tsayi sosai,tana da round face ga kumatunta ma daidaita,gashin girarta haɗe yake wuri guda tare da bada shape ɗin V,sannan tana da zara-zaran gashin ido,wani abun ban mamaki shi ne,idanunta basuyi kama da idanun ƴan Nijeriya ba,domin ƙwayar idonta mai launin gore ne a turance ana kiransa da green eyes,farare ne idanunta tar! Gasu manya-manya,ba ƙarya dole a kirata da mai idon mujiya saboda girmansu musamman ƴan ƙauye wa'inda basu saba ganin masu kalar idanunta ba,ɗaiɗai ku ne a cikin mutane suke da irin kalar idanun Hujayrah.
Turo baki Hujayrah tayi tana cewa
"Kakulle ni kinsan ba daukar raini nake ba,yanzu nan za mu samu matsala da mutum,gwara tun kan a yi kar a fara,kin san halinsu da habaici ni kuma ba ɗauka zanyi ba"
Ƴar wata kujera Kakulle ta ɗauko daga ƙarƙashin gado mai rumfa tare da zama tana cewa
"Yanzu haka zaki gansu suna aiki bazaki tayasu ba,kin kyauta kenan "
"Ya Salam! Ni fa na faɗa miki babu inda zani,ina gama hutawa zan wuce sashensu Mammi na tayata aiki,sannan musha hira da Abbuna "
Shiru Kakulle tayi tana kallon Hujayrah tare da tuno abinda Hujayrah tayi a dauji duk da mahaifiyarta tasha fad'a mata abubuwan da Hujayrah take yi,sai da ta gane ma idanunta, sannan tabbas akwai abubuwan ban al'ajabi a tattare da jikarta masu ban mamaki.Musamman gane-ganan da take yi.
*Waiwaye*
A lokacin da suke tsaka da tafiya cikin dauji bayan sun samu sak'e-sak'in itatuwa da gayayyaki a wani b'angare na cikin dauji sai suka nufi wani sashen don sake samun gayayyakin, Hujayrah na gaba da buhu a bisa kanta,ita kuma Kakulle na biye da ita suna hira,suna cikin tafiya sai Hujayrah ta tsaya cak! tana kallon wuri ďaya tare da kai hannunta saman k'irjinta,ganin Hujayrah ta tsaya sai Kakulle takai dubanta ga inda Hujayrah ke kallo,dutse ne ďan babba, cike da mamaki Kakulle ta ce
"Hujayrah lafiya kika tsaya tare da tsirama dutsen idanu"
Hujayrah ba tare da tabar kallon dutsen ba ta ce
"Kakulle an binne sihiri a k'asan dutsen nan"
Cike da mamaki Kakulle ta ce
"Ban gane an binne sihiri ba"
Hujayrah ba tare da ta amsa ma Kakulle tambayarta ba,ta sauke buhun da ke bisa kanta wanda akwai gayayyaki a ciki da sassaƙe-sassaƙen bishiyu har da sauyar k'asa amma ba da yawa ba,ciro adda tayi daga cikin buhun,sai tayi k'ok'arin matsar da dutsen amma ta kasa saboda girmansa , duban Kakulle tayi wacca baki sake tana kallon ikon Allah,ce mata tayi
"Kakulle ďan tayani matsar da dutsen nan"
Dafe k'irji Kakulle tayi tana cewa
"Waaa! Ni Hindatu! Tab! Allah ya sawwake,ina zaman-zamana kisa kwankwasona ya tsage na mutu! "
Dariya maganar taba Hujayrah 'wai kwankwasonta ya tsage ta mutu' Kakulle akwai tsoron mutuwa,sai da Hujayrah tayi dariya ma'isarta sannan ta tsagaita tana duban kakarta ta ce
"Haba Kakulle yanzu wannan dutsen ne zaisa kwankwasonki ya tsage har ki mutu,O'o ni Hujayrah ďiyar Audu jikar Kamalu Angon Hindatu mai tsoron mutuwa"
Dariya ta sake b'arkewa tana yi,cikin fushi Kakulle ta ce
"Kinga idan dariya kika zo yi, ni tafiyata zanyi"
Da sauri Hujayrah ta ce
"Ba à yi haka ba Kakulleta ,na ji zan matsar da dutsen da kaina,taimako ne zanyi domin bansan wani irin k'ulli da mugunta aka ma bayin Allah ba"
Tana maganar tana matsar da dutsen kaďan kaďan har Allah ya bata ikon matsar da dutsen, kallon da zata yi sai ta ga babu komai a wurin.A wannan karon Kakulle ce ta ke ce da dariya tana mata Allah ya k'ara,ďan ďagowa Hujayrah tayi tana kallon Kakulle sai ta ce
