SCARS BENEATH HER STRENGTH
by @saddiqahhh
One thing data arowa kanta shine jarumtar da bata da ita da hakan yasa ta mugun hana kanta kuka duk kuwa da shi take son yi. Har yanzu tana nan dai a mai kukan nan da alama wannan wani hali ne da ba zata taba iya denawa ba sai dai ba zaka taba ganin tayi kuka agaban mutane ba idan kuwa acikin mutane ne tana mugun daurewa kar tayi saboda sabon halin da tayi developing na rashin son raini.
"Afif..." She called his name in a voice so fragile that he was the only one who could hear the pain she was trying to hide.
Shima adaya bangaren sosai take karyashi idan tana magana da kalar muryar nan "Adda kina so na ajiye karatun na dawo?"
Da sauri ta girgiza masa kai don one thing data sani shine tana cewa eh wallahi babu abinda zai hana ya ajiye karatun duk da ya kusa gamawa. Don ya sha fadar haka itace take hanashi tana tuna masa da burin Abbansu ne wannan yayi karatu.
"Ki denamin magana ahaka Adda don Allāh wallahi yana sani na rasa nutsuwa na..."
"Na dena biyayye am... Ka maida hankali saura wata uku komai zai dawo daidai kawai na qagu ka dawo na gaji da komai... Nagaji da rayuwar gaba daya biyayye..."
"Adda karki je kiyi sabo, jarabawar mu ne ahaka kuma ina ji ajikina yazo qarshe muna phase din qarshe shisa zakiji komai kamar yafi tsanani yanzu..."
"Biyayye shekara biyu ana fadar haka.. nasan Allah yana so yaga haqurinmu ne... I will try In Sha Allah... "
"kunyi waya da Mami? "
Kai ya girgiza mata yana cewa "a'a wannan satin duka wayarta baya shiga..."
Shiru tayi don ita tun last week ma ta dena shiga ko da ta kira hakan yasa tace "kaje kayi karatu bara na mayar mata da wayarta..."
"To Adda don Allah ki kula da kanki kici abinci kuma.." Kai ta gyada masa tana cewa "Fi Amanillah biyayye am..." Da haka suka yi sallama ta qarasa ta a mayarwa da Nabila wayarta sannan ta koma dakinsu.
Bacci ta tarar ya dauke Inna sai ta qarasa ta dauki awaran da ba taci ba ta cinye tass ta kora da ruwa. Bin dakin tayi da kallo tana tuna rayuwar da suka yi a KANO right from lokacin da ta fara wayo ta taso tare da Abbanta da Mami har zuwa lokacin da komai ya sauya. Ta kalli Inna dake baccin wahala lokaci daya tana jin qiyayyar da take mata kamar yana qaruwa ne with each passing days. Ba iya rabata da Mami tayi ba, ta rabata da Karatunta hatta da garin da ta taso aciki ta rabata dashi.
Suna KADUNA yanzu a Mando! Shegen son kudin Inna ya saka ta jawowa kanta masifar da dole ta bar Kano ba tare da sun shirya ba.
Ture tunanin tayi ta miqe ta gyara wurin da take ta kwanta bayan tayi addu'a sai dai bacci yaqi zuwar mata kamar dai ko yaushe.. acikin two years din nan bata iya wani baccin arziqi ta dade tana bacci shine tayi three hours ko bai qarasa ba and the thing is gradually affecting her brain.
Ta tuna first abinda ya fara taba Inna bayan ta rabata da Mami shine yaudararta da Rabe yayi ya gudu da gaba daya kudin da Alhj Labaran ya basu and she can't help but smile. Har yau idan ta tuna abin nan sai tayi dariya ko tayi murmushi, blame the Fulani blood in her.
Kallon Inna ta juya tayi har sannan da murmushi kan fuskarta bawai abin yaci ayi masa dariya bane kawai the fact that ba taci kudin siyar mata da Mami ba yafi komai yi mata dadi, duk kalar burin da Inna taci kan kudin nan ko biyar bata samu ba Rabe ya gudu dashi.
