BA NI DA MADOGARAFree

ArewaPen original

AdventureFreeOngoing

BA NI DA MADOGARA

  • 1views
  • 1chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

Sample · Chapter 1

*_The Amazing Pen_ ✍️...**Bani da Madogara*  (Sai Allah...)001*Kwanar faru k'wai Kaduna State,Nigeria*•••••••••••••••••Gida ne babba mai kyau da tsari daidai gwargwado,idan kaga gidan baza kayi tunanin a k'auye a kayi ginin ba.Mata ne zaune a saman bencina tuna murza flawa,wasu kuma na yanka kwab'abb'an flawan k'ananu,wasu bangeren matan  na tuyar cincin ,kowacce kana ganinta kaga ƴar k'auye  saboda shigar da ke a jikinsu ba wata shigar kirki bace,riga daban ɗan-kwali daban haka suketa faman aikin tuya.Wata ce a cikinsu ta dubi ƴar uwarta ta ce"Wai in tambayeki Harira"Wacca aka kira da Harira ta ce"Ina sauraranki Balki" Balki ta ɗan nisa sannan ta ce"Wai ina Hujayrah mai idon mujiya take ne,naga tun da aka fara shirye-shiryan bikinsu Maryamu  bana ganinta"Taɓe baki Harira tayi sannan ta ce"Yooo ke kuwa Balki ina zaki ga mai idan mujiya,baƙin hali ya hanata kataɓus! Bata nan bata can,ita ce bin Kakulle dauji samun saiwar ƙasa da  gayayyaki na magunguna,ita ga mai bada magani Mtws! ""Wai da gaske Kakulle Hujayrah mai idan mujiya taba laƙanin magani yanzu,bayan Baba Audu ya makance? "Gyara zama Harira ta yi don ta ji daɗin ba da labarin da kyau ta ce"Hmmmm ke dai bari,na ji takaicin hakan wallahi,maimakon Kakulle taba Babana ko su Baba Zubairu,Baba Musa ko kuma ƴaƴanta mata kamar su Gudidi amma ta ɓige da ba Hujayrah laƙanin bada magani, daman tun fil-azal tafi ƙaunar Baba Audu sama da su Babanmu,ai gashi yanzu ya makance ƙila ita ma d'iyar tashi mai idan mujiyar tana gab da makancewa""Da na ji dad'i kuwa" cewar Balki tana dariya "Ku ta laƙani kuke,da kun ƙyaleta kun daina saka mata ido don abin duniya ya gama isarta yanzu ,kalla mu sa'aninta duk munyi aure mun hayayyafa amma ita ko mashinshini ta gagara samu,sai shegen iyayin zuwa boko,wallahi na ji dad'i da su Baba Zakari suka  hanata kammala makarantar " cewar takusa da Balki"Nima na ji dad'in hanata karantun da Baba yayi,ai sai muga yadda za ta yi,wallahi har islamiyar da take zuwa naso Baba ya hanata amma Kakulle ta ce babu wanda ya isa ya hanata zuwa karatun addini" cewar Harira tana k'ara gyara goyon yarinyarta"Ya akayi kika sani?"  Balki ta tambaya.Sai da ta kai cincin bakinta tana taunawa sannan ta ce"Ai ranar na taki sa'a ne,su Baba sun saka shegiyar a gaba suna mata fad'a akan bazaka sake zuwa boko ba,wanda tayi ya isa haka,sai na ma mama rad'a a kunne a kan ta cema Baba har da islamiyar ma a hanata, ai kuwa itama  rad'an tayi ma Baba a kunne,sannan ya ce har da islamiya ta daina zuwa daga yanzu,to a nan ne Kakulle ta ce atafau babu wanda ya isa ya hana Hujayrah zuwa koyan addini, su Baba sunyi-sunyi su fahimtar da Kakulle amma tak'i fahimta, kuma ta ce tana akan bakan dole sai Hujayrah ta ci gaba da zuwa islamiya, haka suka k'yaleta,ni yanzu ...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters1
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play