"Kakulle kenan a tunaninki wahalar banza na yi ko? "
"Sosai ma kuwa Hujayrah, har da kinaso na biye miki kwankwasona ya samu matsala,ki sakani neman magani "
Murmushi mai sauti Hujayrah tayi sannan ta ce
"Komai a rayuwar nan ana yinsa da lissafi ne,mutanan da suka binne sihirin nan ba shashashu ba ne da za su kawai ďaga dutse su binne kayan tsubbunsu, sunyi amfana da k'wak'walwarsu ne ta hanyar ďaga dutsen sannan suka hak'a rami sai suka binne sihirin, kuma bara ki gani"
Bata jira mai Kakulle zata ce ba,ta fara hak'ar wurin da take tunanin sihirin yake,sosai take hak'a, ita ko Kakulle kamar wacca aka daskarar ta tsaya tana kallon ikon Allah,cikin ikon Allah bayan wasu y'an mintuna sai Hujayrah ta tsaya daga hak'ar da take,gyara hijab ďinta tayi sannan ta nannaďe hannun rigarta kar tab'o ya b'ata mata kaya ,hannunta tasa cikin ramin a hankali ta ciro wata kwalba fara wacca duk tab'o ta baibaye kwalbar, Mik'ewa Hujayrah tayi daga duk'yen da take tana nunama Kakulle wacca ta saki baki tana kallon ikon Allah,a zuciyarta tana cewa 'Maganarki Zaituna(mahaifiyar Hujayrah ) ta tabbata, kenan Allah ya bata baiwar ganin wasu abubuwan da mu bama iya gani,ashe.....' bata k'arasa zancen zucinta ba Hujayrah ta Katse ta da cewa
"Kin gani Kakulle, ai na faɗa miki an binne sihiri a wurin nan baki yarda ba,to yanzu ba gashi ba"
"Yanzu kam na yarda na shaida, ashe dai maganar Zaituna na kam hanya,ta ce min kina gane-gane tun kina k'amarki har mugayen mutane da mayu kina gane su"
Murmushi Hujayrah tayi har dimple ďinta yana lotsawa ta ce
"Kakulle nima bansan ya aka yi nake gane-gane ba ko kuma gane mugayen mutane da mayu,sai dai idan na kalli mutum ko kuma na gitta wani wuri sai na ji zuciyata ta bada Dummmmm!!! wanda ni na rasa dalilin hakan, idan misali wuri ne na wuce na ji hakan to kenan akwai k'ulalla a wurin ma'ana akwai wani sihiri a wurin,idan kuma mutum ne na gani zuciyata ta buga da mugun k'arfi wanda ban cika ji ba,to hakan yana nuni da abu biyu ne;ko dai mugu ne mutumin ko kuma maye ne"
Shiru Kakulle tayi tana kallonta ba tare da iya cewa komai ba,sai can kuma kamar an tsikareta cikin muryar tsufa ta ce
"Yanzu Hujayrah ya za ki yi da wannan kwalbar da kika ciro"
"Fasa shegiya zanyi yanzun nan naga uwar me ta k'unsa ciki"
Ďaga kwalbar tayi sama sannan ta karanto Bismillah, Falak'i, nasi da k'uhuwallahu ahad sau uku-uku sannan ta rotse kwalbar a k'asa ji kake ta ba da Tusss!!! A k'asa,nan take laya mai launin ja ta bayyana, a nan ma sai da Hujayrah ta karanto addu'o'i sannan ta ďauki layar da Bismillahir-rahmani-rahim, ita dai Kakulle babu bakin magana sai kallo domin abun ya wuce tunanin k'wak'walwarta da lissafinta, tabbas ba sau ďaya ba sau biyu ba Mammin Hujayrah na sanar mata da abubuwan da Hujayrah take gani amma bata gasgata hakan ba sai yanzu da abin ke faruwa a idonta kamar a mafarki.Buďe layar Hujayrah tayi a hankali bakinta na ďauke da addu'a,layar matsakaiciya ce wanda aka nannaďe ta da bak'in zare, bayan ta warware zaren sai ta buɗe layar nan ma da bismillah, sai a lokacin Kakulle ta k'ara matsowa kusa da Hujayrah don ganin me layar ta k'unsa,gashi ne da farce aka nannaďe su da farin zare sai wasu abubuwan da ni mai ďaukar rahoto na k'asa gane mene ne balle na sanar muku,sai wata ýar takarda mai ďauke da rubutu kamar larabci amma kuma ba larabci bane kuma rubutun kamar da jini aka yi.