Dauke kanta tayi tana dena murmushin lokaci daya bayan tunaninta yana son kaita wajen Mami da har yau, shekara biyu bata qara saka Mami a idonta ba.
Abu taji ya tokare mata wuyanta wanda ya saka take jin zuciyarta nayi mata wani kalar zafi da ta tabbatar zafin rashin Mami ne. Ta dauka auren kawai Inna tayiwa Mami ashe rabata tayi da ita gaba daya.
Miqewa zaune tayi da sauri bayan taji tunaninta yana shirin kai ta ranar data fara zuwa gidan da Mami take, kalar cin mutuncin data fuskanta awajen mai gidan.... Da sauri ta miqa hannu ta dauki Qur'ani ta bude ta fara karantawa.
Acikin this though two years shi kadai ne abinda take karantawa taji sanyi aranta, shi kadai ne abinda idan tana yi take samun comfort har taji kamar bata da damuwar komai aranta. Hakan yasa the rate at which take karanta Qur'ani ya mugun ninka yadda take karantawa da sanda suna cikin kwanciyar hankali and it was like wannan shine abinda yayi maintaining mata zuciyarta bata buga ba with all the calamities. Bata ajiye Qur'anin ba har sai wajen qarfe biyu da taji bacci yana shirin fizgarta sannan ta miqe da sauri ta fita ta sake sabuwar alwala ta dawo ta tayar da nafila tayi guda biyu ganin ta kawo lokacin ido biyu gwara ta kai kukanta wajen Allah a irin wannan lokacin da yake rabon gafara yake kuma amsa daga bayinsa da suke hana kansu bacci.
Da yake dagaske baccin yazo mata yanzu tana idar da sallar ya dauketa anan inda take ko tashi ba tayi ba sai bayan da aka idar da sallar asuba daga masallaci ta farka.
Dan yamutse fuskarta tayi jin jikinta yayi tsamin yadda ta kwanta don ko juyawa ba tayi ba haka ta miqe ta fita ta dauro alwala ta dawo ta tayar da sallar raka'atanul fajr raka'a biyu masu tarin falala.
Bayan ta idar da sallar ne ta matsa wajen Inna ta taba jikinta jin normal yasa ta fara tashinta salla. Da kyar ta miqe taje ta dauro alwala ta dawo tayi nata sallar. Har ta idar Nuri kallonta kawai take irin kece kika rabani da farin cikina.
Irin wannan kallon tun Inna bata saba dashi ba har tazo ta saba kuma sosai yake qarawa Inna guiltiness din da take ji especially yanzu da ya kasance Nuri ke kula da dawainiyarta. Dan kusan ma duk kudin da Nuri take samu kan Innan yake qarewa itace yau lafiya gobe babu ga Innan har yanzu da shegen taurin Kai idan sunje asibiti bata yadda ayi mata wani gwajin arziqi za tace taji sauqi.
"Ina kwana.." da muryarta da ta tsufa da wahala suka canza ta amsawa Nuri dake kallonta
"Ya cikin ya dena?"
Kai ta gyada mata tana cewa "eh da sauqi yau Alhamdulillah.." haka kawai Innan tana jin ita dai haihuwa banda Abdullahi ba tayi mata rana ba. Bayan Rabe daya cuci Inna zakiya wadda kebin Abba ce ta biyu data jefasu a wannan halin rayuwar da suke ciki. Ba'a dade da auren Mami ba ta dawo da sauyin hali kamar ta shiryu ashe da sabon salo ta dawowa ta kwashe takardun gidan taje ta siyar suna cikin zamansu aka zo aka koresu shine silar shigarsu wani hali. Wato duk abinda kayiwa wani kaima za'ayi maka. Ta kori su Nuri daga nasu gidan ita 'yar cikinta ce ma ta koresu, duk da ba ita ta koresu ba amman itace silar barin gidan.. Sai kuma Salama da take aure a Lagos wadda ke shan wahalar gidan miji tace zata kashe auren ta dawo Inna tace tayi zamanta ahaka ta qara haquri.
