RU'UYAA (The dreams we never lived)

36. ...na dena son shi...🖊️

by @autum17

                 






Jingine Roman yake da bango a hallway ya lumshe ido, hannunshi daga gefen shi sunyi fari shaking slightly by his side,ga wani layin zufa daya wanke gaban goshin shi numfashin sa na fita sama sama kamar akwai wani abu daya doɗe hanyar numfashin memories ɗin baya na yawo a kanshi


____

Ƙaramin Roman ne kwance a ƙasa ya damƙe cikin shi yana juyi kamar zai mutu yayi tsamo tsamo da zufa,sai ihu yake amma babu wanda yaxo dan ya cece shi..idonshi sai lumshewa suke kamar wanda rayuwa ta fara barin jikinsa ga wata na fita daga bakin shi numfashin sana fita sama sama daidai nan aka banjo ƙofar..

___

'' Sir! Sir!" Firgit Roman ya buɗe idon shi da suka yi ja kamar gauta ya sauke su akan Leonardo

'' yarinyar ta tashi...'' ya faɗa da Italian haɗe da ja baya Roman yayi gaba yana biye dashi,tsayawa yayi ya juyo ya kalli Leonardo '' you can wait in the car..." 


Ina zaune likitar tasa ni agaba da tambayoyi kamar yar jarida Roman ya shigo ɗakin idon mu ya haɗu dai dai likitar na faɗin

 '' idan mace na al'ada ta guji shan abubuwan sanyi da zaƙi,sannan ta dinga sauya pad akai akai harda pant dan akwai masu yini da ƙwaya ɗaya...''

Ji nayi kamar ƙasa ta haɗiye ni,likitar ta juya ta cigaba da magana dashi ni kuma ina ƙara nutsewa cikin kunya,yanzu sai ya dinga tunanin ni ƙazama ce bana canja pant. haɗe hannayena nayi wuri guda ina wasa da yatsuna, likitar ta fita tabar mu biyu kawai naji ɗakin ya matse duk da faɗin da yake dashi sau ɗaya ya kalleni ya ɗauke ido.

Ya zauna yana latsa wayarshi ko irin sannu ya jikinki baiyi min ba...kai wannan mutumin...taya akai na kamu da son mutum irin wannan ba Khalil ba?


'' yanzu ko sannu baza ka iya yimin ba?" nayi maganar da turo baki.. batareda ya kalle ni ba yace '' you seem fine... I'm not blind!'' 


saukowa nayi daga saman gadon na matso kusa dashi..na duƙa kaɗan ina leƙo fuskar shi duk da yanda ƙasa na ke ciwo

'' Laaa blushing kake...kalla kunnen ka yayi ja!" Na faɗa ina taɓa kunnenshi...da babu wani jan da yayi..share min hannu yayi

 '' dama na sani lafiyar ki lau,ke...'' nake kallonshi da dariya a fuskata ina jiran ya ƙarasa sentence ɗin,sai naga yayi gefe da fuskarshi data yi ja kamar tumatur yana zarar ido

Dariya na farayi har da riƙe ciki sai kuma na fahimci dalilin dayasa,huh!!! ƙasa nayi da idona suka sauka akan gaban rigata da yayo gaba har ana ganin pink singlet ɗin dana sa da kuma saman ƙirjina Innalillahi wa inna ilaihi raji'una🙆ya ganni fa 😳😳 he saw my babies! MY FREAKING BABIES!!!!🫢

Kunnuwa na suka ɗau zafi da sauri na koma na zauna inda na tashi bayan na jawo hijabina na saka...meye wannan? naji na takura shima bai sake kallon sashen da nake ba...ko meya ke tunani a ranshi? Ko in tambaye shi? Hakan yayi..har na buɗe baki zan tambayi me yake tunani aka turo ƙofa..likitar ce ta dawo riƙe da wata paper a hannunta...

Miƙa mashi tayi tay mashi bayani ya gyaɗa kai...kallona tayi tace ''.ki kiyaye abinda na faɗa maki kinji...''

''.ina canjawa fa!" Na kare kaina ganin yana tsaye a wurin...fita yayi daga ɗakin bayan na faɗi haka,da alamun pink a fuskar shi sai kunyata kaina nake a gaban shi...