Kallon Kakulle Hujayrah tayi sannan ta ce
"Kinga mugunta ko Kakulle, gashi da farcen wata ko wani a kayi amfani dashi don cutar dashi,ke duniya ina zaki damu, shiyasa fa Kakulle bana yarda da mutane,ana ganin na cika matsifa da rashin son mutane,duk saboda ire-iren haka ne nake gudu"
"Haka ne Hujayrah ni nama rasa abin faɗa, domin kinsan k'wak'walwarmu ta tsofaffi ba iya ďaukar ire-iren abubuwan take ba,Allah ka Karemu daga sharrin masheranta"
"Ameen ya Allah, bara kiga tattarasu zanyi na k'ona idan mun je gida, nasan in shaa Allah duk wanda aka ma sihirin zai warware "
"Hakan yafi, amma karki bari mutane su san da wannan b'oyayyar baiwar taki Hujayrah "
Dariya Hujayrah maganar ta bata sai ta ce
"Baki da case in ji turawa duk da kun k'i barina na shiga SSS class da nima na gama secondary,amma ba damuwa nasan wata ran zanyi bokon "
"A lahira ko"
"A duniyar nan kuwa, muna nan da ke,sai dai kuma idan kin mut....."
Bata k'arasa maganar da take da niyyar fad'a ba Kakulle katseta da cewa
"In shaa maka Allah ina nan daram! Abuna, sai dai ke ki mutun bani ba"
"Kai Kakulle wannan tsoro haka, bafa kiji mai zance a k'arshe ba "
"Ummm ni Kinga tafiya ta,na fara jin yunwa gashi bamu kammala aikin da ya kawo mu ba, kin b'ata mana lokaci "
Hujayrah na biye da ita ta ce
"Taimako ne nayi ai Kakulle "
bata mai da mata da maganar ba ta duk'a aikin ciro shukokin da tasan magani ne,ita ma Hujayrah duk'awa tayi tana tayata aikin,wanda ya zama musu jiki duk bayan ýan wasu kwanaki suna zuwa dauji ciro gayayyaki da sassaƙe-sassaƙen bishiyu don bada magani wa mutane irin ciwon Sanyi,masassara,tafiyar ruwa na yara,ciwon daji,maganin kambun baka,har da gyaran k'ashi suna yi ita da Kakulle domin bayan makantar da mahaifinta ya samu,sai Kakulle ta zab'eta a matsayin wacca zata gajeta wurin bada magani tunda mahaifinta Allah ya jarabceshi da makanta,lak'ani ne wanda Kakulle taba mahaifin Hujayrah kasancewar baya gani yanzu yasa taba Hujayrah lak'anin ganin tafi kowa cancanta duk a cikin jikokinta da yaranta , bayan haka ga b'oyayyar baiwar da Allah ya bata na musamman. Wannan kenan.
*Cikin labari*
Suna zaune shiru sai suka tsinkayi sallamar Salim ɗakin.Amsa masa Kakulle tayi don ita Hujayrah ƴan shirun na kai,shigowa ɗakin yayi tare da gaishar da Kakulle, cike da kulawa take amsa masa,Salim duban Hujayrah yayi tare da cewa
"Yaya, Abbu na nemanki yanzu sannan ya ce ki hato masa da maganin ciwon kai"
Ai da sauri Hujayrah ta dube shi da cewa
"Abbu ne maida Lafiya Salim?"