Miqewa Nuri tayi taje ta dauki wata roba da take jiqa hypo da Omo ta fita waje taja ruwa a rijiya ta shiga bandakinsu ta wankeshi tas don ta saba duk sanda za tayi amfani dashi haka take saboda sam bata jin zata iya shigarsa a yadda yake. Wanka tayi da safiyar nan da ruwan rijiyar da yake da dumi sannan ta fito ta dawo ta shirya abinta duk da sai goma zata fita amman ta fiso take shiryawa da wuri ba sai zata fita ba sannan kowa yana shirin fita.
Zaman jiran qarfe tara ta zauna yi tana yi ta miqe ta zira hijab dinta ta fita taje wani shagon da Afif yake turawa mai shagon kudi ta ciro kudin da yace ya turo mata jiya. Ahanya ta tsayaa ta sai musu kosai da fanke kamin ta qarasa, Inna ta bawa ita kuma ta juya da sauri ta fita ganin kamar ta sake masu gidan kuma ba wai Allah ya basu mutunci bane. Don ma itama akaran kanta yanzu ba mutuncin ne da ita ba shi yasa.
Napep ta tare ta hau ya kaita Kabala qofar wani gida da kana gani kasan yes masu shi suna da kudi ta sauka ta sallami mai napep ta shiga gidan.
Wani kalar tsaki taja ganin motar mai gidan a fake alamar bai fita ba kenan. Ciki ta shiga fuskar nan nata babu wani annuri akai. Babu kowa kamar yadda tasan ba zata tarar da kowa ba. Da sauri ta fara da share qaton parlourn gidan tayi mopping dinsa tas ya dawo yana qyali sannan ta qarasa ta share sauran parts din gidan. Duk wannan uban aikin da take musu 8 thousand kawai suke bata amman asalin yadda mutumin yake biya ba haka bane, matsalar daga matar gidan ne da take danne mata haqqi ba tare da Nuri ta fahimta ba don maybe da tuni ta bar aikin. Kawai dai aikin ma kansa wahalar samu yake shima ta wani fannin so koda ta sani zata iya haqura.
Sai da tazo wanke wanke ne ta sha takaici, ta rasa wacce irin mata ce matar gidan da qananan abu ma idan tayi amfani dasu ba zata iya wankewa alokacin ba. Wannan ba damuwarta bane haka ta wanke su tas sannan ta fita ta shiga dakin yaran gidan ta kimtsa musu shi. Tayi zamanta anan don tana jiran su dawo tayi musu girki ne sannan ta koma gida.
Bin dakin da kallo tayi da yake nan abin shawa sosai musamman da ya kasance a gyare yake ta kimtsa shi. Tana zaune tana tunani taji an shigo dakin da sauri ta daga kanta ta sauke kan mai gidan.
Wani sake hade rai tayi tana kallon cikin idonsa ganin yana shirin shigowa dakin yasa ta miqe tsaye da kyau tana kallonsa
"Nuriyya ki fito kiyi breakfast.."
Tana kallon cikin idonsa ta girgiza masa kai tana cewa "a qoshe nake ban buqata.." ganin zai shigo dakin yasa tayi saurin sake cewa "Yallabai kasan dai madam dinka tana nan ko..."
Kai ya gyada mata yana cewa "na sani Nuriyya, tun ranar da na fada miki abinda yake zuciyata kika barni cikin son jin amsar da zaki bani... "
Tasan maza suna da maita akan mace idan suna sonta to amman bata taba sanin akwai wanda zai fi Khaleel maita ba sai wannan mutumin.
" Amman dai kasan na fada maka an ba dani agidan mu ko?" Har yanzu bata dena fadar haka ba ga duk wanda zai biyo ta da kalmar so. Kalmar da sam bata qaunar jinta saboda tabon data bar mata wawakeke a zuciya.
Ba iya so ba, ta tabbatar maza suna da wani hali daya ne kawai zasu saka mace ta so sune sannan su guje ta aqarshe. Wasu ko sallama ba su iya ba sai dai su gudu su barka da jinya a zuciya......
To be continued.....
like, comment and share🙏