Tare da likitar muka fito lokacin yana inda ake sayarda maguna...ina ganin yanda yan matan dake wurin suke binshi da kallo kamar zasu haɗiye shi...zuciyata tayi baƙi ji nayi likitar na dariya na kalle ta tace '' i can smell your jealousy....''

Ƙasa nayi da kaina ''..b..ba kish....''

'' kwantar da hankalin ki...a wannan shekarun naki it's normal to feel attracted to a guy or even have a crush...kada ki bari hakan ya dame ki!..'' gyaɗa kaina nayi an gano ni...

likitar ta cigaba da magana akan soyayya yanda a shekaruna it's totally normal..ban tabbatar ba idan ma ina jin abinda take faɗa idona na kan yan matan dake magana akan Roman suna dariya...sai dana kusa cin karo dashi na dawo hayyacina.. likitar ta sake yin dariya...nikam a raina addu'a nake kada tayi maganar da zata sani a kunya...


sallama likitar tayi ma Roman sannan muka fita daga asibitin...waje da hadari harabar asibitin babu mutane da yawa. parking lot muka isa yana gaba ina biye dashi,na ɗauka ya buɗe min in shiga kamar yanda Khalil yake ko yanda ake a TV naga ya shige ya zauna ya rufe ƙofar nayi tsaye a wurin...ƙasa yayi da glass ɗin '' ba zaki shigo ba?" 

'' ai na ɗauka buɗe min ƙofar zakayi sai naga ka shige ka zauna...''.na juya idona

'' hannun ki sun dena aiki ashe...'' yayi Maganar yana kwashe gashin shi...'' kai dai ba gentle Man bane...'' na furta dajin haushi har lokacin ina tsaye gashi an fara yayyafi

'' dama na taɓa cewa ni gentle Man ne? zamu tafi mu barki fa!'' ya faɗa da seriousness ɗin daya sa naji kamar inyi kuka ido cike da hawaye nace

 '' to ku tafi ɗin baza'a shiga motar ba!" Na juya na fara tafiya ina share hawaye... Hmph! Idan ba ƙaddara ba,ai da ko kallo bai isheni ba...


Taɓe baki Roman yayi ya jinginar da bayanshi da kujerar yayo gaba in a lazy manner...yace ma Leonardo dake zaune a gaba '' Guida (tuƙa)" hesitantly Leonardo ya juyo yace ''E la signora?(yarinyar fa)"

Lazily Roman yace " ( Lei conosce la strada)tasan hanya" 

Leonardo ya ƙara faɗin ''Ma sta piovendo... e lei non sta bene(amma ruwa ake..kuma bata jin daɗi...) Kallon da Roman yayi mashi yasa ya kama bakinshi ya tada motar suka bar wurin


Har suka wuce Abeedah along the way...

ban damu ba na cigaba da tafiya a ƙasa ai bayaune ranar farko dana ke tafiya ƙasa ba ko?

duk da dai naso in shiga motar ko dan saboda ruwan da ake yi...sannan banda lafiya sosai...Hawayen da suka silalo na share duk da har sun haɗe da yayyafin daya sauka a Fuskata...nayi nisa naji ƙafafuna sun fara ciwo har zan samu wuri in zauna sai kuma ruwan saman suka ƙara ƙarfi..kuma babu inda zan iya fakewa...

Wasu maza da yawa na wuce a ƙarƙashin wata rumfa...daga ganin su kasan mutanen kawai ne...zuciya ta tashiga bugu da ƙarfi... addu'a na fara sai na ƙara saurin tafiya ta duk da yanda nake jina...

Koda xan juya nagansu bayana...zaro ido nayi kafin na fara tafiya tafiya gudu gudu..suma suka ƙara saurinsu...ruwan ma kamar ana kwararo su..kayana sun jiƙe har ina tsiyaya

'' yan mata ji mana...'' daga jin wannan na kwasa da gudu namanta da ciwon da nake ji gaba ɗaya suma suka dafa min baya. oh ni Abeedahtuwo meyasa koda yaushe irin waya'nnan mutanen suke biye dani ?

gabana biyu suka sha sauran huɗun a bayana kafin suka zagaye ni na shiga uku ni Abeedatuwoooo...ja baya na farayi naji bayana ya haɗu da ɗaya daga cikinsu


'' subhanallahi!!!!" Na faɗa da ƙarfi

'' kin ɓata mana lokaci da kuma ƙarfi!" wani cikinsu ya faɗa...wani yayo gaba ya wasge min hijabi...wani yaja gefen rigata..take ta yage dan dama tun daga SS one nake tare da rigar...


