BOOK ONE CHAPTER 13
A gaban ta yai tsaye yana kallon ta ta cikin glass din dake sanye a idanunsa.
"Lafiya...? Meke damunki?!"
Idanun Zainab ta waro cike da mamaki. Tana kallon mutumin dake tsaye sanye da manyan kaya na alfarma.
Kai ta girgiza alamar ba komai. Zuciyar ta na umartan tan data juya tai tafiyar ta, kada ta buɗe cikin ta ga kuwwa, rayuwar yanzu mugayen mutane sunyi yawa.
"Kinga ki saki jikin ki ki gayamin menene? In wani abu kike buƙata ki gayamin kada kiji nauyi na, wurin nan mallaki Na ne."
Ƙwalla ne suka ciko idanuwanta, tai saurin shaye su da furta"aiki nake buƙata."
Mamaki ne ya kwanta akan fuskar mutumin, se kuma ya kawar da murmushi kadan mai laushi a gareta.
"Zo muje ciki mui magana."
Ba musu ta bishi. Suka shiga cikin restaurant din har office ɗin shi. Zama sukayi.
Alh.Haruna ya bude fridge ya ɗauko ruwan, ya bude ya zuba mata a glass cup ya miƙa mata.
Zainab tai godiya ta amsa.
Ya ɗauki waya yai dialing wata number ya soma magana akan ko sunada vacant.
Bayan ya sauke wayar, ya kalli Zainab dake zaune duk a takure, kanta a ƙasa ya soma magana.
"Zaki soma aiki gobe acikin daya daga cikin masu kai abinci, tun karfe 7:00am se karfe 4:00pm. Dubu ashirin a wata."
Wasu siraran hawaye ne suka sauko saman fuskar ta, ta silale ƙasa akan guiwoyinta ta nai masa godiya.
Alh.Haruna ya kura mata idanunshi, wani irin abu mai nauyi na danne zuciyar sa akanta.
"Dan Allah zan iya samun wani kaso na albashi na....akwai uzurin da nake sonyi dashi...."
Ta jaddada maganar ta na farko ganin kallon da take mata.
"Ba zaki sami wani kaso na albashin kiba saboda dokan wurin nanne a haka, albashin ma'aikaci adunkule ake basa aƙarken wata, amma zaki iya samun wannan."
Ya ƙarke yana bude drawer din dake gaban table din shi, ya ɗauko wasu kudade ya miƙa mata.
Hannu ta sanya ta ta karɓa idanuwanta na bayyanar da tambayar ta agaresa.
"Kyauta ne na baki."
Wasu siraran hawaye ne suka sauko saman fuskar ta, ta bude baki kalaman dake cikin kanta na suɓucewa, imbanda ƙyallin godiyar Alh.Haruna ba abinda yake haskawa acikin ƙwayannin idanuwan ta.
"Kinga base kince komai ba."
"I don't know what I'm saying.... thank you so....Ya rabh! Na gode matuƙa. My God bless you...!"
Haka ta dingi godiya hawaye na saukar mata. Bayan ta fito ta tsaya awani shop tai musu siyayyan kayan abinci, daga cikin dubu goman da aka bata ta rage dubu biyu ta ajiye a hannun ta.
Gida ta nufa. A inda ta barsu anan ta samesu. Khadijah ta buɗe baki daƙyar tai mata sanda zuwa.
Ramlat ta ɗago jajayen idanunta daƙyar ta kalleta, ba tare da tace komai ba.
"Sannu da dawowa. Amma ina kika je?"
Khalid yai mata sanda zuwa, tare da tambaya lokaci guda.
Da murmushin jin dadi akan fuskar ta, tazare hijjab ɗin jikinta ta soma bashi labari.
Shiru kawai yayi. Yabi bayan ta zuwa kitchen suka girka spaghetti jellop ɗin da yaji albasa.
Bayan sun gama suka hadu suduka suka cii, se alokacin Ramlat ta samu bakin tsokanan Anis mai kukan yunwa.
Washe gari suka shirya suka tafi makaranta. Ita kuma ta wuce wurin aiki. A ranar ne aka bata t-shirt green color da p-carp na wurin wanda aka tanaza domin ma aikata.
*USTAZ RAYYAN*
Tun lokacin da ya baro gidan Baba Ishaq zuciyarsa ta ƙi samun nutsuwa.
Yana tuka babur ɗinsa a hankali, amma hankalinsa ba ya kan hanyar da yake bi.
Hoton ƙaramar jaririyar da ya bari a gidan yana ta dawowa masa a zuciya.
Yadda ta kalle shi.
Yadda ta riƙe hannunsa, cikin nata ƙaramin hannun.
Da kuma yadda ta yi masa dariyan jarirai da har yanzu take yawo a cikin kansa.
Ya sauke numfashi mai nauyi.
Akwai wasu abubuwan da mutum kan so ya manta da su...
amma wasu abubuwan ba sa barin mutum ya manta da su.
Lokacin da ya iso gida, ya kashe injin babur ɗin ya zauna na ɗan lokaci bai sauka ba.
Idanunsa suka sauka kan ƙofar falon su. Ya san Aliya tana ciki.
Ya kuma san da zarar ya shiga, za ta gane cewa wani abu ya faru.
Ba don yana son ya gaya mata ba. Sai don bai iya ɓoye abin da ke zuciyarsa yanzu kamar yadda ya saba abaya.
