MEERAH

027

by @oumfatima33

*MEERAH*

     *027*


  *Bayan sati biyu.....*


   A cikin sati biyu da suka wuce Ajmal yaje Turkish da wasu ƙasashen, a yanzu maganar buɗe Company ake yi wanda aka kammala komai na cikinsa.

   Ɓangaren Sultan shima ya fara aiki a matsayin C. E. O na A M G groups, yanzu haka maganar tsayar da ranar auren sa ake yi shi da Amani.

   Company Ajmal a Abuja yake domin yaso ya fara buɗewa a Kano Mamy ta hana, hakan ya sa ya haƙura ya fara buɗe wa a Abuja ya bari daga baya sai ya buɗe a Kano. Domin so yake ya buɗe rassan Companynsa a jahohi da dama da amincewar Ubangiji.


>>>>>>>>>>

   Yau ta kama saura kwana biyu tafiyar mu Abuja wurin bikin buɗe sabon Company Ya Ajmal wanda tun da ya saka ƙafa ya tafi bai samu damar dawo wa Kano ba, saboda ayyukan da suka yi masa yawa.

   Gaba ɗaya gidan zamu tafi don haka kowa a gidanmu cike yake da murna da farin cikin wannan gagarumar nasara da Ya Ajmal ɗin ya cimma wa, musanman ma Ya Sultan wanda yafi kowa kusanci da Ya Ajmal a gidanmu.

   A ɓangaren Momy ma irin farin cikin da take nuna wa babu wanda zai ce ba ita ce ta haifi Ajmal ɗin ba, domin kuwa yanda take farin ciki ko Mamy da ta haife sa iya abinda zata yi kensn. Sosai take shirya abubuwa da za'a tafi da su don haka ta yi busy sosai.

   A ɓangare na ni kam ban wani zafafa ba, abinda kawai na sani shine na taya sa murna a matsayi na na ƴar'uwarsa. Sai kuma murnar zuwa Abuja da nake yi, don na jima ban yi tafiya ba.

_________


   Yau Nawaz ya amince zai zo gidanmu, don tun bayan dawowar su Ya Sultan bai zo ba ina ta yi masa ƙorafi a kan ƙin zuwan nasa, amma kullum sai dai ya ya bani uzuri kan cewa wani abu ne ya hana shi zuwan.

   Yau da kansa ya sanar min zai zo don haka nake cikin farin ciki sosai, da yamma yace zai zo don haka tun ƙarfe 4 na yamma na kammala shiryawa na zauna jiransa. Koda Momy ta tambaye ni shirin me nake yi da yanmar nan ce mata na yi.

   "Ya Nawaz ne yace zai zo Momy." Kasancewar yana ɗan zuwa lokaci zuwa lokaci yasa Momy bata damu ba, amma dai duk da haka sai da ta ce min.

  "Kin cika rawar kai Auta, ki dai bi a hankali na faɗa maki."

   "To Momy." Na bata amsa da shi kawai na mayar da hankalina kan wayata da jiran lokacin da zai ƙaraso don na yi matuƙar kewar sa. Ina zaune ina chat aka yi knocking Bintu taje ta buɗe.

   Zeezee ce ta shigo da sallama tana nufo inda nake, miƙewa na yi tsaye cike da farin cikin ganinta na nufi inda take muka rungume juna.

   "I miss you Bestie." Na faɗa cikin farin ciki ina ƙara rungumeta.

   "I miss you too my Bestie." Zeezee ta faɗa ita ma tana rungume ni. Rakata na yi ta gaishe da Momy sannan muka haye sama zuwa bedroom ɗina. Kallo ta gama ƙare min sannan tace.

   "Kina lokaci Bestie, wannan irin kwalliyar fa?." Ta faɗa lokacin da take cire mayafinta ta ajiye a saman gado ta zauna a bakin gadon. Zama na yi a kusa da ita sannan na bata amsa da cewa.

   "Ta tarbar masoyi ce, Ya Nawaz yana hanyar zuwa ya ganni." Na ƙare maganar ina lumshe ido na buɗe.

   "Gaskiya Nawaz Baffa ya ciri tuta da ya samu nasarar kama zuciyar Bestiena. Ina mamakin yanda kike son Nawaz duk da cewa kin fisa matsayi da arziƙi haɗi da kyakkyawar nasaba." Zeezee ta faɗa cike da mamakin da take yi a kan irin soyayyar dake tsakanina da Nawaz.

  Murmushi na yi mata sannan na bata amsa da cewa.