Wanda kamar shine babba cikin su yana faɗin a sani a runfa...na shiga tashin hankali...kada ace dai irin abinda yake faruwa da yan mata nima zai faru dani...ƙanƙame jikina nayi ruwan na dukan mu duka..sai dariyar shaƙiyanci suke min

Wasu biyu daga cikin su ne suka yo gaba suka ɗaga ni sama..ina shilla ƙafafu da ihu amma babu wanda zai jini..basu sauke ni a ko ina ba sai wannan rumfar...

Babban cikinsu ya shigo yana dariya biyun suka fita...miƙewa tsaye nayi ina ja baya idona sun yi ja babu wanda nake tunani a wannan lokacin sai Mama inna sarai ya zasu yi idan wani abu ya same ni? Nima ya zan kalli kaina?


'' oga ayi sauri a bamu ɗanɗano!" daga can waje wani ya faɗa....i

Faɗuwa nayi saman guiwowina hannu haɗe hawaye kamar ruwa'' na roƙe ka dan girman Allah dan Rahamar Allah kada kumin komai.mama ta mutuwa xatayi idan wani abu ya same ni na roƙe ka '' dariya sosai mutumin ya kwashe da ita..kamar hawaye na basa nufin komai


Sai gaban wandon shi daya kama gabana yayi mummunan faɗuwa '' baki ji abinda suke faɗi ba a waje? Kada ki ɓata Hawayen ki...''


Wa'yanda ke waje da suka jiyo roƙona suka saki dariya suma...kamar nice babbar wasa mai ƙayatarwa a wannan lokaci...

Matsoni ya shiga yi tare da yin ƙasa da wandonshi... Innalillahi runtse idona nayi...na daskare wuri ɗaya...

Da ƙarfi ya wazgoni yana ƙoƙarin haɗa jikin mu...wani irin gigitaccen ihu na kurma dayasa shi daɗe kunnen shi tare da sauke min marin daya sa naga taurari....


Ya sake ficiko gaban wandona...a wannan gaɓar ji nayi kamar ruhina yabar gangar jikina duk saboda Mutum ɗaya inama ace ya barni ɗazu dana suma? Ina ma ace bai kaini asibiti ba...


Mutumin dake gabana wani irin wari yake mai sa mutum yaji kamar yayi amai... mutanen dake waje na dena juyo ƙarar su ƙila suna jira suji ihuna

Runtse idona nayi,zafafan hawaye na sauka da gudu kamar ambaliya...

Ina jiran abinda zai biyo baya.naji mutumin ya sake ni tare da kurma ihu... sautin karyewar ƙashi da numfashin takaici biye da ihun shi sai roƙon yake abarshi ayi haƙuri tsoro da kunyar yanayin da nake ciki ya hana ni buɗe idona...


nayi kwance a inda ya sake ni tun ina jiyo ƙarar mutumin har na dena. koma waye yayo inda nake banda shirin kare kaina daga koma meye zai biyo baya...duƙawa yayi ya kwashe ni...ƙamshin turaren shi ya bani damar sanin waye amma ban buɗe ido na ba har muka fita daga runfar ya sauke ni a bayan motar shima ya shigo maƙalewa motar nayi jikina na rawa kamar maxari na shiga shock fiye da zaton mai karatu zuciyata zafi take ... Motar ta fara tafiya amma har lokacin ban dawo hayyacina ba... ƙwaƙwalwata sai ƙara tariyo min inda ya jawo gaban wandona take..

har da ƙarawa da abinda zai biyo ba daga gefen cikina har zuwa saitin awazuna waje yake tsabar yanda suka yage min riga,Allah yasa yar singlet ɗin atleast ta ɗan wuce ƙirjina da kaɗan


'' You o...''