"Eh Yaya ai tun safe da kuka fita dauji ke da Kakulle ya fara ciwon kai,ganin babu wanda yasan maganin da ya dace yasha daga ke sai Kakulle,shi kuma ba iya tan-tan ce launin maganin zai iya ba,shiyasa kawai aka jira ku dawo"
Ai da sauri da miƙe zuwa wurin gado mai rumfa,duƙawa tayi ta ciro wata kwalla ƴar babba,cike kwallar take da kullun magani kala-kala,ɗauka tayi ɗaya bayan ɗaya tana dubawa,ita kuma Kakulle tana kallon yadda take duba kulle-kullen magani cike da ƙwarewa,a zuciyarta tana cewa 'Tabbas kece maya gurbina Hujayrah, domin haka na taso kamarki ina taya Babana bada magani' suna a haka,Hujayrah ta ɗauko wani ƙullin magani ta miƙama Salim sai ta ce............
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
***
002🔥
"Salim riƙe maganin nan bara na baida kwallar mu tafi,ai zama bai ganni ba,daman hutawa nake kafin na wuce sashenku"
Tana maganar lokaci guda tana tura kwallar ƙarƙashin gadon,miƙewa tayi tare da cewa
"Kakulle bara naje sashen su Mammi na duba Abbu,anjima sai mu gyara magungunan ko"
"To kiyi mishi sannu anjima zan shigo dubashi"
"To Kakulle"
Fita suka yi daga ɗakin,Hujayrah na gaba Salim na biye da ita,ta inda ƴan uwanta suke aikin cincin na biki ta wuce ba tare da ta kalli gefansu ba ,su kuma da kallo suka bi ta,wasu na taɓe baki wasu na mata dariya wai tayi kwantai babu mashinshini,haka ta wucesu zuwa n ɓangaren mahaifanta,duk a gidan shi ne mafi muni domin ginin ƙasa ne bana bulo ba irin na sauran gidan gashi ko simintin ƙasa babu balle flasta da fenti,ƴar katanga ce wacca ta yi shamaki da sauran b'angarorin gidan sai ƙofar katako a tsakiya,direct Hujayrah ta buɗe ƙofar tare da sallama ta shiga ciki Salim na biye da ita.Wata mata ce tana fiffita wutar murhu ta amsa mata sallama.
"Mammi barka da rana,ya jikin Abbu, Salim ya ce tun safe da muka tafi dauji yake fama da ciwon kai"
Wacca aka kira da Mammi na kai dubana gareta,suna ɗan kamanni da Hujayrah a fizge,amma ita Mammi fara ce ba kamar Hujayrah ba,shima Salim fari ne kamar Mammi, amsa mata tayi da cewa
"Da sauƙi,ki shiga ciki ki dubashi,nima gani nan shigowa ciki da na d'aura ruwan wankan auta"
Haka ta fad'a sai ta ci gaba da fiffita wutar murhun saboda iccen yaƙi kamawa kasancewar lokacin damuna ne.Da sallama Hujayrah ta shiga ɗakin,lokacin Abbu na zaune a bisa tabarmar kaba,amsa mata yayi cike da kulawa amma muryarsa a can maƙoshi.Zama tayi kusa dashi sai ta amsa ƙullin magani daga hannun Salim tana cewa
"Abbuna ya jikin?,ni da Kakulle muna dauji tun safe,bamu daɗe da dawowa ba,ashe tun safe kake fama da ciwon kai Abbu? "
Jinjina mata kai yayi sai ya ce
"Eh Hujayrah amma ciwon kan ya ɗan lafamin yanzu,kinsan ba gani nake yanzu ba,da sai na binciko maganin da kaina"
"Ai gashi na zo maka da maganin"
Tana maganar tana kwance ƙullin,babban yatsarta da wacca take kusa da manuniya ta ɗan ɗibo maganin kaɗan sai ta goga mai a ƙasan hancinsa,ai nan take,ya fara jero atishawa babu ƙakƙautawa,ji kake Aaatttijinn! Aaatttijinn! ,ƙulle maganin tayi,sai ta ce
"In shaa Allah zaka samu sauƙi da yardar Allah,amma dai yau bazaka fita waje ba koh Abbuna,ina nan kusa da kai,muyita hira abunmu"
Murmushi yayi mai sauti tare da ƙara jin so da ƙaunar ɗiyarsa,ce mata yayi
"Tunda bakya son in fita na haƙura,sai kibani labari mai daɗi"
"Yawwa Abbuna shiyasa nake sonta fiye da........"