A ƙarshe ya sauka. Ya shiga gida falon da sallama.
Aliya tana zaune tana jera abincin data kammala a dining.
Da ta ji sallamarsa, ta ɗago kai. Tana amsa sallamar da murmushi akan fuskarta.
"Wa alaikumussalam."
Idanuwanta na sauka akan fuskar sa, murmushin dake kan nata fuskar ya gushe.
Ya amsa sallaman a hankali, ya wuce ya zauna a gefen kujera.
Aliya ta bishi da kallo.
Ta lura da yadda ya jingina bayansa da kujera, sannan ya ɗora hannunsa kan goshinsa.
Ba shi da kuzarin magana. Ba shi da kuzarin tambayar komai. Hatta fara'ar da kwana biyu take gani akan fuskar sa, babu shi yanzu.
Kamar akwai wani abu da ya ɗaure masa zuciya.
Ta ajiye abin da ke hannunta. Cikin natsuwa ta tako zuwa falon ta zauna a gefen sa tana kiran sunansa da tattausan muryanta mai kamada raɗa, wacce babu hayaniya ko kaɗan acikin ta.
"Ustaz..."
Ya ɗago kai.
"Na'am?"
"Me ya faru?"
Ya ɗan yi murmushi.
"Ba komai."
Aliya ta kalleshi na ƴan daƙiƙu.
"Ka ce ba komai, amma fuskarka tana cewa akwai komai."
Rayyan ya ɗan sauke idanunsa.
"Aliya..."
"Na'am."
"Ki bar maganar."
Ta yi shiru. Ba don ta yarda ba. Sai don ta fahimci cewa akwai wani abu da yake ƙoƙarin ɓoyewa.
Ta matsa kusa da shi kaɗan.
"Idan ba ka son ka gaya min, ba zan tilasta maka ba."
Ta ɗan tsaya. Kamar tana ba kalaman ta daman zama akansa kafin ta ɗora da
"Amma idan abin yana damunka, ka sani ba sai ka ɗauke shi kai kaɗai ba."
Kalaman suka tsaya a cikin zuciyarsa. Ya ɗago ya kalleta.
A karo na farko tun da ya dawo, idanunsa suka nuna abin da yake ƙoƙarin ɓoyewa.
"Na je wajen Ummina."
Aliya ta yi shiru. Ta jira ya ci gaba.
"Na je ganin yarinyata."
Murmushin da ke fuskarta ya ragu.
"Ta na lafiya?"
Rayyan ya gyada kai. Sai ya yi shiru na ƴan daƙiƙu kamar ba zai sake cewa wani abu ba. Sautin muryanshi ya sake bayyana.
"Amma..."
Kalmar ta fito daga can wani wuri mai nisa azuciyarsa.
"Amma me?"
Ya haɗiye yawu.
"Yadda ta lalle ni..."
Ya tsaya.
Idanunsa suka kauce daga nata.
"Ban san dalilin da yasa abin ya taɓa ni haka ba."
Aliya ta yi shiru tana kallonsa.
"Na dade ina ƙoƙarin ganin cewa duk abin da ya faru ya wuce."
Ya yi murmushi mai raɗaɗi.
"Amma da na ganta yau... sai na ji kamar akwai wani ɓangare na rayuwata da na bar shi a can."
Aliya ta sauke numfashi.
Ba ta tambaye shi abin da ya faru tsakaninsa da kuwwa ba agidan. Ba ta buɗe tsohon ciwo ba.
Sai dai ta ɗan matsa kusa da shi. Ta kira sunan sa can ƙasan throat.
"Ustaz..."
Ya kalleta.
"Ba laifi ba ne ka ji haka."
Ya yi shiru.
"Ɗiyarka ce."
Ta faɗa a hankali.
"Ko da akwai abubuwan da suka faru tsakanin ka da mahaifiyar ta, da sauran mutane, hakan ba zai canza cewa ita ɗiyarka ba ce."
Rayyan ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci.
"Na sani."
"To me yasa kake hukunta kanka?"
Ya buɗe idanunsa.
Aliya ta yi murmushi mai taushi.
"Ka je ka ga ɗiyarka ne. Ka yi abin da uba ya kamata ya yi."
Ya kalle ta.
"Amma har yanzu zuciyata tana min nauyi."
"To ka bar ta ta yi nauyi na ɗan lokaci."
Ya ɗaga gira.
"Me?"
Ta yi murmushi.
"Zuciya ce fa, tana dauke da abubbuwa da dama, masu tarin yawa."
Sai ya kalleta kamar yana ƙoƙarin fahimtar inda take son kaiwa.
Aliya ta ƙara cewa"Idan zuciyarka ta yi nauyi, ka zauna. Ka huta. Ka sha ruwa."
Ta ɗan kalle shi daga gefe.
"Idan kuma har yanzu bata sauka ba..."
Ta ɗaga hannunta tana nuna kirjinsa.
"...ka bani rabin nauyin."
Rayyan ya zuba mata ido.
"Ki ɗauki rabin?"
"Eh."
"Ta yaya?"
Ta ɗan yi shiru alamar tinani. Daƙiƙa ɗaya...biyu...uku sai ta kallesa cikin idanu ta furta
"Mu cigaba da zama a haka...nauyin zai sauka a zuciyata."