Da wani irin fushin da ban taɓa jiba tsawon rayuwata na juyo na wanke fuskar Roman da mari,har yana da bakin yimin magana bayan abinda yayi min? fuskarshi ta koma gefe bai ɗaura hannun shi a wurin ba bai kalle niba,bai share gashin daya rufe fuskarshi ba,ya cigaba da numfashi da sauri.cikin hargagi da ƙunar rai hawaye masu zafi na sauka daga idona da suka ƙanƙance gray ɗin ya ƙara duhu sosai nace

 '' amma baka da imani baka da zuciya,na ɗauka kawai duk wannan coldness ɗin da kake nunawa bai kai har zuciyarka ba ashe zuciyarka tafi dutse tauri idan ma kana da ita kenan!!ba'a so a zauna cikin motar taka ku sauke ni..ai ina da ƙafafu lafiyayyu! '' na shiga ƙoƙarin buɗe motar..

'' stop the car!" Ya furta da rashin imani tsayarda motar Leonardo yayi,ya zare locket ɗinshi daya leƙo daga aljihuna batareda ya kalli sashena ba 

hakan ba ƙaramin ciwo yayi min ba na fita suka ja motar su suka ƙara gaba nayi tsaye cikin ruwan da daɗewa bayan tafiyarsu,kafin na kawo hannu na saitin zuciya ta,

taya na iya son mutum mara zuciya kamarshi? a da na ɗauka rashin zuciyar shi bai kai har zuci ba ashe nice a duhu bai da zuciya ko kaɗan shiɗin ba kamar Khalil bane ko kusa...

Share Hawayen nayi. bai cancanci in dinga zubar da hawayena saboda shiba.na cigaba da tafiya cikin ruwan babu hijabi babu hula ba takalmi ni kaɗai da yagaggun uniforms masu datti...dawowar da yayi dan abun shine kawai badan niba wurin wani shago nazo wucewa naji wata waƙa na tashi,hakan ya ƙara ma zuciyata wani irin nauyi duk nisan da nayi ina jiyo lyrics ɗin suna bina kamar suna nuna min abinda na kasa fahimta

🎶 Talking with my mother she said where did you find this guy
              I said young ppl fall in love 
With the wrong ppl sometimes 🎶


🎶 Some mistakes get made that's alright, that's okay 
              You can think that you're in love when you're really just in pain 🎶


🎶 Some mistakes get made that's alright that's okay
                In the end it's better for me that's the moral of the story babe..🎶

na rufe kunnuwa na,na ƙara sauri amma saurin bai wadatar ba,kawai sai na fara gudu kamar zautacciya ina kuka, lyrics ɗin kamar anyi printing ɗinsu a zuciya ta 



Sai wurin ƙarfe shida da arba'in na iso gida... lokacin duhu ya fara saukowa...da farko banga kowa a farfajiyar gidan ba... nacigaba da tafiya salin alin

.can sai ga Khalil ya fito riƙe da lema yana tafiya da gaggawa..ko daga nesa ina iya gane shi...ban tsaya ba


Sai da ya juyo sashen da nake ƙafafuna suka kasa cigaba da tafiya kunya da rauni suka fara dabaibaye ni nayi ƙasa da kaina...takun shi ya rage sauri... idonshi akaina lemar ta faɗi daga hannun shi...mu biyun kamar lokaci ya tsaya mana ne...bai bi takan abun da ya faɗi ba...cikin ruwan ya nufo ni,sauri sauri...gudu gudu...rungume kaina nayi cike da kunya...kafin ya ƙaraso ya cire rigarshi ta sama..ya yafa min sanda ya iso duk da naso in zama mai ƙarfi kada inyi kuka ..kada in nuna rauni na.a gaban Khalil...na kasa yin hakan....ƙare min kallo yayi daga sama har ƙasa... utterly speechless '' Abe...ed..ah.. '' ya kira sunan a rarrabe,ido waje

Faɗawa jikinsa nayi hawayen da suka tsaya suka ƙwace,nake kuka fiye da wanda nayi a baya ina ƙara ƙanƙame shi, wrapping hannayensa yayi a baya na, numfashin sa na fita da zafi,idonshi sunyi wani mahaukacin ja yana shafa bayana gently,har ina jiyo yanda zuciyarsa ke bugu da mugun ƙarfi