"Fiye da wa?" cewar Mammi wacca yanzu ta shigo ɗakin bayan ta gyara wutar murhun sai ta tsinkayi maganar Hujayrah ta ƙarshe wacca tasan da ita take.Manyan-manyan idanunta ta fara wiri-wiri dasu alamun mara gaskiya,cikin inda-inda ta fara magana
"Uhmm uhmmm daman Mammi,kawai dai na ce ne fa........"
"Eh dole kifi sonshi sama dani mana Hujayrah,ba yana biyewa shirmanki ba,Ai dole ki ce haka"
Dariya sosai Abbu ya tintsire yana yi,Salim ma na taya Abbu dariya ,wannan ba sabon abu bane ga wannan ahalin,musamman Hujayrah da Mamminta, basu cika jituwa ba, kasancewar Hujayrah akwai ta da da banzan surutu,neman magana,shiga sharu ba shanu yasa basa shiri da mahaifiyarta,tafi son Mahaifinta saboda yana biye mata suyi ta labari,ko kuma shige mata faɗa,tun tana ƙaramarta Hujayrah take da neman faɗa da surutu,ga shegen ƙarfi kamar namiji,duk girman budurwa Hujayrah na tsayawa tayi dembe da ita,ko tasha wuya haka za ta tayi ta nacewa har sai tayi galaba sannan take haƙura,koda kuwa ba a lokacin ba ne,amma tana nan rik'e da mutum har sai ta rama sannan hankalinta ke kwanciya,ko ƴan matan gidan sa'anninta kafin suyi aure tsoranta suke saboda ta fisu masifa da ƙarfi,shiyasa ko gulmarta ake da ta tun karo wurin za ka ji kowa yayi tsit! Tsoron karta balbalesu da faɗa, Saboda ire-iren wa'innan halayen Hujayrah yasa basu cika shiri da Mamminta ba,kullum cikin nusar da ita take akan ita mace ce,irin wa'innan halayen da maza aka sansu dashi ba mata ba,har misali take mata akan ƙaninta Salim,babu ruwansa da neman faɗa balle surutu ko kuma faɗa amma sai ita mace.
Wuri Mammi ta samu kusa da Abbu ta zauna tare da cilla ma Hujayrah wata uwar harara,da sauri Hujayrah tayi ƙasa da kanta tana turo baki.Mammi ce bayan ta zauna ta ce ma Hujayrah
"Miye na bin Kakulle dauji bayan kinsan an fara aikace-aikacan biki a gidan"
Kumburo fuska Hujayrah tayi don ita komai za a ce mata babu abinda zai sa ta je aikin biki,bata ɗaukar wulaƙanci balle raini,su kuma halinsu ne kamar gado.Jin shirun Hujayrah Mammi ta sake jefo mata tambayar wannan karon a zafafe tayi maganar da cewa
"Kurma ce ke! Ina tambayar amma kinyi kunnan uwar shegu dani! "
"Mammi kema kinsan halinsu ba jituwa za muyi ba,koda naje aikin bikin habaice-habaice za su yi ta saki,ni kuma kinsan ba ɗauka zanyi ba,shiyasa kawai nace bazani ba,ko Kakulle ta tambayeni meya hanani zuwa ita ma na sanar mata dalilin rashin zuwa na"
"Dole sai kin tanka musu,kiyi aikinki kawai,kin manta sai an kula kashi ke ɗoyi haka-zalika sai an kula karuwa ke yanga,koda nima iyayen ba ƙyaleni su ka yi ba,suna sakarmin habaici,amma tun tasowarki kin taɓa jin faɗana dasu,kin taɓa jin ina tanka musu,manna musu hauka nake inyi kunnan uwar shegu dasu don a zauna lafiya,amma ke kullum sai an ce ga abinda kika yi,ke baki jin tsoran bakin mutane nHujayrah"
Shiru Hujayrah tayi tana sauraron Mamminta, ita ba mai jayayya ba ce ko kuma musu idan Mamminta na mata faɗa,a zahiri tana sauraron abinda Mamminta take faɗa mata amma a baɗini duniyar tunani ta lula,a zuciyarta tana cewa 'Mammina ke ta daban ce a rayuwa ba kowa zai iya haƙurinki ba,musamman kalar rayuwar da kike yi da shegun matan gidan nan munafuka,wa'inda mazajensu suka ɗaure muku gindi suke miki iskanci,kowa ina kallonsa ne,ranar da zan kwance musu biri har wutsiya yana gab da zuwa,sai dai su Baba Zubairi su kasheni.....' Katse mata tunanin Mammi tayi da cewa