   "Nice naci sa'a da samun masoyi irin Nawaz wanda yake matuƙar so da ƙauna ta, Nawaz yana da qualities ɗin da ko wace Mace zata so shi Bestie. Ni zuciyata bata duba matsayi ko dukiya yayin zaɓen wanda zata so, kawai ina son mutum mai sanyin hali, mai tausayi wanda zai so ni matuƙar so." Dakata wa na yi na sauke ajiyar zuciya sannan naci gaba da cewa.

    "Duka waɗan nan abubuwan da nake nema Nawaz ya haɗa su, to me zai sa ba zan so shi ba Bestie?, kar ki manta irin taimakon da ya yi min a baya, wanda shine silar kasancewata a matsayin cikakkiyar Meerah da nake a halin yanzu." Na ƙare maganar cikin sanyin murya ina tuna abubuwan da Nawaz ya min.

   Ajiyar zuciya Bestie ta sauke zata fara magana kira ya shigo wayata, wanda shine ya dakatar da ita daga faɗar abinda ta yi niyya. Wayar muka kalla nida ita sannan muka kalli juna, a hankali na furta.

   "Kin ga shine yake kira." Na faɗa ina ɗaga kiran, cikin ƙaramar murya nace.

   "Har ka ƙaraso?."

       "Eh na ƙaraso." Nawaz ya faɗa daga can ɓangaren. Zeezee na kalla nace.

   "Bestie ya ƙaraso ki tashi muje mu same shi."

   "Okay muje." Ta faɗa tana miƙe wa haɗi da ɗaukar mayafinta ta yafa. Tashi na yi nima ina gyara mayafin abayar da na saka muka fice. 

   Ɗakin Momy na fara zuwa na same ta ta fito daga bayi nace.

   "Momy Ya Nawaz ɗin ya ƙara so."

   "Okay kije ki shigo da shi." Momy ta faɗa kasancewar duk lokacin da yazo gidan har cikin Palo yake zuwa su gaisa da ita. 

  A compound muka same shi yana tsaye hankalinsa a kan wayarsa yana danna wa, sallama na yi ina tsaya wa ɗan nesa da shi na zuba masa ido. Ɗagowa ya yi ya kalle ni fuskarsa ƙawace da murmushi yace.

   "Ƙaraso mana abar ƙaunar Nawaz." Ya yi maganar cikin daddaɗar muryarsa da take matuƙar birge ni. Murmushi mai yalwa na saki ina saka hannu na rufe fuskata sannan na shiga taka wa a hankali zuwa inda yake, sai da naje dab da shi sannan na tsaya.

  Murmushi mai sauti ya saki yace.

   "To a buɗe min fuskar mana." Buɗe fuskar na yi ina sunkuyar da kai cike da jin kunyar kallon da yake min nace.

   "Barka da zuwa, da fatan kazo lafiya?." Sai da ya lumshe idanu jin saukar siririyar muryarta a cikin kunnuwansa, a hankali ya buɗe idon ya zube su a saman fuskarta sama mata sassanyan kallo mai cike da soyayyar da yake mata.

   Buɗe baki ya yi a hankali cikin sanyin muryarsa mai daɗi ya bata amsa da cewa.

    "Lafiya lau, Alhamdulillah, ina fatan abar ƙauna ta tana cikin ƙoshin lafiya?." Kunya naji ta kama ni don haka na saka hannu na rufe fuskata sannan na bashi amsa da cewa.

   "Ina lafiya, Momy tace ka shiga ciki."

      "Okay." Ya bani amsa. Gaba na shiga ya bi bayana har zuwa cikin babban living room inda Zeezee ke zaune tana jiran shigowar mu. Wurin zama na nuna masa ya zauna sannan nace.

    "Bari na yi wa Momy magana, ga Bestiena nan ku gaisa kafin na dawo."

   "To ranki ya daɗe." Nawaz ya faɗa fuskarsa ɗauke da murmushi haɗi da sara min irin na girmamawa. Murmushin nima na yi sannan na juya na haye sama ina jin wani irin shauƙi na mamaye zuciyata.


****** Nawaz kuwa sai da ta ɓacewa ganinsa sannan ya ɗauke kallonsa daga saman stairs ɗin da ta haura, ya lumshe idanu yana jin yanda soyayyarta mai girma take ɗawainiya da shi.

   'Ya Allah, wai dama haka so yake?.' ya yiwa kansa tambayar a cikin zuciyarsa. Muryar Zeezee dake gaishe sa ce ta dawo da shi daga duniyar shauƙin da ya yi nisa a cikinta.

   Zamansa ya gyara yana saita natsuwarsa sannan ya amsa mata da.

   "Barka dai Bestie ɗin mu, kina lafiya?." Murmushi Zeezee ta yi ta bashi amsa da cewa.