'' it's okay... I'm here'' ya furta yana kare ni daga ruwan dake zuba da babban jikin shi wannan shine ya kamata ace naso...ba mai zuciyar ƙarfe ba...Khalil..shi na daban ne...sosai..raba jikin mu yayi ya share min hawayen da suka ƙi dena zuba..ya ɗaura hannun shi a kafaɗata muka fara tafiya,babu abunda jikina yake sai rawa


Yan gidan dake zaune a parlor suka bimu da ido ƙara gyara min rigar data zame yayi ɗumin jikinshi na sani a salama ina jiyo maganganun mutanen wurin daga bayan mu ƙasa nayi da kaina...

Sanda muka kawo sashenshi,zaunar dani yayi a ɗakin dana kwanta ranar, ya kunna room heater ya lulluɓe ni da blankets da yawa...ya shiga baye ya haɗa min ruwa masu zafi...nake binshi da kallo yanda ya damu yake up and down saboda ni....

dawowa yayi ya tayani miƙewa tsaye ya rakani har ƙofar bayen... kafin ya juya ya fita daga ɗakin...

Shiga ciki nayi na cire sauran abinda ya rage na daga uniforms ɗina...jiki ba ƙwari na zauna cikin ruwan zafin...haɗe kaina nayi da guiwa ina kuka sosai...meyasa abubuwa marasa kyau suke faruwa dani koda yaushe? Wannan shine karo na huɗu da aka kawomin hari...meyasa bazasu barni insha iska ba?


Wanke jikina nayi na ɗaura towel,sai dana fara leƙowa naga babu kowa a ɗakin sannan na fito duka...naji daɗi da ɗakin yake da ɗumi saboda heater daya kunna...

kaya na gani ajiye saman gado,da alamu kayan Khalil ɗin ne...riga da wando blue masu taushi sai singlet irin ta maza can gefe,idona suka fito da naga Pad da pants bakina ya kasa rufuwa najin kunya sosai,

a gaggauce nasa kayan.na tsaya bakin window, abunda ya kusa faruwa dani na maimatuwa a ƙwaƙwalwa ta,daidai Roman na fitowa daga motarshi da ƙarfi naja labulen na rufe tagar idona suka ɗuri ruwa...ban bari sun zubo ba na matsa baya 

Daidai nan Khalil ya dawo da tiren abinci,ido na ya shiga cikin nashi ..ƙasa nayi da kaina...kunya tasa na kasa motsi...

ajiye abincin yayi saman table ya ƙaraso inda nake da murya mai laushi yace '' xoki ci abinci..'' girgiza kaina nayi hawayen da na ɗauka sun koma suka shiga saukowa da sauri sauri ..

Da muryar kuka nace '' bana jin yunwa...'' lallashina ya fara yi hakan ya ƙara ma kukana ƙarfi...ya rasa yanda zaiyi sai naji ya ban tausayi '' stop crying pls...'' ya riƙe fuskata yana share min hawaye....

Ƙasa nayi da idona ina girgiza kaina...'' da... wani abu ....da Mama...'' 

'' shhh... it's okay...'' zagayo da hannunshi yayi a ƙuguna..na kwantar da kaina a ƙirjinshi...kafin wani lokaci har gaban rigar shi ya jiƙe da hawaye...babu abinda yake sai lallaɓa ni...

Tausayin shi naji yasa na dena kukan mukayi tsaye cikin shiru..bai sake ni ba,Nima ban ja baya ba...na tsawon lokaci kafin ya ɗago ni daga jikinshi ya riƙo hannu na zuwa parlor...da kanshi ya ciyar dani abincin...I was grateful to him...fiye da kalamai zasu bani damar faɗa....


ya zauna tare dani,abinda kaɗai ke tayar dashi sallah..koda nace zan koma sashen mu,yace in kwana a can ɗakin... banga matsala tare da hakan ba yasa na yarda...


Da safe da ƙarfe goma na tashi na same shi zaune a can ƙarshen gadon yana kallona '' Oh kitten...'' ya furta tareda matsowa kusa...