"Ai nasani,a haka kamar kina saurare na,amma kina fita kuma za ki kakkaɓe nasihata ki jefar"
Sai yanzu Abbu yake da niyyar tofa albarkacin bakinsa a maganar tasu,yana cewa
"Haba Zaituna kibar Hujayrah ta huta mana,ke kullum cikin mata faɗa kike akan wa'inda ba darajarki suka sani ba"
"Hakane Abbu" Cewar Salim don shima abubuwan da ƴan gidansu suke ma iyayensa baya masa daɗi a rai kamar ba ƴan uwansu ba,saboda sunga Mahaifinsu Allah ya jarabceshi da makanta shi ne suke wulaƙantasu musamman matan gidan.Salim yafi Hujayrah haƙuri da daɗin zama da mutane kamar mahaifiyarsu,ita ko Hujayrah bata barin ko ta kwana *sha yanzu magani yanzu ne* .
Suna cikin hira suka ji sallamar Kakulle,da fara'ah suka amsa mata sallamar,ciki ta shigo ta zauna,Mammi ce ta gaidata cike da girmamawa,murmushi a fuskar Kakulle take amsa mata,don duk a cikin sirikanta tafi son Mammin Hujayrah saboda girmamawar da take bata.
Bayan ta zauna ta ce
"Audu ya jikin,Salimu ya ce tun safe kana fama da ciwon kai"
"Eh Inna naji sauƙi sosai"
"To Allah ya ƙara afuwa Audu"
"Ameen Ameen Inna"
Hira suka ci gaba dayi har autan Mammi ya shigo daƙin da sallama,wurin Mamminsa ya zauna yana cewa
"Mammi zan ci abinci"
"Har kun tashi daga makaranta Haroon" cewar Hujayrah
"Eh yaya,yau da wuri aka tashe mu"
"Je ka cira kayanka tukunna"
"To yaya"
"Maza ka jire kayanka Autana abincinka na jiranka,ina sauke girkin kaine farkon wanda na fara zubama abincin, har ruwan wanka na d'ora maka,maza je ka sauya kaya"
Da sauri ya miƙe zuwa uwar ɗaka,su kuma suka ci gaba da hirarsu har da Kakulle.
🌍🌍🌍🌍🌍🌍🌍🌍
A wani b'angare na gidan wanda yafi kowani b'angare kyau da had'uwa,sautin magana na ji har da yana fitowa daga b'angaren,shiga nayi don jin wace waina ake toyawa,ciki na shiga har inda najiyo sautin muryar mutanan,mata da miji ne suna zaune a bisa tank'ameman gadonsu na alfarma,dukkaninsu sun manyanta amma baza a ce tsofaffi bane sosai,mijin na gaban gadon ita kuma matar tana zaune a gefan gadon suna hira,cikin hira matar da shigo da wani sabon zance wanda bashi suke tattaunawa ba,gyaran murya tayi har da lank'wasa murya irin na mata masu kissa ta ce
"Alhaji wai ku haka zaku zauna a matsayinku na Babanin Hujayrah kuna kallon duk ƴan uwanta sunyi aure amma ita sai iskanci take a gari" cewar Hannatu
Wanda aka kira da Alhaji ya saki wani munafikin murmushi sannan ya ce
"Me kike ci na baka na zuba Hannatuwata,hmmm! akwai wani babban shiri da nake akan Hujayrah tun satowarta, ana kallama biki zan bijiro da nawa maganar,kuma dole abi shawarata ko anƙi ko anso,sha kuruminki Hannatuwata ai Hujayrah na gab da barin gidan nan,ke bama gidan nan ba garin ma baki ɗaya"
Wani irin daɗi Hannatu taji a ranta jin mai idon mujiya ta kusa barin garin dama ita ce take hanata rawar gaban hantsi domin indai ta binne abubuwan sirkullanta sai Hujayrah ta tono kamar wata aljana,cike da farin ciki ta ce
"Mai gidana abin alfaharina,wani shiri ne haka kake yi akan shegiyar yarinyar nan"
"Sirri ne Hannatu, ba sai kin ce wani abu ba,ana kammala biki za ki ji komai,nasan har ruwa a ƙasa za ki zuba a ki sha"
"Sosai ma kuwa Alhajina,don yarinyar nan da addabi kowa a gidan nan,ba yaran ba bamu ba kowa ta hanashi rawar gaban hantsi,ai gwara tabar garin,shike nan mun yada ƙwallon mangoro mun huta da ƙuda"
"Baki da kirki Hannatuwata "
Yana maganar yana dariya, ita ma dariya tayi,sai suka ci gaba da hirarsu hankali kwance.