   "Lafiya lau Alhamdulillah, da fatan anzo lafiya?." 

   "Alhamdulillah." Ya bata amsa daga haka gaisuwar ta tsaya ya mayar da hankalinsa kan wayarsa. Yayin da Zeezee ta shiga tunani a cikin zuciyarta.

   'Allah Sarki Yaya Abdul dole za ka yi haƙuri da Bestiena, domin kuwa soyayyar waninka ta riga ta yi mata kamun da zai yi wuya a samu sauran gurbi a zuciyarta.' zancen zucin da Zeezee ke yi kenan tuna wa da yanda Yaya Abdul ɗinta ya mace a soyayyar Meerah.

   Kullum sai ya roƙe ta a kan ta taimaka ta shawo masa kanta, a gaskiya ita kuma tunda Meerah ta nuna mata cewar Yaya Abdul ya yi haƙuri a matsayin Yaya ta ɗauke shi. Sannan ta faɗa mata wanda take s.  

   Ita da kanta ta fahimci irin tsananin soyayyar da suke yi wa juna ita da Nawaz ɗin, hakan yasa bata son matsa mata a kan Yaya Abdul ɗin gudun kar abotarsu ta samu matsala.

  Sallamar Momy da Meerah ita ta katse tunanin da Zeezee ke yi. Nawaz ma ƙara natsuwa ya yi sosai har sai da Momy ta zauna sannan ya tsuguna ƙasa ya shiga gaishe ta cike da girmamawa.

   Amsa masa ta yi da kulawa tamkar yanda ta saba sannan tace.

   "Ka tashi ka zauna mana." Zaman ya yi amma kansa a ƙasa ya kasa ɗago wa ya kalle ta. A da tana ɗaukar hakan da yake yi a matsayin kunya da baƙunta ne suka sa baya iya sake wa sosai da ita.

  Amma bayan maganar da suka yi da Meerah yanzu sai ta fahimci cewa kunya ce irin ta surukuta Nawaz ɗin ke yi mata.

  "Ya su Umman naka?." Momy ta katse shirun da ya ratsa wurin ta hanyar tambayar sa.

  "Suna lafiya sun ce a gaishe ku." Nawaz ya faɗa kansa a ƙasa.

   "Masha Allah, ka gaishe mana da su idan ka koma." Momy ta faɗa, daga haka ta miƙe ta shige ciki. Sai bayan shigewar Momy sannan ya sake muka ci gaba da hira. 

   Kallonsa na yi cike da so da ƙauna nace.

   "Kasha ruwan mana."

      "To ki bani da kan ki." Ya faɗa min yana min wani sassanyan kallo. Tashi na yi na zuba ruwan a cup na miƙa masa, karɓa ya yi fuskarsa ɗauke da murmushi yace.

   "Thank you abar ƙauna." Murmushi kawai na yi masana duƙar da kai ba tare da nace komai ba.

   "Bestie bari na shige daga ciki na jira ki." Zeezee ta faɗa tana miƙe wa ta haye sama. Ganin babu kowa a wurin yasa ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya kaina yana min sassanyan kallo mai cike da soyayya.

   Mun jima muna hira kafin ya miƙe yana kallon agogon hannunsa yace.

   "Bari na wuce masoyiya." Shagwaɓe fuska na yi ina kallonsa nace.

      "Har zaka tafi?." Idanu Nawaz ya lumshe yana jin tamkar ya fasa tafiyar ya zauna ya yi ta kallonta, saboda shagwaɓar tata ba ƙaramin susuta shi ta yi ba. Da ƙyar ya iya buɗe baki yace.

   "Kin ga an kusa kiran magrib shi yasa zan wuce, da zarar kun dawo daga tafiyar zan zo na gan ki ai." Ya faɗa a hankali yana kallona cike da son ya rarrashe ni.

   "Are you sure?." Na faɗa ina kallon sa. Hannayensa ya harɗe a ƙirjinsa sannan ya bani amsa da cewa.

   "Yes, I'm very sure."

   "Okay tam muje na raka ka." Na faɗa ina nuna masa hanya, jera wa muka yi muka yana yi min magana a hankali ina sakin murmushi.

   Sai da na raka sa har bakin gate sannan muka tsaya ya zuba min ido yana kallona, shagwaɓa nake yi masa a kan ya fa cika alƙawari.

    "In sha Allah zan cika alƙawari." Nawaz ya faɗa, hannu ya ɗaga min yana ƙoƙarin juyawa aka yi a ƙofa mi gadi ya buɗe.......



  *Oum Fatima*