'' akwai inda ke maki ciwo?" na girgiza kaina ina murza idona...'' phew! That was a relief!" 


nayi murmushi.... '' I'm sorry for what happened yesterday,dana ga baki dawo gida ba i should have gone out sooner to look for you,maybe.. maybe '' da sauri na ɗaura hannu na a bakin shi

murya ƙasa nace

 '' You don't have to apologize..abunda ya faru ya riga da ya faru kuma Allah ya taƙaita wahalar so no damage was caused. da ban san yanda zan rayu ba'' cire hannu na yayi daga bakin shi ya matso kusa,hannunsa riƙe da gefen fuskata 

'' I'm so sorry kitten'' 

'' you don't have to be... infact na gode Allah daya sa akwai ka cikin rayuwa ta...kai ɗin na daban ne and I really appreciate you fiye da yanda zan iya bayyanawa..'' a hankali na sauke idona cikin nashi dake kallo da wani irin intensity 

I found myself reciprocating the intensity of his gaze

 '' you mean a lot to me.. you're the best thing that has ever happened to me!" yayi murmushi mai bala'in kyau ya rausayar da kanshi gefe har lokacin yana kallona

'' I'm glad to hear that!" na gyaɗa kaina cike da kunya,sai kuma na sauke idona na kasa cigaba da kallon shi

 

na sauka daga gadon na shige baye ina ..sanda na fito babu shi a ɗakin gyara shimfiɗar nayi na fito zuwa parlor..jikina ba ƙwari sosai... badaɗewa ba ya shigo ɗauke da tray'n abinci ya ajiye a gabana...

Ya ɗauki remote yasa min MSA... Batareda nayi niya ba murmushi ya wanzu a fuskata na zuba abincin a plate da yawa...nasa cokula biyu '' muci tare!" waro ido yayi yace '' ni ai na karya!"

'' kada ka shaƙeni da idonka yasa nake maka Bismillah...'' na ƙanƙantar da idona yayi dariyar ƙirji data bani dariya...ya ɗauki cokalinshi muka fara cin abincin...muna kallo


Can aka turo ƙofar parlor'n... batareda na kalli ƙofar ba Nasan waye...ƙin kallon sashen shi nayi har ya zauna a kujerar dake gaban mu...ya shiga daddanna waya


babu wanda yace mashi komai cikin mu,shima bai ce ma kowa komai ba.. hakan ya baƙanta min rai...ko haƙuri bazai iya bani ba wato...

Share shi nayi na cigaba da kallo '' ahah! Kadai ce zaka kaini nan ko?" Nake nuna mashi Aurora ɗin da cokali...

''ashe baki manta ba...'' 

'' taya zan manta...?"

'' ai masoya kaɗai ke zuwa wurin Kitten...''

'' wai ma,su wa'yannan iyalai ne fa...''

'' it's all the same...''

''.hmph kawai dai baka so ka kaini ne...''

'' be my girlfriend sai in kai ki...'' dariya nayi daya faɗi hakan..ya ɗage gira nace '' ai ina da saurayi...gidan mu har an bada ni...''

Na ajiye cokalin ina fuskantar shi '' Dan Allah?" Ya tambaya kamar wata mace yana buɗe min manyan idonshi...hakan ba ƙaramin dariya ya bani ba...'' eh mana...''

'' wayyo zuciya ta!" Yayi baya da kanshi yana dafe ƙirji...ya dena ƙifta idonshi kamar irin mutum ya mutu ɗin nan


'' wayyo ABRAHAM ɗina...'' sai ya tashi zaune muna dariya tare..sosai yake ƙara kyau idan yayi dariya ko murmushi...



gani mukayi Romo ya miƙe ya fice..ni harna manta dashi duka. ..'' oh ina zuwa..''

Khalil yabi bayan Romo..na ɗage kafaɗuna...bayan abinda yayi min na dena sonshi...

    🌹 ❤️📖✨



***

RU'UYAA…📖



₦500 ne idan ya kammala zai koma 800

Biya ta wannan account ɗin 9138091955..Salma Aliyu opay

Shaidar biya ta ***

Autumn writes 📖🖋️