🌍🌍🌍🌍🌍🌍🌍🌍🌍🌍
Wasa-wasa har anyi bikin y'an uwan Hujayrah,duk sha'anin da ake yi Hujayrah bata shiga ciki ba,tana tare da Abbunta suna hira,Mamminta tayi fad'an akan rashin shigarta sha'anin bikin amma ta gaji ta hak'ura tare da zuba mata ido.
Bayan biki da kwana hud'u Alhaji Zakari ya bijiro da maganar dole Hujayrah tayi aure saboda kusan duk sa'aninta da k'ananta sunyi aure,kamar jira sauran y'an uwan mahaifanta suke,haka suka zafafa da magana.
Meeting suka had'a saboda wannan maganar,duk wani taro a sashen Alhaji Zakari ake yi kasancewar shi ne babba a gidan.Falon ya cika da y'an uwan mahaifin Hujayrah, Kakulle,Baba Zubairu da matarsa,matar Baba Musa kasancewar bai cika zama a garin ba yam ma haka yana Zaria wurin sana'arsa,Abbun Hujayrah da Mamminta,sai sauran y'an uwansu mata guda biyu,Attine da Larai,shi kansa Alhaji Zakari da matarsa Hannatu suna zaune suma.Uwar gayya Hujayrah tana zaune a tsakiyar falon gabanta sai fad'uwa yake,tana tunanin wani k'ulalla ake shirin k'ulla mata.
Alhaji Zakari ne ya dubi kowa sannan yayi gyaran murya ya ce
"Tunda kowa ya hallara sai muje kai tsaye ga mak'asudin abinda ya tara mu a nan,Ke Hujayrah! "
Dummmmm! Haka k'irjin Hujayrah ya bada jin an kirata a kakkausar murya,cikin rawar murya Hujayrah ta amsa da
"Nnna'ammm"
Gyara zama Alhaji Zakari yayi sannan ya ce
"Ba Wasa muka zo yi a nan ba,sannan karki kuskura kiyi mana yawo da hankali,abinda ya taramu a nan ba komai bane illa, maganar auranki,shin kina da saurayi wanda yake da niyyar auranki, ko kuma har yanzu babu"
Ras! Ras! Ras! Tashi hankali wanda ba a sa mai rana, ita ina ta ga wani saurayi wanda yake da niyyar auranta,Yooo tunda take babu wani saurayi a garin nan da ya tab'a furta maka kalmar so balle maganar aure, ita ta rasa dalilin haka,bata san wani irin bak'in jini take dashi ba.
"Dake fa muke Hujayrah!!! "
Da k'arfi yayi maganar, firgigit kamar wacca aka tsikara ta dawo cikin hayyacinta, cikin inda-inda Hujayrah ta fara magana
"Ummm Ummm ni ni babu kowa"
Wani munafikin murmushi Alhaji Zakari ya sake wanda ba kowa ya fahimci murmushi yake ba sai Mammin Hujayrah wacca tun da suka zo hankalinta ke kansa domin tun lokacin da Hujayrah ta fara girma take ce mata Baba Zakari mugu ne, gabanta mugun fad'uwa yake idan ta gansa,tun bada yarda har ta fara gasgata maganar Hujayrah musamman yau d'in nan da ya saki munafikin murmushi dan kawai ta ce bata da saurayi.Shi kuma Alhaji Zakari ya ji dad'in haka ,a ranta yana cewa 'An zo gab'ar,daman nasan bazaki taba samu mai auranki ba' k'ara gyaran murya yayi sannan ya ce
"Shin a cikinku akwai wanda zai tofa albarkacin bakinsa"
Girgiza kai kowa yayi,don su basu san mai za su ce a game da wannan al'amari ba.Abbu da Mammi babu wanda a cikinsu yake da niyyar cewa wani abu ba,musamman Abbu wanda yanzu ta kansa yake,shi ba gani yake ba sannan ya yarda da y'an uwansu akan duk abinda zasu zartar ga yaranta, in ma hukunta su ne ko kuma gyara musu tarbiyya da dai sauransu,a wurin Mammi dalilin rashin maganarta shi ne tozarta y'arta suke da niyyar yi,sannan wannan taron akwai wata a k'asa don da alamu Alhaji Zakari yana da abinda yake k'ullawa a kan Hujayrah saboda tun ba yau ba take ganin take-takensa amma babu komai Allah na nan,shi suka dogara domin *BASU DA WATA MADOGARA SAI ALLAH*
Ganin kowa bai da abin fad'a sai Alhaji Zakari ya ce
"To tunda babu mai abin fad'a,sannan ita kuma bata da wanda zai aureta,ni yanzu ina da wanda ya ce yana sonta kuma zai aureta tsakaninsa da Allah,to amma shawara ce fa,ganin kar tayi ta zama a gida ga y'an uwanta da k'annanta duk sunyi aure,yasa na zo da wannan shawarar"
Dummmmmmm! K'irjin Hujayrah ya buga,a zuciyarta tana cewa 'Aure? Aure? Akwai wanda yake da niyyar aurana kuma tsakani da Allah ta hannun Baba Zakari wanda duk lokacin da na gansa sai k'irjina yayi mugun bugawa,hmmm daman na sani akwai muguntar da kake shirin aikata min,*Bani da madogara sai Allah* domin shi zai tsareni daga sharrinka' Abbu ne ya fara magana cike da farin cikin y'ar shi itama za tayi aure kamar sauran yaran gidan(Allah Sarki Abbu kaban tausayi babu ruwanka, kana zaune da y'an uwanka da zuciya d'aya )
cewa yayi
"Alhamdulillah ai wannan shawara ce mai kyau,na baka wuk'a da nama kayi yadda kake so,domin Hujayrah kamar y'a take a wurinka,komai ka yanke a kanta ni bani da jayayya akai"
Wani k'asaitacce kuma munafikin murmushi Alhaji Zakari ya sake, ya ji dad'in bashi wuk'a da naman da Audu yayi,daman shi Audu bai da matsala ko kuma jayayya tun lokacin da yake gani balle yanzu da makanta ta sameshi, da dai Musa na nan ne shi ne zai iya kawo masa tangard'a a plans d'in,ba ta Zubairu ake ba don kusan tafiyarsu d'aya ce banbancin ka'dan ne Don kowa yasan sirrin d'an uwansa,a zuciyarsa yana cewa 'ashe kuwa zan yanka naman filla-filla na ware k'ashi da tsoka' ,cike da dumbin farin ciki Alhaji Zakari ya ce
"To babu damuwa Audu daman ba kowa bane wanda yake son Hujayrah da aure illa Alhaji Sambo Dala,kuma a shirye yake,ya ce ba sai anyi mata kayan d'aki ba don ana d'aura aure washe gari zai tafi da amaryarsa Katsina inda yake da zama tare da iyalansa "
Daram!!! Dam!!! Dadammmmmm! !! Haka zuciyar Hujayrah ta bada,fashewa tayi da matsanancin kuka mai ratsa k'ashi da b'argon duk mai sauraranta, cikin kuka ta fara magana da cewa
"Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un!!! Na shiga uku na lalace ni Hujayrah yanzu a rasa wanda za a had'ani dashi sai da........................"
*Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️*
***